Showing 39001 words to 42000 words out of 90573 words
Chapter 14 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
"Shikenan Allah ya baka ta gari."Ya ƙarashe maganar daidai lokacin da ya fice. Har ga Allah
yana son ya auri Mufida, amma ya san ba zai iya mishi dole ba.
Bayan ya gama gaisawa da mutanen gidan, sannan ya shiga cikin ɗakin Anty fuskarsa a ɗaure
ganin yadda 'yan matan gidan suke rawar jikin gaishe shi.
Da fara a Antyn ta amsa sallamar sa tana kallonsa.
"Na ga ka yi sauri Captain? Lokacin da muka yi waya na tambaye ka don na ɗora girki, amma
kari ga ka taso ko?"
"A'a lokacin wanka na fito." Ya bata amsa yana ƙoƙarin zama kan kujera.
Ɗakin ya bi da kallo cikin sha'awa. Tana da tsafta sosai, domin duk da sauran matan gidan ba a
za kira su da ƙazamai ba, amma ita kaɗai yake iya cin abincinta ruwan ɗakinta.
"Na ga ka yi sauri sosai yanzu da ka shigo na sanya ganye." Ta karashe maganar tare da buɗe
frij ta ɗauko ruwan faro da ta siya mishi, sai zoɓo mai sanyi da ta haɗa da kanta.
"Kar ki damu Anty, ni ma bana jin yunwa ki gama a tsanake."
"Ok, tom bari na je na duba, saboda ganin ka iso na mayar a gas."
Ba tare da ya amsa mata ba, ta fita ganin ya mayar da hankalinsa kan wayarsa da ake kira.
Ganin Lubaynah ce sai ya mayar bai amsa ba.
Hanifah da take tsaye kusa da kofar Anty. Tana ganin ta fito sai ta bita kicin.
"Kin cika zumuɗi Please ki bari ya ci abinci ya natsu."
"To Anty amma ganinsa da yadda yake haɗe rai na tsorata."
"Ya zaki yi? Hakannan za ki daure tun da kin ga ni kina so."
Haɗa hannayenta ta yi, ta murza cikin rashin dubara zuciyarta na bugu. Kallon kanta ta yi sai ta
ga kamar bata yi kyau ba, ganin shiga da kyawun da ya yi.
Daga sashin Maman Mufida, tana zaune da Mufida da ta karaya, ganin ta gaishe shi ya ce mata
lafiya kawai.
"Ki karɓa ki shafa a fuskarki Mufida ki daina jin tsoronsa, duk wannan ɗaure fuska da yake yi.
Namiji ne fa yana fara sonki sai kin yi mamaki."
"Mama Ya Captain daban yake da sauran maza. Ko Hanifa da yake tare da Anty Amarya ba ki
ga kallon bazan da ya yi mata ba."
"Kar ki karaya malamin na ya ce wannan maganin na farinjini ne, kuma mai kyau ne. In har
Aliyu ya haɗa fuska dake zai kamu da sonki. A yarda ya yi mini bayani kece wacce ake son ya
fara gani."
Ganin ta karɓi maganin mai kama da turare a sanyaye, sai ta ce,"Ki tashi mana ga Hanifa can
da wancan makirar matar suna magana. Kika sani ko suma sun je gurin Malami ne? Ni wallahi
na tsani yarinya can ƙarama da ita, amma sai kinibibi ko yadda ya shaƙu da ita bana tunanin
haka ta bar shi. Tun damu da aka haife shi a gaban idanunmu, bai saki jiki damu ba sai ita
zuwan jiya."
Mufida miƙewa ta yi, ta buɗe labulen windonsu, tana hangen Hanifah Anty Amarya da suke
magana.
Ƙara gyara fuskarya ta yi, bayan ta shafa turaren maganin. "Yauwa kar ki karaya ma za ki je,
sannan ki tabbatar da kun haɗa idanu."
"To," Ta ce tare da buɗe ɗakin ta fita cikin sanyin jiki.
Ganin haka ta kamo tare da riƙe mata hannu."Ki kwantar da hankalinki, ba ki da wani miji sai shi
duk yadda zan yi na fita, sai na sai na yi kin auri Aliyu, don haka kije ko ya yi miki rashin
mutunci kar ki damu kin ji? Dama duk abin da kake so sai ka wahala."
"To Mama." Ta ce tare da ficewa.
