Showing 12001 words to 15000 words out of 90573 words

Chapter 5 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8075

da take tasa hotonsa tana gani hawaye na bin
kuncinta.

Ranar da takaici ya ibeta, ta karɓe wayarta za ta fasa."Wallahi kin ji haushi shashashar banza
kawai! Haka kawa ki sanya wa kanki damuwa saboda soyayar wanda bai san kina yi ba? Tun
da kika dawo ko kuskuren kiranki bai taɓa yi ba, amma kullum kina rungume da waya kina
kallon hotonsa. Ni ina mamaki da takaicin 'yan matan yanzu da suke ɗorawa kansu fitina da
sunan soyayya. Soyayyar ma so maso wani. Idan ba ya sonki ki yi haƙuri ki nemi Allah ya baki
wanda ya fishi."

"Ba za ki gane son da na ke masa ba. Ni na san in har bai so ni ba, wataƙila sonsa zai kashe
ni."

"Ubangiji Allah ya jiƙanki." Ta ce tare da wurgar mata wayar ta shige ciki.

Zama ta yi ta fara gwada numbarsa, amma har ta gama ringing ba tare da ya dauka ba. Daga
ƙarshe kashe wayar ya yi. Ganin haka hankalinta ya ƙara tashi. Tsaƙonnin ta fara tura masa da
haƙuri.

Aliyu kuwa tun da ta tafi sai hankalinsa ya kwanta. Fatansa kar ta dawo yana ta shirye-shirye
tafiya Kaduna.

A ranar da ya shirya ya kulle gidan, ya bawa Peter makulli da zai rinƙa zuwa yana duba gidan.

"Na gaya maka in har Lubaynah ta dawo kar ka bata makulli, ka barta ta shiga, karka ƙara zuwa
inda na ke."

"Ok sir," Ya ce bayan ya miƙa masa makullin.

Kayansa ya sanya a cikin motar, sannan ya rufe masa bayan motar ya ce,"Oga safe journey."

Kansa ya ɗaga, ya shiga cikin motar da Peter ya gama wankewa, sai ɗaukar idanu da sheƙi
take yi.

Aliyu yana tuƙi ya jingina da kansa, a jikin kujerar motan yana shafa kansa. Iska yake shaƙa
idanunsa lumshe, yana jin tsananin yadda ya yi missing ɗin su.

Sosai Mommy ta shirya ma zuwansa, sanin baya cin abincin kowa, ta shiga kicin ta yi masa
abinci kala-kala.

Da ya isa gida cikin farinciki Mommy ta fito. Sosai take jin daɗin ganinsa, yadda ya yi shiga ta
mutunci.

"Mommy, na same ku lafiya?"

"Lafiya lau ya gurin aiki?"

"Alhamdulillah momi kowa lafiya."

Gaisawa suka yi da Badamasi maigadi, sannan ya shiga cikin gida.

Sashinsa ya wuce ya yi wanka, sannan ya kwanta. Bacci sosai na gajiya ya yi, wanda bai ta shi
ba sai da aka kira sallar magariba.

Bayan ya yi wanka, ya fito daga cikin ɗakinsa, yana duba tsaƙonnin da Lubaynah ta turo masa.

Daddy da yake zaune yana ganin ya shigo cikin falon, ya taso ya rungume shi cikin so da
ƙauna.

"Son, you are welcome."

"Thanks daddy, I missed you."

"Missing you too son." Ya ce tare da zama gefensa.

"Soja mazan fama." Ya ƙara cewa suka yi dariya.

Murmushi ya yi jin abin da ya faɗa, daidai lokacin da Nufaisah ta ƙaraso gabansu ta ce,"Dad,
and Ya Aliyu food is ready."

"Ok," Ya ce mata yana kallon ta sai kuma suka miƙe zuwa dinning ɗin.

Suna cin abinci suna hira cikin ƙaruwar ɗan nasu. Daddy ne ya kalle shi ya ce,"Yauwa kafin ka
tafi don Allah, ina son muje wani ƙauye wai shi Damagaran"

"Ƙauye kuma?" Ya yi masa tambayar yana ya mutsa fuska kamar ya ga kashi.

