Showing 24001 words to 27000 words out of 90573 words

Chapter 9 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8065

rayuwarta. Dubi jikinta yadda take cikin dauɗa babu tarbiya babu ilmi.

"Dama na san ita ma abin da za ta ce kenan. Na rantse ta ƙara ce mini ƙazama sai na...."

Sallamar da aka yi ya sanya ta yi shiru cikin mamaki."Ina zuwa jikalle, na san ba zai wuce kiran
mai gari ba."

"Shi ne tun da na ji muryar wannan mara mutunci, yana ji da wuya kamar mariƙin lema." Ta furta
tana zabgawa Hajiya harara.

"Bari na fita yau ma kamar kullum muke da nasara. Wane dare ne jemage bai gani ba?" Ta furta
tare da fita bayan ta yafa mayafinta.

Kallon wulaƙanci ta yi masa tare da ba ka masa harara."Kai dai ka zama mujiya ganinka ba
alkhairi ba."

"Ko kuma kune ku ka zama ganinku ba alkahiri ba. Kun addabi ƙauyen nan, muna fatan ranar
da Maigari zai sanya mu yi muku korar kare, donn har da jifa za mu haɗa muku."

"To in ya kasa korarmu kai ba sai ka kore mu ba, ina nan ina haƙonka watarana sai na ja maka
asarar da har ka mutu ba za ka manta ba." Jimmalo tace tana aika masa da mugun kallo.

"Kafin ki aikata kin bar garin nan. Kwanan za mu ja miki Yasin ki mutu kowa ya...."

"Sai dai duk yaranka su mutu, amma ba jikalle ta ba." Kaka Tani ta ce tana kallonsa.

"Maigari yana kiranku kuma ya ce ƙafata ƙafarku."

"To sai ka kama mu ka kaimu."Ta faɗi hakan cikin tsananin rashin kunya ba tare da ta duba
girman shi ba.

"Kar ku zo ku jira ya zo da kansa. Ni ɗan tsaƙo ne kuma na isar." Ya ce tare da wucewa.

Sororo suka yi suna kallonsu."Ɗauko mayafinki muje jikalle." Kaka Tani ta ce tana gyara nata
mayafin.

"Mu je kawai na ci ɗanmara ba sai na yafa ba, amma wallahi yau duk wanda ya yi mini ba
daidai ba sai na shuka masa rashin mutunci."

"Mu je wa ya isa ya taɓa ki." Ta ce tare da kama hannunta.

Har sun yi nisa suna bambami sai ta tuna da Hajiya. Dawowa ta yi inda take."Don Allah ki yi
haƙuri yanzu za mu dawo."

"Mu je tare saboda na ga ba haƙuri za ku bayar ba."

"Saboda me zan ba da haƙuri? Yaron nan shi yake takalarta. Ana soyayya dole?"

Shiru ta yi suka kama hanya ba ta tanka ba, don ba ta da abin da za ta ce. Ganin haka Daddy
ya bi bayansu cikin takaici.

Da suka isa gidan maigari, shiga suka yi ba tare da fargaba ba. Cikin tsananin ɓacin rai ya fara
magana, amma sam ba su razana ba. A maimakon su ba da haƙuri yana faɗa suna mayar
masa, musamman Jimmalo da harshenta ya fi na kowa. Da ma ga ta da murya zaƙwai. Su
Hajiya da suka zo sai suka ɓuge da ba da haƙuri. Da ƙyar aka kashe maganar, bayan sun ɗauki
alkawarin kula da lafiyar Bala.

Da suka kai shi kyamis ɗin Audi aka yi treatment ɗinsa. Sai da suka ba da kuɗin da za a kula da
shi. Ransu ya ƙara ɓaci ganin ba babu nadama a fuskarsu, sai ƙorafin kuɗin da suka ba da suke
yi.

"Tani tarbiyar da kika ɗora kenan? In kika mutu kika barta sawe irin rayuwa kike so ta yi?"

"Kuka kawai suka ji ta fashe da shi."Wallahi Kaka ba za ta mutu ba, sai dai ki mutu ki barta."