Anty ta fito daga kicin ɗin, ɗauke da kular dambu ta shiga cikin ɗakin. Yana zaune da waya a
hannunsa fuskarsa ɗauke da murmushi. Chatting yake yi da Lubaynah tana gaya mishi ta yi
missing ɗinsa. Hotonta ta tura masa, wanda ta ɗauka cikin wata rigar bacci, mai shigen kyau da
ta siya boutique.
Lumshe idanunsa ya yi, lokaci guda suka yi ƙanana ganin kyawun da ta yi a cikin rigar. Kallon ta
sosai yake yi yana jin feelings ɗinta na ta so masa.
Gwalo ta yi masa tare da sakin masa kiss da stikers. Murmushi yake yi sosai.
Sojana, ka yi sauri ka dawo Abuja in har rigar tayi mata kyau, saboda na siya sun fi kala goma.
Ina fatan ina sanya maka ɗaya, sauran na yi amfanin da shi a matsayin matarka?
Tsaki ya yi tare da neman tsari da addu'ar da ta yi.
Yana ƙoƙarin bata amsa, Anty Amarya ta yi sallama ta shigo. Kashe wayar ya yi, sannan ya
amsa yana kalonta.
"Abinci ya sauka azo aci dambu." Ta ce tare da ije mishi kula, a gaban shi tana kallonsa.
Ije wayar ya yi, sannan ya sauko ƙasa ya shaƙi ƙamshin dambun, tare da lumshe idanunsa."Kin
san na yi missing dambun nan? Kwanaki sai da na ji kamar ki yi mini na turo a karɓa."
Dariya ta yi jin abin da ya ce,"A kawo dambu tun daga Zariya har Abuja?"
"Eh za a iya mana. Ina fatan matata macen da ta iya abincin gargajiya kamar ki, saboda Anty
ina son abincin Hausawa don kawai Peter bai iya bane, amma kuma ina jin daɗin abincinsa."
"Auren dai shi ne za ka yi, sai ka samu wacce ta iya girkin Hausawa."
"Shi ya sa na ba ki zaɓi."
"Zaɓin ka yana da wuya, ba kowace mace za ka samu da abin da kake so ba."
"Za a iya samu zan ci gaba da nema. Ina da burin na auri salihar mace wacce ranar first night
ɗinmu zai zama memorable, amma kin ga Anty duk 'yan matan nan yawancinsu second hand
ne."
"Akwai mata na gari masu kare mutuncin kansu Aliyu, don mace ɗaya ta bada kanta bai zama
hujjar da za ka yi musu jam'i ba, kuma in kana son irin matan nan sai ka je ƙauye akwai yara
sosai a ƙauye waɗanda na sa zance da maza. Wasu ma ba su fahimci mene ne auren ba, sai
ka ɗora su a hanya."
"God forbid!" Ya ce tare da murza hannunsa.
Hmmmmh Captain ka tsaya ruwan ido ba zan ce komai ba. Aci gaba da zafafan comments
yanzu aka fara.
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/KusyXgwh9wEAHDTn6dzD43
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 12
Tallah
Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin
result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka
sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan
ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama
kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast
Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta
wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na
gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da
ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina
shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606
ina zaune a kano
"Akwai mata na gari masu kare mutuncin kansu Aliyu, don mace ɗaya ta bada kanta bai zama
hujjar da za ka yi musu jam'i ba, kuma in kana son irin matan nan sai ka je ƙauye akwai yara
sosai a ƙauye waɗanda ba sa zance da maza. Wasu ma ba su fahimci mene ne auren ba."
"God forbid!" Ya ce tare da murza hannunsa.
Ganin haka ta kalle shi cikin mamaki."Anty da na auri 'yar ƙauye gara na mutu ban yi aure ba.
Matan ƙauye har wani abu suke dashi wanda namiji zai kalla? They are illiterate kuma ba su da
wayewa."
"High expectations na ka yayi yawa kan matar da zaka aura. Ni kaina zan so na ga mai sa'ar da
zaka ɗauko mana."
"In sha Allahu macen kirki mai natsuwa da kamun kai zan aura."
"Ina maka fatan hakan, Wani lokaci sai ka ga namiji ya kasa aure ya yi ta ruwan ido, amma
daga ƙarshe sai ya je ya zaɓi macen da duk 'yan matan da suka so shi ba ta kaisu ba."