"Eh, ƙauye ka ji na ce. Ka san Hajiya da rikicinta. Cewa ta yi akwai wata 'yar'uwarta da aka
neme ta aka rasa, sai yanxu suka samu labarinta. Shi ne take son ta je ƙauyen, ni kuma na
hana ta, na ce ta bari na je na ga yanayin ƙauyen. Ka san yadda 'yan baddits suka yi yawa a
ƙauyaku?"
"Haka ne daddy. Besides ni fa sam bana son abin da zai sanya na je ƙauye."

Dariya ya yi jin abin da ya ce,"Ban da abin Aliyu ƙauye ai tushen kowa ne. Duk wanda ka ga
yana birni asalinsa ƙauye ne."

"I really hate village and villagers, saboda wani irin rayuwa za ka ga suna yi, musamman 'yan
matansu babu wayewa da ilmi, ni fa mamaki na ke yadda 'yan matansu suke samun miji, ko da
yake ai maza bagidaju suke aurensu."

"Abincin wani ai gubar wani. Waɗannan matan da kake rainawa, su ne suke sanya maza cikin
wani hali in suka rasa su."

"Shashashu kamar su ba, amma ni ina namiji kamata Daddy ai duk ƙauye babu wanda zan
shiga damuwa saboda ita."

"Don kawai ba a ƙauye kake bane."

"Hmmmmh!" Kawai ya ce tare da ci gaba da cin abincinsa.

"Yaushe za mu je ƙauyen?" Ya yi masa tambayar yana kai loma a bakinsa.

"Please daddy, ku je ban da ni." Ya ce masa cikin rashin kulawa.

"Dole za ka je, domin kowa a gidannan za shi har su Nufaisah da Umma."

Nufaisah ta saki murmushin jin daɗi jin abin da ya ce.

"Yauwa Daddy zan je ni ina son ƙauye, musamman kwalliyarsu dariya suke ba ni." Cewar
Umma cikin farinciki.

"Duka za mu je har da mominku da auta, tun da ranar weekend za mu je."

"Ubangiji ya kaimu lokacin." Cewar Mommie tana kallonsa.

Daddy ne ya kalli Aliyu da ya haɗe rai, saboda tilasta masa zuwa Damagaran da ya yi."Aure fa
Aliyu sai yaushe za ka yi?"

Shafa kansa ya yi yana ɗan murmushi jin abin da ya ce,"Lokaci ne da zarar ya zo zanyi ai
kamar mutuwa yake."

"Shiririta kawai ka tsaya ba wai lokacin ne bai yi ba." Mommy ta furta tana kallon sa.

Jin abin da ta ce, ya ɓata ransa ba tare da yace komai ba, ya ci gaba da cin abincin.

"Ya dai kamata ya yi, saboda lokaci na gudu. In ka duba sa'anninka a Zariya duk sun yi aure har
da yara. Mus'ab ɗan gidan Gwaggo Fatu aure na biyu yake nema, amma kai har yanzu ba ka
fara neman na farko ba.

"In sha Allahu zan yi. Matan ne sai a hankali yanzu rashin tarbiyya da kamun ka ya yi musu
yawa, dole na tsaya na natsu na samu mace ta gari wacce zata bawa yarana tarbiya.." Ya ce
musu yana kallonsu.

"Haka ne ka yi tunani mai kyau amma duk wayonka, da ƙoƙarin zaɓar mace ta gari, dole sai ka
haɗa da addu'a, saboda kamar yadda maza ba a ƙwanƙwansawa haka su ma matan. Shi ya sa
ake son mutum ya zama na gari, sai Allah ya duba ya ba ka mace ta gari mai irin halinka."

Jin abin da ya ce sai gaban shi ya faɗi. Tunani ya yi halinsa, nan take ya ji ya ƙara tsanar
tarayyarsa da Lubaynah.

Duk yadda captain Aliyu ya kaucewa zuwa ƙauye Damagaran, amma bai ci nasara ba, domin
kwana biyar da dawowarsa, Daddy ya shirya sha tara na arziki suka tafi.

