Showing 9001 words to 12000 words out of 90573 words

Chapter 4 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8084

kenan? Ita Lubaynah da ka ɓata, wa kake son ya aure ta?"

"Kan me za ka tambaye ni? Sai ka ce ni na kawo ta barikin?"

"Saboda ita ma watarana uwa za ta zama, amma ka ɓata mata rayuwa, Lubaynah is not wore
son ka ya sanya ta aminta da kai."

"Dole na yi mata? I didn't force her, kuma ni kaina ina fatan Ubangiji ya shirye ni na daina aikata
hakan."

"Hmmmmh!" Ya ce masa yana kallonsa cikin mamaki ganin ya haɗe rai.

"Ni dai a tunanina bai kamata ka yi wa Lubaynah haka ba, musamman da she was virgin kai ka

fara sanin..."

"Kuma ni na kawota barikin da za ka tilasta mini na aure ta? Na ga kaima ya kamata ka auri
matan da kake hurɗa da su."

"Duk cikinsu babu wacce na fara saninta. Sannan Lubaynah yarinya ce, wacce ta fito daga
gidan mutunci. Iyaye ta they well of. Ga shi duk tana da qualities da kake so."

"Ba zan iya aurenta ba, kuma don ni na fara sani ta bani da tabbacin ni kaɗai take kulawa,
sannan inda ba ta yi ninyar zama, mara kamun kai ba za ta yarda da ni ba."

Cikin mamaki yake kallonsa."Yarinyar nan fa soyayyar da take maka ya sanya ta faɗa irin
rayuwar nan."

"Ok, in na fahimce ka, so kake sai ka ce dole sai na aure ta? Tun ba yau ba na sha gaya maka
matar da zan aura. Yarinya natsatstsiya mai addini, wacce na san iyayenta sun ba ingantacciyar
tarbiyya, sannan ba zan yarda na auri mace jahila mara ilmin addini ba. Duk cewa da kake
Lubaynah na da ilmi, sam ba ta da na addini, domin duk macen da ta je makaranta, ba za ta
mallaka ma namijin daba muharraminta kanta ba. So don haka Please kar ka ƙara mini
sha'awar mace irin ta. I dan na tashi aure za ka yi mamakin uztaxiyar da zan aura."

"Da irin halayenka Captain Aliyu? Karka manta azzaniyatu wazzani."

"Wace mace kaga na taɓa kulawa, bayan Lubaynah da ta kawo mini kanta?Da har za ka
danganta ni da auren mazinaciya?"

"Ina dai ba ka shawarar ka aure ta, saboda duk saboda kai ta faɗa wannan harkar."

"Ba zan iya auren mace da ranar first night ɗinmu, zai kasance mini baƙar rana ba, domin na
riga na santa sam ba zan yi ɗokin ranar ba. Bayan haka da kake cewa na aure ta, wane
tabbacin kake da shi na cewar ni kaɗai take kulawa? Ni fa ban yarda da ita ba, saboda idanunta
ya buɗe, don haka ko xan yi mu'amala da ita sai na yi amfani prevention."
"Duk ba mafita bane Captain. Sannan Lubaynah ba za ta zura ido tana kallo ka yi aure ba,
yarinyar she is mad in loving you. Za ka kunna wa kanka wutar da ba za ka iya kashewa ba.
Kasan yadda mahaifinka ya yarda da kai, amma ka zamar masa fuska biyu. Duk ranar ta da ta ji
za ka yi aure. Tabbas za ta sanar da iyayenka, kuma hakan zai rushe yardar dake tsakaninka
da su. Kar ka manta ka yi wa Daddy alƙawarin duk ranar duk ranar da ya kamala da wani hali
mara kyau za ka ije aiki, ko kuma ya ɗauki duk hukuncin da ya ga dama. Ina ba ka shawarar, ka
auri Lubaynah in ya so sai ka auri kalar macen da kake so."

"Duk abin da za ka ce, sam ba zan yarda na auri mace da ta siyar da mutuncinta a waje ba, don
haka ka daina wahalar da bakinka, sannan am very smart and wise, Daddy ba zai taɓa gane

fuska biyu na ke da shi ba."

"Hmmmmh! A juri zuwa rafi watarana tulu zai fashe. I'm a good friend am just advising you. Ka
san A friend in need is a friend indeed."

"I know my friend, stop fearing am so wise nothing bad will happen."

"I hope so." Ya ce masa sai kuma ya buɗe baki zai kara cewa wani abu, domin yana kallonsa a
matsayin azzalimi mai son kansa.

"Please let's change the topic. I'm frustrating." Ya ce masa cikin ɗaga murya.

Dariya ya yi ganin lokaci ɗaya yadda ya hau. Hannu ya ba shi da nufin su tafa, amma sai ya ƙi
yana harararsa.


