Showing 60001 words to 63000 words out of 90573 words
Chapter 21 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
a yi miki."
"A yi mini dariya, na fasa bakin mutane don ba ni da wasu kayan sai su." Ta ba wa Mommy
amsa tana zare ido.
"Ba zai yiwu ki rinƙa sanya Waɗannan kayan ba, saboda za ki shiga makarantar boko da
islamiya, kuma dole uniform za ki rinƙa sawa."
"Ni fa ba zan zauna da ku ba, dole a mayar da ni Damagaran." Ta furta tare da sakin ihu, ganin
kamar wayo suke son yi mata.
"Za a mayar dake ki zo ki ci abinci."Mommy ta furta tana toshe kunninta.
"Ki dai na mata ƙarya Karimah, dole a gaya mata gaskiya, a yanzu ba ki da 'yan'uwan da suka
wuce mu, kuma a nan za ki zauna tare da mu, don haka ki fuskanci rayuwar da za ki yi gaba.
Kakarki ta mutu kuma duk wanda ya mutu ba zai dawo ba."
"Wayyo Allah! Ni ba zan zauna da ku ba. Amayar da ni ƙauye ku ba zan yi rayuwa da ku ba." Ta
furta tare da fashewa da kuka.
GabakiÉ—aya sai suka zuba mata idanu suna kallonta. Ganin ba za ta daina kukan ba, sai Daddy
ya miƙe ya tsaya a gurinta. Damuwa ce sosai a fuskarsa, saboda gabakiɗaya ta hana su
karyawa ta daÉ—i, sai kallonta suke yi cikin takaici, musamman Mommy da take ji kamar ta rufe ta
da duka.
"Ya za mu yi da ita? Gaskiya kukanta yana damuna?" Cewar Mommy tana kallon Daddy.
"Ita ba yarinya ba ce dole ta zauna. Yanzu ina gama zan je makarantar su Umma na yi mata
rigistration da kuma na islamiya har da hadda, dole in ta ga babu sauƙi ta haƙura."
"Za ta iya guduwa daga makaranta."
"Direba zai rinka kaisu kuma zan gargadi malaman." Ya ba ta amsa kamar ya ƙosa da maganar.
Jimmalo ganin sun shareta suna karyawa, sai ta ɗora hannu akanta ta ƙara fashewa da kuka ta
yi ƙofar gida.
"Wayyo Allah! A mayar da ni Damagaran ba zan zauna a birni ba. Kaka Tani ki taso daga ƙabari
ki tafi da ni." Kalaman da take furtawa kenan, cikin muryar kuka har ta isa bakin get. Zama ta yi
ta É—ora hannu tana ihu.
Sun kasa cewa komai suka raka ta da idanu har ta fice.
Mommy ce ta leƙa ta hange ta a bakin get tana ta ihu. Dai ta dawo ta zauna xuciyarta na tafasa
kamar ruwan zafin da yake cikin kwatami ana shirin saukewa mai jego.
Aliyu
Captain Aliyu a ranar da suka baro England za su dawo Nigeria, sai ya ji kewar gida ya kama
shi. Ya so ya wuto, amma kan dole sai da suka je Barrack don sai da suka yi aiki. Kwana biyu
ya yi, ya shirya zuwa Kaduna. Kasancewar da sassafe ya shirya, domin akwai É—aurin auren da
yake son zuwa, bayan haka yana son ya yi bacci kafin lokacin. Don haka ya yi wa Kaduna
shigowar safiya.
A lokacin da ya fara hon, cikin mamaki Mommy da Daddy suka kalli juna.
"Kamar hon ɗin Ya Captain?" Cewar Nufaisah tare da miƙewa za ta leƙa.
"Ba kama bace shi ne, saboda mun yi waya da shi jiya. Ya sanar da ni da zarar sun gama aiki
zai zo gida, kuma akwai É—aurin auren abokinshi." Cewar Daddy.
Gaban Mommy ne ya faÉ—i, domin ba su san yadda za su kwashe da Jimmmalo ba, amma za ta
san yadda za ta yi masa magana kar ya shiga sabgarta.
Murna suka fara yi daidai lokacin da motar ta shigo ciki.
"Wallahi Mommy Ya Captain ne." Auta ya furta tare da rugawa waje.
