Showing 30001 words to 33000 words out of 90573 words
Chapter 11 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
go and marry."
Rintse idanunta ta yi, hawaye yana zuba tana mamakinsa da yake gaya mata ta je ta yi aure, ba
tare daya san halin da take shiga ba.
"Ba zan iya auren wani in ba kai ba. Ka riga ka koyar da ni soyayyarka, in har ba kai na aura ba.
Sojana ba na jin zan iya mallakawa wani jikina. Kai ne kawai ka iya sace zuciyata da sarrafa ni
yadda kake so. Ba na son na yi rashin ka. A shirye na ke na ƙara shekaru in har za ka aure ni."
Jan numfashi ya yi sannan ya fesar. Ya zuƙi ta tabarsa ya ja fesar da hayaƙi. Lokaci guda ta yi
nasarar sauko da fushinsa. Wani irin feelings na ta ya taso mishi domin ta saba mishi da kuma
ya yi missing.
"Ok, ki zo gidana mu yi maganar na dawo."
"Gani nan zuwa babyna." Ta ce mishi tare da yi mishi kiss ta kashe wayar cikin murna.
Jikinta har rawa yake yi, tana haÉ—a kayan da za ta yi kwanaki da su. Ta rasa irin son da take
mishi har yake wulaƙanta rayuwarta, amma ta kasa rabuwa da shi. Da ta kuma tuna Captain
Aliyu, ƙarshe ne gurin sace zuciyar mace sai ta daina ganin laifinta.
Tana sanya kayan kwalliyarta a jaka Anty Hannah ta shigo. Tsayawa ta yi tana kallonta wacce
ba ta san ta shigo ba.
"Lubaynah, ina za ki kike haÉ—a kaya?" Ta yi mata tambayar tana kallon ta.
Sosa kanta ta yi, cikin rashin gaskiya ganin yadda ta tsareta da idanu."Zan je bikin wata friend
É—ina, kuma zan yi kwana biyu.."
"Ki fito ki gaya mini za ki je gurin lalataccen yaron nan Aliyu."
Ranta ne ya ɓace jin ta zage shi."Anty saboda me za ki zagi wanda na ke son aure?"
Dariya ta yi mata cikin takaici."Ok, a tunanin ki zai aure ki ko?"
"In sha Allahu ba ni da miji sai shi."
"Yaudarar kanki kike yi Lubaynah. Ki rubuta ko mata sun ƙare ba zai aure ki ba, domin kin riga
kin sayar da darajar da kike da shi."
Ga mamakin ta sai kawai ta saka mata kuka."Fatan da kike mini kenan kar ya aure ni? Mai na yi
miki kike mini wannan fatan? Domin gara ki yi mini addu'ar Allah ya É—auki raina akan na rasa
Captain Aliyu."
"Ashe za ki mutu kuwa, saboda na gaya miki ki rubuta ki ajiye ba zai aure ki ba."
"Na gode da fatan da kike yi mini, a matsayinki na 'yar'uwata wacce muka fito ciki É—aya. In sha
Allahu ba ni da miji sai shi. Sai kin zo gidana kin gammu muna soyayya."
"Ki dai yi tunani kafin ruwa ya ƙarewa ɗankada."
Banza ta yi da ita ta yi, tare da ɗaukar trolley ɗinta da ƙaramar jakarta za ta fice.
Ganin haka ta sha gabanta tana faÉ—in,"Babu inda za ki kin san Allah zan kira Daddy na gaya
masa abin da kike yi."
"Ki matsa mini na gaya miki bikin ƙawata zan je." Ta ce tare da ture ta
"Lubaynah, zan mare ki babu inda za ki j..." Maganar ta maƙale mata sakamakon ture ta da ta yi
ta fice daga gidan.
Biyo ta ta yi tana kiran sunanta, amma da sauri ta shige cikin motarta ta ja aguje.
Bayan ya kashe kiran sai ya miƙe zuwa ɗakinsa. Sigarin ya kashe ya sanya a trash. Murmushi
ya yi tare ƙara sawa gaban mirror yana shafa sajensa. Sosai yake jin ya yi kewarta. Ya san
cewa Lubaynah mace ce, wacce ta amsa sunanta, amma sam ba zai iya zaɓawa yayansa ita a
matsayin matarsa ba. Yana wannan tunanin wayarsa ta yi ƙara a tunkinsa ita ce ta zo, amma
sai ya ga numbar Anty Amarya uwar ɗakinaa kuma ƙawarsa ce ta kira.
Ba tare da ya É—auki wayar ba har sai da ta katse ya kira."Hello Antyna akwai news ne?" Ya yi
mata tamabayar yana dariya tare da zama gefen gado.