Lubaynah 'ya ce ga wani shahararren mai kuɗi a garin Kano, mai suna Alhaji Adamu Laska.
Mutum ne da yake da kantina sosai a garin Kano. Matarsa ɗaya kamar rai Hajiya Shuwaima.
Suna da 'ya'ya huɗu, ita ce ta biyu tana bi wa Yayarta Hannah da take aure a garin Abuja.
Rayuwa suke yi cikin hutu da sangarta, domin a gidan duk abin da suke so shi suke yi.
Mahaifinsa ba ya zama mahaifiyarsa 'yar boko riƙaƙkiya, sam ba ta da lokacin kanta. Rayuwa
suke yi kowa abin da ya ga dama yake yi. Sakandire da firamare duk a Kano ta yi, bayan ta
kammala ta shiga Jami'ar Abuja. Sosai idanunta ya buɗe, domin mace ce classical wacce ta
iya wanka.

Ta haɗu da Captain Aliyu, a lokacin da ta raka wata mate ɗinta, Barrack ɗin sojoji gidan 'yar
uwarta. Captain Aliyu shi kuma mijinta abokinsa ne. Tun ranar da ta ganshi ta mutu a kansa. Sai
dai duk nacinta kallon kirki ba ta samu ba.

Tana mugun sonsa kamar za ta kashe kanta. A lokacin da ta bayyana masa ƙaunar da take
masa, sai ya watsa mata ƙasa a ido, domin bai ɓoye mata ba, ya sanar mata ba type ɗinsa
bace. Hankalinta ya yi mummunar tashi sosai ta shiga cikin damuwa.

Ta rinƙa nace masa tun ba ya kula ta, har ya fara kulata. Ganin ta kasa samun kansa sai ta
shiga seducing ɗinsa, domin a tunaninta wannan hanyar kawai za ta iya shawo kansa.

Captain Aliyu, tun yana shareta har ta ci karfinsa ya fara kulata, domin a wancan lokacin
tsananin addu'a da tuna kashedin da Daddy ya yi mishi, ya sanya shi ɗauke kansa daga matan
bariki, duk da yadda abokansa suke ƙoƙarin cusa masa wannan halin. Sai dai, shigowar
Lubaynah cikin rayuwarsa, ya sanya shi manta alƙawarin da ya yi wa mahaifinsa. Samunta da
ya yi a matsayin budurwa ya sanya ta samu daraja a gurinsa. Wani lokaci in zai yi tafiya, har
ɗaukar ta yake yi su tafi tare. Shi kansa yana sonta, amma ba soyayyar aure ba. Wani lokacin
inta ɓata masa har dukan ta yake yi, amma ta kasa rabuwa da shi. Burinta kawai ya tura a yi

bikinsu, amma kullum ta yi masa ƙorafin haka sai ya fara kaukauce mata yana kawo mata ƙauli
da ba'adi.

Washegari bayan sun tashi ta yi sallah. Kicin ta nufa don ta haɗa musu abin karyarwa. Tan
ƙoƙarin ɗora ruwan zafi a gas, ya dawo ya buɗe ƙofar kicin ɗin ya shgo.

Ganin za ta ɗaura girki ya ƙarasa gunta."Ki bar Peter ya yi mini breakfast, na gaya mini daga
abincinsa sai na Momi na ke iya ci."

Kallonsa ta yi cikin takaici ganin ya kushe ƙoƙarinta."Haba baby, duk lokacin da na so na faranta
maka sai ka nuna ba ka so. Nufinka in mun yi aure wa zai rinƙa muka abinci?"

"God forbid." Ya furta a ransa amma a fili jawota ya yi zuwa jikinsa.

"Kar ki damu da wannan ki bari lokacin ya yi, bayan nan matata ba za ta rinƙa girki ba."

"Don Allah Sojana, ka amince ka turo iyayenka gidanmu ayi maganar bikinmu. Ina sonka na
matsu da mu yi aure." Ta ƙarashe maganar hawaye yana bin fuskarta.

"Mene ne abin damuwa bayan muna tare? Ina sonki kuma kina mini duk abin da na ke so,
sannan duk lokacin da kika buƙaci ganina za ki iya zuwa gidana. Haka kuɗina ATM ɗaya na
baki, a ganina rayuwa mu ke yi kamar mata da miji..."

"Akwai bambancin sosai. Aure yanada daraja kuma ko ina ana bayyana shi, amma zamammu
babu wanda zan yi fatan ya sani. Da ace iyayenka za su buƙaci zuwa inda kake korana za ka yi,
amma in ina matsayin matarka cikin farinciki xan jira zuwansu. Wallahi my man ina sonka, na yi
maka alƙawarin duk abin da kake so zan yi maka."
Juya mata baya ya yi zai fice, ganin tana son ta ƙaryar da zuciyarsa, amma ko mai za ta ce ba
zai taɓa aurenta ba. So yake ya auri matar ƙwarai.

"Ki yi haƙuri lokaci zai yi saboda ban shirya aure ba."

