Showing 15001 words to 18000 words out of 90573 words
Chapter 6 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 5
"Bayin Allah lafiya kuwa, ko dai makuwa ku ka yi?" Ta yi musu tambayar tana kallon su.
"Nan ne gidan Tani ƙanwar Malam Aifi, wanda yake wankin hula. A Ƙauyen Madu?"
"Eh, ni ce bayin Allah ya aka yi kuka san Yayana marigayi Malam Aifi?" Ta furta tare da zare ido
tana kallonsu cikin tsananin mamakin yadda aka yi suka san shi, ganin su 'yan birni kyawawa
da su.
Murmushi ya yi, ganin yadda ta shiga damuwa.
"Ki kwantar da hankalin ki baƙi kika yi daga birni."
"Ikon Allah ni?" Ta yi masa tambaye tana nuna kanta.
"Eh, zan iya shigowa saina yi miki bayani?"
"Ku zan tambaya don yadda na ganku jikinku kamar tsada, wataƙila ba za ku iya shiga ba."
Murmushi ya ƙara yi a karo biyu, ya kalli iyalansa ya ce,"Mu shiga ciki."
Captain Aliyu da yake tsaye yana kallonta a wulaƙance ya ce,"Wa ni? Allah ya tsare ni ku je
kawai." Ya ce masa yana kallonsa yana taɓe bakinsa kamar ya ga kashi.
Ganin abin da ya yi, sai kunya ya kama shi, ba tare da ya iya cewa komai ba, ya shiga cikin
gidan.
"Ni ban san wane irin jarrabawa na faɗa ba, har daddy ya sanya na biyo shi ƙauyen nan, domin
wallahi da na san zan zo ƙauyen nan ba zan dawo ba, saboda takura da kashin shanun da
nake gani a ƙauyen nan, har ji nake numfashinsu zai ɗauke." Ya ce tare da buga bayan motar.
A cikin gida, Kaka Tani mamaki sosai ya kamata bayan sun sanar mata daga inda suke.
"Ikon Allah, yanzu kai ɗan gidan Yaya Binta ne?"
"Eh wallahi nine ɗanta na farko, ita ta turo ni kan na zo na ga inda kike, kuma tun da na gani in
sha Allahu za mu zo."
Kuka ta fashe da shi tana faɗin,"Ashe Binta ba za ta manta da ni ba? Oh Allah dube ka yadda
ka yi ƙatoto abin ka, ka girma ka tara iyali. Rabona da ita tun da ta zo ganin gida a lokacin da ta
yi arba'in ɗinka."
Shafa kansa kawai ya yi, ba tare da ya ce komai ba, yana murmushi.
"Umma, ku ce wa direba ya shigo da kaya a mota." Ya ce yana kallon Kaka Tani da take ta
kallon su, kamar za ta lashe su.
A ƙofar gida kuwa, captain Aliyu yana tsaye cikin ɓacin rai yana kallon wayar da, da network har
yanzu bai dawo ba.
"In har ana son mutum ya mutu ba tare da lokacin su ya yi ba, ace ya yi rayuwa a ƙauyen nan."
Ya ce yana kallon wasu almajirai da suka zo wucewa.
Jimmalo ce take tafiya tana dariya, tuna abin da ta yi wa aljani. Idan dariyar ta ciyo ta har sai ta
daka tsalle.
Ƙawarta Karime ta jawo da sauri wacce ta hango ta, ta rugo da gudu tana nishi.
"Ke zo ki ji labari?"
"Ni ma zuwa na yi na gaya miki..."
"Don ki tsaya ki ji nawa, kin san dai in ina magana bana bari a katse ii?"
"Ina jin ki to." Ta ce tana kallonta.
"Balaraben aljani na tsorata.."
"Aljani kika ce?" Ta yi mata tambayar tana matsawa kamar ita ce aljanin.
