Showing 63001 words to 66000 words out of 90573 words

Chapter 22 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8073

canza rayuwarta." Ta furta tare da kwanciya.

"Amin," Ya ce sannan ya bi bayanta ya kwanta.

Jimmalo, kamar yadda ta sanya sai tayi abin da zai mayar da ita gida. Tun safe tana tashi sai ta
nufi daidai windonsa ta zauna.

Captain da bai samu bacci da wuri ba sa da ya dawo sallar asuba, sannnan wani irin bacci mai
daɗin gaske ya kama shi, domin har ya ɗauki wayarsa ya kunna Qur'an yana karantawa, sai
bacci ya ɗauke shi waya ta faɗi kan kirjinsa.

Kamar a mafarki ya ji an tsanadara ihu tare da cigaba da kuka. Da sauri ya buɗe idanunsa
lokaci guda kansa ya sara.

Fitowa ya yi daga gadon,cikin zafin mama ya ɗauki bel ɗin wandonsa. Jimmalo da take kuka
tana faɗin,"A mayar da ni Damagaran, banzan zauna a birni..." Ta kasa ƙarashe maganar
sakamakon dukan da ta ji ya rufe ta dashi.

Wani irin ihu ta saki, kawai sai ta yi kuka kura ta yi kansa ta cakume shi. Ganin abin da ta yi ya
sanya ƙafarsa babu imani ya tokari bakinta ya fashe jini yana zuba. Ganin abin da ya yi mata ta
ƙara kukan kura ta yi kansa. Idanunsa ya rufe, ya fara dukansa kamar yana dukan ɓarawo.

Maigadi ya ji kukanta da sauri ya fito yana salati tare da kurma ihu yana faɗin,"Jama'a ku fito za
a yi kisa."

Mommy da take kicin tana girki, Daddy kuma yana falo yana karatu, suka ji muryar da kukanta
sama-sama. Labule ya ɗaga daidai lokacin da Mommy ta fito a sukwane tana faɗin,"Na shiga
uku Aliyu zai yi kisa."

Da gudu ya bi ta zuwa waje ransa a ɓaci. Yana zuwa ya wanka masa mari, wanda ya sanya ya
yi mutuwar tsaye, saboda zai iya cewa tun da ya girma bai taɓa dukansa ba.

"Ka wane irin mahaukaci ne kashe ta za ka yi?" Ya yi masa tambayar yana kallon sa, sai ya juya
gurin Jimmalo da bakinta ke zubar da jini sosai tana ihu, amma idanunta ba hawaye.

"Na rantse sai na kashe shi tun da ya buge ni, saboda an ga Kakata ta mutu shine za a kashe
ni. Wayyo Kaka Tani ki dawo duniya ki ga ni ana cutar dani babu mai rama mini. Kaka Tani don
Allah ki zo ki rama mini duka da ya yi mini." Ta ƙarashe maganar tare da ka tsalle ta faɗi ƙasa
tana birgima.
Ganin haka duk sai jikinsu ya yi sanyi. Daddy ya kalle sa da yake huci kamar mesa ya ce,"Aliyu
in har ka ƙara ɗora hannunka a jikinta ban yafe maka ba." Ya ƙarashe maganar da muryar da ya
bayyana

"Wacce irin mahaukaciya ce za ki zo daidai windona tana mini kuka, amma ba ka gani ba
Daddy ka mare ni?"

"You need to settle with her she is you sis..."

"Never!"Ya ce tare da ɗaga hannunsa jin abin da ya ce, ganin Daddy ya yi shiru sai ya ɗora da
cewa,"Never wannan gidahumar ta zama sister na. In har yarinyar nan za ta ci gaba da zama a
nan, ba zan ƙara zuwa Kaduna ba." Yana ƙarashe faɗin haka, ya wuce cikin ɗakinsa, ba tare da
ya damu da kiran da suke masa ba.
"Ka gani ko? Dama na san haka zai faru, babu yadda za a yi su yi rayuwa under roof ɗaya."

"Ya zama dole su yi I know what I will do." Daddy ya ce tare da juyawa ya shiga cikin falo.

Hannunta Mommy ta kama cikin takaici da take kuka miyau da jini duk ya haɗe. Kallonta ta yi
sai taji tamkar za ta yi amai.

"Please Jimmalo, wannan abin da kike yi don Allah ki daina. Kin wuce yin haka duba ki ga yada
kika yi ƙazanta?"

