Showing 78001 words to 81000 words out of 90573 words
Chapter 27 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
advice?"Ta furta cikin ɓacin rai tana
kallonta.
Ni this isn't workable! Kin san abin da haka zai kawo? Ni fa ban ga wani amfanin wannan
banzar shawarar ta ki ba. Aliyu tsanata zai ƙara yi, kuma kin san ba zan iya rayuwa babu shi
ba."
"Daɗina da ke ba kya jiran kici ribar ƙarshen zance." Ta ce mata cikin takaici.
"Saboda gurguwar shawara kike ba ni. Mahaifin Aliyu ya sanya yarda sosai a kansa, kina ganin
in har na yi sanadin rushe yardar nan. Aliyu zai ƙara kallona da fuskar rahma?"
"Ba ki da wayo Lubaiyna. Hutu da wayewa da kika taso cikinsa ya sanya kanki ba ya kawo
wuta. Wannan yardar da mahaifinsa ya yi masa da shi za mu yi amfani ki samu Aliyu a
hannunki."
"Hmmmmh!" Kawai ta ce tana mamakin wautar shawararta.
Ganin ta yi shiru kawai sai ta ɗora da cewa,"In har ya tafi sai ki bishi kije ki saka kuka ki ce wa
mahaifinsa Aliyu har ciki ya yi miki, sannan ya yi miki alƙawarin aure ya ƙi aurenki. Iyayenki sun
yi fushi dake shi kuma ya guje ki. Ki gaya mahaifinsa in har bai yarda ba zai iya bincike sosai
domin ba za a rasa wanda suka san mummunar halinsa ba. Kina iya cewa aje gidansa domin
hatta kayan sawanki yana can. Kin ga anan mahaifinsa zai zurfafa bincike ya gano gaskiya.
Wannan condom da kika sanya mishi sai ki ce ko Kaduna ya zo, sai ya kira ki kin biyo shi, kin
ga zai bincika har ɗakinsa na gida, ya ga condom ɗin. Kin ga bayan ya gano gaskiya ba zai ƙi
aura miki shi ba, domin na san ta wannan hanyar zai huce fuska biyu da ya zama, don in har
zai yi adalci ba zai ƙi ba, saboda shi ma na san yana da 'ya'ya mata. Ba zai so hakan ya
kasance da shi ba. Bayan haka ya faru sai mu shiga bin malamai don mu jawo hankalinsa
gareki, amma yanzu kun rabu ko magani aka ba ki, don ki sanya masa cikin abinci ba za ki
samu hanya ba."
Shiru ta yi xuciyarta na son yarda, amma tunaninta yana gaya mata gurguwar shawara ce.
Lokaci guda sai ta fara yadda musamman da ta tuna yaudararta da ya yi. Kuma sai ta ga in har
za ta aure shi ta rayu da shi, sam ba za ta damu da tozarci da wulaƙancin da zai yi mata ba,
sannan yana matsayin mijinta dole ta yi amfani da kissar da za sanya har ya gaji da tsanarta ya
daina. Lokaci guda sai ta yarda, da shawarar ta kuma ta amince har ta yi mata alƙawarin aikaita
haka.
A haka suka bar shawarar, Lubaiyna ta koma gida cikin tsananin farinciki. Wayarsa ta fara kira
amma ya sanya ta a black list. Ba ta damu ba, don haka ta sanya ranar da za ta je gidansa
Aliyu
A ranar da Anty Amarya ta sanar da shi ya yi kwanar farinciki, domin tun kafin ya ga yarinyar ya
riga ya gama ji a jikinsa ya samu matar aure. A daren ba ƙaramin ƙoƙarin ya yi ba, da bai karɓi
numbarta ya kira ta ba, har ya miƙe zai je gurin Anty amarya ta ba shi numbar, sai kuma ya fasa
ya kwanta, da nufin ya kira ta tun da ba ta online.
Har ya dubo numbar zai kira, zuciyar sa ta ba shi shawarar, kan ya yi haƙuri zuwa nan da
kwana biyun, domin ba ya iya tunanin zuciyarsa za ta iya wuce kwanakin.