Aliyu Gwarzo zaki. Ya fito cikin shiga ta alfarma. Yana sanye cikin dakakkiyar shadda gizna. An
yi masa É—inkin mai kyau riga da wando waÉ—anda suka É—an kama shi kaÉ—an. Takalminsa
agogonsa da kalar gold. Sai bakin glass da ya sanya wanda ya ƙara masa kyawu. Kasancewar
sababbin kaya ne bai taɓa sanya su ba, sai yake ganin sun fi kowanne kayansa yi masa kyau,
har da kakin da in ya sanya yake ji da tamkar wani sarki. Wani irin turare mai sanyin ƙamshi da
daɗi ya fesa wanda ya cika motar nashi. Dama kun san mutumin da son ƙamshi, domin zai iya
kashe ko nawa ne ya siya. Jinsa yake yana É—aya daga cikin jerin mazan da suka amsa
sunansu, saboda kwalliyar da ya yi yana ji da za a je gasar kyawu na maza, tabbas sai ya karɓo
kambun. Shi kansa ya yi wa kansa kyawu domin jefe-jefi yake kallon kansa ta maganin motar
har ya ƙaraso Zariya. Shi kansa yana ganin ya yi kyawu, ballantana ga 'yan matan da suke son
namiji ɗan kwalisa kuma mai tashe da ƙuruciya da kuɗi da nera. Ya san cewa yau sai ya kasa
hankalin ƙawayen amarya, don haka ya gama tsarawa ana ɗaura auren zai dawo gida, domin
ba shi da lokacinsu. Jira yake kamar yadda yake classical ya samu wacce za su yi compatible.
Nishadi sosai yake ji, sakamakon bikin abokinsa da zai halatta. Zuciyarsa ta fara kwaÉ—aita masa
ya kamata ya yi aure, ganin duk abokanansa suna yi, sannan ya rabu da Lubaynah da ta zamar
masa ƙarfen kafa. Lokaci ya yi da zo samu mace ta ƙwarai, wacce namiji bai taɓa riƙe mata
hannu ba. Ya aura sannan ya killace ta a gidansa, su yi rayuwar aure su cikin so da ƙauna.
BuÉ—e motar ya yi yana ji da kansa da isa. Wayarsa ya É—auki da jakarsa daidai lokacin da
ƙanninsa suka rugo cikin tsananin farinciki.
Sai dai me, ya buÉ—e baki zai yi magana sai ya fasa, sakamakon kukan da ya ji mai kama da ma
gardi. Da sauri ya waiwaya inda yake jin kukan cikin ɓacin rai. Kallonta ya yi cikin tsananin
mamaki domin a tunaninsa ko fatalwa ce. Ko kaÉ—an bai yi tunanin ganinta a cikin gidan ba,
domin tuni ya shafe babinta ta, tun ranar da Hajiya ta gaya mishi sun yi rabuwar rashin mutunci.
Ko da suka yi waya da Hajiya ba ta gaya masa tana gidan ba.
"Wancan mahaukaciyar 'yar iskan fa?" Ya yi wa Nufaisah tambayar cikin tsananin tashin
hankali.
"Ta dawo nan da zama Ya Capta.."
"What?!" Ya furta tare da cire gilashin idanunsa.
Kafin ta ba shi amsa cikin tsoro ganin rikicewar da ya yi, sai ya ji muryar Daddy yana faÉ—in,"Eh,
Jimmalo ta dawo gidan nan da zama saboda kakarta ta mutu."
"Kuma Daddy, sai a rasa wanda zai É—auki wannan mahaukaciyar sai mu? Wannan abin kunya
ne tana rayuwa a gidan nan."
"Hajiya ta yi mini umurni da na kawo ta gida nan, kuma marainiya ce ba ta..."
"There's no way! Wannan mahaukaciyar za ta zauna a gidan nan." Ya furta yana harararta
daidai lokacin da ta ƙara buɗe baki ta rushe da kuka.
"Ita kanta ba ta son zama da mu. Kaddara ce ta sanya ta shigowa cikinmu, kamar yadda ba mu
da abin da za mu yi da ya wuce mu rayu da..."
"No daddy, na yi alƙawarin zan ba da ko nawa a kaita wani gida can. Ko gidan marayu ne,
saboda ba zan iya zama da ita ba na tsane ta bana son ganinta, in har kuka sanya ta zauna a
gidan nan zan iya kashe.."
"Kul! Karna ƙara ji. Karka ƙara maganar kisa saboda ba ta da gurin zama sai nan gidan, don
haka ya zama dole ka sanya wa ranka haƙuri, ka ɗauketa a matsayin da ka bawa su Umma."
