Showing 81001 words to 84000 words out of 90573 words
Chapter 28 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
ransa ya ɓaci sosai ganin yadda iyayen yaron suka yi fushi. Zai iya cewa tun da yake a
makarantar, wannan karon na farko kenan da ya faru.
Daddy hankalinsa ya tashi sosai jin yadda yake magana cikin fushi. Duk haƙurin da yake ba shi
bai saurare shi ba ya kashe wayar. Dafe kansa ya yi cikin takaici jin abin da ta yi.
Kan dole ya baro kasuwan ya dawo hankalinsa a tashe. A lokacin da suka iso gidan, Maigadi ya
shiga ya kira Mommy. Cikin fargabar wanda ke kiran ta fito ita.
Tana fitowa ta ga Jimmalo ta ci kika tana zare ido. Gabanta ne ya faɗi sosai ta kasa ƙarasawa
gurin. Sai da ta ɗan ɗauki lokaci cikin rashin madafa, sai ta ƙarasa tana faɗin,"Sannunku bayan
Allah. Jimmalo mai kika yi?" Ta yi tambayar tana kallon Principal ɗin da ya ci magani.
"Yarinyar nan ba ta da mutunci ta karya yaro."
Salati ta saki sai ta rasa abin da za ta ce. Tana cikin wannan jimamin sai ga motar Daddy. Wani
irin ajiyar zuciya ta saki ganinsa, domin ba ta san abin da za ta ce ba.
Daddy parking ya yi sannan ya fito cikin motar cikin damuwa.
"Jimmalo, ba kya jin magana ko? Saboda me za ki karya shi?" Ya yi mata tambayar, daidai
lokacin da Captain ya sanya maigadi ya buɗe masa get zai fita.
Ganin Daddy a gurin da Mommy ya tabbata ba lafiya ba, musamman yadda fuskokinsu suke
ɗauke da tashin hankali.
"Wannan sheɗaniyar yarinya mai ta yi?" Ya furta a ransa sannan ya fasa shiga cikin motar ya
ƙarasa gunsu, daidai lokacin da ta ce,"Tonona ya yi ni kuma na yi masa ƙufula ɗaya."
Dukanninsu babu wanda ya gane hausar da ta yi musu. Jin abin da ta ce Aliyu ya kawo mata
mari ba tare da ya ji abin da ta yi ba.
"Akwai sa'anki a gurin nan? Da za a tambaye ki ce kin yi masa ƙufula. Uban mene ne ƙufula."
"Ɗaga shi na yi na maka shi da ƙasa."
"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un! Kika ɗaga ɗan mutane kika maka da ƙasa kamar dutse?"
Daddy ya yi tambayar cikin damuwa.
"Ai dole ki karya shi. Yaro ɗan primary one!" Mommy ta jinjina kanta tana faɗin haka.
Aliyu zare idanunsa ya yi ya ce,"Ta karya yaro fa kuka ce?"
"Karya shi ta yi, kuma babu ruwan mu da hukuncin da iyayen yaron za su ɗauka, sannan mun
koreta daga makarantar." Jin abin da ya ce sai ya harzuƙa Aliyu. Da sauri ya kama hannunta
yana faɗin,"Tun da kika karya yaro saboda rashin imaninki. Nima sai na karya ki." Kafin su yi
aune ya murɗa hannunta da ƙarfi.
Wani irin ƙara ta saki jin zafi yana shiga ƙwaƙwalwarta.
"Aliyu lafiyarka kalau, in ta karya shi ka ma sai ka ƙaryata?" Daddy ya yi masa tambayar cikin
ɓacin rai tare da daka matsa tsawa.
"Zalinci ta yi dole a rama masa. Shashashar banza daƙiƙiya ko kunyar ba kya ji. Kina cikin
ƙananan yara, ba dole ki yi zalunci ba."
"Wayyo Allah! Mugu kawai azzalumi. Wallahi ya karya mini hannu." Ta furta tare da saka ihun
da sai da suka matsa.
"Aliyu, kar na ƙara ganin haka in ba sulhunta zancen za ka yi ba, maza ka bar gurin nan."
