Showing 45001 words to 48000 words out of 90573 words

Chapter 16 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8081

Lubaynah is outside like she is not feeling well."

Tsaki ya saki lokaci guda zuciyarsa ta ɓaci. Ya rasa yadda zai yi da ita ta fita cikin rayuwarsa,
domin ta zame masa ƙarfen kafa.

Agogo ya kalla ƙarfe bakwai da rabi."Don't open the get for her."

"Ok sir." Ya ce tare da juyawa ya koma yana mamakin rashin zuciya irin nata.

Zuwanta ya canza mood ɗinsa har ya kasa aikin da yake yi. Kashe laptop ɗinsa ya yi sannan ya
koma ya zauna, bayan ya janyo sigari ya kunna. Miƙewa ya yi zuwa cikin ɗakinsa ya kwanta.

Lubaynah tana gurin har zuwa sallar Isha. Saboda karya ganta a gida ya yi sallarsa ya kwanta.
Ganin ya ƙi fitowa sai ta nufi gidan Kalim.

Kalim yana zaune a cikin falonsa yana kallo shi da Nadiya da ta zo masa kwana biyu.
Mai-gadinsa Dupe ya knoking ya shigo.

"Sir a lady is looking for you outside."

Kallon juna suka yi shi da ita. Ranta ne ya ɓace amma ba ta ce masa komai ba, ganin haka ya
ce,"Ok"Sannan ya miƙe ya ce,"Please, ina zuwa I don't have any appointment with another lady
but lemme see her."

Ba ta ce masa komai ba, ganin haka sai ya sanya doguwar riga ya fita. Ganin Lubaynah da tana
ganinsa sai ta fashe da kuka.

"Lubaynah lafiya?" Ya furta tare da ƙarasawa gurinta ganin yadda take kyarmar sanyi.

"Mai na yi wa abokinka wanda ya zaɓi ya wulakanta rayuwata, ko soyayya yana zama laifi ne?"
Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka.

"Is ok Lubaynah let's go to his house, I will talk to him." Ya ce tare da fara tafiya zuwa gidansa.

Kasancewar babu nisa suka isa. Layinsa ya kira, sannan ya sanar masa yana ƙofar gida."Are
you with Lubaynah?"

"Please Captain open the get we need to talk." Ya ce nasarar da kashe wayar ba tare da ya
amsa masa ba.

Solo ya kira ya sanar mishi da ya buɗe get ɗin. Lubaynah na shiga falon ta saki kuka sosai tare
da zuwa za ta rungume shi. Da sauri ya janye jikinsa yana watsa mata mugun kallon daya

sanya jikinta sanyi sosai.

"Captain Aliyu, Lubaynah ba ta cancanci haka a gurinka ba. Please settle with her, the girl
deserve your love."

"I already broke up and a told her am done into this toxic relationship. Kalim, mahaifina ya yi
matuƙar yarda da ni sosai, haka family ɗina suna mini kallon mutumin kirki, na zama kura da
fatar akuya. I need to change tun kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada. Duk ranar da mahaifina ya
gane abin da na ke yi ba zai yi sausauci a gare ni ba, sannan zan rushe duk yardar da ke
tsakaninmu."

"Then ka aure ta tana sonka kai kaɗai take kulawa."

"No, it is absolutely impossible!" Ya furta babu kunya.

Jin abin da ya ce sautin kukanta ya ƙaru.

"You know what? Lemme leave you with her, please reconcile." Ya ce tare da ficewa.

Yana fita ta miƙe ta kama hannunsa da yake shirin shigewa bedroom. "Aliyu don Allah ka so ni
ka tura iyayenka, domin mahaifina ya tsaurara mini dokar hana ni zuwa Abuja, sannan ya ce in
har sona da gaske kake yi ka turo iyayenki."

"Lubaynah am so sorry da na yi disvirgin ɗinki, but I can marry you. Go look for another man
and marry. Na yi miki alƙawarin duk abin da kike so zan baki. Ki faɗa mini ko nawa zan baki
matuƙar za ki fita daga rayuwata."

"I don't need your money. My dad has money on him. Zuciyata kai take muradi so na ke yi na
mallake ka a matsayin mijina. Ina sonka don Allah ka aure ni. Na yi maka alƙawarin kasancewa
duk yadda kake son matarka ta zama." Ta ƙarashe maganar tare da durƙusawa ta dafa
ƙafafunsa.
Rintse idanunsa ya yi cikin damuwa. Zuciyarsa take son tausaya mata, amma ba ya amince ya
aure ta ba, domin ya san ko da ya yi hakan, ba za su taɓa samun zama lafiya a rayuwar auren
su ba. Don haka zai lallaɓe ya shawo kanta ya bata kuɗi sosai ta fita daga rayuwarsa.

