Showing 21001 words to 24000 words out of 90573 words
Chapter 8 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
ba tare da ta yi musu ta yi ba, in kuma ta ga na wani jikinta har rawa yake yi.
Ko ba a yi mata tayi ba sai ta sanya hannu. Ka yi magana ta ce za ta nuna ma mutum ƙarfi.
Yanzu ma ɓoyewa ta yi tana mazurai.
"Ke wallahi Salame, gidanku kamar ba a iya tarbiya ba. Na gaya miki ki dinga sallama kafin ki
shigo gidan mutane, tun da ba tsoho da tsohuwa suka gina ba."
Kama bakinta ta yi tana kallonta daidai lokacin da ta ƙaraso."Ke har bakin magana kike da shi?
Ke da sai dai ki shigo ɗakin mutane da gudu, saboda an yi miki sai ki ji haushi?"
Harararta ta yi, tana tana ƙara ɓoye indomie ɗin ba tare da ta ce komai ba.
"Jimmalo, wai mai kike ci kike ɓoyewa? Bayan ke mutum ko a takashi ya sanya sai kin
ƙwakulo?"
"Babu komai." Ta ce tare da ƙara yanke fuska.
Shammatarta ta yi ta ture ta ta ɗauki indomie."Kai Jimmalo, da ma taliyar birni kike ci shine za ki
yi mini rowa?"
Cikin masifa ta miƙe za ta cakume ta, ammma jin ta ce taliya ya sanya ta tsaya."Uban wa ya
gaya miki taliya ce? Biskit ɗin birni ne fa, kuma waallahi kika ƙara mini haka, sai na shuka miki
rashin mutunci." Ta ce cikin fushi tare da komawa ta zauna.
Ba tare da ta ji kashedinta ba ta ƙara kai hannu ta karɓa."Ke wallahi taliyar birni ne. Kin san
Yaya Kabiru yana zuwa birni? Da zai dawo ne ya siyo ya koya mana yadda ake dafawa, kamar
taliya aka dafata ga daɗi wallahi."
"Mai ƙarya?" Ta furta tana juya ledar.
"Ɗan wuta kuma in ba ki yarda ba ki gwada girkawa."
Ba musu ta miƙa ta ɗauki tukunya ba tare da ta ɗauke ba, ta ɗora a wuta tare da kumbula ruwa
rafin tukunyar.
"Kan uba sai ka ce za ki dafa ganda?"
"Ya ake yi kin san ba girki na ke yi ba?" Ta yi mata tambayar tana zare idanu.
Tukunyar ta sauke ta rage ruwan sosai, don kusan juyewa ta yi sannan ta mayar da tukunyar.
Suna tsaye ruwan ya tausa ta zuba.
"Laa, Salame ashe wallahi da gaske ne! Kin ga Kaka Tani, har ta dahu." Ta ce tana kallonta
cikin tsananin farinciki.
"Ikon Allah ta dahu sai ƙamshi take." Ta ba ta amsa daidai lokacin da ta ƙaraso.
Zaman ci suka yi duk wahalar da ta sha gurin girkin, kaɗan ta sam mata ta cinye tana lashe
hannu. Bayan sun gama ci. Kaka Tani ta rarrashe ta don ta fasa ƙara girkawa da za ta yi."Kin ji
jikalle, ki bari sai kin dawo sarin ayabar, kin ga rana ta ja yi."
"Ai da kin bar ni na ƙara wallahi daɗi ya ke da shi sosai."
"Je ki dawo kin ji?.Ga kuɗin ki kula kar ki yi faɗa da kowa."
"To,"Ta amsa tare da janyo ɗankwali tasha ɗammara suka fita.
A hanya suna tafe suna hira har suka isa. Bayan sun sari ayabar suka wace tasha, anan suke
siyarwa. Sai da ta sayar duka, sannan ta shigo musu rogo da gyaɗa da za su ci da daddare.
A gajiye ta koma gida, babu tunanin yin sallolin da ba ta yi ba ta kwanta. Bacci ta yi kafin
magariba ta miƙe ta shiga bayi. Da ta fito zama ta yi kan turmi tana irga cinikinn da ta yi."Ga shi
Kaka Tani, wannan zan sayi ɗantamatsitsi da hanjin ligidi, a dandali."
"Allah ya yi miki albarka, amma ya kamata na saro miki gyaɗa ki kai dandalin?"
"Eh ki saro da yawa."
"Yauwa jikalle." Ta ce tare da ɗaukar mayafinta ta fita.