Da ya ga ya samu kalar matar da yake so, sai ya ji zuciyarsa da gangar jikinsa sun bijiro masa
da buƙatar aure. Wataƙila lokacin da ya ɗauka yana jin ba ya sha'awar auren, don bai samu
wacce yake so ba, amma yanzu sai ya ji yana son ya samu wacce in ya dawo gida. Za ta rugo
da gudu ta faɗa jikinsa tana ƙamshi mai daɗi da shiga mai jan hankali, sannan gidan yana fitar
da wani ƙamshi mai daɗi, ga abinci wanda zai rinƙa ɗauke masa yunwarsa.
Shi kuma cikin shauki ya haɗa ta da jikinsa ya manna mata kis. Lokaci ya ja, har akwai lokacin
da za ta haifa masa kyawawan yaran da ba su wuce guda uku ko huɗu. Ya ba su kyakyawar
tarbiya, da duk wani ji daɗi na rayuwata. Sosai ya ƙosa ya je ya ganta domin har ya fara shiri.
Duk da kasancewarsa ba mace ba, amma gyara da ƙalƙala da yake yi, bana tunanin ko ita
macen aka ce zai zo za ta yi wannan gyaran.
Anty ta so su koma a washegarin da suka zo, musamman yadda ɗan gidan nata ya ƙosa ta
koma don ba ya son ganinta da Jimmmalo, wacce a yanzu take tunanin ta samu wacce za ta
zamar mata makwafin Kaka Tani. Da dare ya yi Daddy ya dawo, sai ya sha giyar mamaki.
Domin ko kafin ya shigo cikin gidan, ya ji muryarta tana dariya suna hira da Anty Amarya. Da ta
cika ta surutu har ta ji.
Da sallama ya shigo yana al'ajabi. Turus ya yi ganin yadda ta shige jikinta.
Ganin ya shigo duk duk haɗa baki cikin girmamawa suka fashe shi. Jimmalo har da motsi da
bakinta duk da ba gaisuwar ta yi ba, ganin yadda Anty ta tsareta da ido.
"Ikon Allah!" Ya furta lokacin da ya ije tsarabar da ya shigo da shi.
"Hmmmmh! Ni kaina abin ya ɗaure mini kai. Tun da Amarya ta zo, Jimmalo ta saki take zuba a
cikin gidan nan kamar ya'yan kanya."
"Na yi mamaki ƙwarai ban san sa'ar da kike shi ba." Cewar Dady bayan ya zauna.
"Sa'a ace babba ma kuwa, domin tun lokacin da na ga Aliyu, ba shi da wacce yake kulawa a
Zariya sai ita ma tabbatar da ita mai sa'a ce, mutumin da mutane bai dame shi ba. Ko ni da na
ke mahaifiyarsa ba ya damuwa da ya yi hira da ni. Ga kuma Jimmalo wacce ta gagari kowa a
kauyen Damagaran."
Dariya suka yi Daddy ya miƙe, bayan sun ɗan taɓa hira ya shiga ciki yana murna sosai. Da aka
kira sallah sai Anty ta miƙe zuwa ciki ta yi alwala.
Jimmalo tana zaune tana kallo. Ganin kowa ya tashi a falon, amma tana zaune sai ta fito daga
cikin ɗakin ta ce,"Ta shi ki yi sallah."
Motsi ta yi da bakinta kamar za ta yi magana. Ganin haka ta riga ta da cewa,"Sallah ita ke
bambance tsakanin musulmi da kafuri. In har ba kya sallah wuta za ki shiga."
"Ba zan shiga ba tun da ban girma ba."
"Kin girma Jimmalo tun da kika haura shekara sha huɗu. Addini daga shekara bakwai ya yi
mana umurni damu fara dukan yaro in har bai yi sallah ba, don haka ki tashi ki yi sallah ko na
fasa daina magana da Captain."
Babu musu ta miƙe duk da ba haka ranta ya so ba.
"Ki shiga bayi ki yi alwala, ina jiranki mu yi." Anty ta ce mata ganin yadda ta sha kunu.
Ba haka ta so ba, domin ta so ta yi ita kaɗai yadda za ta ci karenta babu banbaka, amma tuna
za ta fasa alƙawarin sai ta shiga bayin, ba tare da ta ce komai ba, domin ita so take yi in za ta
tafi Zariya su tai tare.