Kamata ya yi ya miƙar da ita ganin haka sai ta faɗa jikinsa. Da sauri ya janye ta daga jikinsa, ya
yi da zafin jikinta ya sanya shi jin wani iri.

"Is ok stop crying we will talk later. Yanzu kina buƙatar kici abinci ki samu lafiya."

"Sojana ka yi alƙawarin za ka aure ni?" Ta yi masa tambayar tana share hawayenta.

"I will sleep on it." Ya ce mata tare da kama hannunta zuwa bedroom ɗinsa. Kwantar da ita ya yi
kan gadon sannan ya kira doctor ɗinsa don ya duba ta.

Ganin yadda yake tattashinta, sai yaji hankalinta ya ɗan kwanta tamkar ta yi baƙo ya mutu. A
ranta tana addu'ar Allah ya sanya ya amince ya aure ta.

Bai daɗe da kira likitan ba ya ƙaraso. Ganin yadda jikinta ya yi har ɗakinsa ya shiga ya yi
treatment ɗinta. Bayan ya yi mata allura ya ɗaura mata drip, sannan ya yi masa sallama ya tafi
kan cewar Aliyu zai cire mata.

Tana kwance a kan gadon tana bacci idanunta rufe. Tea ya ba ta da ƙyar tasha sannan ta samu
bacci. Kallon kyakyawar fuskarta ya yi da baccin da take yi ya ƙara mata kyau. Ramar da ta yi
sai ta ba shi tausayi.

Yana son ya tursasa zuciyarsa ya aure ta, in ya so sai ya auri zaɓinsa daga baya, amma duk
lokacin da ya yi ƙoƙarin haka, zuciyarta gargaɗinsa take yi. So yake ta fahimce shi domin yana
fatan ya daina ƙaxamiyar rayuwar da take yi, musamman daya san cewa Kama tudini tudanu.
Wato duk abin da ka yi kai ma sai an yi maka.
A ranar bai yi bacci ba domin kwana ya yi yana jinya. Sosai zazzaɓin ya kamata. Sai zuwa
asuba ta samu bacci. Ganin haka sai ya koma falo ya ɗauki Laptop ɗinsa yana aiki, daga baya
bacci ya kwashe shi.

Lubaynah ta yi tunanin zai hau gadon su kwanta, musamman da zazzaɓin ya tashi sai da ya
rage mata kaya ya shafa mata ruwan sanyi, amma sam jikinta da in ya gani ba ya iya ɗauke
idanunsa, sai ta ga bai kwanta a kusa da ita ba don ya shiga jikinta ya rage zafi.

"Hakan na nufin za mu yi istibira'i mu yi aure ne?" Ta yi wa kanta tambayar tana fatan ya
kasance hakan.

Da safe sai ta tashi babu zazzaɓi sai dai rashin ƙarfin jiki. Ya shigo bayan ya yi sallah ya dawo.

"Good morning baby?" Ya ce mishi tana ƙoƙarin tashi. Ganin haka ya taimaka mata ta zauna.

"Da fatan kin tashi lafiya ya jiki?"

"Da sauƙi." Ta furta tana miƙa.

Ɗauke kansa ya yi daga gareta, domin daren jiya ba ƙaramin ƙoƙarin ya yi, har ya iya kwanciya
ba a gurinta ba. So take su daina ƙaxamiyar rayuwar da suke yi, su fuskanci gaskiya, domin
gina kyakyakwar rayuwar da za su yi alfahari da ita.

Abinci Peter ya haɗa musu, a tare suka ci domin ta samu sauƙi. Da ta yi wanka ta yi sallah, sai

ta ji duk ciwon ya tafi. Yana falo zaune ta fito cikin doguwar riga sosai ya kamata. Ɗauke kansa
ya yi daga kallonta.

"Please Lubaynah je ki sanya mayafi."

"Kallonsa ta yi tana son tambayarsa ko sun fara istibira'i ne, amma sai ta fara tafiya zuwa ɗaki,
ganin babu fuskar tambayar.

Gyale ta ɗauko ta yafa duk da cewar abin da yafi gyalen ya so. Lubaynah tana da sura mai
kyau, duk namijin da zai keɓe da ita dole ne ya ja hankalinsa, wannan surar ta ci galabarsa har
ya fara mummunar harka da ita.