Daddy ya ce masa yana nuna masa hanya.
Babu musu ya juya domin bai zo don ya sulhunta. Abin da ya kawo shi ya yi zuciyarsa fes ya
shiga cikin gidan don ya shiga mota.
"Yaron nan ba shi da imani da gaske ya karya ta." Cewar Mommy ganin yadda take ihu domin
ko ba karaya bane, tabbas ya yi mata tsaguwar kashi ko targaɗe.
Principal sai ya tsaya cikin mamakin abin da Aliyu ya yi, sannan ya tafi ba tare da tausayi ba.
"Ni fa ban kawo muku ƙara ba, don ku ƙaryata. Ku dai shirya duk matakin da iyayen yaran za su
ɗauka." Ya ce ma Daddy yana kallonsu.
"Tare zamu tafi asibitin gurin yaron. In sha Allahu zan sasanta lamarin. Mommy ki shiga da ita
ciki, ki sanya direba ya kaita a gyara mata hannun." Ya ce mata yana kallonta.
Jin abin da ya ce sai ta kama hannu Jimmalo da take ta ihu tamkar an kashe ta.
"Wayyo hannuna ya karya ni kaka Tani." Ta furta tana kallon hannun da har ya fara tasawa.
"Mu shiga ciki ko ranki ya ɓaci. Ai kin cancanci haka tun da shi yaron da kika karya ba mutum
bane. Haba Jimmmalo wallahi ba kya jin magana." Mommy ta daka mata tsawa tana faɗin haka.
"Wallahi sai na rama, tun da ya karya mini hannu sai nayi masa tabon da ba zai manta da ni
ba." Ta furta tana ɗaga hannunta da yake raɗaɗin zafi.
"Ba kya ji ko? Zuwa zaki yi ki ƙara takalarsa. Allah ya ba ki sa'a kin san ke za ki wahala." Ba ta
ce mata komai ba, tana kuka ganin haka sai ta kama hannunta suka shiga ciki.
Anty da take juye abinci a kula ta ji kukanta yana tashi, Mommy na yi ta mata faɗa, wanda ya
sanya ta rufe ƙular da sauri ta fito suka yi magama a falo.
"Subuhanallahi! Ciwo ta ji?" Ta furta tare da isa gareta ta kama hannun.
"Yarinyar nan tsaf za ta iya kashe mutun da mugun halinta. Zuwa ta yi ta karya yaron mutane.
Shi ne masu makarantar suka kawo ƙara. Shi kuma Aliyu ya karya ta ita ma."
Salati ta saki tare da zare idanu. Sai ta rasa cikinsu wa yafi rashin imani.
"Jimmalo, da gaske kin karya yaro? Shi kuma Aliyu yana da hankali kuwa?"
"Na rasa hukuncin da zan yanke. Yaran nan so suke su kashe ni." Ta furta tare da zama kan
kujera. Fuskarta bayyane da damuwa dake xuciyarta.
Ganin ihun da ta ishe su da shi. Kan dole ka je asibiti aka gyara mata hannu. Mamakin kukan
da ta yi suke yi, saboda targaɗe ba karaya ko tsaguwar kashi ba.
"Idan ke kina kuka haka, shi kuma yaron da kika karya sai ya mutu ko?" Anty ta yi mata
tambayar tana kallon hannun daya suntuma.
"Rashin kunya ya yi mini kuma na gaya musu zan iya karya shi."
Tsaki suka saki a tare ba tare da sun ce komai ba, domin kowa ta kai shi wuya.
Da suka koma gida, tana ta kuka da ƙyar Anty ta rarrasheta sannan ta ji abinci. Da ta tuna an
koreta a makarantar, sai hankalinta ya kwanta ta daina jin zafin ciwon, amma ta ɗau alwashin
tun da ya ƙaryata, sai ta yi masa abin da ba zai manta ba.
Tana zaune har sauran yaran suka dawo. Nan suka yi mamakinta sosai domin ta wuce
tunaninsu. Hanifa da Mufida da suka dawo gidan ƙawarsu, sun cika da mamakin abin da ta yi.