A ranar da za su tafi ransa a ɓaci yake. Ya shiga cikin motar yana kallon ƙasa fuskarsa kamar
an aiko masa da mala'ikan mutuwa. Daddy yana lura da shi, amma bai ce masa komai ba, har
suka fara tafiya.

Sun yi nisa yana zaune yana kallon hanya, har suka fara shiga cikin ƙauyuka. Ƙaramin tsuka ya
ja, saboda yadda motar take ta bugawa da duwatsu tana tsalle kamar za ta kife.

"Kai gaskiya ba zan iya tuƙa motarta na shiga ƙauye ba, domin asara kawai zan yi. Haba, ya

kamata a ace an samu cigaba an gyara musu titin su."

"Laifin gwamnati ne ba ta kula da rayuwarsu ba."

Tsaki ya ja ba tare da ya ce komai ba, ya zaro wayarsa ya zai kunna data. Haushi ya sa shi jefar
da wayar kan cinyarsa ganin network ya ɗauke.

Gabakiɗayan su sun gaji da zaman, Captain Aliyu ya kalli Daddy da yake kallon hanya.

"Da wannan nisan Hajiya take son ta zo ƙauyen nan?"

"Don na hanata da tare za mu taho."

"Aiko da tasha baƙar wuya, saboda da na san haka zamu zaunu a hanya, babu abin da zai sa
na zo."

"Wallahi ni kaina na gaji so na ke na huta." Mommy ta ce tana gyara zama.

Nufaisah da Umma da auta duk bacci suke yi.

Sun shigo cikin ƙauyen motarsu ta lalace. Fitowa suka yi cikin damuwa, suka tsaya suna kallon
direba da yake ta ƙoƙarin gyara motar.

"Alhaji, ruwa ne ya yi ƙaranci a motar dole na je tafi na samo." Ya ce masa yana kallonsa tare
da buɗe Boot ya ɗauki jarka.

"Na gaya maka ka rinƙa kula, ka tabbatar da ka duba ruwa da mai, saboda mu kiyaye ɓata
lokaci."

"Sai da na yi hakan kasan ƙarfe nasara."

Shiru ya yi, ba tare da ya ce komai ba cikin takaici. Ganin haka ya sa shi fara tafiya don ya
samo ruwan.

"Karo na farko da na je ƙauye kuma na tsani zuwa." Ya ce tare da dukan bayan motar.

Babu wanda ya tanka masa domin su kansu a gajiye suke.

Fara taku ya yi, yana kallon dajin da yake ɗauke da kayan lambu. Kamar su mangwaro, kashu,
gwaiba, da malmo.

Tsintar kansa da son ganin dajin ya yi, saboda shi mutum ne mai tsananin son shuke-shuke,
domin duk shukar dake cikin gidansu shi ya shukata.

Bishiyar mangaro ya ƙarasa, yana kallon yadda suka girma suka yi jajir. Ba sha zai yi ba, kalan
mangwaron ya burge shi.

Yana ta kallon mangwaron cikin sha'awa, yana tunanin in ya koma sai ya nemi kalarta. Wayarsa
ya ɗauki zai ɗauki hoton.

Daga saman bishiyar kuwa, Jimmalo ce zaune tana ta shan mangaro. Tun da Kaka Tani ta aike
ta, ta je gidan ba ta nan, sai kawai ta taho nan tasha mangwaro. Duk cikin mangwaron ƙauyen
babu wanda take so sai ita.

Tana cikin sha, ta kama reshe ta yi ɗare-dare sai ta kalli ƙasa.

Da sauri ta kama bishiyar tana salati don saura ƙiris ta rikito.

"Wa innahu sulaimanu.Tuf-tuf." Ta ce cikin tsananin razana tare da ƙwala ƙara.

"Wayyo na yi gamo da Balaraben aljani." Ta furta tana zare ido, saboda tsananin kyansa ya
firgita ta. Sam ba ta yi tunanin shi mutum bane, saboda ba ta taɓa kawo cewar mutum mai kyau
kamarsa zai iya zuwa ƙauyen ba.

