Showing 27001 words to 30000 words out of 90573 words

Chapter 10 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8070

yi wanka, saboda in har ba ki ba ni kuma ba za ki ci ba."

Baki ta buɗe za ta yi kuka, sai kuma ta fasa tana kallon Kaka Tani."Kaka Tani kina jin abin da ta
ce, ki gaya mata gaskiya, saboda kin san ko sama da ƙasa za ta haɗe ba xan yi ba."

"To zan gaya mata kar ki yi kuka kin ji." Ta furta cikin sigar rarrashi, sai kuma ta kalli Hajiya da ta

yi sororo ta kasa magana, saboda tsananin haushinta da takaici.

"Hajiya jarabar kafiya ce da ita in har ta ce baza ta yi ba, sam ba za ta yi ba ko zan kashe ta. Da
ina dukanta, amma da na ga halinta ne sai na haƙura. Addu'a kawai za ki taya ni da shi."

Kallonta ta yi, ta kasa cewa komai zama ta yi tare da ƙwalawa mai aikinta kira.

Da sauri ta fito ta ce,"Hajiya ga ni."

"Ki kawo musu abinci."

"To," Ta amsa tare da shigewa cikin kicin ɗin.

"Kan buta uba! Wallahi nan daga jin ƙamshin abincin, zai yi mugun daɗi kin ji ƙamshi Kaka
Tani?"

Zare ido ta yi jin ashar ɗin da taƙunduma ta kasa cewa komai.

"Na ji jikalle ta ke dai bari 'ya birni suna hutawa."

Tun kafin ta ije abincin, Jimmalo ta yi kanta tare da kwace tiren da a'a shirya abincin. Ƙasa ta
saukar da shi."

Ganin haka Hajiya ta yi maza ta ce,"Ku zo mu je dinning ba a cin abinci a nan?"

"Jimmalo me take cewa kamar dannin kara take cewa?" Ta yi wa Jimmalo tambayar tana haɗiye
miyau ganin ta buɗe lafiyayyen dafadukar shinkafa da ta ji nama.

"Ni ma ƙila dannin kara take nufi." Ta ƙarashe maganar tare da kai hannu ta ibo shinkafar da
nama.

"Wayyo dadi."Ganin haka Kaka Tani takai nata hannun ta iba.

Asibi da ta kawo cokali da abin zubawa, ganin yadda suke kai loma sai ta tsaya kawai tana
kallonsu.

Jimmalo loma take kai wa hankalinta kwance tana santin abincin. Hajiya sai ta shiga mamaki
ganin yadda ta kusa cinye abincin. Sai da ta ga ta cinye komai, sannan ta saki gyaza babu tsari.
Shafa cikinta ta yi tana faɗin,"Aradu zaman birni duniya ne. Kaka Tani ba za mu koma ƙauye
ba."
"A'a Jimmalo dole mu koma saboda ba zan iya barin ƙauye ba."

"Ki koma ke kaɗai amma ni na ga gidan zama." Ta ce tare da murje abincin da ta ci a jikin
kujera.

"Ke Jimmalo lafiyarki kuwa? Kin ci abinci a madadin ki wanke hannu, sai kuma ki shafe jikin
kujera?"

"Hajiya ba ki ga na murje hannun nawa ba, kuma sannan sai da na shafa a gwiyar hannuna don
na samu albarka."

"Tabɗijam!" Ta furta don ta kasa cewa koma.

Suna zaune sai surutu suke yi suna yaba kyawun gidan.

Hajiya sororo ta yi tana kallon Jimmalo da magana ɗaya, sai ta saki ashar sannan da ƙarfi take
yin maganarta.

Sai ta cika da mamaki take ta ga abin da Daddy ya gaya mata.

"An kira sallah bari na shiga ciki na yi sallah, kuma ku tashi muje na nuna muku masaukinku sai
ku yi sallah."

"Gaskiya ba zan iya sallah yanzu ba, saboda gabakiɗaya jikina ciwo yake yi. Zan bari ina zo
kwanciya so na haɗa duka." Ta furta tare da mike ƙafa tana hamma, alamun bacci za ta yi,
domin dai ta faɗi haka ne a idanun Hajiya.