"Eh, wallahi yarinya. Ba ki ga yadda ya firgita ya riga da gudu ba." Ta ƙarashe maganar tana
yaba jarumtarta, tare da sakin mahaukaciyar dariya.
"Ni dai na san ance duk wanda ya ga aljanu sai ya mutu Jimmalo?"
"Au ƙarya zan yi miki kenan? To aradun Allah yau idona idon aljani, kuma gani a gaban ki ras
ban mutu ba, an gaya miki ni matsoraciya ce?" Ta ce da muryar ƙatti.
"A'a ni ban ƙaryata ki ba, kawai mamaki na ke yi."
"Ki daina mamaki, ina kan bishiya na ganshi yana tsaye kyakkyawar gaske! Da fari na firgita,
amma da na daure na janyo masa aya, sai kawai ya fara hayaƙi zai ƙone, ganin haka na maka
masa mangwaro , da sauri ya ɓace ɓat." Ta shirya mata ƙarya tana jinjina kanta.
"Kai Jimmalo ki ji tsoron Allah. Ke da ba kya zuwa makarantar allon sai kin ga dama, har
yaushe kika iya karatun da za ki ƙona aljani?" Ta yi mata tambayar cikin mamaki.
"To uban me kika ɗauke ni? Ai gara ni ina zuwa in na yi ninya.. Ke da ko kin je kanki kamar
ɗankwali yake ba ya ɗauka? Ina fa ji ranar nan kina karatun sallah kika ƙaranta addu'ar shiga
bayi a maimakon sura"
"Ni Jimmalo ƙarya za ki yi mini?"
"Ki rantse da Allah ba haka aka yi ba?"
Cikin jin kunya ya ce,"Ai Allah ya halicce ni a haka." Don ta tuna ranar.
"Kar ki yi mini rashin kunya, na ci uban haure mai gindi. Kin san duk da ƙawata ce ke, wallahi
rufe idanu zan yi, na gurza miki rashin mutunci. Yanzu zan wanke miki baki da yashi. Da ma na
ga kwana biyu ba kya wankewa, haka juya kika dame mu da wari da kina waƙa a dandali."
"Hmmmmh! Wai sauba na gaya wa dirimi nisa. Ba gara ni ina wankewa watarana in Innata ta
matsa mini ba, ke kuwa haƙoranki har gansa kuka suke yi."
"Kutumar uba! Wallahi yanzu zan canza miki kamanni, yau ba ki ba fitowa dandali. Sai dai ki yi
kunyar bakinki." Ta ƙarashe maganar tana gyara ɗammara za ta shaƙota.
Dariyar yaƙe ta yi jin abin da ta ce." Ke kuma ba ki san wasa ba? Kamata ya yi ma ki yi mini
kyauta, saboda alkhairi na zo na gaya miki"
"Aikin san bana ɗaukar raini. Ko kujerar maka kika ba ni zan iya gurza miki rashin mutunci, in na
gama sai na yi miki godiya." Ta ce tare da kwance ɗammarar da ta yi.
"To ki yi haƙuri na yadda kin ƙona aljani. Kina jina ko? Yanzu na zo wuce ta ƙofar gidanku,
kawai na ga jirgin sama an faka ta a ƙofar gidan wai kun yi baƙi daga birni."
"Jirgin sama da yake yawo a sama, shi ne aka faka a ƙofar gidanmu.?"Ta yi mata tambayar
cikin tsananin mamaki.
"Zai iya faruwa mana, ba yanzu kika gaya mini kin ƙona aljani ba?" Ta ce mata cikin gatse.
"Share zancen jirgi. Kika ce mun yi baƙi 'yan birni?"
"Eh, wallahi masu kyau, sai shiga ake da abincin birni a gidanku."
"Da gaske kike 'yan birni sun zo gidanmu? Kin san a ƙauye nan, babu wasu wanda suke da
'yan'uwa a birni, sai ɗan maigari da ya yi karatu ya ke aiki a can?"