Captain Aliyu, da yake ɗaukar hoton mangwaron sam bai ji ihu ta ba, saboda tazarar da ke
tsakaninsu.

Yana shirin juyawa, daidai lokacin daidai lokacin da ta furta a ranta.

"Wannan aljanin sam kar ya tsorata ki Jimmalo, domin kin sha tabaraka kin sha yasin. Ki tsorata
shi kawai ya bar gurin ki gudu."

Ga mamaki sai ta ji ta fara rage tsoron. Mangwaro ta tsinko wace ta nuna. Da sauri ta sanya
hannu ta ligwigwitata, sannan ta saita shi ta maka masa aka.

Cikin tsoro ya ɗaya kansa yana kallon sama, sai kuma ya kalli kansa ganin yadda farar
shaddarsa ta lalace, saboda mangwaron ta fashe duk a jikinsa.

Tsoro ya kama shi yana zare ido yana kuma kallon sama

Ganin yadda ya ruɗe sai ta saki dariya tana faɗin,"Shegu aljanu ashe suna tsoron bil'adama."
Ta ce tare da tsinko mangwaron har uku ta ƙara kwaɗa masa aka.

Zafi da takaicin yadda kayansa ya ɓaci suka tunzura shi.

"Ko da ace aljani ne yake jifa na da mangwaron nan, wallahi sai na yi maganinsa." Ya ƙarashe

maganar yana kallon kayansa cikin takaici.

Ganin yana kallon bishiyar kuma zai iya hangenta, sai kawai ta fara girgiza bishiyar tana kukan
jaki.

Da sauri ya bar gurin cikin tsoro. Dakewa ya yi, amma zuciyarsa ta razana.

"Lafiya Aliyu, mai ya faru da kayanka?"

"Please mu bar gurin nan, akwai aljanu a gurin."

Yadda ya yi maganar ya ƙara tsorata kansa, kuma ya tsorata su.

"Mun shiga uku! Mu bar gurin don Allah." Cewar Nufaisah tana kuka saboda tana da tsoron
aljanu.

Bayan Mommy ta ɓoye, don gani take aljanin sun shiga jikinsa yadda yake zare ido.

"Don Allah, mu bar dajin nan, in motar ta ƙi gyaruwa sai ya gyara ya kawo."

"Ku shiga cikin mota in sha Allahu za ta tashi." Direba ya ce yana kallonsu yadda suka firgice.

Cikin sa'a yana kunna motar ta tashi. Da sauri suka shiga ya fara tafiya. Da tarin gajiyar da suke
ɗauke da shi, da kuma tsoro ya sa babu wanda ya ce uffan, har suka ƙarasa cikin ƙauyen.

Gidan maigari suka isa, tare da yi musu kwatancen gidan da suke nema. Maigari ya cika da
mamaki jin sun ambaci Tani. Tsananin mamaki ya kama shi ganin mutane 'yan birni kyawawa
suna nemansu.

"Aminu," Ya yi kiran ɗaya daga cikin ɗansa.

"Na'am," Ya amsa tare da ƙarasowa yana kallonsu kamar zai cinye su.

"Ma za ka nuna musu gidan Tani, kuma kar ka sake ka shiga gidan, ka dai san halin yarinyar
nan."

"To Baba." Ya masa tare da fara tafiya yana kallon su kamar zai lashe su.

"Kai gaskiya ƙauyen nan da akwai sunan da ake kiran inda yafi ƙauye, haka ya kamata a kira.
Dubi ɗan ƙauye kamar a haɗa a yi gida ɗaya, kuma wai a haka suke rayuwa har suke farinciki?
Allah na gode maka da ka halicce ni a birni, domin wannan ƙauye ba shi da maraba da
maƙabarta, shi ya sa tun da muka shigo ventilation ya canza. Ga mutane kamar kaji kuma babu
hyiegene, ai dole ya rinƙa wari." Ya ƙarashe maganar, cikin tsananin ƙyama yana kallon ƙauye

tamkar kashi, sannan ya ɗora da cewa,"

"Ga turosu ake ce masa ko turasa, wannan kashin shanun?" Ya ce yana kallon Mommy.

