Showing 87001 words to 90000 words out of 90573 words
Chapter 30 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
mata tambayar tana kallonta da tuhuma.
"Babu komai." Ta ba ta amsa tana ƙoƙarin fita fuskarta a ɗaure.
Duba ɗakinsa ta yi sai bata ga komai, da zata zarge ta ba, saboda ta mayar da kayan. Ganin
haka sai ta gyara masa ɗakin ta wuce cikin gida.
Jimmalo ba ta fito da bulumbulum ɗin ta ba, sai washegari da ya yi tafiyar, don har ta manta sai
kawai ta tuna. Cikin sauri ta ɗauko cikin kayanta sannan ta fito waje tana ƙoƙarin hurawa, amma
duk yadda ta so ta hura ya ƙi tashi irin na bulumbulum.
"Kai wannan bulumbulum na manya ne bari na zuba masa ruwa." Ta ce tare da ƙarasawa bakin
tanki ta fara ɗura ruwa a cikinsa.
Nufaisah, da ta fito da gudu-gudu sauri-sauri za ta fita daga gidan, saboda makaranta za ta je
kuma suna da test ta yi latti.
Har ta wuce Jimmalo, sai kuma ta ja ta tsaya cikin mamaki tana zare idanunta.
"Safeeya, ina kika samu wannan abin? So kike cuta ta kama ki?" Ta yi mata tambayar tare da
ƙarasawa gurinta tana son ta ƙwace.
Matsawa ta yi ta ɓoye condom ɗin a bayanta.
"Ba zan ba ki ba, bulumbulum ne na ke wasa da shi."
Jin abin da ta ce, sai ta kalle ta cikin mamaki."Ba bulumbulum bane condom ne."
"Ni fa ban san wani candoom ba, kawai ki bar ni na yi wasa da shi." Ta ƙarashe maganar za ta
gudu.
Da sauri ta kai hannu za ta ƙwace ta ce,"Cuta ake samu a cikinsa a gina kika samu? Sannan
abin da ake y.." Sai kasa karasa maganar rashin sanin yadda za ta gaya mata abin da ake yi da
shi.
"A ɗakin wancan mai kama da zabiyan."
"Kina nufin ɗakin Ya Captain?" Ta yi mata tambayar cikin shakku da razana.
"Eh, a ɗakinsa na samu, na san kuma so kike na baki ki mayar masa."
Mamaki da al'ajabin abin da yake yi da shi ya kama ta. Fara tunanin ta yi ko ƙarya take masa,
amma ganin yadda take sanya abin a bakinta tana hurawa, sai ta gasgata bata san abin da ake
yi da shi ba.
"Ke nan ya Captain ɗan iska..." Ta kasa ƙarashe zancen tana son kore tunanin da ya zo mata.
"Kai Ya Captain mutumin kirki ne." Ta ce tare da surfatan Jimmalo, zata kamata ta karɓe don ta
rufe sirrin ɗan'uwanta.
Kamar ta fahimci abin da take shirin yi, sai kawai ta ruga Nufaisah ta bita zuwa falo, tare da
addu'ar Allah ya sanya babu kowa a cikin falon.
Tsananin tashin hankali ya kamata, ganin Mommy da Daddy suna saukowa. Don haka ta juya
zata fita, gudun kar Jimmalo ta nuna musu.
"Nufaisah, kika ce mini kin yi latti?"
"Eh, mantuwa na yi." Ta furta tana sosa kanta.
"Ƙarya take yi Mommy, za ta kwace mini bulumbulum ɗina ne." Ta furta tare da ɓoyewa a
bayanta.
"Bulumbulum, a ina kika samu bulumbulum? Kar dai kin fara ɗaukan kayan mutane a
makaranta?" Daddy ya yi mata tambayar yana murmushi.
"A ɗakin mai kama da zabiya na..."
"Ba na gaya miki Yaya zaki rinƙa ce masa b...."
Maganar ta maƙale wa Mommy, ganin Jimmalo ta tura bakinta, ta fito da condom ɗin za ta
sanya a baki ta hura.
"Innnali wa inna ilahir raju'un! Safeeya, ina kika samu wannan?" Suka yi mata tambayar cikin
tsananin razana.