"Eh mana ba ki ga wani namiji ba, na ɗauka daga sama ya faɗo saboda tsananin kyansa."
"Wallahi in kika yi mini ƙarya sai na koya miki hankali, don har na fara tunanin rashin mutuncin
da zan yi, in rama yangar da yarinyar mai gari take mana."
"Da gaske na ke yi kike ki gan..."
Wani irin sufa ta yi, kawai sai ta ganta a can nesa da ita tana gudu.
"Jimmalo, ki jira ni." Ta furta tare da bin ta da gudu.
Gudu take yi, ba ni da iya gudu ba kamar ba mace ba, duk wanda ya ganta sai ya ɗaga mata
hannu yana faɗin,"Jimmalo jikar Tani."
Ba tare da ta kula su, ba ta ƙarasa ƙofar gidan tana nishi, sai dai da sauri ta tsaya tana zare
idanu. "Innalillahi wa inna ilahir raju'un!" Ta dafe ƙirjinta tana faɗin haka, a lokacin da ta ƙaraso
ƙofar gidan.
"Wa innahu sulaimanu, tuff!tuf." Ta ce cikin razana tana tofawa, ganin Captain Aliyu a tsaye ya
jingina da mota, saboda rashin haƙuri ji yake kamar ya shiga mota ya koma. Sam ya ji ƙauye
bai yi masa ba, da mutanen ƙauyen musamman 'yan matan da suke kallonsa.
Ya saki tsaki, daidai lokacin da wata mai tallar rogo ta zo za ta wuce ta gabansa. Ganinsa da
fari ta tsorata sai da ta fahimci mutum ne sannan ta washe haƙora tana waigensa, har sa da ta
kusa kifewa sannan ta daina kallonsa.
"Banxiya ƙazama kawai." Ya ce yana dafa motar cikin ƙosawa.
"Jimmalo lafiya kika tsaya..?" Ta yi mata tambayar lokacin da ta ƙaraso tana haki.
"Ke na shiga uku! Wallahi aljanin da na ƙona ya biyo ni." Ta ƙarashe maganar cikin razana,
kawai sai ta ruga cikin gida tana ihu.
"Wayyo Kaka Tani aljani na ƙona ya biyo ni." Ta ƙarashe maganar tare da shallake su Daddy ta
haye kan Kaka Tani.
"Ke Jimmalo, lafiyarka ƙalau kuwa?" Kaka Tani da hankalinta ya yi mugun tashi ta riƙe ta tana
tambayarta.
"Aljani ya biyo ni har ƙofar gidanmu saboda na ƙona sa."
"Ina aljanin yake?" Suka haɗa baki har da Mommy da Daddy gurin tambayar hakan cikin tsoro,
tunawa da suka yi Aliyu yace da aljanu, yanzu kuma ita ma ta faɗa.
"Eh, wallahi aljani ne a waje ya biyo ni, saboda na ƙona....". Maganar ta maƙale mata,
sakamakon masu kama da shi da ta gani.
"Kaka Tani, su waye waɗannan?" Ta yi mata maganar tana nuna Nufaisah da ta fi kama da shi
sak! Wacce ta ƙanƙame Mommy tana duk addu'ar da ta fito cikin bakinta.
"Ki natsu baƙi muka yi daga birni." Cewar Kaka Tani tana sakinta ganin ta natsu.
"Birni! Dama muna da 'yan'uwa a birni?"
"Eh mutum ɗaya ce,mahaifiyarta da mamana yan uwane ita ma mijin da ta aura birni yake zama
yana kasuwanci, shi ne da Allah ya buɗa masa ya zo ya tafi da ita. Waɗannan jikokinta ne da
ɗanta ya haifa."
"Har da wanda yake waje?"
"Eh, shi ma ɗan uwanmu ne. Shine ɗana na fari." Daddy yace yana mata wani irin kallo, ganin
yadda ta yi shiri, kamar wata mahaukaciya.
Wani irin dariya ta saki tana kallonsu tana matsawa cikin tsananin farinciki.