"News daga gareka na ke sauraren ji, amma labarin da zan ba ka yadda ka rikita 'yan matan
gidanmu da biki. Kowacce ta yi kwalliya ta yi burin ganinka don ta burge ka."
Tsaki ya saki yana mamakin rashin kunyarsu."Amma Anty sun raina ni. Marin da na yi wa bai sa
sun daina haukarsu ba ko? Uban mai zan yi da su? Ko mata sun ƙare ba zan iya auren wata
daga cikinsu ba."
"Bana son wulaƙanci soja. Yaran nawa kake gaya mini haka?"
Dariya ya yi yace,"Dole na gaya miki don ki sanar da su, su daina haukar da suke yi."
"To wa za ka aura kuma yaushe za ka yi? Captain na matsu na ga kana zuwan mini da matarka
Zariya."
"Zan yi aure Anty ni kaina ina buƙatar haka, amma har yau na kasa samun macen. Kin san
kalar macen da na ke so. Don Allah na ba ki cigiyar mai addini mahaddaciya kuma ustaxiya mai
kyau."
Dariya sosai ta yi jin abin da ya ce."Ka san halin ka kuma kake son mace irin wannan?"
"Eh saboda yarana za zaɓar musu uwa ta gari, kuma irin wannan macen ne kawai zan aura
hankalinsa ya kwanta."
"Saboda kana ɓata matar wani ko?"
Shafa kansa ya yi jin maganar da ta yi ba tare da shakka ba."Anty ke dai kin san komai. Ina
fatan lokacin da zan yi aure Lubaynah ta fita daga cikin rayuwata. Zan daina duk abin da nake
yi in sha Allahu, domin ba na fatan ranar da Daddy zai fahimci fuska biyu gare ni."
"Ya kamata ka daina, saboda in har kana son irin wannan matar dole ka zama na gari, kuma
maganar auren lokaci yana ƙurewa."
"Na baki cigiya? Har yau na kasa samun wacce take da duk wannan halin."
"In ka ba ni zabi kana tunanin zan guji 'ya'yana na nema maka wata ne? Mene ne aibun su
Hanifah sun da kyau kuma da natsuwa, in kuma ba ka so ya ga Mufida nan, da kuma sauran
'yan matan ka zaɓa a cikinsu. 'Yan mata huɗu da suke crushing ɗinka a family kuma duk cikinsu
babu wacce ta yi maka? Kada haƙƙin su ya kama ka, musamman Hanifa yarinyar ta zurma da
yawa."
"Bana son su, kuma bana son na auri mace wacce take sanya gyale. Matata ina aurenta Anty
kullum cikin hijabi da niƙabi za ta rinka zama sam bana son wani ya kalle ta."
Mamakin abin da ya ce ta yi."Duk za ka iya canza Hanifah yarinyar tafi sonka kamar hauka.
Kabar batun ita yarinyar mijina ne, ka san zan iya barin kowa na É—auke ka, kuma kun dace da
juna."
"Don Allah ba ita ba sam ba zan iya auren ta ba. Bana son mace da zan aura na canza ta.
Matar da na ke son na aura wacce zan same ta a kan tarbiyyar da na ke so ne."
"Hmmmmh! Soja lamarinka sai kai."
"Ki dai bincika ba za a rasa ba."
"Ba zan yi maka wannan alƙawarin ba, saboda in har aka ji nice na samo maka mata zan yi
baƙin jini,a yanzu ma haka ana ganin kamar yadda muka shaƙu wani abu na yi maka,
ballanatana aji duk ka guji 'yan matan family na nemo maka wata? Don haka duba da kanka."
Shiru ya yi saboda ya kuma fahimci gaskiyarta.
"Ok, zan duba Anty ki taya ni da addu'a. Zan shigo Kaduna zan zo Zariya. In zan zo zan kira ki
ki yi mini dambu."
"Shikenan ba matsala É—an gidana." Ta ce tare da kashe wayar.
Wayar ya bi da kallo don kuma ya kashe yana murmushi. Sosai jininsu ya haÉ—u da ita. Tana da
hankali sannan ta fahimce shi fiye da iyayensa. Babu abin da ya ƙara mata girma da mutunci.
Ta san duk munanan halinsa, amma ko suɓutar kalami ba ta taɓa furtawa ba. Sai dai tayi ta
mishi nasihar ya daina.
Yana ije wayar kiran Lubaynah ya shigo. Ba tare da ya É—auka ba ya fita zuwa get. Da kanshi ya
buÉ—e mata get É—in ta shigo, saboda ya tafi kasuwa.
Tana shigowa ya ware hannunsa ta faÉ—a jikinsa. Bakinsu ya haÉ—e domin ya yi missing na ta
kamar yadda ta yi na shi. Sakinta ya yi yana kallon ta ganin tana hawaye.