"Ni dai a mayar da ni Damagaran, na tsani kowa a gidan nan." Ta furta ba tare da shayin komai
ba.

"Ok, shiga ciki ki wanke bakinki yanzu driver zai mayar da ke." Ta faɗi hakan ba tare da yanke

shawarar ba.

"Ƙarya kike yi haka jiya haka kika ce mini, don haka sai kin rantse."

Jin abin da ta faɗa sai mamaki sosai ya kamata. Ganin duk girmanta ta tsare ta sai ta rantse.

"Let's go in Jimmalo." Ta kama hannunta da ƙarfi suka shiga ciki.

Daddy da yake safa da marwa ciki tsananin damuwa a falo. Ganin sun shiga cikin sai ya wuce
sashin Aliyu, wanda ya gama haɗa kayansa yana shirin fita.

"Aliyu." Ya ji muryar Daddy ya kira sunansa. Cikin fushi ya jiyo zuciyarsa har tafarfasa yake yi.

"Aliyu you are no going anywhere and dole ka ɗauki Jimmalo a matsayin ƙanwarka, don haka
ka ake jakarka yanzu ka kaita makarantar su Umma ayi..."

Kallon da ya yi masa sai ya kasa ƙarashe maganar, domin dama ƙarfin hali ya ke yi, amma
kuma ya zama dole ya san yada zai yi ya haƙura da tafiya.

"Ni na ɗauki wancan kucakar a mota ta? Over my dead body!" Ya ce tare da zagaye kansa da
yatsu biyu ya murɗa shi.

"Dole za ka ɗauke ta, a matsayina na mahaifinka na yi maka umurnin haka." Ya ce yana kallon
sa cikin ɓacin rai.

Lokaci guda ya yi dana-sanin zuwa Kaduna, domin abin da ya gani ya gwammace bai zo bikin
ba. Idanuwansa suka kaɗa suka yi jajir, saboda tsananin tashin hankali. Tunani yake ya za a yi
ya sanya ta a cikin motarsa, har ya shaƙi numfashi da wannan bordy odour da take da shi.

"Am sorry daddy, I can take her to the school you can send your driver, saboda kafin na ƙarasa
na tabbatar na amayar da kayan cikina."

"You must go and it is an oder." Daddy ya ce tare da juyawa zai fita.

Ganin haka ya tari gabansa cikin tashin hankali."Daddy, you are going to waist your money,
saboda wannan mahaukaciyar nan, da ko alphabets I don't think she can read."

"Ko da ace ba ta iya ba dole zan saka ta, saboda babu yadda za a yi na zauna da ita ba ta
zuwa makaranta, alhalin nawa yaran suna zuwa. Taimakonta zan yi ka san yadda taimakon
maraya yake, don haka ina maka kwaɗayin samun wannan lada.

"Then You can go ahead, amma am not going anywhere."

"You must go bari na ke na yi mata magana ta yi wanka." Ya furta cikin muryar da yake
gasganta masa da umurni ya ba shi.

Yana fita ya kaiwa iska naushi, tare da zama cikin ɓacin rai."Mai ya sanya na zo Kaduna? Da na
san wannan mahakauciyar na nan, babu abin da zai sanya na zo, saboda na tsane ta sosai." Ya
furta cikin takaici.

Tun da Daddy ya ce dole sa ya je, ya san cewa ba shi da mafita, abu ɗaya ya sani yana
dawowa zai koma Abuja.

Ɗaukar turare ya yi, wanda zai rinka fesawa a motar duk bayan minti, kuma ya rantse ba dai a
motarsa zai kai ta ba.

Haka ya zauna cikin takaici kamar zai fashe da kuka. Daddy da ya shiga ciki kai tsaye ɗakin su
Umma ya wuce, ya samo Mommy tana zuba mata ruwa tana wanke jinin da yake zuba.

"Allah sai ya saka mini mugu azzalimi mai kama da zabiya wa..."

"Ke Jimmalo, wa ya gaya miki ana zagin babba? Ɗan'uwanki ne don haka karki ƙara zaginsa
daga yau ya Aliyu za....."

"Da na kira shi da Yaya gara bakina ya sari kashi. Shi ba Yayana bane, kuma zan ci gaba da
zaginsa inhar zai cigaba da mini mugunta. Ni ma soja zan zama na sanya bindiga na harbe shi,
bayan na rama zalincin da yake mini." Ta ƙarashe maganar cikin zallar rashin kunya.

