Showing 54001 words to 57000 words out of 90573 words
Chapter 19 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
kiran sunanta.
Ta ba su tausayi sosai har sai da Daddy ya yi ƙwalla. Dama ita Hajiya kuka take yi.
Ganin da gaske take yi ba za ta koma gida ba, saboda har an yi kiran sallar magariba, sai
Daddy ya sanya maza suka kai ta gida aka kulle ta.
A ranar bana tunanin ko ruwa ta ka bakinta. Ta yi kuka har ta ji babu daɗi. Idanuwanta sun
kumbura sosai. In ta duba ta ga babu Kaka Tani sai dai kayanta sai ta ji kamar za ta shiɗe. Za ta
iya cewa tun ta girma ba ta taɓa nesa da ita ba, domin ko anguwa za ta je da ita take zuwa na
kwana. In har ba tallah ko dandali suka je ba suna tare, saboda watarana har wasa take taya ta.
Yau ga shi babu ita kuma ana tsammanin ta ci gaba da farinciki? Ita da farinciki har ƙarshen
rayuwarta, domin za ta yi ta ƙunci, tana jiran lokacin da nata mutuwar za ta zo, ta je gurin Kaka
Tani.
Duk rarrashin da suka yi mata, taki yin shiru kuma ta ci abinci. Jimmalo ko haka kawai akwai
kafiya, ballantana an raba ta da abin da take ganin babu na biyunsa a cikin rayuwarta.
Haka ta kwana cikin dare, zazzaɓi mai zafi ya rufe ta. Ba ta sha magani da Hajiya ta bata ba,
don haka zazzaɓi mai zafi ya kamata har asuba tana makyarkyata.
Hajiya da Daddy, kwanar wahala suka yi, saboda babu gurin bacci mai kyau. Haka dai suka
daddage har aka yi sadakar uku. Aka raba gadon da ta bari aka bawa Jimmalo dama ita ce
kawai. Tunkiya guda uku sai kaji da kuma hatsi da take tarawa, sannan sai gidanta ya rage.
A fadar maigari akayi rabon gadon. Maigari ya kalli Hajiya da Daddy ya ce,"Tani ta rigamu gidan
gaskiya Allah ya yi mata rahma."
"Amin," Suka amsa ban da Jimmalo da take sharan hawaye.
"An raba abin da ta bari saura gidanta, domin shi ma ya kamata a siyar a bawa Jimmalo
gadonta."
Jin abin da maigari ya ce, sai ta miƙe tana zare idanu."Wallahi babu wanda ya isa ya siyar mana
da gidan da na ke gani nake tuna Kakata! Kuma in kuka siyar a ina zan rinƙa rayuwa?"
"Ba ki san Kakarki ta bada wasiyar ki koma birni ba? Ai ta gaya wa Audi mai kyamis da Innar
Salame 'yan birni su tafi da ...."
"Kan uba!" Ta furta tare da miƙewa tana zare idanunta, domin ji ta yi kamar wasa ko tsokanar ta
yake yi.
"Ni ce zan koma birni! Saboda me na rantse ba zan bi kowa birni ba, ina nan a ƙauyen nan,
domin rayuwar ƙauye yafi mini rayuwar birni, sannan ba zan je gurin mutanen da nake zargin su
suka cinye mini Kakata ba, domin tun da muka je birni muka dawo Kaka Tani ta fara ciwo ta
mutu."
Daddy da Hajiya zare idanunsa suka yi, cikin tsananin mamaki jin sharrin da ta yi musu.
Jimmalo ina taya ki rashin Kaka Tani domin mutuwa babu daɗi, musamman da ta sangartata ki.
Yanzu ne za a fara wasa yanzu za a shiga cikin littafin. Ƙiyayyar jini akwai cakwakiyar gaske. Ku
ci gaba da bibiyar labarin sannan da sambaɗo zafafan comments.
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 16
"Ni ce zan koma birni, Saboda me? Na rantse ba zan bi kowa birni ba, ina nan a ƙauyen nan,
domin rayuwar ƙauye yafi mini rayuwar birni, sannan ba zan je gurin mutanen da nake zargin su
suka cinye mini Kakata ba, domin tun da muka je birni muka dawo Kaka Tani ta fara ciwo ta
mutu."
Daddy da Hajiya zare idanunsa suka yi, cikin tsananin mamaki jin sharrin da ta yi musu.
"Jimmalo, ki ji tsoron Allah! Bana tsafi ko maitar da zan cinye 'yar'uwata." Hajiya ta faɗa cikin
muryar kuka.