"Turoso kake nufi?"

"Yauwa eh shi." Ya ce mata yana hangen kashin kamar zai yi amai.

Dariya Mommy ta yi, ba tare da ta ce masa komai ba tana kallon hanya.

Sai ƙorafi yake yana jan tsuka. Su kansu sai da suka yi dana sanin zuwa da shi.

Sun yi shiru suna kallonsa cikin mamaki, jin yadda yake sakin magana, ko kunyar ɗan maigari
ba ya yi.

"Captain Aliyu, zan iya rantse maka akwai waɗanda suke rayuwa a ƙauye nan kuma suka fi ka
farinciki. Ba kuɗi ko jin daɗi bane farincikin rayuwa. Duk wanda ka ga Allah ya halitta, sai ya ba
shi abin da zai sanya shi farinciki."

Kauda kansa kawai ya yi, tare da jan tsaki, ba tare da ya ce masa komai ba. Ji yake ya takura
saboda gabakiɗaya baya jin daɗin ƙauyen..Ga kayanshi da suka yi staining duk da ya goge da
tissue paper.

A lokacin da suka yi sallama, Kaka Tani tana kicin tana gyara tukwane da ta gama wankewa.

Jin sallamar sau uku ya sanya ta zabga tsaki, sannan ta fara tafiya tana faɗin,"Na san ba ya
wuce 'yan kawo ƙara. Bari na je na ji uban abin da za a ce ta aikata, kuma wallahi ko sama da
ƙasa za ta haɗe ba wanda zai duƙar mini jikalleta."

Tana wannan ƙorafin ta isa ƙofar gidan, don bala'i ko sallamar ba ta amsa ba.

"Waye ya dame ni da sallama kamar na ci masa ba shi?" Ta yi tambayar, daidai lokacin da ta
isa ƙofar gidan tana yafa mayafi.

Kallonsa ta yi ta ce,"To yau kuma mai za a ce ta yi? Don na san zuwanka ba alkairi bane."

"Halinta ya sanya ba na zuwa da alkhairi."

"Au rashin kunya za ka yi mini?" Ta ce masa tana kama baki.

"Baba ya ce na kawo ɓaki suna neman gidanki."

"Ni ƙawar mai daddawa! Su waye ne?" Ta yi masa tambayar tana dafe ƙirji.

"Ni ma ban san su, amma a mota suka zo kuma ƙatuwa, don kawai a ƙasa take tafiya da na ce
jirgi ne."

"Nufinka mai kama da jirgi?" Ta yi masa tambayar cikin ruɗu.

"Eh, ga wani sanyi kamar raɓa a ciki."

"Kai muje na gani anya ba makuwa suka yi ba?Saboda iya sanina babu wanda zai zo a mota
yace yana nemana."

Fara tafiya ya yi tana binsa a baya, yayin da zuciyarta take cike da tsoro.

Turus! Ta tsaya tana kallonsu cikin zallar mamaki.

"Su waye waɗannan?" Ta yi ma kanta tambayar tana kallon su.

Kamar yadda take kallonsu haka suke kallonta, musamman Captain Aliyu da yake mata kallon
ƙaskanci.

"Da ma gurin wannan tsohuwar mai kama da lagwani muka zo? Na sha wannan wahalar." Ya
tambayi kansa yana mata kallon sama da ƙasa. Tsananin mamaki ya kama shi, duk da cewar
ya san ba wasu mutane masu aji za su gani ba, amma bai yi tunanin 'yar tsohuwa kamarta za
su zo gurin ta ba. Siririn tsaki ya saki ganin tana sanye da riga da zani da ɗankwali, dukanninsu
daban-daban, sannan fuskarta duk ta yi rama alamun tsufa, har idanunta sun fara shigewa ciki.
Har ta fara duƙawa.

"Bayin Allah lafiya kuwa, ko dai makuwa ku ka yi?" Ta yi musu tambayar tana kallon su.

Wai ya ne readers ba kwa comments gaskiya ya kamata na ga ruwan comments yana tashi.


FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242


Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login