Gyalen ya kalla duk da bai wani rufe jikin ba, sai ma kyau da ya ƙara mata, amma babu laifi tun
da daina ganin surarta da take rikita shi. Zai iya cewa tun da yake da ita bai taɓa ganin ta sanya
hijabi ba, sai dai na sallah shima don ya tsawatar mata ne, amma da gyale take yi.

Suna cin abincin bai wani hira da suke yi, sai ita data zuba masa idanu kamar za ta cinye shi.

Bayan sun gama cin abincin, sai ya fita domin yana da appointment. Ita kadai ta zauna a gidan
har zuwa yamma.

Kano
Hankalin iyayen Lubaynah ya tashi sosai har da Anty. Wayarta sun kira yafi sau a ƙirga, amma
ta kashe wayarta.

Daddy ya yi fushi sosai, neman gidan Captain Aliyu ya so ya yi, don duk da yake soja sai ya
wulaƙanta rayuwarsa, na mayar masa da yarinya farkarsa.

Suna ta neman layinta, har yamma sai suka ci sa'a, ta kunna wayar don ta kira Captain Aliyu da
bai dawo ba.

Ganin kiran Daddy hankalinta ya tashi sosai, amma sai ta daure ta ɗaga. Ganin ta ɗaga Daddy
ya ce,"Lubaynah, kin zaɓi namiji kan iyayenki ko?"

Shiru ta yi ta kasa magana, sai hawaye da yake zuba a ƙuncinta. Jin haka ya cigaba da
magana cikin fushi.

"Tun da kin zaɓe shi na barki da shi kike namiji ne, kuma zan yafe mishi .."

"Don Allah Daddy ka yi hakuri ni da Aliyu za mu zo ya nemi aurena."

"Shashashar banza mara hankali. Tun da an gaya miki shi banza ne kamar ki zai aure ki.
Wallahi in har ba ki dawo gida ba, sai na yi miki mummunar duka." Ya ce tare da kashe wayar

yana huci.

Kuka ta fashe da shi jin yadda ya ɗauki hushi sosai. Ta san Daddy yana matuƙar sonta, domin
karo na farko da suka samu saɓani a tsakaninsu.

Tana cikin kukan Aliyu ya yi sallama ya shigo. Cikin hawaye ta amsa sallamar. Ganin waya a
hannunta ya tabbatar masa da iyayenta suka kira, don haka bai tambayi ba'asin kukan ba ya
ƙarasa ya zauna a gefenta.

"Lubaynah, let's face the reality I can't marry you. Ina sonki amma wallahi bazan iya auren ki ba,
saboda bazan ɓoye miki ba, in har na aure ki zan kasance cikin wasiwasi da zarginki, kuma kin
ga babu kyau a aure. Mun yi kuskuren da ya zama katangar daya hana aurenmu. Ki je ki samu
wani xan ba ki du...."
"No!" Ta daka masa tsawa tana faɗin haka tare da toshe kunninta.

"Captain I told you several times. Kai nake so kai na ke so na rayu da kai. Matuƙar ba za ka
aure ni bana son koma daga gareka. Kuma wallahi ba zan zauna na zura ido ka auri wata ba,
domin sai na zame maka ƙadangaren bakin tulu. Aliyu you are so selfish. Why zaka ki aurena
bayan kai sheda ne, kaine namijin da na fara sani?" Jin yadda take kuka tana faɗin haka sai
ransa ya ɓaci.

Miƙewa ya yi cikin zafi ya ce,"Ba zan iya auren ki ba, that is the final answer. Please ki fita daga
rayuwata."

Kallonsa ta yi kamar zautacciya sai kuma ta miƙe ta kalle shi, a razane ganin yadda ya
harzuƙa."Haka kace?"

"Yes and I will not think again. Fine another person. "Ya ƙarashe maganar yana kallonta.

"Ok, fine. Zan koma gida, amma wallahi ba zan rabu da kai ba, duk yadda zan yi sai na mallake
ka. Kuma ka rubuta ka aje in har ban aure ka ba, babu wata 'yar iskar da za ka aura a matsayin
zabinka. Captain ka yi kuskure keta mini haddi na da ka yi, sannan ka ce za ka jefar da ni, ka
ɗauki wata ba zan taɓa barin haka ba, matuƙar ina da numfashi. I will go but you will see what
will happen." Ta ce tare da shiga cikin ɗakinsa ta tattara komai na ta ta fice.