"To ni na daban ne Anty yadda na ke da kyau ga kuɗi ga kyawu, kin san matar da zan aura kaf
a family ɗin mu babu kalarta. Ko Ya Anas ɗan gidan Baba Lamiɗo da na ji ance ya auri shuwa,
matar da zan aura sai ta fi tashi kyau. Kin san saboda ni mijin mace ɗaya ne shi ya sa zan duba
da kyau, don kar na zo na yi zaɓen tumin dare."
"To ko Shuwar za ka ɗauko mana?"
"A, a cikin Hausawa akwai 'yan mata kyawawa waɗanda suka fisu kyau. Ku dai jira lokaci ku ga
matar da zan kawo cikin family."
"Muna jira kuma muna taya ka da addu'a. Allah ya ba ka na gari mai tsoron Allah."
"Amin,"Ya amsa tare dakai hannu yana ƙoƙarin buɗe kular.
Mufida da ta ga Hanifa na ƙoƙarin shiga, da sauri wuce Hannifa da ta buɗe ɗakin za ta shigo.
Sallama ta yi gabanta na faɗuwa. Anty ce kawai ta amsa, amma shi sai ya mayar da murfin
kular ya ɗauki wayarsa.
Kafin ta yi magana Hanifa ta yi sallama ta shigo.
"Ya Captain ina wuni ka zo lafiya?" Mufida ta yi saurin faɗin hakan muryarta na rawa.
Ba tare da ya ɗago idanunsa ba ya amsa da cewa,"Lafiya."
Ganin haka sai jikinta ya yi sanyi sosai.
Hanifa ta kalli Anty Amarya kamar za ta yi kuka. Da idanu tayi mata nuni da ta gaishe shi.
"Ya Captain ina wuni?" Yadda ta yi maganar cikin sanyin murya, mai haɗe da tsoro shi sanya
ɗago idanunsa.
"Lafiya lau ya karatu?" Ya ce mata sannan ya mayar da kansa.
"Alhamdulillah hutu muke yi."
"Ok," Ya ce yana danna wayarsa.
Ganin haka duk suka yi shiru jikinsu a mace. Ba tare daya kalle su ba ganin sun yi shiru ya
ce,"Please I need my space zan ci abinci."
Da sauri suka miƙe suka fita Hanifa har da hawaye, domin tana son shi sosai.
Mufida cikin kuka ta yi ɗakin Mamanta. Tana shiga ta fashe da kuma. Da sauri Mama ta taso ta
rungume ta."Ko kallona bai yi ba, domin gara Hanifah har yana tambayarta ya makaranta kuma
ya kalle ta."
"Zai kalle ta mana tun da matar ubanta ta shanye shi. Ai ni dama tun da aka auro Maryam na
san sai haka ya faru, saboda ubanta malamin zaure ne fa. Yar kusfa duk wanda ya aure ta ai ya
san mai ya auro wa kansa. Shi kansa Yaya Sama'ila ba ki gata shanye shi da kamar yadda ta
shanye uwar Hanifah? A ce kishiya kin bar mata yaranki sun saba da ita."
"haka ne don Allah ni dai Mama ki yi wani abu bana son na rasa shi, kuma in har ba zai aure ni
ba, bana son ya auri kowa a gidan nan, domin zan iya kashe kaina in har ya auri Hanifa."
"Ki bari kawai, wallahi kin ji na rantse ko suna tsafi da mutum in dai Ali bai aure ki ba, ba zai auri
kowa ce yarinya a gidan nan ba. Zan je na samu Anty Amina ai ta an wani malami a kusfan."
"Yauwa Mama," Ta ce tare da share hawayenta sai ta zauna kan kujera, tana ayyana abin faɗa
ta yin in ta zamo matarsa. Kallon irin soyayyar da zata yi masa take yi.
Hanifa kuwa tana shiga cikin ɗaki sai hawaye. Zama ta yi kan kujera Mama ta kalle ta watsar
tare da sakin tsaki.
"Iska na wahalar da mai kayan kara.Na gaya miki ba a dole ba ya son ki dole za ki yi masa?" Ba
ta amsa ba sai hawayenta ya ƙaru.
Yayanta Musa ne, ya fito daga cikin ɗakin Mama bayan ya gama shafa mai. Kallonta ya yi yana
faɗin,"Mama, mai ya samu Hanifa?"