Ko wace mace ta yi wanka, tasha kwalliya cikin riga da zani daban ɗankwali daban. Jimmalo ce
kawai ta buga daka tsami ta zo. Dama duk ranar da za ta je dandali take ƙuru ta ke yin
dakatsamin. Duk wanda ya yi kuskuren zama kusa da ita sai ya rinƙa kauda hanci. Tana zaune
da tiren gyaɗa suna hira da Ladiyo. Wani saurayi mai suna Bala ya ƙara so gurinta. Wani irin
tsuka ta ja tare da kauda fuskarta tana harararsa.
Ganin haka ya tsaya sororo a kusa da ita."Jimm..."
Kafin ya gama kiran sunan ta taso masa kamar za ta cinye shi."Na gaya maka Bala ka fita
idanunka, saboda wallahi ko maza sun ƙare ba za iya auren ka. A yadda kake siririn nan kamar
tsinke, in ka ɓata mini rai tsaf zan sanya hannu na karya ka."
Kunya ce ta kama shi, ganin yadda take maganar cikin ɗaga murya. Samari da 'yan mata na
dandalin suka tsaya suna kallonsu.
"Ke!" Ya daka mata tsara yan huci tamkar mesa, sannan ya ci gaba da da cewa,"Don kin samu
na ce ina so ki?In ban da rashin zuciya irin tawa, uban me zan yi da mace ƙazamiya irin ki, da
ko wanke baki ba kyau yi. Dubi kayan jikin ki, kamar wacce take suyan kifi. Kin taɓa jin warin da
kike yi kuwa?"
"Kutumar ƙaniya!" Ta ce tare da ƙara sakin wani ashahariyar, sannan ta miƙe ta cakumi
wuyarsa."Ni za ka yi wa rashin mutunci? Ka san ina wurin uban wa ya ce ka ce kana sona?" Ta
furta tare da shaƙe masa wuya.
Duk iya ƙoƙarin su don su raba su, amma ta ƙwaƙume shi sai cizo da yakushi take kai mishi. Da
ƙyar suka samu suka raba su. Kallonsa ta yi tana huci."Dubi yadda na yi maka jina-jina a haka
kake so na so ka?"
Harara ya gallah mata ya wuce cikin tsananin jin kunyar yadda ta disga shi. Ihu da tafi suka
ɗauka suna mata kirarin,"Jimmalo jikar Tani kin gagari kowa har da maigari."
Kanta ne ya fadi ta ji kamar ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba, tare da murmushi a fuskarta.
Saboda faɗan da suka yi, sai dandalin bai yi wani armashi ba. Ba su kai yadda suke daɗewa
ba, suka tashi kowa ya nufi gida.
Hajiya tana zaune da littafin Hisnul Muslim a hannunta tana dubawa. Daddy ne ya yi sallama ya
shigo.
Zare gilashin idanunta ta yi wanda yake medical. Kallonsa ta yi cikin tsananin ƙauna. "Barka da
zuwa ka iso?"
"Eh, tun jiyada kika gaya mini kina son ganina, na so in zo, ban tashi kasuwa da wuri bane." Ya
faɗa bayan ya zauna kusa da ita yana gaishe ta.
Amsawa ta yi idanunta na kansa."Kan maganar da muka yi da kai, na zuwa ƙauyen na ga inda
'yar'uwata take."
Gabansa ya faɗi jin abin da ta ce. Sam ba ya son zuwa ƙauyen nan, ba wai don abin da ta yi
musu ba, hatta hanyar ƙauyen fargabar bi yake yi, musamman da Aliyu ya ce masa akwai
aljanu.". Gyaran murya ya yi, don ya kawo uzurina da zai hana zuwansa.
"Hajiya na ɗauka mun gama maganar cewar tun da..."
"Ka ga ban son dogon bayani in har ba za ka je ba, sai ka haɗa ni da direba mu je."
Kallonta ya yi da sauri jin abinda ta ce,'Haba Hajiya, ace kina da ɗan da ya iya mota sai na bari
direba ya kai ki?"
"To zan yi maka dole ne? In ka ce ba za ka je ba, ai dole na je tun da dangina ne."
"Shikenan, ki sanya rana yaushe za mu je?"
Jin abin da ya ce fara'arta ta ƙaru."Ai ni ko gobe ka ce a shirye na ke. Ka faɗa mini ranar da za
ka je."
"Ki bari sai ranar sati Hajiya."
"Allah ya kaimu." Ta ce tare da cigaba da jan carbinta.Miƙewa ya yi jikinsa a mace ya
ce,"Hajiya, zan wuce kasuwa."
"To shikenan, Allah ya yi maka albarka, sannan karka manta goro na ya ƙare."
"Hajiya ya kamata ki rage cin goro, sam ba shi da amfani."
"Allah ya kyauta, in ka ga na daina cin goro sai dai in bani da rai, ai goro ya zama tamkar
abinci."