A ranar sai da ya sanya ta manta komai ta shiga lambun ƙaunarsa. Wannan dalilin ya sa take ji
kamar za ta haukace duk lokacin da ya ce mata bai shirya aure ba . Tana ji a ranta saboda
zarsa da ta É—anÉ—ana take kishinsa za ta iya kashe duk wacce ya aura.
A ranar sun sha soyayya tamkar wasu sababbin ma'aurata. Bayan sun yi bacci sun tashi.
Wanka suka yi Captain Aliyu ya shirya suka fita zuwa gurin shaƙatawa. Sosai take murna ganin
yadda ya sakin mata bakin aljihu ya yi mata siyyayya. Da suka dawo wanka suka yi sannan
suka kwanta.
Kwana uku ta yi a gidansa suna shayar da junansu zumar ƙauna. Hankalinta kwance take
shayar da shi madarar ƙauna. Burin ta kawai ta kawo hankalinsa ya amince zai aure ta, domin a
shirye take da jure duk halayensa ta zauna da shi.
Damuwar da shi wani lokacin duk sonta da ƙaunarta da yake yi. Haka zai rufe idanunsa ya
shukamata tashin mutunci, amma hakan nan za ta shanye sai ma ta ba shi haƙuri.
A ƙalla sai da suka yi sati, suna soyewa sannan ya shirya zuwa Kaduna. Kan dole ta tattara ta
koma gida, ba don ta so ba saboda ta so ya barta a gidan tun da ba daÉ—ewa zai yi ba amma sai
ya ƙi.
Misalin ƙarfe sha ɗaya ya iso garin Kaduna. Kai tsaye gidan Hajiya ya wuce, saboda ya yi
kewarta sosai. Tun da incident É—in nan ya faru bai kira ta ba, domin yafi jin haushinta fiye da
komai. Sanin cewar zai sha ƙorafi sai ya siya mata kayan toshi.
Hon ya yi maigadi ya buÉ—e masa ya shiga. Parking ya yi sannan ya fito daga cikin motar. Yana
sanye cikin ƙananan kaya riga da wando kalar kakin soja, sai hulan sojoji da ya sanya.
Kasancewar yau Hajiya ta tashi tana zazzaɓi sai ba ta fito ba, tana cikin ɗakinta tana bacci.
Kaka Tani ita ma tana inda aka sauke su. Jimmalo ce kawai a falo tana kallo tamkar za ta shige
cikin tibin. Sai surutu take yi ita kaÉ—ai.
Da sallama ya shigo cikin falon fuskarsa a sake. Nufinsa ya yi ido biyu da rigimarmiyar kakarsa,
amma sai ya ja ya tsaya cikin tsanannin ɓacin rai ganin wacce ya tsana fiye da komai a
rayuwarsa.
Ƙare mata kallo ya yi a wulaƙance, wacce ba ta san ya shigo ba. Gabakiɗaya hankalinta yana
kan tibin. "Ye wallahi ya kashe shi ka amma wannan sojan ba shi da imani mai zuciyar kafurai."
Ta furta tare da lailayo ashar ta danna masa.
"Ke!" Ya daka mata tsawar da ya sanya ta juya da sauri tana kallonsa.
Miƙewa ta yi da sauri tana maƙonsa domin ta razana, amma sai ta dake saboda da fari ta yi
tunanin yawan zaginsa da tunanin ranar da Allah zai haÉ—asu ta yi mishi rashin mutunci ne, ya
sanya yi mata gizo, amma kuma da ta tuna zai iya zuwa inda take, sai ta É—auke fuska tana
kallonsa.
Captain Aliyu sai ya toshe hancinsa yana watsa mata kallo. Ya rasa duk lokacin da ya ganta dai
ya ji amai zai zubo masa. A yadda yake jin tsanarta da ƙyamarta ko mutuwa zai yi da yunwa, in
har tana gurin ba zai iya kai abinci a bakinsa ba.
"Uban me ya kawo ki gidan nan?" Ya furta yana ƙoƙarin ƙarasawa inda take sai kai mata mari.
"Kai dakata!" Ya ji muryar Kaka Tani a bayansa tana faɗin haka, amma saboda baƙar zuciya sai
da ya kai mata marin. Kafin ya sauke ta ɗaya hannunta za ta mayar masa da na ta. Ƙafarsa ya
sanya ya yi ball da hannun. Ta ji zafi amma sai kawai ta ƙara kai hannun cikin fusata
Kaka Tani ta shiga tsakiyarsa ganin zai kashe ta. "Kai dakata wane irin zuciyar kafurai kake da
shi?"
"Ki bari na nuna miki irin zuciyar, domin na rintse sai na kashe wannan jikar ta ƙi."
"Wayyo na shiga uku! Hajiya ki fito wannan mara imanin zai yi kisa!"Kaka Tani ta fasa kuka
ganin ya kai mata hauri.