"A ɗakin Ya Aliyu." Ba ta san lokacin da ta kira shi da ya Aliyu ba ganin yadda suka ruɗe.
"Condoms?" Suka haɗa baki gurin faɗi, lokacin da Mommy ta sanya hannu ta karɓa.
Ganin yadda suka razana, sai ta sakin musu tana zare idanu, domin ta yi tunanin mutuwa ta
riƙe a hannunta.
"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un! Daddy ya furta yana mamakin abin da ya kai condom
ɗaƙinsa."
Mommy kuwa ji ta yi kanta yana juyawa, ta fara zargin yana bin mata ne.
Nufaisah, sai ta rasa tunanin da za ta yi, ta manta makaranta za ta je.
"Aliyu mazinaci ne?" Daddy ya yi musu tambayar cikin tsananin tashin hankali.
Mommy ta rintse idanunta, jin mummunar sunan da ya danganta shi da shi.
"Kai Aliyu mutumin kirki ne, na yarda da tarbiyyar da na ba sh.." Kafin ta gama maganar sai
Lubaynah ta yi sallama ta shigo, wacce ta tsaya a bakin ƙofa jin ana magana cikin tashin
hankali. Nan ta ji duk abin da ke faruwa, sai ta yi murmushin nasara ta shiga ciki.
Saboda tashin hankalin da suke ciki, sai suka kasa amsawa har ta yi sallama na uku. Da ƙyar
Nufaish ta amsa tana kallon fuskarta.
Ganin baƙuwar fuska, sai suka yi ƙoƙarin ɓoye damuwar da ke fuskarsu, amma zuciyarsu zafi
take musu, musamman Daddy, yana jin tashin hankali yana ƙara xiyartarsa.
"Baiwar Allah daga ina?" Mommy ta ce, lokacin da Nufaisah ta kawo mata ruwa da lemu.
"Na san ba za ku gane ni ba, amma ni daga Kano nake sannan na zo da wata magana ne."
Kallonta suka yi, suna mamakin maganar da ta zo da ita.
"Ok, muna jin ki." Cewar mommy da ta kasa motsawa.
"Sunana Lubaiynah,kuma iyayena a Kano suke. Mun ɗauki tsawon lokaci muna soyayya da
Aliyu, har ya yi mini alƙawarin zai aure ni." Ta furta tare da ɗago idanunta ta kalle su, tana son
ganin yadda suka karɓi zancen.
Ganin sun zuba mata na mujiya, sai ta gyara murya ta ɗora da cewa,"Aliyu ya yi mini alƙawarin
aure, har ta kai ga na mallaka masa jikina, sai bayan nan ya ce ba za aure..."
"Ƙarya kike yi sharri za ki yi masa, amma yarona bashi tarbiyyar da ba zai iya kula matan bariki
ba, domin duk macen da take da daraja, ba zata yarda wani namiji ya yi taraiya da ita ba."
Jin abin da Mommy ta ce, cikin fushi sai ta fashe da kuka."Na yarda da haka domin Aliyu yayi
mini alƙawarin aure, amma tun daya ga ya mayar da ni farkarsa ya gama wulaƙanta rayuwata
sai ya ƙi aurena. Da gaske nake yi game da abin dana faɗa domin har kwana na ke yi a
gidansa, wani lokaci in zan yi tafiya tare take tafiya da ni. In kuma baku yarda ba na yarda a kira
shi, sannan a yi bincike. Abin da ya sa na zo na gaya muku, iyayena sun yi fushi da ni sun
daina kula ni. Shi kuma ya gaya mini ba zai auri mace mazinaciya ba, bayan shi ne ya lalata
mini..."
Daddy da yake tsaye yana kallonta, cikin tashin hankali. Wani irin jiri yake gani, domin fuskarta
ya bayyanar da duk abin da take faɗa.
"Aliyu da ma abin da yake aikawa ya kenan, ya sanya ya ƙi aure?" Ya yi wa kansa tambayar,
yana jin zuciyarsa na zafi duhu yana rufe ganinsa.
"Ta shi ki fita kar ki yi wa ɗana sharri, domin zan iya shedar shi. Sai da in wani Aliyu kike amma
ba yarona..."