"Allah ya kyauta." Ya ce sannan ya doshi ƙofar fita.
"Amin," Ta ba shi amsa tana kallon sa.
Hajiya shirye shiryen tafiya ta fara ta haɗa musu kaya sosai. A ranar da ta kasance ranar da za
su tafi, tun safe suka ɗauki hanya. Kallon hanyar take tana mamakin nisan gurin, musamman
da ta ga sun shiga cikin turɓaya suke yi.
Da suka isa da ƙarfi ta samu ta fito, sakamakon ƙafafunta da suka yi mata nauyi sosai. Bayan ta
fito da gyalenta a hannun."Ikon Allah! Allah ɗaya gari bambam. Dubi inda 'yan'uwana suke
rayuwa, babu abababen more rayuwa?" Ta furta tana kallon ƙauyen cikin mamaki.
Daddy bai ce komai ba suka kama hanyar zuwa gida. Kaka Tani tana zaune a tsakar gida tana
kasa ayabar da Jummmalo za ta je tallah inta dawo daga iban ruwa rafi.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
Follow the ƘIYAYYAR JINI channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P
PAGE 7
Da suka isa da ƙyar ta samu ta fito, sakamakon ƙafafunta da suka yi mata nauyi sosai. Bayan ta
fito da gyalenta a hannunta."Ikon Allah! Allah ɗaya gari bambam. Dubi inda 'yan'uwana suke
rayuwa, babu abababen more rayuwa?" Ta furta tana kallon ƙauyen cikin mamaki.
Daddy bai ce komai ba suka kama hanyar zuwa gida. Kaka Tani tana zaune a tsakar gida, tana
kasa ayabar da Jimmmalo za ta je tallah inta dawo daga iban ruwa rafi.
Sallamar da aka yi ya katse mata hanzarin ta. Ba ta amsa ba, sai ta yafa gyalenta ta nufi ƙofar.
Turus! Ta tsaya tana kallon Daddy, tana masa kallon kamar ta gane shi. Mayar da idanunta ta yi
kan Hajiya. Ganinta ya sanya ta saki fara'a. "Ikon Allah Atine! Ashe za mu ƙara haɗuwa?" Ta yi
mata tambayar cikin tsananin mamaki tana kallonta.
Hajiya rungumeta ta yi tare da ƙanƙame ta."Ga shi Allah ya sake haɗamu Tani." Sosai suka
rungume junansu kamar ba za su rabu ba. Da ƙyar suka saki juna sannan suka shiga cikin
gidan.
Kallon gidan take yi wani iri mai ɗauke da ciki ɗaya guda biyu, sai kuma ɗan tsakar gida da
kicin. Ruwa ta ibo mata a randa mai tsanannin sanyi ta kawo mata. "Ga shi kisha Tine, wallahi
ban yi tunanin da gaske ɗanki bane, musamman da yaronsa ya zo ya yi mana ɗiban albarka."
"Ki yi haƙuri haka ya gaya mini, da san tare zai zo da shi zan hana shi, saboda shegen zuciya
ce da shi kamar kuturu, ga shi saboda rashin tunani suka bar shi ya zama soja."
"Soja?" Ta dafe ƙirjinta tana kallonta."Haba biri ya yi kama da mutum. Shi ya sa zuciyarsa sam
babu imani. Wani naushi da ya yi wa jikalle sai da ta yi sati tana jinya. Kin san sojojin nan ba
imani ne da su ba, haka kawai za su iya kashe mutum. Ni dama tun da na ga fuskarsa babu
fara'a, na san cewa ba shi da imani."
Maganarta ta ƙarshe ya sanya Hajiya ta kalli Daddy, ganin babu kunya tana kwashe wa ɗansa
albarka a gabansa."
"Hmmmmh!" Allah ya shirya." Ta furta tana son kauda zancen.
Dady kuwa kallon ta yake cikin tsananin mamakin ƙarfin halinta.
"Ka sanya direba ya shigo da tsarabar." Ta ce masa tana kallon da.
Fita ya yi daga cikin gidan ba tare da ya tanka ba.
"A Hajiya ba ku gajiya? Kayan da ku ka kawo mana bamu gama amfani da shi ba."
"Ai yiwa kai ne. Kune fa kawai kuka rage mini dangin mahafiyata, Allah ya yi mini arziki in ban
taimaka muku ba, wa zan taimaka wa?"
"Haka ne Allah ya ƙara buɗi." Ta ce sannan suka ɓarke da hira ana tuna baya.
A guje ta shigo cikin gidan tana ihu murna. Da sauri Kaka Tani ta miƙe ta tare ta tana
faɗin,"Jikalle, murnar mai kike yi haka? Ina tulun da kika je uban ruwa?"