Da ƙyar Daddy ya samu aka kashe zancen, bayan ya biya kuɗin da aka kashe, sannan ya toshe
bakin iyayen da kuɗi. Yana asibitin har sai da aka yi kiran sallah. Sam ya manta da batun abinci
saboda samuwar da yake ciki. Abin da ta yi sai ya ci alwashin sai ya yi mata dukan tsiya, amma
sai kuma Aliyu ya yi hukuncin mahaukata.
Da ya dawo, faɗa sosai ya yi mata kamar zai aro baki. Ita dai hankalinta a kwance. Burinta ya
ce ba zai iya zama da ita ba, sai a a haɗa ta da Anty Amarya ta koma gidanta. Tana wannan
tunanin sai ta ji ya ce,"Dole ki koma makaranta, domin ba za ki rayu da jahilci ba
Ko islamiya har na siya miki form. Jira na ke a yi miki ɗinkin kayan islamiya da hadda."
Wannan mummunar albishir da ya yi mata ya sanya xuciyarta ɓaci. Fuu ta yi ɗaki ta faɗa kan
gado. Kuka ta ci gaba da shi, babu wanda ya kula ta har Anty Amarya saboda ita kanta
haushinta take ji.
Anty Amarya da take tunanin za ta fito amma shiru. Ganin haka ta ɗauki abincinta ta shiga
dakin."Ki tashi ki ci abinci."
Tana kwance ba ta motsa ba jin abin da ta ce."Sam ba kya ji Surfy. Ba za mu shirya ba in har
kika ce rashin ji za ki yi."
Ita kanta sai ta yi mamakin rashin jin daɗin da ba ta ji ba, da furta hakan domin ko lokacin da
Kaka Tani take nan ba ta damu ba don ta yi fushi.
"Shi ne ya tone ni."
"To sai ki karya shi?" Ta yi mata tambayar cikin ɓacin rai.
Ganin yadda fuskarta ya bayyana damuwar fushinta sai ta hau kan gadon."Kar na ƙara jin kin yi
haka. Maza ta shi ko ci abinci. Kin ga ga shi kin ja Aliyu ya ji miki ciwo."
Har ta buɗe baki za ta yi magana, sai ta ga rashin dacewar sanar da ita abin da za ta yi masa,
domin ta san a ƙarshe cewa za ta yi kar ta yi. Ita kuma ta rantse sai ya yi kukan da ya fi nata.
"Ki ci abincin." Ta furta tana kallonta
Babu musu ta janyo filet ɗin za ta sauka ƙasa, wanda ganin haka ta taimaka mata ta saukar da
abincin kasa.
Anty Amarya sai da ta tabbatar ta ƙoshi, sannan ta kaya zuwa falo suna kallo.
Mufida damuwa sosai ta shiga ganin har ana gobe za su tafi ba ta samu hanyar da zata sa
mishi maganin ba. Tana wannan tunanin duk suna falo sai aka kira Mommy a waya.
Kamar ance ta saurara sai ta ji tana faɗin,"Ok, yanzu za ta kawo maka har da ruwan tea da na
dafa maka."
Tana kallonta har ta kashe wayar ta kalli Umma ta ce,"Yayan ki ya ce ki kawo masa abinci,
sannan ki juye ruwan shayinsa a fulas."
Da sauri ta tashi jin abin data ce. Ganin haka sai Mufida ta bita zuwa kicin ɗin.
Tana ƙoƙarin juye ruwan flaks sai ta shigo."Na ga ba ki so ki taso daga kallon ba. Ki kawo na kai
mishi sai ki je ki ci gaba." Ta furta cikin murmushi da sakin fuska.
"Wallahi, da yake ina son na kalla ban ga na wannan satin ba, amma kar ki damu zan kai
mishi." Ta ce da ta tuna zai iya mata faɗa.
"Don Allah ki bani na kai masa, dama ina son nayi masa maganar ya biya mini kuɗin
makaranta, saboda wannan semester Baba ya ce ba shi da kuɗi ne tambaye shi."