Harara ta banka mata ta ce,"Ban yarda ba, saboda ko qur'ani za ki bani zan dafa ku kuka kashe
mini Kakata."
Daddy kuwa kasa magana ya yi jin sharrin da ta yi musu.
"Magana ta ƙare ko cinye ki za su yi, kin san Allah sai kin bar ƙauyen nan. Dama albarkacin
Tani kike ci, amma yanzu wallahi ba za mu barki a ƙuyennnan ba, in kuma kika kuskura kika
zauna, duk rashin mutuncin da kika yi sai mun yi miki na jaki."
"Dallah malam Jatau, ka fita idanuna kai ne za a ce ka bar ƙauyen nan, tun da ba ka da gidan
kanka haya kake yi. Ni kuwa ina da gidan da Kakata ta bar mini zama daram ɗan karo kawai."
Yadda ta yi maganar, ya tabbatar wa mutane mutuwar Kaka Tani bai canza ta ba.
"Ke Jimmalo wace irin ɗiya ce mara tarbiyya? Wannan tsohon kike wa rashin ɗa'a? Wato
mutuwar Kakarki bai zamar miki aya ba?"
"Au dama kun yi tunanin mutuwarta, zai sanya na kwanta sai ku taka ni yadda kuka ga dama
ko? To yanzu ne zan nuna muku kalata, don wallahi ko yatsa mutum ya nuna mini sai na karya,
saboda babu Kaka Tani dole na miƙe na ƙwaci kaina."
"Tab ashe har yanzu rayuwarki da saura." Cewar Kallah yana mamakinta.
"Ke Jimmalo zauna!" Maigari ya daka mata tsawa yana faɗin haka.
Gungunan ta yi sannan ta zauna a ɗofane. Kallon su take yi tana ganin duk azzalumai ne, sai
kuma ta fara hawaye tuna da yanzu tana bayan kaka Tani tana kare ta.
"Yan birni kun ji wasiyar 'yar'uwarku? Kun dai san babu kyau mamaci ya yi wasiyya ba a cika
masa ba, don haka ya kamata ku cika ku ɗauki wannan guyababbar yarinyar mu samu sauƙi a
cikin ƙauyen nan, saboda mutuwar kakarta kamar wasu kalar rashin mutunci ta fito da su."
"Ni fa ko mai za a ce ba zan bar ƙauyen nan ba, kuma duk wanda ya takale ni wallahi sai na yi
mishi wankin babban bargo ko da gemunsa na jan ƙasa ne." Ta ce tana jijjiga.
Daddy da Hajiya suka ɗago kai suka kalle ta cikin sanyin jiki. Hajiya tsoro ta fara bata. Wato
suna son su raba kansu da masifa su jajiba musu? To amma ya za su yi tunna sune 'yan'uwanta
kuma har ta bar wasiyya. Ta gane kuskuren ta na irin tarbiyar da ta ɗora ta har ta bar wasiyar a
gyara rayuwarta. To ta ina za su fara da yarinyar da bata ganin kowa da gashi, sannan ba ta da
tsoro idanunta a tsaye suke? Irin wannan tarin tambayoyin ya cika zuciyar Hajiya da Daddy.
"Eh za mu tafi da ita a sayar da gidan nata, sai a bani zan koma birni yau." Daddy ya ce yana
kallon maigari.
"Sayar da gida ba mai wahala bane, don ko ni yanzu zan siya, in har za ku bar mana garin da
wannan ja'irar yarinyar."
"Na rantse, in har ka sayi gidan nan sai mun rinƙa muku fatalwa ni da Kaka Tani. Wayyo Kakata
ki taso daga ƙabari ki ga maigari zai sayi gidanmu." Ta ce tana kuka sai ta miƙe tana zare ido.
Tana gani aka kira dillalai aka sigar da gidan. Daddy ya bayar da kyautar kayan gidan yana
shirin raba kayan Kaka Tani ta riƙe akwatin."Na rantse ba wanda za a ba kayan nan. Su zan
rinƙa sanyawa na tuna da Kaka Tani."
Zare idanunsu suka yi suna kallonta."Kayan tsohuwa za ki saka kina yarinya? Ki bari muje birni
zan siya miki wasu."
"Allah ya kyauta an gaya muku zan biku birni ne? Ni ma ku je ku yi tsafi da ni, bayan kun gama
da Kakata. Ina nan ƙauye ko a kusa da ƙabarin Kakata na yi rayuwa."
Kasa cewa komai suka yi, suna tunanin yadda za su sanya ta a mota. "Yarinyar nan fa in har ba
ɗaure ta aka yi ba, sam ba za ta biku ba, saboda in kuka shigar da ita haka za ta iya ja muku
hatsari ba ta da tsoro." Maigari ya furta yana kallonsu.
