Showing 51001 words to 54000 words out of 90573 words
Chapter 18 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
tashi kafaɗunki don ki ci gaba da rayuwa da jikarki, saboda kin san babu
wanda zai iya da ita sai ke.
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 15
Miƙewa ta yi jin abin da ta ce ta fita. Bayan ta yi mata kamun, sai ta kasa tafiya ganin halin da
take ciki.
"Wash! Jimmalo, mutuwa zan yi ki zo mu yi bankwana." Haka Kaka Tani take faɗi, hawaye yana
zuba ƙuncinta tana tausayin rayuwar Jimmalo.
Audi mai kyamis ya shigo ya sanya mata ruwa, sannan ya yi mata allura. Kallonta yake yi ya
ce,"Yaushe ta fara wannan ciwon?" Ya tambaya yana kallonta yadda ta koma.
"Shekaranjiya ne kuma na bata bauri."
"Ina ganin in dai ruwan nan bai yi ba dole kaita asibitin birni, saboda gaskiya tana buƙatar kula
da magunguna."
"Na shiga uku! Kaka Tani ciwo lokaci guda? Kar dai mutuwa za ki yi ki barni?" Sai hawaye shar
ganin yadda take nishi da ƙyar.
Tana zaune a gefenta tana ta share hawaye. A maimakon jiki ya yi sauki sai ya ƙara zafi, domin
har jijjiga take yi jikinta kamar tukubar mai tsire. Ganin haka hankalinta ya tashi sosai, ta koma
ta kira Audi mai kyamis
"Jimmalo, akai Kakarki birni gaskiya ciwonta ya fi karfin kulawata."
"Wayyo na shiga uku!" Ta furta tare da kamo ta tana hawaye.
"Bari na kira miki abokina Tanimu ya kaiku. Na bar shi a shagona yana cin abinci zai je birni." Ya
ƙarashe maganar tare da ciro wayarsa Tecno mai botira.
Bayan ya kira shi ya sanya ta shirya mata kaya. Jimmmalo tana shirin kayan tana hawaye,
ganin yadda ta koma. Tunawa da shekaranjiya suna zaune suna hira cikin raha.
Da sauri ta yarda kayan, da ta fito za ta sanya mata ganin idanunta na ƙafewa." Kaka Tani! Ba
mutuwa zaki yi ki barni a duniya ni kaɗai ba?" Ta yi mata tambaya tare da fashewa da kuka.
Ganin halin da take ciki na tsananin wuya, sai Audi mai kyamis ya kama hannunta yana
dubawa, can kuma ya sauke hannunta ya fara ƙoƙarin kamata zuwa keke napep.
"Don Allah kar ku kai ni ko ina saboda mutuwa zan yi. " Kaka Tani ta furta cikin murya mai rauni.
"Ba za ki mutu ba Kaka Tani! In kika mutu ki barni da wa a cikin duniyar nan? Ke ce wacce na
rayu da ita kuma na ke ƙauna."
"Jimmalo, ki yi haƙuri lokacina ya yi, saboda wannan ciwon ba na jin zan tash.."
"Na shiga uku!" Ta furta tare da sakin kuka ta ƙara rungumeta.
"Kaka Tani don Allah kar ki mutu ki bar ni. Ki bari har na yi aure ki ga jikarki. Kaka Tani zan so
Bala mu yi aure in har ba za ki mutu ki bar n..."
Innar Salame ta kalle ta ta ce,"Lokaci ya ƙure Jimmalo, Kakarki Allah ya aiko mata da mala'ikan
da gaggawa. Halin yanzu ki bari mu maimaita mata kalmar shahada in tana da rabo ta yi." Ta
ƙarashe maganar tare da janyeta daga jikinta.
"Wayyo Allah Kakata. Don Allah kar ku bari ta mutu ku taimaka mini." Jimmalo tace tana ihu
sosai, ganin halin da take ciki.
Audi mai kyamis ya duƙa kusa da ita, yana maimaita mata kalmar shahada.
"Jimmalo, ina son na yi magana da ita." Ta furta tana jin kukanta har cikin zuciyarta, amma babu
abin da za ta iya, saboda ga ta yau a kwance tana ciwon ajalin da za ta bar ta ita kaɗai, a cikin
duniya ba tare da ta san mai zai faru nan gaba a cikin rayuwarta ba.
"Kakata ina jin ki gani a kusa da ke, don Allah ki gaya mini ba mutuwa za ki yi ba na yi shiru?"
Ta ce tare da kama hannunta ta ɗora a fuskarta.