Ɗan jim ta yi, domin ta san da wuya in haka ne. Tsoro take kar ta je ta yi masa kwarkwasa,
saboda ta san tana son sonshi, amma tun da ta roƙa babu yadda za ta yi.
"Ok, ga shi sai ki haɗa masa da ruwan tea."
"Ok, na gode. Bari na nemi tawul na ƙara gogewa kin san yayan namu mai tsafta ne."
"Da yake kular a tsaftace take, amma ni dai na tafi kallona ke kika sani." Ta ce mata tare da
ficewa da sauri tana ja mata ƙofa.
Fitan ta yi sai ya yi mata daɗi sosai, da sauri ta ciro ƙunshin maganin da tun da ta zo da shi take
yawo da shi, amma ba ta samu hanyar sakawa ba.
Tana ƙoƙarin zubawa Jimmalo da ta ji tana son shan ruwa, sai ta nufo kicin ɗin don ta iba a
famfo, domin duk frij ɗin gidan ba ta iya buɗewa ba.
"Kai! Uban wa za ki kashe?" Ta ji ta yi mata tambayar da ya razana ta, wanda ya sanya ta juyo
da sauri cikin tashin hankali, amma kuma ganin Jimmalo ce sai hankalinta ya ɗan kwanta kamar
ta yi baƙo ya mutu, domin sam ba ta ɗauke ta a masu hankali ba.
Kasa amsa mata tambayar ta yi, tana in'ina wanda ganin haka ta ce,"Na rantse sai kin gaya
mini ko na gaya wa mutanen gidan, domin tun da kika zo ban yarda da ke ba, sai wani zare
idanu kike yi, sannan kina kallon Anty Amarya a yatsine in tana magana da Hanifa."
Sosai ta yi mamakin abin da ta ce, saboda ba ta taɓa tunanin za ta iya gane hakan ba.
"Tun da ba zaki gaya mini ba, sai na gaya wa mutanen gidan."Ta ƙarashe maganar tare da
wage baki za ta yi ihu
Da sauri ta toshe mata baki ta ce."Ba fa kisa zan yi ba. Ni musulma ce da imani."
"To me kike sawa a abincin!" Ta jefa mata tambayar.
"Abincin Ya Aliyu ne kuma ma...."
"Kashe shi za ki yi? In har kashe shi za ki yi ba zan damu ba, domin babu amfanin rayuwar
mugu azzalimi." Ta furta abin da Mufida ta karanta har cikin zuciyarta, wanda ya sanya ta
ce,"Eh, ka.sh..e shi zan yi saboda kamar yadda yake miki mugunta haka ya yi mini."
"To me kike jira ki sanya masa maganin da yawa, yadda da yaci zai fara shure-shure, domin na
tsane sa da zan samu dama zan iya kashe shi." Ta furta tare da rufe mata kofar cikin farinciki.
Mufida sai ta cika da mamaki sosai jin bin da ta ce. A yadda ta nuna a fuskarta da gaske ba za
ta gaya wa kowa ba. Mamaki sosai na tsanar da suke wa junansu. Cikin kwanciyar hankali ta
saka maganin ta ɗauka.
Gabanta na dukan tara-tara ta kwanƙwasa ƙofarsa. A tunaninsa Umma ce don haka ya ce,"Yes,
come in."
Yana zaune daga shi sai gajeren wando babu riga. Gefensa abokinsa Imran yana danna
wayarsu suna hira.
Ɗaurewa ta yi ta shigo. Ganin yadda yake sai jikinta ya kama rawa ta kasa ƙarasawa.
Captain Aliyu yana kallon wayarwa ya ce,"Umma, ije Allah ya sa kin zuba da yawa, na manta na
ce miki ina tare da Imran, duk da ba da...." Maganar ta maƙale masa lokacin da ya ɗago ya ga
Mufida ce.
"Ke! Are You stupid?" Ya ce mata tare da miƙewa yana zare mata idanu.
Ganin yadda ya daka mata tsawa sai ta ije abincin ta fice da sauri.
Tsaki ya yi ya zauna."Yarinyar nan ba ta da hankali, amma zan koya mata." Ya ce yana hararar
abincin.