" I can't babu yadda za a yi, na haÉ—a matsayin masu hankali da mahakauci guri É—aya." Ya furta
cikin ɓacin rai tare da ɗaukar jakarsa, ya nufi cikin ɗakinsa a maimakon falon iyayensa.
Kallonsa suka yi cikin damuwa, ganin yadda yake huci kamar mesa.
"Saboda Aliyu na ji tsoro sosai da Hajiya ta ce anan za ta yi rayuwa, na san cewa dole za a
samu matsala. Ya kamata ka fahimtar da Hajiya Jimmalo ta koma gidanta, saboda bana son a
samu matsala ya karya musu yarinya watarana."
"Hajiya ita ma gudu ta take yi ba zata iya da ita ba. Ni kaina yarinyar nan tun da ta dawo gidan
nan nake cikin damuwa. Dole zan yi magana da shi, sannan na san yadda zan yi ya É—auke ta a
matsayin ƙanwa. Zaman Jimmalo a gidan nan babu fashi." Jin abin da Daddy ya ce sai ta kalle
shi tana girgiza kanta.
"Da kamar wuya hakan, saboda ka san yadda Aliyu yake in ya tsani abu."
Shiru suka yi suna kallonta da take ta ƙara sautin kukanta.
Jimmalo ganinsa sai ta zare idanunta. Duk da cewar ta tsorata, amma sai ta yi maza ta shanye
tsoranta. Ganinsa sai ta ji daɗi sosai, domin dama ce ta samu da zata koma ƙauye, don haka ta
ƙara sautin kukanta cikin zallar taɓara.
Captain kuwa cikin tsananin ɓacin rai ya shige cikin sashinsa. Buɗe falonsa ya yi ya shiga,
sannan ya fara safa da marwa bayan ya ije jakarsa.
"Impossible! Ba zai taɓa yiwu ba yarinyar da na tsana ta zauna a gidan iyayena." Ya furta tare
da dunƙule hannunsa ya naushi isa, sai kuma ya tsaya cak cikin tsananin ɓacin rai. Lokaci guda
ya nemi farincikin da ya zo da shi ya rasa. Turare ya ɗauka ya ƙara feshe jikinsa dashi, domin
ganinta ya sanya shi har ya fara jin warin jikinta.
Ruwan faro ya É—auka ya buÉ—e zai sha, sai kuma ya fasa ya yi jifa da gorar. Jakarsa ya laluba
don ya É—auki sigari, amma sai ya tuna inda yake. Da sauri ya mayar da zif É—in jakar tare da wirgi
da ita, tuna ko ya zo da ita bai isa ya sha ba.
"Ba zan taɓa zama da ita ba dole za ta bar gidan nan." Ya ce tare da kwanciya kan gadonsa
yana mayar da numfashi.
Da sauri ya daga labulen jin ta ƙara tsandara ihu. Cikin fusata ya buɗe kofar ya fice. Saboda
muguntar har sauri yake yi, don ya isa ya yi ball da ita.
Daidai lokacin da ya ƙarasa, Daddy ya fito kamar ya san za a rina."Aliyu!" Ya daka matsa tsawa
da sauri yana zare ido.
Cikin takaici ya fasa haurin ta da ya yi ninya. Kallonta ya yi cikin tsananin ƙyama musamman
kayan da yake jikinta.
"Karka ƙara gigin kai mata duka, saboda in har ka ƙara zan ɓata maka rai." Daddy ya ce cikin
fushi daidai lokacin da ya ƙaraso.
"Daddy this girl is stupid! Doguwar tafiya na yi, amma ta zo saitin windona tana kuka."
"Jimmalo, rashin kakarta ta yi wacce take komai a gurinta, baya haka akai tata wani guri ta yi
rayuwa. Dole sai mun yi haƙuri kafin ta saba da mu."
"No I cant tolerant her nonsense. It either to keep quiet ko na yi mata shegen duka." Ya faÉ—a
cikin zafin rai yana hararta.
"Koma dakinka I will talk to her."
Watsa mata harara ya yi, sannan ya juya tamkar kububuwa.
To Captain Aliyu da Jimmmalo a inuwa É—aya. Ko ya ya zamansu zai kasance? Ku ci gaba da
bibiyar littafin ƙiyayyar jini.