"Zan iya yarda da maganarta in har ta nuna mini sheda." Daddy ya furta cikin damuwa yana
kallonta
Babu musu ta ciro wayarta, tana share hawaye ta fara nuna musu hotunan da suka yi da Aliyu,
har da waɗanda bai kamata ta nuna musu ba. Daidai lokacin da ta nuna musu, hoton da suka
ɗauka da Aliyu yana kwance da ga shi sai gajeren wando na sojoji ita kuma tana gefenda da
matsatstsun kaya.
Da sauri suka kauda idanunsu cikin tsananin tashin hankali.
"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un Ubangiji!" Daddy ya furta tare da rintse idanunsa yana jin jiri na
ibansa.
Taga-taga ya yi zai faɗi, sai kuma ya dafe kujera jin yadda jiri ke ibansa.
Mommy salati ta furta, tana zare ido cikin tsanannin tashin hankali.
"Tabbas ta yarda ba ka shedar ɗan yau. Ashe duk kame kan da yake yi Aliyu masha'a yake
aikatawa? Sai ta rinƙa jin tamkar za ta haukace, saboda wani irin tashin hankali da yake ziyartar
ta.
Kallon Daddy ta yi, da ya dafe ƙirji yana ƙoƙarin magana, amma ya kasa sai buɗe baki ya ke yi.
Sai kuma ya yi taga-taga zai fadi. Kafin ta yi yunkurin tare shi har, ya yanke jiki ya faɗi ƙasa.
Jimmalo da take kallon su cikin mamakin maganganun da suke faɗi. Mamaki ta fara dama ɗan
iska ne yake mata kallon banza? Lokaci guda ta ƙara tsanar shi, domin tun a ƙauye ta tsani ace
mutum ɗan iska ne. Ba ta manta wani Tanimu da ya ke ɓata mata a ƙauye su. Da Jimmmalo ta
tasa shi a gaba har sai ya bar garin, domin ita ganshi da dutse take raka shi.
Mommy da Nufaisah, suka saka ihu sosai ganin ya kice suna kira sunan shi, amma Daddy ya
sume ƙau babu numfashi.
Ganin ba ya motsi, sai Mommy ta ƙwala ihu ta kira direba. Cikin sauri ya kinkime shi zuwa
asibiti.
Lubaiynah
sai hankalinta ya kwanta ta ɗauki jakarta ta fice. Zuciyarta fes ta san cewa da zarar ya farfaɗo,
dole zai sanya a neme ta don ya aura mata shi.
Murmushi ta saki tana gyara zaman jakanta, domin daga yau ta fara yarda Aliyu zai zamo nata.
Kai tsaye gidan su Fadila ta wuce ta rungume ta.
"Na gode da kika bani shawarar nan, domin mahaifin Aliyu ya sume lokacin da na gaya masa.
Sannan abin mamaki lokacin da na je, sun ga condom hankalinsu ya tashi."
"Kin ga shawarar da na gaya miki ko? Yanzu dai ki jira kira daga mahaifin Aliyu ya aura miki
shi."
"Zan koma gida na zauna ina jiran kira, amma na san cewa zan fuskanci ƙalubale a gurin Aliyu."
"Kar ki damu komai zai wuce."
"Haka ne, amma ba ki ji yadda na ji ba wallahi na tsorata. Don kawai na kira shi ya ce mini yana
hanya, amma da ba zan iya zuwa ba, saboda inda ace yana gidan Aliyu zai iya kashe ni."
"Ki daina jin tsoronsa, ki dake don kin san ba za ki sha ruwan daɗi ba, amma in kika jajirce za ki
same shi a hannu."
"Na gode ƙawar kirki, zan kira ki da zarar mahaifin Aliyu ya kira ni."
"Ok, Allah ya tsare sannan in ya kira ki, kar kiji tsoron idanunsa ki gaya musu gaskiyar abin da
ke tsakanin ku."
"Zan faɗa ai ba zan cuci kaina ba." Ta furta tare ɗaukar jakarta, ta yi mata sallama ta wuce
Kano.
Mommy cikin tsanannin tashin hankali suka isa asibiti. Da sauri likitoci suka yi kansa don bashi
taimakon gaggawa. Ba a ɗauki tsawon lokaci ba, suka yi nasarar farfaɗo da shi.