Da ta shiga cikin bayin ta fara alwala, sai Anty Amarya ta zauna a bakin gado ta jira ta. Sai dai
lokacin da ta ɗauka ta fito ya sanya ta kalle tada sauri.
Kallon mamaki Anty ta bi ta da shi. Jimmalo har kin yi alwala a sakanni?"
Jin tambayar ta bata fuska ba tare da ta bata amsa ba, domin ita kanta ta san cewa ba alwalan
ta yi ba ta dai watsa ruwa.
"Shiga na ya yadda kike yi." Ta ce mata tare da buɗe mata bayin
Ganin za ta yi mata musu ta ce,"In har kina son na cika miki alƙawarin da na ɗaukar miki. To ki
cire tunanin mini musu a rayuwarki."
Ba ta amsa ba ta shiga ciki. A nan ta shayar da Anty duniyar mamaki. Domin ba alwala ba, shi
kanshi tsarki ba ta tunanin ta iya.
Ganin wasa kawai take da ruwa, sai ta nuna mata yadda za ta yi alwalar. Suka fito bayan ta
kammala tana mamakin yadda Kaka Tani ta yi mata rainon dabbobi, domin za ta iya cewa
bayan gangar jiki da take da shi na mutane, gabakiɗaya rayuwar dabbabibi ta koyar da ita.
Ba ta ƙara shan mamaki ba, sai da suka zo yin sallah. Sai kawai ta ji hawayen tausayi yana bin
ƙuncinta. A ranta ta ji tana son taimaka mata a rayuwarta. Don haka ta ƙudurta za ta roƙi
Mommy, in suka yi hutu ta kawo Jimmalo hutu Zariya.
Da suka idar da sallah falo suka koma. Bayan sun yi kallo suka kashe kayan kallon sannan
suka shiga don su kwanta.
A daren tana naniƙe da ita kamar angon da ya yi sabuwar amarya. Ko da aka zo bacci sai ta
daka tsalle ta ce alan baran ɗakin da Anty Amarya za ta kwana.
Mufida
Tun daren ranar Mufida, take ta tunanin yadda za ta samu ta sanya maganin kafin su tafi. Suna
kwance kowa ya yi bacci, amma ban da ita da ta lula duniyar tunani, sai dai har ta fara jin bacci
ba ta samu mafita ba.
Da safe da suka tashi, tun asuba Anty ta sanya Jimmalo ta yi sallah. Duk da cewar sallar da ita
gwara babu, haka dai ta yi ta kallonta har ta sallame. Ta san cewa a yanzu ta ce za ta koya
mata karatun sallah ɓata baki ne.
Jimmalo tana zumɓura baki, Anty ta taimaka mata ta shirya zuwa makaranta. Ita babu abin da
ta tsana a rayuwar birni zuwa makaranta.
Kayanta gogaggu wanda Alu, mai wanki da guga ya goge mata ta sanya. Ga shi Anty ta tilasta
mata ta yi wanka. Sai ta fito cas abin ta. Suna zaune a falo ana karyawa.
Mommy ce take kallonta cikin sha'awa ganin yadda ta canza. Ta so ace Anty ta daɗe yadda za
ta gyara mata ita, amma da ta tuna an kusa yin hutu sai ta bari in an yi hutu sai ta kaita.
Da suka je makaranta wanna karan babu harare-harare, ta yi zamanta kan kujera. Ko yaran da
suke kallonta ganin yada ta yi shiru suna son tononta ba ta kalla ba.
Har aka yi darasi uku, sannan aka kaɗa break tana zaune bata tare da ta kula kowa ba. Ko
malamar da ta shigo, duk maganar da ta yi mata ta yi rubutu kan dole ta gaji ta ƙyale ta.
Bayan ta fita, sai ta je ofishin Principal ta yi masa ƙorafin ba ta rubutu. Jin hakan ya yanke
shawarar zai kira Daddy, da kansa ya bashi shawarar a ɗaukar mata tuitor.
Tana zaune tana cin abincinta a cikin kula, wani yaro mai suna Muntazar ya kalle ta ya kwashe
da dariya.
"Ke maman Aji ba haka ake cin abinci ba."
Jimmalo jin abin da yace sai ranta ya ɓaci da sauri ta kalle shi."Wuce ka bai guri mara kunya,
don ni karya ka zan yi." Ta ce mishi tare da daka masa tsawa.