Hajiya sai ta kalli Kaka Tani a tunaninta za ta yi magana, amma sai ta ga ta yi dariya ta ce,"Allah
ya sa in kin zo kwanciyar ki yi, saboda na san halinki yadda kika san aljihun baya haka kike."

Zuwa yanzu ta daina mamakinta sai al'ajabi."Tani yanzu irin tarbiyyar da kike ba ta kenan?
Wannan ƙatuwar budurwar amma ba ki koya mata sallah ba?"

"Ya zan yi Hajiya? Wallahi ina ƙoƙari sosai a kanta, kawai shegen kafiya ne da ita. Kuma kin ga
ita kaɗai ta rage mini in ban kula da ita ba wa zan kula da shi?"

"Hmmmmh! Haka ne." Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta yi cikin ɗaki cikin mamakin rayuwarsu.

Bayan shigarta ciki Kaka Tani ta kalle ta ganin ran Hajiya ya ɓaci."Jimmalo ki yi sallar don Allah
kar ta ga ba ki da kunya. Kin ga ita babba ce."

"Ai na ce zan yi da ma ban gaya mata ba zan yi ba. Ni kawai na fi son na yi sallah a lokaci guda
ba wai na yi tsugul-tsugul ba."

"To shikenan Allah ya shirye ki. Jimmmalo da ba na yin Sallah sai ace halina kika ɗauko."

"Ni ma ai ba wai ba na yi bane in zan kwanta zan yi." Ta ce tare da sakin hamma ta kwanta sai
bacci.

Kaka Tani ciki inda aka nuna mata ta shiga. Bayan ta yi sallah, sannan ta zauna tana ta kallon
gidan cikin mamaki.

Jimmmalo ba ta tashi ba sai karfe huɗu, saboda gajiyar hanya da ta yi. Da ta tashi kai tsaye
kicin ta nufa."Yunwa na ke ji ki zuba mini abinci, saboda shegen rowarki da aka ce ki kawo
mana kaɗan kika zuba."

Mamaki sosai ya kamata jin abin da ta ce, domin abincin da ta ci ko wani gardi ba zai ci shi ba.

Ganin ta yi tsaye tana kallonta sai kawai ta wuce gurin ƙular binci. Ɗauka ta yi zuwa falo ta
zauna.

Hajiya ta yi mamakin rayuwar da Jimmalo take yi, saboda da dadddaren ba ta yi sallah ba ta
kwanta. Babu yadda ba ta yi da ita ba, don ta kashe kallo ta yi sallah, amma ta ƙi Kaka Tani
kuwa sai dariya ta ke yi tana faɗin,"Hajiya ba ki ga komai ba."

Miƙewa ta yi ta kashe kallon ganin har sha biyu ta yi."Ki je ki yi sallah ki kwanta gobe sai ki ci
gaba."

"Ni fa so na ke yi na ƙarashe kallon him ɗin nan."

"Ki bari sai gobe dare ya yi." Ta ce mata bayan ta kashe kallon.

Ba don ta so ba su dai don babu yadda za ta yi. Miƙewa ta yi tana hamma ta wuce cikin ɗaki.
Tana zuwa ta faɗi kan gadon tana cewa,"Wayyo yau zan kwana a gadon 'yan gayu."

Kwanciya ta yi, da kayan jikinta ba tare da ta ɗauki tsawon lokaci ba sai bacci mai ƙarfi ya
kwashe ta.

Tun da ta zo gidan ta zamar mata ciwon kai, saboda duk yadd ta yi don ya yi wanka ta ƙi. Tun
tana ganin lamarin na ta wasa ne har ya wuce tunaninta.

Mamaki take yi sosai yadda take iya rayuwa. Ganin yadda take tashi da wari, sannan kanta kan
shi abin ƙyama ne. Kullum tana cikin kaiwa kan rankwashi. Da susa kamar mai ƙazzuwa.
Sannan inda ta ci abinci nan za ta tashi ta bar shi. Kuma ba ta wanke hannu in za ta ci haka in
ta gama sai da ta goge a kayanta ko kujera.
Washegarin da suka zo ta siyo mata brush, amma babu yadda ba ta yi da ita ba ta ƙi yi. A
cewar ta jini zai zuba a bakin nata, ita kuma sam ba ta ƙaunar ganin jini a jikin wani ballantana

nata.