Mommy fita ta yi daga cikin ɗakin, ta dawo harabar waje. Wayarta ta jawo, ta danna numbar
Aliyu cikin tsananin ɓacin rai.
Alokacin yana Kaduna gidan Anty, suna shirya yarda tafiyar zai kasance kiran ya shigo.
Da sauri ya ɗauka ganin numbar Mommy. "Hello Mommy..." Ya kasa ƙarashe maganar jin yadda
ta kira sunan shi a fusace.
"Lafiya Mommy?" Ya yi mata tambayar tare da miƙewa.
"Ba lafiya Aliyu domin ka bamu mamaki. Ma za ka dawo Kaduna ko da ace ka kai kai inda za ka
je.."
"Mommy, mai ya faru?" Ya ƙara tambayarta yana mamakin abin da ya sanya ta furta haka.
"Babu abin da bai faru ba. Mahaifinka ya yanke jiki ya faɗi don haka asibiti zaka zo..."
"Innnali wa inna ilahir raju'un! Mai ya faru?" Ya ƙara tambayar, amma ba ta amsa mishi ba ta
ce,"In har ka ƙara minti biyar ba ka juyo ba, sai na yi maka Alllah ya isaa nonon da na shayar da
kai."
"Innnalilahi wa inna ilahir raju'un!" Ya furta tare da wurgi da wayar cikin tsananin tashin hankali.
"Captain mai ya faru?"Anty da tun da ya fara wayar, ganin yadda ya canza take tambayarsa.
Rintse idanunsa ya yi yana tuna kalmar da ta furta."Ban sani ba, amma koma mene ne lamari
ne babba. Mommy da gaske take gaya mini za ta yi Allah ya isa ka shayar da ni da ta yi,
sannan da Daddy ya sume yana asibiti." Ya furta cikin damuwa yana jin tamkar zai yi hauka.
"Ya Salam!" Ta ce jin abin da ya faɗa.Lokaci guda gabanta ya faɗi, domin ƙwaƙwalwarta ce ta
hasko mata Lubaiynah ta zo, amma don kar ta ƙara tayar masa da hankali sai bata gaya masa
tunanin da ta yi ba.
"Bari in je Anty Amarya, zan kira ki."
"To Allah ya sa lafiya. Don Allah da ka koma ka kira ki, dole gobe mu zo."
"Zan kira in sha Allahu." Ya furta cikin sanyi muryarsa a sanyaye.
Sharaf ta zauna tana tunanin lamarin. Dama ta san yadda yarinyar take son shi, da wuya ta
zura masa ido ya yi aure. Ko da ya gaya mata zuwan da ta yi, tun lokacin hankalinta bai kwanta
ba. Ta dai ƙyale shi ne ganin yadda yake ta murna.
Tun da ya fita daga ɗakinta yake gudu, ba tare da ya damu da kula da hanya ba.
Daddy a lokacin da ya farfaɗo. Ya buɗe idanunsa yana kallon saman ɗakin a hankali.
"Sannu Daddy." Mommy da Nufaisah, suka taso zuwa gadon tare da furta hakan a tare.
Ba tare da ya amsa musu ba, sai ya fara tunanin dalilin da ya suma har aka kawo shi asibiti.
Lokaci guda komai ya dawo masa, har da hoton da ta nuna masa.
Daddy ya fara ƙoƙarin tashi, amma sai Mommy ta hana shi. Hawaye yake gangarowa yana jiƙa
kan gadon da yake kwance. Yana kwance ya kasa cewa komai. In ya tuna abin da Aliyu yake
aikatawa, sai ya ji kamar zai haɗiye zuciya ya mutu. Kullum ya yi sallah sai ya yi addu'ar; Allah
ya tsare mishi yaranshi daga zina, amma sai ya zamar masa fuska biyu. Sosai yake zubar
hawaye cikin tsananin ɓacin rai.