A maimakon ya wuce, sai ya kwashe da dariya, domin kamar shi ma irin taƙadiran yaran nan
ne.
"Maman aji! Maman aji." Ya fara ihu yana faɗin haka jin waƙar da yake yi, sai wasu daga cikin
yaran suka ɗauka har da jan mata hijabi.
Jimmalo cikin tsananin fushi ta miƙe tana huci kamar zata haɗiye su. Ita mamakinsu take yi
domin in har za ta yi musu wani abu, tabbas sai ta illata wani.
Tana shawarar ko ta ƙyale su, amma sai ya ƙara jan mata hijabi. Ba tare da dogon tunani ba ta
fisgoshi tare da maka shi a ƙasa.
Wani irin ihu ya sanya wanda ya sa yaran suka shiga taitayinsu.
"Wayyo ƙafana ta karya ni." Ya furta cikin kuka yana taɓa ƙafar.
Kallon yaran ta yi tana zare ido."Saura ku dama na gaya muku kashe ku zan yi." Ta ce tare da
komawa ta zauna, ba tare da ta damu da ihun da yake yi ba
Ganin ya kasa tashi yana tsala ihu, sauran yaran suka ruga da gudu suka sanar wa Anty. Da
sauri ta shiga cikin tashin hankali. Mamaki sosai ya kamata, na rashin imaninsa tana cin
abincinta hankalinta kwance.
Da gudu ta ƙarasa gurinta ta zuba mata bulalar."Ke wace irin sheɗaniyar yarinya ce? Za ki
kashe musu yaro?"
"Shi ne sheɗani da ya tone n.."
Kafin ta gama maganar ta ƙara zuba bulala. Wanda ya sanya ta zabura ta riƙe bulalar tana zare
ido.
"Dukana za ki yi? Ka ga mini fitsarrarriyar yarinya."
"Wallahi kika ƙara dukana sai na rama tun da bance ya tone ni ba." Ta furta tare da ƙwace
bulalar.
Jin yadda jikinta yake da ƙarfi sai ta sakin mata, domin ko da ta gwada ƙwacewa a yadda ta ji
karfin jikinta ba za ta iya ba."Saki ko in ƙara miki ƙatuwar banza kina ƙatotuwa da ke a sanya ki
a cikin yara."
"Kece jahila da kika kasa gane rashin kunya ya yi mini.."Ba ta ƙarashe maganar ba Principal ya
shigo, ganin tana ƙoƙarin dambe da malamar sai wani ya ruga ya kira shi.
"Safeeya Abdullahi, saki bulalar nan!" Ya daka mata tsawa yana faɗin haka.
Jin tsawar ya sanya ta saki tare da ƙunƙunai. "Ɗauke shi a ka shi asibiti." Ya furta tare da
ƙarasowa ya fara zuba mata bulala.
Tun tana jurewa har ta fara hawaye sosai. Hankalin Principal ya tashi lokacin da aka kira shi,
aka sanar da shi Muntazar ya karye.
Cikin takaici ya karɓi bulalar daga hannun sajan ya ci gaba da dukanta.
"Ku yi mata shegen duka sai mu tafi gidansu."
Don Allah ku yi mini hakuri na yau babu yawa saboda uzuri.
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 23
*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso
kusa kar ayi* *babu ke*
*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*
*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*
*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*
*Iya adadin da kuke so muna turawa*
*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da
hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da
kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*
*Arabian oud*
*Lamsa oud*
*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*
*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*
*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*
*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*
*Adress ringi road, na dorayi, kano*
*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*
*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*
*08130902505*
Sai da suka yi mata dukan tsiya sannan suka tasa ta zuwa gida.
Jimmalo ta ji dukan domin duk juriyarta sai da ta yi kuka.
Mommy da Anty suna kicin girki suke yi. Anty ce take yin gudun kurna, sakamakon abinci da ba
su cinye ba, ya sanya suka ba ri su yi da rana.
Kicin ɗin ya ɗau kamshi Mommy duk ta kosa a kammala. Sai maganar yadda zai yi daɗi take yi,
Anty na yi mata dariya.
Principal tun a hanya ya kira Daddy ya sanar mishi, sannan ya rantse korarta zai yi, domin