"Jimmalo, a yau zan tafi na barki a cikin rayuwar da na ɓata tarbiyarki. Kalaman da Hajiya ta
gaya mini tabbas haka ne. Na cuce ki saboda son da na ke miki ban ba ki tarbiya ba. Na san
cewa ko na mutu babu wanda zai ɗauke ki, har su Hajiya ba za su ɗauke ki ba, amma Jimmalo
in har suka yafe abin da muka yi musu su ka zo gareki, ki tafi birni ki canza rayuwar..."
"Kaka Tani babu inda za ni ina nan tare dake, in kuma kin mutu zan koma da rayuwata a
ƙabarin da aka birne ki, saboda ba zan iya rayuwa babu ke a cikin duniyar nan ba."
Kaka Tani ta buɗe baki za ta yi magana sai ta fara tari tana jijjiga. Kafin kace me ta fita
hayyacinta har idanunta sun fara rufewa. Ganin haka hankalin Jimmalo ya kira tashi. Kuka take
tana ihu tana zambarwa ganin za ta mutu ta barta.
Audi mai kyamis ya rufe mata idanu, lokaci da ya fahimci ta cika, bayan ta amsa kalmar
shahada sau ɗaya.
"Allah ya jiƙanki Tani." Jin abin da Innar Salame ta furta tana share hawaye, sai kawai ta yi wani
irin ƙara ta zube a gurin.
Ruwa aka sanya mata ta farfaɗo, ta rungume gawar Kaka Tani tana wani irin kuka. Gani take
kamar ba ta mutu ba, saboda ba ta taɓa ganin mutuwa ba. Gani take kamar za ta tashi su ci
gaba da rayuwa, don haka ta rungumeta ta hana kowa ya taɓa ta.
"Jimmalo Tani ta rasu ki matsa mutane su fara mata wanka don a kaita gidan gaskiya."
Idanunta ta ɗago da suka yi jajir jina bin da Innar Salame ta ce. "Babu in da zan yarda a kai mini
Kakata, wacce ita kaɗai na sani kuma na yi rayuwa da ita. In na bari kuka kaita ƙabari ni kuma
na rayu da wane? Kaka Tani ba za ta mutu ba, saboda ta gaya mini sai ta ga jikokiina. So kuke
ku raba mu saboda ku samu damar da za ku rama rashin mutuncin da na yi muku." Ta ƙarashe
maganar tare da ƙanƙame gawarta tana faɗin,"Kaka Tani kin ga azzaluman mutanen nan so
suke su raba mu. Kaka Tani ki tashi daga baccin ki gaya musu ba ki mutu ba." Jijjiga ta take yi
tana faɗin haka cikin kuka.
Tun suna sanya ran za ta bari ayi wa gawar sutura har suka cire. Da ƙyar aka samu maza
majiya ƙarfi huɗu suka rabata da gawar, sannan aka fara mata wanka don a kaita gidan
gaskiya.
Jimmmalo, tun da ta ga da gaske za su raba da ita ta cika ƙauyen da ihu tana ƙaraji, domin ta
san cewa rayuwarta ta shiga garari In har babu Kaka Tani a duniya. Wa zai rinƙa tare mata
tsiwa kuma ta rinƙa hira da ita? Jin Kaka Tani take ko iyayen da suka haifeta albarka, tun da ba
ta yi rayuwa da su ba. Tun lokacin da ta mallaki hankalin kanta ita kaɗai take gani kuma ita ce
duniyarta. Saboda mutuwa dare ta yi domin a lokaci har an kira sallar magariba duhu ya yi, kan
dole za ta yi kwanan keso da safe a kaita.
Jimmalo kasa bacci ta yi, har lokaci gani take bacci take yi. A kusa da ita ta kwana sai Innar
Salame da kuma wata tsohuwa ƙawar Kaka Tani. Daren ranar Jimmalo ta kira shi a baƙin dare,
saboda ba ta yi bacci ba tana ta jijjiga ta tana kiran sunanta, a haka ta kwana har gari ya waye
aka fara shirin kaita.
Tana cikin wannan halin da take ganin kamar duk a mafarki ne, aka yi mata sutura aka kira ta
don ta yi mata addu'a a kaita makwancinta. A nan ta zama mahaukaciyar domin ƙaton icce ta
ɗauka, ta tsaya kan gawar duk wanda ya zo sai ta kai mishi duka.
"Babu wanda zai raba ni da Kakata. Ashe ƙiyayyar da kuke mini ta kai haka? Har zaku iya cewa
Kakata ta mutu, don kawai ta warke ta samu dogon bacci?" Duƙawa ta yi kusa da ita ta shafa
fuskarta.