"Dole zan mutu amma ba yanzu ba jikalle. Share hawayenki ina nan tare da ke." Ta ce tana
jijjiga ta sai ɓare baki take yi.

Gani lamarin yafi ƙarfin ta sai ta zauna ta yi shiru."Ki yi haƙuri yarinya ya ce, kuma ita kaɗai ta
rage mini." Ta ce tare da zama a gurin ta.

"Ni zan koma." Ta faɗa cikin ɗaure fuska.

Jin abin da ta ce ya tabbatar mata da ta yi fushi."Ki yi haƙuri don Allah na ɗauka kwana za ki
yi?"

"Ki barta ta tafi Kaka umma ta gaida ashsha." Jimmalo ta ce tana wasa da ƙasa da ta zuba ruwa
ta kwaɓa.

"Ba a yi haka ba domin baƙonka Annabinka. Ta so mu ba ta haƙuri."

Miƙewa ta yi ba tare da ta ce komai ba, ta shige cikin ɗaki tana wakar sharmandu.

Hajiya sai ta kasa cewa komai. Tunani ta fara dole ta yi haƙuri in har tana don ta canza su,
amma to ta yaya za ta iya? Tambayar haka ya faɗo cikin ranta. Za ta gwada domin sai an
gwada akan san na ƙwarai.

Zama ta yi sannan ta kalle ta."Ba kwana za mu yi ba, amma sai yamma za mu tafi, kuma ina
son mu je damu sai kuga inda na ke zama tun da na zo na ga gurinka."

Fara'ar Kaka Tani ya ƙaru jin abin da ta ce."Wai kina nufin mu biku birni?" Ta yi mata tambayar
cikin murna.

"Eh, sai ku kwana ko biyu ne."

Murna suka ji Jimmalo ta fara tana tsalle tana faɗin,"Za ni birni na ci daɗi, sai kuma ta tsaya da
rawar ta ɓata fuska ta fito waje.

"Hajiya, mene dangantakar ki da wannan mara mutuncin da ba shi da mutunci?"

"Jikana ne." Ta ba ta amsa.

"Taɓ aradu ba zan je ba, saboda na tsani wannan mutumin, kuma in har zan ganshi sai na rama
dukan da ya yi mini."

Zare idanunta ta yi jin abin da ta ce.Sai kuma ta yi murmushi."Kar ki damu ai ba gidana yake
zama ba, kuma soja ne ba ya zama a garin."

"Au to zan je. Wato dama soja ne shi yasa ba shi da imani? To ai ni bana tsoron soja, saboda
tsaf zan iya zama soja, na rinƙa harbe kan 'yan ta'adda. Wallahi tsaf shi ma zan kara da shi,
saboda duk ranar da ya ƙara dukana sai na fasa masa kai." Ta ce tare da matsowa gunta, tana
washe baki tamkar ba ita ta gama mata rashin kunya ba.
Hajiya jinjina kanta ta yi domin ta fara jin tsoronta, saboda yadda take maganar har cikin
zuciyarta. Kallo ɗaya za ka yi mata ka san bata da tsoro. Har ta fara tunanin an ya za tafi da su,
saboda kar ta kai tashin hankali gidanta, don ta san duk ranar da Aliyu ya zo haɗuwar ba za ta
yi kyawu ba, amma da ta tuna Aliyu ba cika zuwa ba, saboda yanayin aikinsa, sai hankalinta ya
ɗan kwanta tamkar ta yi baƙo ya mutu.

"Yee za ni birni bari na je na gayawa ƙawayena." Ta saka ihu tana faɗin haka.

"Amma za ki yi wanka ko Jimmalo?"

Jin tambayar da ta yi mata ya sanya ta ɓata rai." Ni ba wani wanka da zan yi, saboda ƙaiƙayi
yake sani."

Zare idanu suka yi ita da Daddy."Ni dai na san in mutum ba ya wanka ne jikinsa yake ƙaikayi."

"Ba dole Hajiya jikinta ya yi ƙaikayi ba, domin daga ganinta tana shafe wata ba ta ga ruwa ba,
ko ta yi wankan dadti kawai zata ta so."