Lamarin na ta sai ya ba ta mamaki, babu sallah babu hankali sai zagi kamar jikar maguzawa.
Ko kallo take yi ta rinƙa ashariya kenan tana zargin wanda ya ba ta haushi. Gabakiɗaya
rayuwar da take yi babu tsari da hankali a ciki.

A ɗaki ta samu Kaka Tani cikin tsananin ɓacin rai."Kina tunanin rayuwar da kika ginata akai shi
ne gata? A haka za ta yi rayuwa kamar ta dabbobi. Ita fa mace ce aure za ki yi mata. Wane ne
zai kalle ta da sunan zai aure ta. Yarinyar ba ta da maraba da mahaukaciya. Gaskiya Tani kin
cuci yarinyar nan saboda tarbiyyar da kika ɗora ta a kai, babu nagarta wallahi yarinyar nan sai
ta yi kuka da ke. Ba ilmin addini babu boko. Gata ƙazamiya sannan sai shegen kafiya da rashin
kunya. Kina gani na yi mata maganar sallah tsaki ta yi mini har da harara, amma ba ki ce komai
ba, sai ma ita kike rarrashi. Jimmalo watarana uwa za ta zama, ita ce za ta tarbiyanci yaran da
za ta haifa."

"Ya kike so na yi? Yarinyar nan ita ce kaɗai gare ni. Har gobe in kuka domin ba ta da kowa sai
ni, sannan a ƙauyen kowa ya tsane ta. Ni ce kawai na ke sonta. Dole na ƙaunace ta domin na
san cewa na kusa mutuwa, ganin tsufan da na yi. Har yau ina tuna zan mutu na barta babu
kowa a duniyar ina shiga cikin tashin hankali." Ta ƙarashe maganar cikin kuka.
"Dole ki yi kuka, amma ba wannan ya kamata ya sanya ki kuka ba. Kuka za ki yi saboda ba ki
ba ta tarbiyya ba, in kika mutu babu wanda zai iya ɗaukar ta. Wallahi a yadda yarinyar nan take
babu wanda zai zo ya ce yana sonta."

"Ni ma ba zan so kowa ba." Jimmalo ta katseta tana faɗin haka da ta shigo.

Kallonta Hajiya ta yi jin abin da ta ce. "Ba zan yi aure ba, domin maza ba su a gabana da zan
wahalar da kaina sai na yi tsafta. A haka nake son rayuwata kuma ina jin daɗinta. In har kin gaji
da zamanmu bai sai kin yi mana kora da hali ba, za mu tafi saboda ni ma na gaji da takura ni da
kike yi."
Kallonta ta yi ganin yada take maganar babu ɗa'a.

"Kaka Tani ki zo mu bar gidan nan tun kafin ta kore mu. Dama na lura ta fara mana kora da hali.
Ina je zan ci abinci sai ta ce kar a bani sai na yi sallah."

"Ki bari mu gama kwanakin da muke ce za mu yi."

"A'a mu tafi kawai saboda ni da jikina ba za ta rinƙa sanya ni dole na yi wanka ba."

"To shikenan za mu tafi, amma ki bari mu ƙara kwana biyu."

Shiru ta yi bata ce komai ba, domin ita kanta ba ta son tafiyar, barazana take yi mata don ta

daina takura mata da maganar sallah da wanka.

Hajiya kuwa sai ta yi shiru tana ganin lamarin yafi ƙarfinta. Ita da take son su haɗu da Kaka Tani
su canza mata rayuwa.

Juyawa ta yi ta fita daga ɗakin jikinta a sanyaye.

"Jimmalo ki rinƙa sallah da wankan don Allah har mu gama kwanakin da zamu yi."

"Ni fa ba zan yi ba domin babu wanda zai yi mini dole."

"Kin dai san wanda ba ya sallah ɗan wuta ne?"

"Na sani amma da manya ake yi ni kuwa guda nawa na ke?"

"Kin girma saboda sa'anninki duk suna ɗakinsu."

Banza ta yi da ita ta kwanta, ba tare da ta ce mata komai ba. Ganin haka ta ci gaba daban
carbinta da take ja, wanda in aka tsareta ba za ta iya faɗin abin da take cewa ba.

Iya kwana huɗu suka yi, amma ji take kamar sun shekara, saboda yadda Jimmalo take sanya ta
magana. Saboda yawan maganar da take yi har zazzaɓi ta kwanta. Daddy da ta kira shi tana
ƙorafi haƙuri ya bata, don abin da yake mata gudu kenan, amma ta na ce sai ta je ta ɗauko su.