Hajiya da take bacci tana ƙudundune cikin muryar ɓacci ta ji kukan Kaka Tani. Da sauri ta duro
hankalinta a tashe. "lafiya Tani?" Ta yi mata tambayar dai kuma ta tsaya turus tana kallonsa da
yake huci.
"Ina da lafiya wannan mara imanin ne zai kashe mini jikalle."
"Aliyu, wai mai ke damunka, kuma tashe ka shigo gidan nan?" Ta yi masa tambayar tana
ƙarasawa gurin sa.
"Hajiya don me za ki ɗauko wannan ƙazamiyar kika ije ta a gidanki?"
"Alhamdulillah da ka ce gidana ka ba wa kanka amsa." Ta furta masa tana harararsa, sai kuma
ta É—ora da cewa,"Ko so kake kar na yi zumunci saboda kai?"
"Na tsani yarinyar nan, sam ba ta da tarbiyya. Ban taɓa ganin ƙazamiya irin ta ba.
"Ni ma na tsane ka, saboda ba ka da imani mai zuciyar kafurai?" Mamaki sosai Hajiya ta ji ganin
yadda take masa magana babu tsoro.
"Ke Jimmalo ki kiyaye ni Yayanki ne. Tani ki shiga da ita ciki." Ta furta tana kallonta.
"Allah ya tsare ni ya zama yayana, saboda ba ni da maƙiyi kamarsa masu kashe mutane
kawai." Ta ce tana murguÉ—a masa baki da galla masa harara.
Hannunsa ya sanya ya kai mata bugu, amma sai ta ƙwace tare da yi masa daƙuwa.
Daƙuwar ya fusata shi ya bita zuwa ciki. Da sauri Kaka Tani ta sanya ɗan makulli."Ki bar shi ya
shigo wallahi na fasa masa kai. Koɗaɗɗe kawai mai kama da zabiya." Ta furta tana ƙara aika
masa da daƙuwar duk da ba ya gani.
"Jimmalo, wancan sojan sam ba shi da imani. Dubi yadda yake kallon ki zai iya kashe ki. Na
tsorata kawai mu koma ƙauye."
"Babu ƙauyen da zan koma sai na gama kwanakina. Ke ma kin san daidai na ke da shi, don
wallahi yana soja ba zan ji tsoron sa ba. Don ma ban zo da gwafata ba, da sai na sauti ƙeyarsa
zan É—ana masa." Sai kuma ta,ce,"Na manta ashe na zo fa ita."
"Mu dai koma ƙauye kawai." Kaka Tani ta ce cikin tsigar rarrashi.
"Babu inda zamu sai na gama kwanakin da zan yi."
A falo kuwa Hajiya ta kalli Captain Aliyu da yake huci ta ce,"Saukar yaushe Aliyu, ba ka gaya
mini za ka zo ba?"
"Bazata na so na yi miki, amma sai dai zuwana sam bai yi amfani ba, domin na ga abin da na
tsana a rayuwata."
"Ka yi haƙuri yarinyar ba ta da kunya amma zan yi mata magana."
"Kar ki yi mata zan kowa mata hankali don wallahi saina ƙaryata."
"Ba za a yi haka ba baƙuwace tafiya za ta yi, duk da na yi shawarar na karɓe ta na sanya ta a
makaranta, saboda yariyar ko karatun sallah ba ta iya ba. Ga ƙazanta tun da ta zo gidan nan na
ke ƙyamar gidan. Ko sau ɗaya ta ƙi wanka."
"Please Hajiya ki kore ta a gidan nan, kuma kar ki yi gigin cewa ta zauna dake saboda ba ta
tarbiya ga ƙazanta. Wallahi tun ranar da na haɗu da ita na ke yi mata ƘIYAYYAR JINI. Da zarar
na ganta sai na ji tsigar jikina yana tashi, jinin jikinsa yana tafarfasa."
"Tafiya za su yi ni kaina ba zan iya ba." Ta ce masa don ya kwantar da hankalinsa ganin yadda
ya harzuƙa.
"Yauwa matata kar ki sanya wa kanki yawan jini."
"Tafi can ja'irihar yanzu ina jin haushin ka Aliyu. Ƙiri-ƙiri ka ƙi zaɓin matar da na yi maka."
"Hajiya ki kwantar da hankalin ki. Duk ranar da na kawo miki matata sai kin ga amfanin jinkirin
da na yi."
"Jinkirin ba shi da amfani musamman ku sojoji,"
Wai ya ne da comments í ½í¹„í ½í¹„í ½í¹„ ina ga tafiyarta hutu zan yi tun da bakwa comments
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruÉ—ani. RuÉ—anin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke
*ƘIYYAYYAR JINI!*