"Kaka Tani ki yi bacci ki tashi, ina gadinki babu wanda zai kai mini ke rami." Ta ce tana kallon ta
sai kuma ta kalle su ta ɗora da cewa,"Kun gani murmushi take mini."
Tsanannin tausayinta ya cika zuciyarsu, domin sun san dole hakan ya faru. Kaka Tani da
tambayar da kanta ƙaramar yarinya take biyewa duk abin da ta yi.
Kaduna.
Cikin dare Hajiya ta kasa bacci, sai mugayen mafarkai take yi. Hankalinta ya tashi sosai da ta
farka ta kasa bacci. Tashi ta yi ta ɗauro alwala ta yi sallah. Addu'a ta yi sosai tana fatan
mafarkin da ta yi ya zamar mata alkhairi.
Da ƙyar ta samu ta koma bacci, sai dai kwanciyarta ke da wuya ta yi mafarkin Kaka Tani. Cikin
firgici ta farka tana yin duk addu'ar da ta fito daga bakinta. Tun da ta yi mafarkin sai ta kasa
komawa. Zama ta yi kan tsakiyar gadon tana tunanin mafarkin da ta yi.
"Lafiya suke?" Ta yi wa kanta tambayar cikin damuwa. Wayarta ta ɗauko ta duba lokaci sai ta
ga ashe har an kira sallar asuba. Miƙewa ta yi ta shiga bayi ta ɗauro alwala ta yi sallah. Addu'a
sosai ta ƙara yi tana fatan suna lafiya. Da carbi a hannunta ta shingiɗa tana ja. Kafin safiya
xuciyarta ya gama kitsa mata ta je Ƙauyen Damagaran, saboda gabakiɗaya ta kasa samun
sukuni. Da Kaka Tani ta faɗo mata sai ta ji gabanta ya yanke.
Wayarta ta ɗaga ta kira numbar Daddy. Yana ɗagawa ya yi sallama, sannan ya gaishe ta.
"Ka shirya safiya za mu je Ƙauyen Damagaran, saboda jiya kwana na yi ina mafarkin Tani."
Mamaki sosai ya yi, jin abin da ta ce har sai da ya cire wayar ya kalli numbarta, saboda ya yi
mamakin jin cewar za ta ƙara shiga rayuwar su bayan ta ce ita da su har abada.
"Kana jina ko Abubakar? Mugun mafarki na yi na Tani. Ba a gasganta mafarki, amma ina jin
kamar babu lafiya, don Allah ka shirya mu wuce da safen nan."
"To Hajiya Allah ya sanya lafiya. In sha Allah ina karyawa zan yi na fito."
"Amin, ka yi sauri don ba zan iya karyawa ba sai a mota."
"To gani nan zuwa." Ya ce tare da kashe wayar yana kallon Mommy cikin mamaki.
Dariya mommy ta yi ta ce,"Ba za ta haƙura da su ba, dama ni na san haka. Hajiya da kullum
nasiharta mutum ya kula da zumunci, sai ta yi watsi da nata? Na san cewa hushi ta yi kuma za
ta huce ta neme su. Yana da kyau ta haƙura ta samu ta ci galabarsu har ta canza musu rayuwa,
wallahi Jimmalo tausayi take bani. Yarinyar nan ba ta san wace ce ita ba, ballanatana ta gane
irin rayuwarta ta dosa. Babu ilmi babu natsuwa ba tsafta. Wannan wane irin rayuwa take yi."
"Duk yadda zaki so ki kawo gyara a cikin lamarinsu sam ba za su yarda ba. Ni fa ba taɓa ganin
mutane irin su ba."
"Gaskiya yadda ka san ba su da hankali. Da ace Kakar tana tsawata mata, wataƙila da an samu
sauƙin haukar da take yi."
"Duka duk halinsu ɗaya. Fito mini da kayan bari na shiga wanka." Ya ce tare da kama hanyar
bayi, ita kuma ta nufi wandrop ɗinsa.
Bayan ya shirya ya karya, sannan ya yi musu sallama ya nufi gidan Hajiya.
Hajiya da ta riga ta shirya, tana jin motarsa ta fito tun kafin ya shigo."Na shirya muje kawai
saboda hankalina a tashe yake."
Yadda ya ga ta tayar da hankalinta, sai ya shiga bata baki har ta ɗan saki."Mafarki ba gaskiya
bane in sha Allahu suna lafiya."
"Ina fatan hakan." Ta ce bayan ta zauna a cikin motar suka fara tafiya.
Kasancewar sun fita da wuri, kuma Daddy ya yi gudu sosai sai suka isa daidai lokacin da aka
ɗaga makarar Kaka Tani. Jimmalo tana ihu tana riƙe da ita aka fito ƙofar gida.