"Hmmmmh. In dai ka ga kare na shinshinan takalmi dauka zai yi." Ya ce tare da jawo abincin ya
fara ci.
"Ashe kuwa iska na wahalar da mai kayan ƙara." Ya furta tare da komawa ya zauna, ba tare da
ya kalli abincinba domin ya fita ransa.
Imran ya ci abincin sannan ya tashi ya tafi. Bayan ya raka shi ya kira Umma ta kwashe
kwanukan.
Mufida,cikin fargabar kar su ci abincin su biyu ta fice daga ɗakin. Duk yadda ta damu da ta
sanya maganin, amma xuciyarta ba ta yi farinciki da samun nasarar sakawa da ta yi ba.
Falo ta dawo ta zauna, xuciyarta cike da tsoron kar Jimmalo ta gaya musu, amma sai ta ga
babu abin da ya dame ta, sai kallonta da take yi, so take tambaye ta ko ta sanya.
Fuska ta daure ta mayar da hankalinta kan tibi, amma sai da ta san yadda ta faki idanun
mutane ta koma gefenta ta zauna cikin raɗa ta ce,"Kin sanya mishi?"
Duk da raɗa ta yi mata, sai da ta zare idanunta tana kallon mutanen falon. Ganin hankalinsu
bashi a kansu sai ta kalle ta da tayi mata ƙuri, xuciyarta na addu'ar Allah ya sanya ya mutu a
yau.
"Eh na sanya maganin amma a hankali zai shiga jikinsa."
"Da kin sani wanda zai ci nan take ya fara shure-shure kika siya." Ta furta xuciyarta a ƙuntace ta
koma gurinta ta zauna.
Hamdala ta yi, tare da sauke ajiyar zuciya ganin ta koma gurin da take zaune, a xuciyarta
mamaki take yi domin Jimmalo ta wuce a kira ta mahaukaciya.
Da safe bayan sun karya suka fara shirin komawa. Tun da Jimmmalo ta fahimci hakan, sai ta
fara haɗa kayanta ta kafe kan dole tare za su tafi. Nan fa aka shiga dirama musamman a
lokacin da suka fito. Duk rarrashin da ta yi mata ta kafe kan dokin na ƙi.
Da ƙyar Anty Amarya, ta samu ta shawo kanta bayan ta yi mata alƙawarin da zarar sun yi hutu
za ta kira a kawo ta yi hutu. Sai kawai ta fashe da kuka ta faɗa jikinta domin har xuciyarta take
ƙaunarta. Ita ma rungume ta tayi tana jin tausayinta don jinta take yi kamar Surfy ƙanwarta da
suka fito ciki ɗaya.
Tana rarrashinta rungume da juna, a haka Aliyu ya fito da makullin mota yana karkaɗawa. Yayi
kyau sosai, domin in har da abin da yafi kyau za a iya fasalta shi da shi.
Kasancewar in ya kaisu Kaduna zai wuce Abuja, sai ya shirya cikin kayan sojoji. Kayan sun yi
masa matuƙar kyawu sosai. Yana riƙe da wayarsa, da makullin mota sai glass ɗinsa da yake
ƙoƙarin sanya wa.
Ganin su a haka ya dakata tare da daka wa Jimmalo tsawa."Haba Anty! Wannan kucakar
yarinyar za ki bari ta shiga jikinki? In har kina son mu shirya gaskiya ki daina kula ta." Ya furta
tare da watsa mata mugun kallo yana bata fuska.
Sakin juna suka yi Jimmalo ta watsa masa mugun kallo."Anty Amarya, don Allah kar ki manta
alƙawarin ki?" Ta ce tana share hawaye.
Murmushi ta yi tare da ɗauke mata hawayen ta ce,"Ba zan manta ba 'yar ƙanwata, amma ki
tuna na gaya miki kar ki rinƙa sanya wa Mommy damuwa?"
"To," Ta furta a sanyaye.
Tsaki ya saki ya shiga cikin motar, tare da sakin musu hon babu ƙaukautawa.
Mufida da Hanifa,