Mommy kasa ce mata komai ta yi ganin yadda take maganar. Sai kuma ta fashe da kuka."Kaka
Tani ki taso ki ga azzalimi nan ya ƙara dukana. Ko yi masa fatalwa ki mayar da shi musaki."

Daddy ne ya yi gyara murya, wanda duk ba su san ya shigo ba. Mommy ta kalle shi tare da
sakin ajiyar zuciya da ƙarfi.

"Ko sanya ta, ta yi wanka Aliyu zai kai ta a sanya ta boko da islamiya, sai daga nan ya kai su
Umma."

Kallonsa suka yi a tare, Jimmalo jin za a sanyata makaranta, ya sanya ta yi masa banzan kallo.
Mommy kuwa jin Aliyu zai kaita.

"Aliyu, ne zai kaita makarantar?" Ta yi masa tambayar cikin razana.

"Makaranta? Aradu babu makarantar da zani har da makarantar arna!" Jimmalo tace tana jijjiga.

Takaici ya sanya Daddy kasa amsa mata, sai ya kalli Mommy ya ce,"Eh, kuma na yi magana da
shi."

"Kar ya je ya kashe yar mutane?" Ta ce a razane.

"Ba zai fara ba, tun da yana da ilmi ya san hukuncin wanda yayi kisa."

"To in ya cutar da ita fa? Kasan Jimmalo, ba kunya ne da ita ba, dole tayi masa abin da zai
harzuƙe shi, sannnan shi kuma bai haƙuri."

"Zan haɗa shi da su Nufaisah, kuma baya haka ya zama dole na kawo sasanci a tsakaninsu.
Ban san lokacin da zan mutu ba, kin ga duk ranar da na kwanta dama Aliyu shi zai zama uba a
gidan nan, in har basa shiri ba zai kula da rayuwarta ba."

"Hmmmmh!" Tace don sam shawarar bai yi mata ba.

"Ki sanya ta ta yi wanka ta canza kayan jikinta, sannan ta fito bari na yi wa su Nufaisah magana
na ga suna falon sama."

Ya yi saurin fita kafin ta gaya masa ba za ta iya ba, domin abin da ya karanta a idanunta kenan.

Mommy kallon Jimmalo ta yi sai ta kasa cewa komai.

"Ki bar kallona, saboda ko sama da ƙasa za ta haɗe ba xan yi wankan nan ba, sannan a mayar
da ni Damagaran."

Dubara ce ta faɗo wa Mommy ta ce,"Kin ga kuma in kika yarda kika yi wankan nan, sannan kika
bi su aka kai ki makarantar kin samu hanya mafi sauƙi da za ki koma Damagaran, kawai
guduwa za ki yi." Ta furta mata hakan, don ta san babu yada za a yi ta samu ta gudu.

Shiru ta yi kamar mai tunani sai can ta nisa ta ce,"Amma ba zan yi wanka ba dakatsami...."

"Ke da an yi magana kice daka tsami za ki yi. Kin san irin warin da kike yi? Zan gaya miki
gaskiya wallahi, in har ba kya wanka Jimmalo mutane gudunki za su rinƙa yi."

"To ni ina ruwana dama ni kaɗai nake son na yi rayuwa." Ta furta ba tare da ta damu da warin
da ta ce tana yi ba.

"Ki yi wankan dai na yau, tun da ana sanya ki a makarantar guduwa za ki yi." Mommy ta ce cikin
rashin dubarar abin da za ta ce mata, wanda zai sanya ta wankan in har ta ƙi.

"To bari na yi wankan, amma na rantse ba zan zauna a gidan nan ba, wancan mugun mai kama
da zabiya yana nan."

Tun da Mommy ta ji ta amince, sai ta nufi hanyar fita kawai don ta gaji da rarrashinta.

Jimmmalo tsaya ta yi cikin takaici, domin an takurata tun da aka ce ta yi wanka. Ita babu abin
da ta tsana kamar wanka. Ta ɗauki tsawon lokaci tana tunanin ta yi ko kar ta yi? Sai kuma ta
rarrashi zuciyarta bayan ta ɓata lokaci.