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruÉ—ani. RuÉ—anin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 18
*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso
kusa kar ayi* *babu ke*
*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*
*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*
*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*
*Iya adadin da kuke so muna turawa*
*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da
hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da
kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*
*Arabian oud*
*Lamsa oud*
*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*
*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*
*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*
*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*
*Adress ringi road, na dorayi, kano*
*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*
*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*
í ½í±‡í ¼í¿¾í ½í±‡í ¼í¿¾í ½í±‡í ¼í¿¾í ½í±‡í ¼í¿¾
*08130902505*
Aliyu
Ya ce "No I cant tolerant her nonsense. It either to keep quiet ko na yi mata shegen duka." Ya
faÉ—a cikin zafin rai yana hararta.
"Koma É—akin ka I will talk to her."
Watsa mata harara ya yi, sannan ya juya tamkar kububuwa ya shige cikin ɗaƙinsa. Wayarsa ya
É—auka da makullin mota ya fice daga gidan, domin ya gwammace ya tafi bikin da ya zauna.
"Jimmalo,ki taso don duk abin da zaki yi ba za ki koma ƙauye ba. Yau zan je na yi miki rigistar
makaranta. Ya zama dole ki sami jikinki, saboda ke da ƙauye har bada."
Jin abin da ya ce sai ta ƙara sautin kukanta. Zuwan Aliyu ya sanya ta miƙe, ta nufi cikin gidan,
tun da ya zo sai ta ji sanyi, domin ta san cewa abu É—aya za ta
Saboda ganinta da ya yi, sai bikin bai yi masa armashi ba, domin ko da ya je duk ransa a ɓace
yake har sai da abokanansa suka gane.
Adil ya zauna kusa da shi bayan an É—aura auren, domin daga gurin É—aurin auren walima suka
wuce. Ya san cewa Captain ba ya cin abinci a gurin biki sai drinks, amma yau ko drinks É—in ya
kasa sha, sai juya ruwan faro yake yi yana tunanin yadda zai ɓullowa Daddy Jimmalo ta bar
gidan, saboda da ya tuna ta sai ya ji ransa ya ɓaci sosai.
"Ya ne Captain? " Ya furta daidai lokacin da ya zauna kusa da shi.
Tsaki ya yi ya ce,"Am good."
"No, you seems moody, don ko a gurin É—aurin auren sam ba ka walwala." Ya ce masa yana
kallonsa.
"Am ok." Jin ya faɗi haka sai ya yi dariya ya ce,"Kai ne ka ƙi aure Captain. At this age na ka You
need a wife da za ta rinƙa kore maka damuwarka. Yarana biyu, amma up to now you are steal
single."
Ƙaramin tsaki ya ja, ba tare daya ce masa komai ba, domin gabakiɗaya ba ya jin daɗi. Ganin
haka sai ya tashi ya zuwa wani gurin.
Captain ya daɗe a zaune yana tsaƙawa da warwara. Daga ƙarshe ya yanke shawarar in har ba
su mayar da ita ba, zai koma Abuja kuma ba zai ƙara zuwa ba.
Bai dawo gidan ba, sai dare ko da ya dawo babu wanda ya nema ya ci abincin da ya yi oder a
yatsine ya kwanta, saboda komai na gidan ƙyama yake ba shi. Ya daɗe bacci bai kwashe shi ba
har zuwa karfe biyu na dare.
Daddy da Mommy sun yi tunanin fushin da ya yi wasa ne, amma ganin ya dawo bai neme su
sai hankalinsu ya tashi, musamman da ya sanar musu in har yana nan sai ya shigo an yi
addu'a, sannan ya yi musu sallama ya kwanta.
Mommy ta kalli Daddy da yake aiki a Laptop É—insa."Yaron nan ya yi fushi sosai haka za mu
barshi? Ga duk abincin da aka yi masa bai ci ba."
Waiwayo wa ya yi ya kalle ta ganin yadda ta nuna damuwarta sosai. Ganin haka ya kashe
laptop É—in ya zauna kusa da ita.
"Kar ki damu zai haƙura dole ya sauko. A yanzu Jimmalo ba ta da waɗanda suka fimu. Ina
tausayinta sosai ina son na ba ta kyakyawar rayuwar da watarana za ta yi alfahari damu."
"Shikenan, na damu ne ganin yadda ya É—auki fushi."
"Mune iyeyensa dole ya sauko ya bamu haƙuri."
"Ba matsala Allah ya bamu ikon