"Sai a ɗaure mutum da ransa?" Hajiya ta yi tambayar cikin mamaki.
"Wannan ne mafitar da za mu iya tafiya da ita birni, saboda in har ba haka aka yi ba wallahi ba
za ta bimu ba." Cewar Daddy yana kallonta da take tsaye, tana girgiza tana aika musu da
harara.
"To shikenan, amma kar a yi mata ɗaurin da zai cutar da ita." Ta furta tana kallon Daddy.
Maigari da Daddy, ba su tanka mata ba ya wuce ya samo majiya karfi da igiyar. Saboda shegen
wayonta sai ta fahimci abin da suke nufi. Rugawa ta yi da gudu suka bita. Ba su kamata ba sai
da suka wahala sosai, sannan suka yi nasarar kamata bayan 'yan ƙauyen sun taimaka musu,
domin kowa murna yake za ta bar ƙauyen. Samun sa'a ta yi ta yankawa Sa'adu cizo a
hannunsa. Cikin tsananin azaba ya saketa yana ihu. Ƙoƙarin guduwa ta fara suka ɗauke ta. Da
ƙyar suka haɗa hannunta da ƙafafunta
Ɗaureta suka yi, tana ihu tana zaginsu domin har maigari sai da ya samu na shi rabon na
bankwana. Gabakiɗaya ƙauyen babu wanda ba ta yi jam'i ba ta zaga.
Haka suka kamata tana ihu tana kuka, tana kiran sunan Kaka Tani. Sai kuma ta kalli Salame da
jikinta ya yi sanyi sosai."Kina gani za a raba ni da ƙauyen da na taso na yi rayuwa? Salame yau
zan rabu da ku ba za ki zo ki cece ni ba? Mutanen birnin nan 'yan shan jini ne, saboda su suka
shanye jinin Kaka Tani da kuɗin jini suke rayuwa, ba ki ga daular da suke ciki ba. Wayyo ki
taimaka mini."
Kawai sai Salame ta fashe da kuka sosai take jin tausayinta da kewarta. Ta san cewa daga yau
za su rabu. Jimmalo zata koma wata kalar rayuwa, domin ba lallai su yarda ta ci gaba da
rayuwar da Kaka Tani ta ɗora ta a kai ba. Rayuwarta daga yanzu must be hard on her. Sun
tashi tare sun yi faɗa sun yi dambe, domin duk lokacin da zasu haɗu sai Jimmmalo ta takali
mutum, tun da ta san cewa ita ce ke da nasara. Duk dacewar ta girmi Salame, amma ba wasu
shekaru can masu yawa ba. Sosai take kuka tana gani aka sanya a bayan mota.
"Don Allah ku ɗauki mini kayan Kaka Tani na rinƙa sanyawa na tuna ta." Tace cikin kuka.
"Don Allah ku ɗauko mata ina har za ta yi shiru." Hajiya tace tana kallon Daddy.
"Hajiya kayan tsohuwa za a bata wane irin rayuwa zata yi a birni? Da shigar tsofaffi mutane
dariya za a rinƙa mata."
"Don Allah a ɗauko mata, in muka je birni na san yadda zan yi mu raba ta da kayan, amma
yanzu in ba a bata ba, haka za ta yi ta kuka muna bin gari da ita. Kar a ɗauka sato ta muka yi."
"Shikenan a ɗauko mata." Ya ce tare da shiga cikin gaban motar.
Ganin an ɗauko kayan, an sanya mata a inda take kwance sai ta ɗan rage kukan. Ta yi ƙoƙarin
ta kalli glass ɗin windon ta ce,"Allah ya tsine wa duk mutanen ƙauyen nan, tun da bakwa sona
kuma gani za a tafi da ni Birni a shanye jinina, kamar yadda aka shanye na Kaka Tani. Kuma na
rantse ina samu na kufto sai na dawo na cinnawa ƙauyen nan wuta duk kun mutu na yi
rayuwata ni kaɗai." Sallamar data yi musu kenan, lokacin da motar ta tashi ta ci gaba da kuka.
"Alhamdulillah! Yau Allah ya kawo mana ƙarshen annobar kauyen nan. Jimmalo ta bar mana
ƙauye can gasu gada..." Maigari ya furta yana daga kirjinsa cikin murna, domin daga yau ya
daina alƙalanci kullum, saboda a ƙalla a rana ba a kawo masa ƙararta sai biyu ko uku ba, har
fargabar gari ya waye yake yi ya shiga faɗa.