"Wahala da ta ɗorawa kanta. Kasan Aliyu ya zo yau?"
"Don Allah yaushe? Ai ban sani ba, bari na je na samu rabona, wataƙila alkhairi ya dawo dani
kasuwa."
"Ya zo bai jima ba son shi take yi, kuma ba ya sonta. Na gaya mata ga yaron nan Auwal da
yake sonta. Yanada ilmi ɗan gidan malamai, sannan ya gama masters ɗinsa yana aikinsa,
amma kin tsaya kina wahala kan wanda bai damu dake ba."
"Wallahi ki cire sonsa, saboda irinsu Ya Captain idanunsu a bude yake. Sam ba zai aure ki ba,
domin ki jira kiga matar da zai ɗauko."
Kuka ta fashe da shi ta shige cikin ɗaki. Tsaki Mama tayi ta ci gaba da ƙullum alala.
Bayan sun fita sai ya kai hannu ya buɗe kular yana murmushi."Anty an ya ba zan tafi da
dambun nan ba? Saboda ƙamshinsa kawai ya tabbatar mini da ya yi daɗi?"
Dariya ta yi ta ce,"Kai Aliyu, daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaki?"
"Anty ai kin iya girki da ace kina da ƙanwa ko bata da kyau zan aure ta, saboda na rinƙa cin
abinci mai daɗi."
"Allah sarki auta ce ni a gidanmu."
"Na sani ai Anty." Yace tare da kai loma. Ya lumshe ido yana santin abincin.
Ya kai loma na biyu bakinsa sai ya tuna da haƙoran Jimmalo, da sauri ya zubar da abincin yana
ƙaƙarin amai. Hankalinta ne ya tashi sosai ta miƙe tare da yin kansa tana faɗin,"Lafiya Captain,
ko ka haɗiye ƙashi ne?"
Ganin yadda ta rikice ya kalleta."Ki kwantar da hankalin bakin wata ƙazamiya na tuna?"
"Baki wace ce ita kuwa da har za ka yi amai, sannan a ina ka ganta?" Tayi masa tambayar tana
mamakin wace irin ƙazama ce ita.
Ganin ya kasa amsawa yana ya mutsa fuska, sai ta ce,"Mai zai kai ka kallon bakin
mahaukaciya?"
"Ba mahaukaciya bace wata irin ƙazamiya, jaka, wawiya, dabba, kuma dakiya na haɗu da ita."
"A ina Captain?" Ta yi masa maganar cikin mamaki.
"Gidan Hajiy.."
"A Kaduna Hajiya K.D?" Ta tambaye shi tunkafin ya gama maganar.
"Eh, amma yar wani ƙauye ne wai ko damagan ne ko me?"
"Sabuwar yar aiki ce?"
"A'a kin san Hajiya da kwashe-kwashen dangi. Wai Kakar yarinyar ƙanwar mahaifiyarta ita haifi
kakar, shi ne kwanan nan ta samu labarinsu, ta sanya muka je ƙauyen. Ina kika ga abin da
yarinyar nan tayi mini sai kin yi mamaki. Ba ta da tarbiyya sannan gata kamar aljana don muni.
Ganinta na farko sai da na yi amai."
Dariya sosai ta kwashe dashi ganin yada yake maganar da gaskiyarta."Ita kuwa wannan
yarinya wace irin ƙazamiya ce?"
"Inda akwai abin da yafi ƙazama za a kira ta, domin da za a bani qur'ani na rantse bata wanka
zan iya. Wallahi ƘIYAYYAR JINI na ke mata, saboda ina ganta jinin jikina har tafarfasa yake yi."
"Taɓ! Ni kuwa zan so ganin yarinyar nan."
"Tana gidan Hajiya ta ɗauko su suna sanya mata yawan jini. Ina komawa zan sanya Daddy ya
mayar dasu ƙauyensu, domin in muka barta dasu, wallahi sai dai Hajiya ta yi bunga ta faɗi ta
mutu. Ni fa a yadda na tsani yarinyar nan Anty zan iya harbin ta da bindiga."
"Kai Aliyu ba a zurfafa so da ƙiyayya." Ta ce masa tana kallon sa.
"I hate her I can explain but I hate her with my whole being."
"Zan so in ga wannan yarinyar kuwa."
"Kar ki yi fata zata iya sanya ki amai." Ya ce tare da mayar da murfin