Mommy mamaki sosai take yi yadda Aliyu ya rufe shi baibai. Ashe iskanci yake yi a can, amma
yake nuna masa mutumin ƙwarai ne. Tabbas Aliyu ya zama fuska biyu. Ya zama kura da fatar
akuya, amma a ransa sai ya ƙudira tunda ya yi masa haka, ya ɗauki alwashin sai ya yi masa
abin da zai kunyata rayuwarsa. Daddy sosai yake ji zafin abin da ya yi masa. Kula yake yi yana
takaicin ɗan da ya haifa da cikinsa ya iya ije mace har yana tafiya da ita. Sai lamarin ya rinƙa ba
shi mamaki, tuna har ya gama samartakarsa bai yi wannan shashancin ba.
Mommy mu ta yi zuru tana kallon sa. Duk rarrashin da take mi shi ya ƙi daina zubar hawaye.
Duk da cewar ita kanta abin ya bata mamaki, amma halin da ya shiga sai ta tsorata, ganin yana
son ya cutar da kansa.
Suna cikin wannan yanayin Aliyu, ya yi sallama cikin tashin hankali ya shigo."Daddy, mommy
mai ya faru?"
Kallonsa suka yi domin sai ya zamo musu baƙo. Sosai yake basu tsoro zama fuska biyu da ya
yi. Tun lokacin ya fara basu tsoro.
Mommy ce ta yi ƙarfin hali, ta ƙarasa gurinsa ta wanka masa mari. Kafin ya gama shanye
mamakin marin Daddy ya rinƙa zuba masa masa lafiyayyu.
"Ashe dama Aliyu abin da kake aikawa kenan? Ashe yaran mutane kake ɓatawa a Abuja? Ka
sa zunubin aikata zina?"
Tambayar da ya yi masa, yafi marin da yake mishi razana shi. Da sauri ya ɗago idanunsa yana
kallon Daddy da yake zuba masa mari.
"Aliyu, ka cuci rayuwarka ka sanya Ubangiji yana fushi da kai! Zina da kake yi Aliyu wane irin
tarbiyya ce ba mu yi maka ba?"
Sai ya ji matsanancin rashin hankali ya ƙara xiyartarsa, har ya kasa cewa komai. Tunanin
yadda a yi suka sani ya fara yi.
"Lubaiynah!" Ya ji zuciyarsa ta zarge shi, sai ya ji tsannanin tashin hankali lokaci guda kansa ya
fara juyawa.
"Wallahi ka bani mamaki Aliyu, ban taɓa tunanin haka daga gareka. A kodayaushe ina gayawa
mutane yarona soja ne, amma kuma na gari, ashe kallon mara hankali suke mini. Duniya ta riga
ta gama sanin kai mazinaci ne, tun da har mace kake ijewa a gidan...."
"Innnali wa inna ilahir raju'un!" Ya furta lokaci guda idanunsa suka kaɗa, sai ya ji tamkar ya
tsaga ƙasa ya shige saboda tsananin kunya.
Dama Hausawa sun ce; kwana ɗari ba ɗaya na ɓarawo, kwana ɗaya na mai kaya. Tabbas haka
ne domin ya daɗe yana sheƙe ayarsa, amma Allah ya tona asirinsa yau.
Rintse idanunsa ya yi, yana fatan ya zama mafarki, domin ji yake ba zai iya haɗa idanu da su
ba. Domin ya yarda ya zama kura da fatar akuya. Sun yarda da shi, amma ya ɓata yardar da ke
tsakaninsa da iyayensa.
Hawaye sosai yake yi ya durƙusa gaban Daddy."Na san cewa na yi kuskure don Allah ku yafe
mini, amma wallahi na tuba tuntuni na zama na gari. Tabbas na aikata ba daidai ba, sai dai duk
na daina halayena."
"Kaconka Aliyu! Ka yaudari ne domin na yi tunanin ƙaryawa za ka yi. Gaya mini za ka yi, ba ɗan
da na haifa da cikina bane yake aikata zina. Na ɗauka za ka gasganta mini cewa gizo idanuna
yake mini har na ga hotonka da ta nuna mini, amma Aliyu kai da kanka kake gaya mini ka
aikata zina. Ina alƙawarin da ka yi mini cewar ba zaka taɓa aikata abin da wasu sojojin suke yi
ba?" Ya ƙarashe maganar yana girgiza shi cikin hawaye.
Kunya, nadama da kuma tashin hankali, suka sanya shi ya sunkuyar da kanshi yana