Dariya ta ƙara saki ta ce,"Bala ya fasa mini tulu ni kuma na fasa masa kai. Wallahi sheme shi na
yi yana can a rafi kwance, jini yana ta zuba a kansa." Ta ƙarashe maganar cikin tsananin
farinciki.
Hajiya ta miƙe da sauri tare da dafa ƙirjinta. Da ta shigo ta ɗauka mahaukaciyar ce, amma tuna
Daddy ya gaya labarinta sai ta tsaya cikin mamaki tana kallonta. Ganin yadda take cikin dauɗa
da ƙazanta ya sanya ta jinjina kanta.
"Yauwa 'yar albarka. Gara da kika ragije mishi kai, sai yan san ke ba sa'arsa bace."
"Wallahi na yi maganinsa domin a nan na sanya sandata na ragije shi, nan take ya zube babu
numfashi. An gaya masa ni sa'ar ce? Ni ko mai gari maigari shakkarsa, domin duk wanda ya
cuce ni ba zan yarda ba sai na rama. Ni fa Kaka Tani a yadda na ke jina zan iya zama soja."
"Za ki iya zama ƙarfi ne dake kamar 'yar doki. Allah ya yi miki albarka ba ki zama marainiya ba,
tun da za ki iya rama ma kanki."
Hajiya ta zare idanu ta yi tana kallon ta."Tani mutum ta fasawa kai amma kike goyon bayanta?"
"Gara da ta yi maganinsa ya takura mata." Ta ba ta amsa tana kallonta.
Sai a lokacin Jimmalo ta ɗaga kai tana kallonta, don ba ta lura da ita ba. Tana ganin shigarta ta
gane daga birni take. Cikin tsananin rashin kunya ta ce,"Ke kuma ina ruwanki dangin dagiro? Ni
bana son shiga sharo ba shanu." A tsiwace ta ƙarashe maganar tana harararta.
Mamaki ya kamata jin abin da ta ce. So take ta toshe hancinta, saboda tsananin wari da ya cika
hancinta. Kallonta ta yi yadda ƙafafunta suka farfashe, ga wani uwar faso da ya cika ƙafar har
mutum zai iya ajiya. Babu abin da ya ƙara munanta fuskarta, sai haƙoranta da suka dafe da
dadti. Sun yi jajur har wani gansa kuka suke yi. Amai ne ya taso mata, amma sai ta daure, tana
jin yadda cikinta ke juyawa. Don kar ta yi ƙarya za ta iya cewa har zarni take yi. Wataƙila tana
fitsarin kwance. Ko kuma tsabar dauɗa da ƙazanta ya sanya kayanta suke tashi. Kalar kayan da
ta saka sam mutum ba zai iya ganewa ba, saboda sun yi duƙu-duƙu.
Bige bakinta da Kaka Tani ta yi tana faɗin,"Bana son rashin kunya 'yan'uwanmu ne daga birni."
Hannunta ta janye tare da kallonta ta balla mata harara,"Ni ki ƙyale ni saboda na tsani duk
wanda zai zo daga birni, tun da ɗan su ya kira ni da ƙazamiya wawiya daƙiƙiya har yana kirana
da dabba! Ita ma na san cewa za ta yi ba ni da tsafta."
Kaka Tani kunya ta kama ta ganin rashin kunyar da take yi, sai ta shiga yaƙen dole."Ki yi haƙuri
kin san sha'anin yara, ta ɗauka kema mara mutunci ne kamarsa, ba ta san kina da mutunci ba."
Kasa cewa komai ta yi, tana kallonta jin abin da ta ce. "Sam Aliyu bai yi ƙarya ba, duk sunan da
ya kira ta da shi ta cancanta."
"Amma Tani kina ji fa, kai ta fasa ma wani kuma kike goyon bayanta?"
"To sannu uwar zugai! So kike ta buge ni? Inda ya kashe ni an kawo mata gawata sai ki yi
farinciki ko? Ki ji daɗi an kashe mata jikallenta ɗaya kamar rai da take da shi."
Kamata ta yi ta rungume tana rufe mata baki."Ki yi shiru ba za ki mutu ba,gara da kika rama
kuma a shirye na ke na je kotun ƙoliya a kanki."
Mamaki ya ƙara kamata sai ta shiga jinjina kai. Daddy kuwa bai yi mamaki ba sam. A ransa ya ji
daɗi da suka yi mata haka, don ta ga ainihin kalarsu. Ta daina tunanin jajibo su cikin rayuwarsu.
"Anya kina kyautawa rayuwarta, ita fa 'ya mace ce, wacce za ta tarbiyyantar da wasu. Irin
wannan gurbata da kike ɗora ta kina ganin daidai ne? Haba Tine kar son zuciya ya sanya ki
ɓata