"Ai in dai Jimmalo ne sai tafi haka, saboda har na gaji na daina magana. Ta rantse sai bikin
ƙawarta za ta yi wanka."

Mamaki suka yi musamman daddy da ko aiki ya dawo bai yi wanka ba, sai ya ji jikinsa na ciwo,
bacci kuwa da ƙarfi yake yi a ranar.

"Zan yi daka tsami, amma wanka sai ranar da na sanya ta zo." Kasa cewa komai suka yi har ta
fice tana tsalle.

"Bari na haɗa kayan da za mu tafi da su, amma da na kin bari mun zo wani lokacin, tun da kin
ga bamu shirya ba."

"Ƙarki damu hatta kaya kar ku ɗauka, akwai komai ita ma Jimmalo zan sanya ta haɗa mata
kaya."

"Masha Allah! Shi ya sa aka ce da arziki a garinku gara a gidanku. Yau ga shi kin yi arziki kin
tuna damu." Ta ƙarashe maganar tare da fashewa da kuka.

"Kar ki damu ki shiga ki shirya, bari ya shigar muku da kayan."

"To," Ta amsa cikin tsananin farinciki

Jimmalo kuwa, sai da ta gama zaga gari tana faɗa wa ƙawayenta, da abokan gabanta za su je
birni a mota. Kafin kace mene ƙofar gidansu ta cika. Wasu suna mata murnar zuwanta birni,
yayin da wasu hassada da baƙinciki. Wasu kuwa fata suke ta tafi kar ta dawo, domin ta zame
musu kaɗangaren bakin tulu.
Ba su ɓata lokaci ba suka kammala shiri. Jimmalo riga da zani ta canza wanda babu bambanci
da kayan da ta cire, domin sun yi duƙu-duƙu tamkar an ƙwato su daga bakin kura. Tun da ta
sanya kayan sai da suka yi kusan sati biyu suna jikinta. Sai dai in wari ya sameta ta shiga rafi ta
yi wanka da kayan. Kayan sallarsa ne tun da aka ɗinka ta daina sanya wasu kaya sai su. Babu
irin faɗan da Kaka Tani ba ta yi mata ba, kan ta ije sai an fita babban sallah, amma ta yi kunnen
uwar shegu da ita.

A lokacin da suka fito za su tafi, har wani yanƙayi take yi tana yanga. Tafiyar ma tamkar ba za ta
yi ba, ita a dole za ta je birni. Kwalliyar da ta yi, sai da ta sanya daddy dariya ganin yadda ta
ɓata fuskarta da kwalli.

Tana shiga cikin motar ventilation ɗin cikin motar ya canza. Daddy har sai da ya toshe hancinsa.
Da sauri ya zuge glasses na motar yana sauke numfashi. Ita kanta Hajiya daurewa ta yi, amma
kamar za ta yi amai.

Motar na fara tafiya, ƙawayenta suka fara bin motar suna ihu tare da kiran sunanta.

Ita kuma sai washe baki take yi tana ɗaga musu hannu.

Ana kiran sallar magariba suka iso Kaduna. A lokacin da direba ya do shi get ɗin gidan,
waigowa suka yi suna kallon juna ita da Kaka Tani.

Sun kasa cewa komai, suna kallon get ɗin gidan mai tsananin kyau. Jimmalo kuwa ji ta yi kanta
ya kulle tsoro ya kamata. Tunani ta fara ko cin kai suke yi. Ba ta ƙara shiga cikin tsananin
mamaki ba, sai da ta ga maigadi ya buɗe get ɗin gidan sun shiga.

Fitowa suka yi a cikin motar, cikin razana suna zare idanu. Ganin yadda suke mazurai Hajiya ta
kama hannunta ta ce,"Ku shigo cikin gidan.."

"Wayyo Allah na shiga uku wallahi ba zan shiga cikin gidannan ba, a cinye mini kai." Ta fasa ihu
tare da yin hanyar ƙofar gida tana faɗin haka.

Ganin yadda ta buɗe sai Kaka Tani ta bita."Mu koma ƙauye, na rantse daga ganin gidan nan cin
mutane suke yi."