"Yan'uwanmmu daga birni?" Sai ta ƙara kecewa da dariya ta nufi Nufaisah da ta yi matuƙar
tsorata da ita ta rungume ta.
Da sauri Nufaisahh, ta matsa saboda wani irin wari da cika mata hanci.
Kallon da take mata ya sanya ta tunzura." Ke dallah me mai yasa kike kallona kamar kin ga
kashi?"
"Ba komai." Ta ba ta amsa da sauri ganin kallon da take mata.
"Kaka Tani ina zuwa."Ta ruga da gudu waje tana faɗin haka.
Kaka Tani dariya ta saki tana kallon inda ta wuce."Jikalle ta ɗaya tamkar da dubu kenan. Ita
kaɗai iyayenta suka haifa suka mutu sakamakon kwalara da suka yi.
"Allah Sarki Allah ya jiƙansu." Suka haɗa baki gurin faɗin haka.
A waje tana fitowa da gudu ta taho zata rungume Aliyu.
"Oyoyo, Yayana daga birni. Yau zagaye ƙauyen nan zan yi da kai, kowa sai ya ga ina da 'yaya
ɗan bir...."
Maganar ta katse sakamakon ingije ta da ya yi, domin da farko ya ɗauka mahaukaciya ce zai
gudu.
"Ke! Are out of your mind?" Ya ce mata tare da wanka mata mari, sai kuma ya matsa yana gefe,
sakamakon wani irin juyawa da jikinsa ya yi, saboda warin da ya shaƙa na jikinta. Kafin ya wani
yunkuri ya shiga kwara amai, saboda ji wani irin ƙarni da hamami jikinta ya ji yana yi.
Marin ya sanya ta tsaya tamkar gunki, domin ta ji shigarshi sosai, har sai da ta ɗauke wuta,
idanunta suka daina aiki na wucin gadi, amma da yake jaruma ce, ba ta nuna ta tsorata ba, sai
kawai ta daure.
Haƙoranta ya kalla, har sai da ya ji tamkar zai amayar da kayan cikin shi, ganin yadda suka
dafe, ga sauran abincin duk sun maƙale sun zama gansa kuka.
Ranta ne ya ɓaci ganin aman da yake kwarawa, wanda ya tabbatar mata da ƙyamarta ya sanya
shi amai.
"Banza ƙazamiya shashasha mahaukaciya! Ke a ba ki da han kawai sai ki zo da nufin ki
rungume ni, saboda ba ki da hankali. Dubi jikinki kamar mahaukaciyar kina ta wari. Dirty girl
kawai."
Zagin da ya yi mata, da abin da ya faɗa wanda ba ta gane da Ylyaren da ya yi mata ba, suka
haɗu suka hautsina ƙwaƙwalwarta wacce ba ta aiki bisa ƙa'ida.
"Kan uba! Ka mare ni? Wallahi daina rama, domin duk faɗin ƙauyennan, babu uban da zai kare
ni ban rama ba." Ta ce tare da nufarsa za ta mare shi.
Captain Aliyu sai mamaki ya kama shi sosai, na jarumtakar da fitsarrarta da kuma rashin
tsoronta. Idanunsa ya xaro yana kallonta. Ganin ta ɗaga hannun da gaske za ta mare shi, sai
kawai ya ƙara ɗaura mata mari ya fara dukanta.
Tun da ta fita hankalin Daddy ya tashi sosai. Ya san cewa da wuya su kwashe lafiya, ganin
yadda take abu kamar sabon kamu.
Jin kukanta ya sa Kaka ta mike cikin tashin hankali tana faɗin,"Innalillahi! Wa ya sanya jikalle
kuka?" Da gudu ta ƙara da har zaninta na shirin faɗi.
Mommy da Daddy suka rufa mata baya, a ransu suna addu'ar Allah ya sa ba zarginsu bane.
Turus! Suka tsaya suna kallonsa da yake kai mata duka.