Miƙewa ta yi tana gungunai ta shiga cikin bayin. Turus ta yi tana kallon bayin da za ta iya kwana
a cikinsa, domin kyawunsa da kyan da ya yi.

Saboda jaraba da safe ba ta shiga cikin bayin ba, tana tashi ta fita zuwa kicin. A maimakon ta
fito ta kira a nuna mata yadda za ta yi amfani da shi, sai ta yi xamanta ta kunna can ta murɗa
can.

Mommy cikin damuwa, ta kira Umma ta zaɓar mata doguwar riga da hijabi mai kyau. Jin shiru
ba ta fito ba sai ta kwanƙwasa bayin.

"Jimmalo, har yanzu wankan kike yi Aliyu yana jiranki ba." Ta yi mata ƙaryar.

Buɗe ƙofar ta yi ta tsaya tare da kama murfin."Ni ban san yadda ake kunna famfon ruwa ya zo
ba, kuma na fasa wankan saboda gaskiya sanyi nake ji."

Mommy ji ta yi kamar ta kife ta da mari. Xuciyarta ce ta harzuƙa domin mace ce mara ɗaukar
raini.

"Ba sai ki kira a zo a nuna miki ba, amma kin zauna a cikin bayi kamar kina ɗaki?"

Tambayar da ta yi ta cikin tsawa sai ta ɓata ranta."A mayar dani Damagaran na yi rayuwa a
kusa da ƙabarin Kakata Tani." Ta ƙarashe maganar cikin muryar kuka kamar wata yarinya.

Mommy watsa mata harara ta yi ji take da ace daga danginta take babu bin da zai hana na ta
kai mata hannu ba, amma duk da haka ba ta tunanin zata iya jurewa.

"Ki je ki yi wankan ni ma na ƙosa ki tafi saboda zama dake sai mara zuciya." Ta furta tare da yin
tsaki ta shiga cikin bayin.

Mamaki sosai ya kamata, ganin yadda ta ɓata ƙaton sabulu guda ɗaya a ruwan buta. Ta buɗe
baki za ta yi magana sai ta ga tana kallonta tana jan majina. Mommy ji ta yi kamar ta saka kuka
saboda har hawaye sun cika idanunta, domin abin da ta yi ko auta ya yi sai ta yi masa shigen
duka. Tara mata ruwan ta yi ba tare data kalle ta ba, sai ta ije mata soson wanka za ta fice
Zuciyar Jimmalo fes ganin yadda ta tunzurata."A mayar da ni damagaran na yi rayuwa a
ƙabarin kaka Tani, saboda ita ce kawai za ta jure halina"

"Dama sai ita da ta ɓata tarbiyarki, ni ma na ƙosa ki koma Damagaran, in ba haka ba sai kin

sanya mini hawan jini.' mommy ta ƙarashe maganar tare da rufe mata kofar.

Ba wani wanka ta yi ba domin datti kawai ta tayar, sannan ta kwara ruwan a jikinta ta fito. Da
ace za a murza jikinta babu abin da zai hana zubar ɗauka, domin ita kanta da ta yi wankan ta
san ba ta wanki ba.

Tana fitowa Nufaisah ta shigo ta kalle ta ta ce,"Mommy, ta ce ga mai da kaya ki sanya."

Harararta ta yi ganin haka ta saki tsaki tana mamakin rashin kunyarta.

Duk da kyawun kayan ba ta sanya su ba, sai ta ɗauki kayan Kaka Tani ta sanya.

"Ni ba zan sanya wannan hijabin ba." Ta ce tare da ɗaukar gyalen Kaka Tani ta yafa.

"Wallahi na yi kyau, sosai kayan Kaka Tani ba ƙaramin ɗaukar jikina yake yi ba. Allah sarki Kaka
Tani na yi rashin Kakata mai ƙaunata." Ta ce lokaci guda idanunta suka kawo ruwa, domin duk
lokacin da ta sanya kayan sai ta ji jikinta ya yi rauni.

"Mommy, ta ce ki zo ki tafi." Umma ta ce sai kuma ta tsaya dariya na son kubce mata ganin
shigar da ta yi.

To Jimmalo za a shiga boko ko ya ya za a yi karatun? Mu je dai zuwa mu ga yadda za ta kaya.
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0


*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*


MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423



PAGE 19



*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso
kusa kar ayi* *babu ke*

*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*

*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*

*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*

*Iya adadin da kuke so muna turawa*

*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da
hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login