Duk yadda Daddy ya so kar ya yi dariya sai da ya dara. Kallah maigadi kuwa, saboda dariya har
sai da ya faɗi ƙasa yana mamakin inda ta same su.

"Cin kai kuma? Wallahi bana cin mutane. Kuma ba sayar da ku zan yi ba."

Da ƙyar suka yi nasarar shiga da shi. Sun zauna kamar za ka ce musu kyat su ruga. Duk rashin
tsoro na Jimmalo sai da ta razana da kyawun gidan.

"Ku zauna don Allah ku saki jikinku, wallahi ba zan cutar da ku ba. Gidan nan wannan ya gina
mini, saboda Allah ya buɗa masa yana da kuɗi sosai."

Miƙewa Kaka Tani ta yi tana kallon gidan."Yanzu Tine kina nufin yanzu wannan gidanki ne,
wanda ɗanki ya gina miki gidan kwalba?"

"Wallahi kin san arziki na Allah ne."

"Haka ne kuwa ganin gidan nan ya tabbatar mini da hakan, amma sai dai ƙauye zan koma
saboda bazan iya rayuwa a cikin gidan ba, don ni har yanzu zuciyata tana tantanmar cewar
ɗanki ba shan jini yake yi ba ko Jimmalo?" Ta ƙarashe maganar tana kallonta.

"Aradu kuwa gara mu koma ƙauye kawai, saboda har na fara jin wuyana yana rawa kamar zai
cire."

"Zo mu koma kafin ya cire mun shiga uku." Kaka Tani ta faɗa tare daka mata hannunta jikinta
yana rawa.

"Ke ki ki ji tsoron Allah Jimmalo babu wani tsafin da nake yi."

Hajiya ta ce cikin mamaki. Ganin yadda Kaka Tani ta rikice, saboda ta ɗauka da gaske ne.

Dariya ta sheƙe da shi tana nuna ta da yatsa."Kai Kaka Tani kin tsufa kina son duniya. Wasa na
ke miki ai ni na ga gidan zama sai na ga daman koma wa ƙauye."

"Ja'irar yarinya kawai ai sai na ga yaranki zan mutu."

"Wayyo abin kallo yana birni Kaka Tani dubi ƙaton tibin nan don Allah."

To Jimmalo jikar Tani a birni. Ko ya za ta kaya?
Captain Aliyu ya kamata ka zo saboda your amaryato be ta zo


Tallah

Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin
result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka
sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan
ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama
kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast

Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta
wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na
gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da
ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina
shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606
ina zaune a kano


FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242


Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da

ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke


*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*


MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423

Tallah

Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin
result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka
sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan
ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama
kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast

Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta
wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na
gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da
ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina
shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606
ina zaune a kano

PAGE 8
Dariya ta sheƙe da shi tana nuna ta da yatsa."Kai Kaka Tani kin tsufa kina son duniya. Wasa na
ke miki ai, ni na ga gidan zama sai na ga daman komawa ƙauye."

"Ja'irar yarinya kawai, sai na ga yaranki zan mutu."

"Wayyo abin kallo yana birni Kaka Tani dubi katon tibin nan don Allah. Wannan sai mutanen da
na ke kallo su faɗo cikin falon."

Dariya Hajiya ta yi ta kama hannun Kaka Tani. "Yanzu dai ku zo ku shiga ciki, ku yi wanka ku ci
abinci ku huta."

"Ni gaskiya ba zan yi wanka ba saboda na yi dakatsami da zamu taho, shi ma ƙyar na yi don
kawai Kaka Tani ta matsa mini ne, amma tun da na yi wanka sai nan da sati..."

"Sai me?" Hajiya ta yi mata tambayar cikin zare ido, tare da gane dalilin da ya sanya ta yi dafe
ta fita hayyacinta.

"Na rantse sai ranar da zan koma ƙauye zan yi wanka."

"Tabɗi ana ƙazanta a gurin nan." Hajiya ta furta cikin mamaki.

"A kawo mini abincin nan dama yunwa nake ji." Ta furta tare da zama a tsakiyar falon.

"Ki dai tashi ki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login