Captain Aliyu saboda ɓacin rai da ya shiga da suka je ƙauye Damagaran, bai yi hutun da yake
don yi ba ya tattara ya koma Abuja.

A ranar da ya isa, ya buɗe wayarsa da ya kashe saboda kiran da Lubaynah ta dame shi da shi.

Tana kwance a falo wayarta ce a hannunta tana kallon hotonsa. Ji ta yi kamar ta yi kuka,
saboda kewarsa da ta yi. Ta san cewa sojanta gwarzo ne kuma namiji ne da ya amsa sunansa
ta ko ina. Tana ma wani irin ƙauna na mutuwa, amma a yadda ta fahimce shi kamar ba zai iya
auren ta ba. Muskutawa ta yi, cikin damuwa tana jin a ranta ba za iya iya barin ya auri wata ba.
Numbarsa ta kira duk da ta san ba za ta samu ba, amma cikin mamaki ta ji ta shiga. Saboda
tsananin farinciki miƙewa ta yi tsaye.

Yana zaune a falo ya ɗora ƙafarsa kan stool. Sigari ce a hannunsa yake sha. Tun lokacin da ta
yi mishi rashin mutuncin ya kasa mantawa. Yanzu ma haka ji yake kamar ya bi shawarar da
zuciyarsa take ba shi. Ya je ƙauyen cikin dare ya harbe ta. Ya tsaneta bai taɓa jin abin da yake
ƙyama kamarta ba. Ba ya fatan ko a lahira Allah ya nuna masa ita. Babu abin da ya fi tsana ya
kalla a fuskarta irin haƙoranta, domin da ya kalla sai da ya ji tamkar zai amayar da kayan
cikinsa. Tun da yake a rayuwa bai taɓa ganin ƙazamiya mara tsafta da tarbiyya kamar ta ba.

Wayarsa ce ta yi ƙara. Gajeren tsaki ya ganin Lubaynah ce. Daƙile kiran ya yi yana mamakin
rashin zuciyarta. So yake ya yarda ƙwallon mangaro ya huta da ƙuda. Sam ba ya son in ya yi
aure matarsa ta gane halinsa, wannan dalilin yake son ya rabu da ita, tun kafin ya samu mace
natsatstsiya kuma mahaddaciyar Alkur'ani, wacce za ta ba wa yaransa tarbiyya.
Yana wannan tunanin da inda zai samo ta, sai kiran ta ya ƙara shigowa. Wannan karan kamar
zai yi jifa da wayar, sai ya fasa ya ɗauka cikin tsawa ya ce,"Why are you pestering me?"

"Sojana." Ta ce tare da fashewa da kuka a maimakon ta amsa mishi.

Banza da ita ya yi tare da jan tsuka."Lubaynah let's face the reality am done." Ya ce mata ba
tare da tausayinta ba.

Jin abin da ya ce, sai ta saki kuka sosai domin ta san cewa abin da yake shirin yi kenan."Ka yi
mini adalci kenan? Ina sonka ba zan iya rabuwa da kai ba, kuma kai ma ka san haka."

Fesar da numfashi ya yi cikin takaici. Baƙincikin ranar da ya haɗu da ita ya yi, ganin ta zame
masa kaska. Ko ya yi ninyar rabuwa da ita don ya zamo na gari, amma sai ta san yadda ta yi ta
dawo cikin rayuwarsa. Yanzu hakan ma ƙoƙarin saukko da zuciyarsa take yi, saboda kukan
kissa da kalaman da take gaya masa.
"Kin san ina sonki ko?" Ya yi mata tambayar ba tare da ya shirya ba.

"Na sani Sojana. Ni shaida ce na san haka."


Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*


MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423



Tallah

Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin
result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka
sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan
ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama
kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast

Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta
wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na
gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da
ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina
shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606
ina zaune a kano

PAGE 9

"Kin san ina sonki ko?" Ya yi mata tambayar ba tare da ya shirya ba.

"Na sani Sojana. Ni shaida ce na san haka."

"Saboda me za ki damu sai na aure ki? Na gaya miki ban shirya aure ba, in har kin matsu You
can

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login