Komawa ya yi ya zauna, yana fata shine na ƙarshe don yasan ba ta da zuciya zata dawo.

Lubaynah tana tafiya tana kuka sosai. A yau ta ƙara yarda duk macen data mallakawa namiji
jikinta ba tare da aure ba, haƙiƙa ta cuci kanta. Yau ga Aliyu ya kasa aurenta, don ta mallaka
masa jikinta kafin aure. Tabbas zina babban tabo ne ga 'ya mace, domin hatta wanda ya aikata
zinar gudun aurenta take yi. Ta yi fatan ina ma ana mayar da hanunn agogo baya, da ta tsare
mutuncinta ta haƙura da son shi da take yi. Ko da ace za ta mutu ne, wataƙila da ya yi mata

sausauci ya aure ta ko da baya sonta, amma gashi yau Aliyu shi yake gudun aurenta yana faɗin
ba zai yarda da ita ba. Ina ga kuma wanda ya aureta ya sameta ba budurwa ba?

Ta yi kuka sosai har sai da ciwon kai ya dawo. Saboda tashin hankalin da take ciki, sam bata je
gida Hannah ba, domin ta san ƙara mata damuwa za ta yi. Kai tsaye tasha ta nufa ta biya kuɗin
zuwa Kano. A ranta ta shirya duk hukuncin da iyayenta zasu yi mata.

A lokacin da ta isa gida duk suna zaune a falo. Kamar wata munafukai ta yi sallama, sannan ta
raɓe a bakin ƙofa. Kallon ta suka yi cikin mamaki domin maganarta suke yi.

Daddy ne ya miƙe cikin tsanannin fushi ya wanka mata mari."Banza shashasha! Ina yake da
kika ce zai zo ya aure ki?"

Kuka ta fashe da shi tare da durƙushewa ƙasa ta ce,"Daddy, na yi kuskure ka yafe mini don
Allah!"

Jin abin da ta ce suka tabbatar da yaudararta ya yi.'Kin cuci kanki Lubaynah. Kin zubar da
tarbiyarki kin bayar da darajarki a banza." Cewar mahaifiyarta tana kuka.

"Na yi kuskure ku yafe mini don Allah." Ta furta tana hawaye.

"Kanki za ki bawa haƙuri domin duk abin da kika yi wa kanki ne."

Daddy bai kalle ta ba ya haye sama, saboda yana jin kamar ya karyata.

Ganin sun watse sun barta a ɗakin sai ta miƙe ta shige cikin ɗakinta. Ta yi kuka sosai har ta
bawa uku lada. In ta tuna yadda Captain yake sarrafata yadda yake son yana mata alƙawarin
banza sai ta ji kamar za ta haɗiye kanta ta mutu. Bayan ta yi kukan ta fahimci bashi ne magani
ba sai ta janyo wayarta ta kira ƙawarta Rauda.
Bugu ɗaya ta ɗauka tana dariya. "Yane amaryar Captain to be? Mommy ta kira ni wai ko na san
gidan Captain na ce musu a'a."

"Hmmmmh! Aliyu ya yaudare ni ya ci amanata. Kin san ya kafe ba zai aure ni ba?"

"Amma Aliyu ya zama mai son kansa. Nufinsa ya more ki zai kuma je ya samu wata ya farke na
ta budurcin?" Kin san Allah bai isa ba. Ki kwantar da hankalinki ki ci abinci ki huta ina nan zuwa
xan shigo, don na yi tafiya ni da Habibina. Kin dai san hanyar da na bi na riƙe shi. Ta bayan
ƙasa za mu bi shi tun da ba shi da mutunci."
"Shikenan sai kin dawo."

"Yauwa kar ki damu bazan daɗe ba. Na raka shi Legos za su yi seminer. Captain na ki ne babu

wata 'yar iskar da zai aura. Shi ma ya san yaudarar kansa yake. "

"Na gode Rauda sai kin dawo." Ta ce tare da kashe wayar hankalinta ya kwanta.


To Lubaiyna wannan sai ya zama darasi ga 'yan matan da suke barin samari na amshe
budurcin su kafin aure, domin duk namijin da kika mallakawa kanki ko ƙaddara ta sanya ya aure
ki ba zai yarda da ke ba. Hattara 'yan mata da zawarawa.

Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.


Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0



*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*


MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya

Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423



PAGE 14


"Amma Aliyu ya zama mai son kansa. Nufinsa ya more ki zai kuma je ya samu wata ya farke na
ta budurcin?" Kin san

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login