Saboda ihun da take musu, Daddy har da gudun tsiya ya haɗa don ya samu ya iso Kaduna.
Gabakiɗaya ta sanya kishi gajiya, burinsa kawai ya isa gidan Hajiya ya je gidanta sha magani
ya kwanta, saboda wani irin azzabben ciwon kai yake ji.
Ganin sun shigo Kaduna ya sami ajiyar zuciya yana hamdala. Haka Hajiya burinta su iso ya kai
ta gidansa, domin ba za ta iya da ita ba.
Ganin ya yi hanyar gidanta sai kalle shi. Abubakar, gidanka za ka kaita ka haɗa da yaranka ka
riƙe marainiyar Allah, saboda ka san ba zan iyada rigimarta ba? A wannan shekarun nawa."
Zare idanunsa ya yi cikin tsananin tashin hankali."Hajiya, na ɗauka a gidanki za ta zauna sai a
ɗaukar mata mai aikin da zata taya ki tarbiyartar?"
"Wa ni rufa mini asiri na mutu maza su kai ni ba mata ba. Ni Jikar Kulama! Ina na ke da ƙarfin
tarbiyartar da ita? Kawai ka kaita ka haɗata da su Nufaisah ka ga Ummu kusan sa'arta ce za ta
iya koya daga gareta. Ga kuma mahaifiyarsu kai ma duk za ku kulada ita, amma in har na kaita
gidana wallahi zata iya sanya mini hawan ruwa. Don haka in har ba so kake watarana ka zo ka
ga na yi bunga ba, to ka kaita gidanka."
Hankalinsa ne ya tashi ya rasa yadda zai yi. Bai taɓa tunanin Hajiya za ta ce a gidansa za ta
zauna ba. Shi kuwa ya zai yi ya gyara yarinyar da take jin za ta ya karawa da kowa. Tun da har
zata iya kallon tsabar idon maigari ta gaya masa magana don ranta, shi kuma bai san abin da
za ta yi masa ba.
Jikinsa mace ya kalle ta."Bari to na kai ta gidanki in ta yi wanka sai na taho da ita."
"A'a muje ni ma zan je gidanka nayi kwana biyu har sai na ga zamanta a gidan." Ta furta mishi
don ba ta son taje gidan.
Babu yadda zai yi kan dole ya nufi hanyar gidansa. Suna isa ya yi hon maigadi ya buɗe masa
get ɗin. Jin ya dawo duka mutanen gidan har da Mommy suka fito don taransa.
Ganin da Hajiya sai Mommy ta duƙa cikin ladabi, ta gaishe ta tare da yi mata ta'aziya.
Daddy ya buɗe bayan mota ya kira maigari ya zo ya kwance ta. Mamaki sosai ya kama su
ganinta a bayan mota. Tun kafin ta sakko suka ji tana ta aunawa mutanen ƙauyen su zagi.
"Subuhanallahi! Alhaji mahaukaciyar ce za ayi mata magani a birni?" Sa'idu maigadi ya faɗa
yana kallonta, ganin shigarta da zagin da take yi kamar bamagujiya.
"Kai ne mahaukaci bani ba mai kama da goriba." Ya samu na shi rabon daidai lokacin da ya
kwance ta.
"Daddy ba ta da lafiya ne?" Auta ya faɗa.
"Lafiyarta lau ta dawo nan ne za ta rinƙa zama. 'Yar'uwarku ce anan za ta rinka zama da m..."
"What?!" Gabakiɗaya suka ja da baya suna kallonta tare da zare ido.
"Daddy, do you mean ta dawo gidanmu da zama?" Umma ta yi masa tambayar cikin tsananin
ruɗani, tana tunanin yadda za su iya rayuwa da ita a cikin gidan.
"Eh anan za ta zauna saboda kakarta ta rasu, kuma kun zama 'yan uwa domin a nan za ta ci
gaba da rayuwarta. Ke Jimmalo ki shiga ciki." Ya ƙarashe maganar yana kallonta.
Wani irin harara ta so ta banka masa, amma kuma sai ta fasa ta kalli ƙaton gidan. Kuka ta fashe
da shi ganin kyawun gidan.
"Wallahi dama na san tsafi kuke yi, dubi gidanku mai kyau, wannan in ba jinin mutane ake sha
ba? A ina za a samu kuɗin nan a yi gidan nan? Wayyo Kaka Tani mun kai kammu inda za a
kashe mu saura ni."
Sororo suka tsaya suna kallonta jin abin da ta ce. Hajiya ta cire gyalenta tare da jan tsuka ta
fara ƙoƙarin shiga ciki. So take yi ta yi wanka ta bar musu gidan, domin ba za ta