"Kai mahaukacin ina ne za ka kama jikata da duka?" Kaka Tani ta yi masa tambayar cikin ɓacin
rai.
"Kafin nan sai ki tambayi fitsarrarriyar jikinki mai ta yi mini." Ya ba ta amsa cikin ɗaurewar fuska.
"Amma kai kuwa an yi mara kunya tambadaɗɗe, saboda rashin ta ido ka biyo ta har cikin
ƙauyen su ka buge ta?"
Jin abin da ta ce Daddy ya lalle shi ya ce,"Aliyu bana son hauka kar ka ƙara dukanta."
"Tunanin kasheta ma nake yi, tsaf zan iya sanya bindiga na harbe ta."
"Aiko da wallahi ka jawo ma kanka tashin hankali da bala'i, kuma ba ƙyaleka zan yi ba, saboda
tun da nake da jikalle ta babu wanda ya taɓa sanya kuka."Kaka Tani ta Male shi cikin tsananin
fushi yana faɗin haka.
"Ko yi haƙuri don Allah mu shiga ciki zan yi masa faɗa."
"A"a mugunta ce bana so, haka kawai ya zo ya duke ta? Ya bar ganin don kun kawo mini abu,
wallahi keta masa rashin mutunci zan yi, don zan iya haƙura da kowa a kan jikalle."
"Ki bar shi da ni Kaka Tani. Aradun Allah yau sai na zubar masa da haƙora, sai dai ya sanya na
roba, in ya koma birni." Ta ce tana neman abin da zata rama dukan da ya yi mata.
Zaro idanunsu suka yi, cikin tsananin tashin hankali, ga in ta ɗauko ƙarin dutse ta buge shi.
"Innalillahi wa inna ilahir raju'un! Don Allah Daddy ka yi wani abu kar ta buga masa..." Kafin ta
ƙarasa da daddy ya yi wani yunƙuri ta wurgar masa tana faɗin,
"Na rantse yau sai ka gane ka dauki Jimmalo, sai na canza maka halitta, na bar maka tabon da
za ka rinƙa tunawa da ni."
Cikin sa'a ya kauce dutsen ya bugu gilashin motarsu. Mamaki ya kama su, suna kallon gilashin
da ya tarwatse har sai da suka matsa a gurin.
"Jikalle, ki yi haƙuri ai abin da kika yi masa zai gane ke ba ƙanwar lasa ba ce." Suka ji muryar
Kaka Tani tana faɗi tare da ƙoƙarin riƙeta, maimakon ta yi mata tsawa, don sun yi tunanin mari
masu zafi za ta yi mata ko ta rufe ta da duka, ganin abin da ta aikata..
"Tofa! Waɗannan wasu irin mutane ne?" Mommy ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin
mamaki.
"Ku yi haƙuri don Allah mu shiga ciki." Ya faɗa yana kallon Aliyu da tsantsar mamakin abin da ta
aikata ya kamasa.
Cikin tsananin ɓacin rai ya sarfaci daddy ya shaƙota. Sai da ya ƙara wanka mata mari, sannan
haure ta ya tofar da miyau yana kallonta a yatsine.
"Ƙaxamiya daƙiƙiya jahila kawai! A yau na taɓa ganin ki, kuma zan yi addu'ar Allah kar ya ƙara
nuna mini ko mai kama da fuskarki, domin matuƙar na ga mai kama da ke, xan iya kasheta. Ke
kuwa in har kika bari muka ƙara haɗuwa, kin ji na rantse sai na harbe ki. Bindiga zan sanya na
yi daga-daga da namanki."
"Ni ma zan yi maka kashedin karka yi fatan mu ƙara haɗuwa, saboda na rantse sai na zaman
maka ƙadangaren bakin tulu. Sai na sanya ka tsani duniya da rayuwarka." Ta ce masa ciki tsiwa
da rashin kunya.
Ana riƙe ta tana fisgewa tare da