"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un! Ni dama na ji a jikina ba lafiya ba, ashe Tani rai ya yi halinsa.
Shikenan ba ni da kowa a dangin mahaifiyata." Ta furta cikin kuka tare da fita daga cikin motar.
Daddy cikin sauri, ya kashe motar ya fito domin ganin mutuwar jikinsa da ya yi sanyi.
"Ya Salam ashe mutuwa ta yi!" Ya furta cikin damuwa.
Hajiya na zuwa ta rungume makaran ta fashe da kuka."Tani ashe ganawarmu kenan ba za mu
ƙara ganin juna ba? Sannan ba mu yi rabuwar farinciki ba."
Ganin Hajiya, Jimmalo ta saki makarar ta kama hannunta. "Yauwa gara da kika zo, don Allah ki
gaya musu ba ta mutu ba bacci take yi. Kin gani za a raba ni da ita?" Sai ta saki hannunta ta
kama hannun Daddy da yake tsaye jikinsa ya yi sanyi sosai.
"Ba ta mutu ba duba ka gani so suke su raba mu."
Kamar ya yadda da maganarta sai ya ƙarasa ya ɗaga likafanin. Da sauri ya mayar yana
hawaye."Ki yi haƙuri Kakarki ta mutu."
Duk yadda suka yi ta bari akai ta makwancinta ta ƙi, har sai da Daddy da Hajiya suka riƙe ta
sannan aka tafi da ita.
Ta yi ihu da kuka, har da zagi ta haɗa musu don su ƙyaleta, amma Daddy ya yi mata riƙo sosai.
Duk yadda ta so ta ƙwace haka ta haƙura, domin duk ƙarfinsa ya sanya ganin tana son ta
ƙwace.
Bayan an je an kaita aka zauna zaman gaisuwa. Sosai Daddy ya yi mamakin irin kukan da
Hajiya take yi. Duk da y an cewar 'yar'uwanta ne, amma ba su yi shaƙuwar da za ta rinka risgan
kuka haka ba. Sai suka zame mishi su biyu. Ita Jimmalo dama duk haƙurin da yake bata kamar
yana ƙara cewa ta yi ne, saboda tunaninta yau Kaka Tani ta rasu to da wa za ta yi rayuwa?
Daddy ne ya siyo duk abin da ake bukata, duk da cewar da sauran abincin da suka kawo musu,
don haka ya ƙaro wasu.
Jimmalo sarfatan mutane ta yi, ta gudu zuwa ƙabarin da aka rufe Kaka Tani ta kwanta tana ta
kuka ta ce,"Kaka Tani dama ba za ki rayu da ni ba, kika yi mini alƙawarin sai kin ga jikokina?
Kaka Tani kin tafi kin barni mutane sun cika gidanmu ana ta cinye mana abincin da muke ci da
ga ke sai ni. Kaka Tani kina jina ki taso mu koma gida, mu ci gaba da rayuwarmu, domin in har
ba ki tashi ba, ni ma a nan zan dawo da rayuwa."
Kuka take yi, tana faɗin suratai da kalamai waɗanda ba su kamata ba. Daddy da Hajiya suka
taho zuwa ƙabarin. Ganinta kan ƙabarin tana kuka sai jikinsu ya yi sanyi sosai. Da ma sun san
za a rina, dole ta yi kukan rashinta, saboda yadda ta shaƙu da ita kuma ita kaɗai ce danginta.
"Jimmalo, Kakarki ta mutu sam ba za ta dawo ba, saboda lokacin tafiyarta zuwa ga mahallicinta
ya yi. Duk wanda kike gani a duniya mutuwar yake jira. Ke ma za ki mutu, don haka ki taso mu
koma gida ki fuskanci rayuwar gaba."
"Ba zan koma gida ba, in har zan mutu to zan jira nawa mutuwar a birne mu da ita." Ta ce wa
Daddy tana zare idanu jin abin da ya ce.
"Jimmalo, ki tashi mu koma gida na yi miki alƙawarin zan kula da rayuwarmu fiye da yadda Tani
ta yi, saboda zan baki gishiri zaman duniya zan i..."
"A'a ba na son ji!" Ta furta tare da toshe kunnuwanta, sannan ta ɗora da ce wa,"Babu wanda zai
iya kulawa da rayuwata, kamar yadda Kakata wacce tafi ƙaunata ta yi. Don haka ku tafi bana
son ganinku na tsani kowa." Ta ƙarashe maganar, tare da ƙara kwanciya kan ƙabarin tana kuka
tana