Jin abin da ya ce hawayenta suka ƙaru."Ba ka sona ne, ko kana tunanin aurena, saboda na
yadda da kai tun kafin mu yi aure? Wallahi bayan kai babu wanda a taɓa mallakawa jikina.
Soyayyarka ce ta makantar da ni har na yarda da kai kafin aure. Don Allah kar ka yi mini
butulcin ɗa namiji. In har ban aurenka ba zan iya mutuwa, saboda ina maka mugun son da ban
taɓa yi wa wani da namiji ba." Ta furta cikin kuka tare da ƙara rungume shi.

"Ban shirya aure ba, in har kin matsu da ki yi aure za ki iya."

Jin kalamansa, hankalinta ya tashi kuka sosai ta fashe da shi. "ka fito fili ka gaya mini baka
sona Sojana, in har ka yi mini haka sam ba ba ka mini adalci ba."

"Kina gaya mini haka, kamar na tursasa ki dole ki ba ni jikinki. Seducing ɗina kika yi har yau ina
dana-sanin saninki a 'ya mace, domin ke ce kika sanya na karya alƙawarin da na yi wa
mahaifina."

Jin abin da yake faɗa cikin zafi kukanta ya ƙaru. Sosai take kuka tana kallonsa."Ni ma ba laifinta
bane, saboda kallon farko na kamu da sonka. Na yi iyakan ƙoƙarina na same ka a matsayin
miji, amma kullum kalmar da kake gaya mini baka shirya aure ba. Na yi tunanin mallakan maka
kaina shi ne kawai zai sanya ka aure ni, amma ashe kuskure ne yi. Kuskuren da yake ƙoƙarin
nisanta ni da kai." Duƙawa ƙasa ta yi, ta riƙe hannunsa da yake son fita.

"Don Allah ka aure ni, wallahi in har ka rabu da ni zan shiga cikin wani hali."

Hannunsa ya fisge, tare da fita daga kicin ɗin yana jin zuciyarsa na zafi. Falo ya zauna ya ɗauki
sigari ya kunna.

Yana zaune a farkon ta fito da gudu ta wuce shi. Haɗa kaya ta fara yi a ranta ta sanya ko shi ne
autan maza ba za ta ƙara dawowa gareshi ba, saboda gara son shi ya kashe ta da ta zauna
tana roƙonsa ya aureta yana wulaƙanta ta kamar ba ta da aji. Hawaye ta share tuna irin mazan
da suke rububinta, amma ta tsaya yana yarfata. Da ta kuma tuna surarsa sai ta ji anya za ta iya
haƙura. Addu'a ta fara tana fatan wannan ya zama na ƙarshe, da zata ƙara dawowa yana more
jikinta, domin faɗin ba shi ne na farko ba.

Cikin kukan ta gama haɗa kayanta ta fito za ta tafi. Kallonta ya yi, sai kuma ya ɗauke kansa tare
da kashe sigarin zai shige ciki.

Ganin haka ta sha gabansa cikin muryar kuka ta ce,"In sha Allahu ba zan ƙara dawowa cikin
rayuwar ka ba. Zan yi nesa da kai, saboda na lura ba sona da aure kake yi ba."

Ba tare da ya ce mata komai ba, ya ɗauke kansa wanda hakan ya tabbatar mata da zarginta.
Da gudu ta fice sai ya bi bayanta.

"Please in ta fita, ka rufe mini get kar ka bari kowa ya shigo." Ya ce wa Solo tare da komawa
ciki, yana addu'ar wannan karon Allah ya sanya kar ta dawo, domin yadda kasan kaska haka ta
manne mi shi.

Lubaynah tana tafiya tana kuka har ta isa gidan Yayarta Hannah. Ganin yadda ta shigo a
birkice, ta wuce zuwa ɗakinta da take sauka sai ta bita da kallo.

Mijinta Nura ta miƙawa ɗansu Fadil da yake shan nono."Please baby ina zuwa na ga ta shigo a
birkice, wataƙila sun yi faɗa da ɗan iska yaronnan da yake yaudararta."

"Ta ke yaudarar kanta dai, har wani namiji za ta rinƙa zuwa gidansa tana kwana, kuma ya aure

ta. Kina tunanin ko ni ne zan zaɓawa 'ya'yana ita a matsayin uwa?"

"Ba ita ta sani ai duk yadda ake gaya mata ta ƙi ji. Ba ta yi kuka ba, sai ranar da ta ji aurensa."
Ta furta bayan ta miƙa masa shi tana gyara zaman rigarta.

"Na gaya mata sojojin nan sam ba su da amana. Ya kamata ta yi wa kanta karatun ta natsu, ta
nemi wanda yake sonta da aura, amma babu kaffara yaron nan ba sonta yake yi ba. Kina ganin
ranar data kawo shi gidan nan, yadda yake fisgewa tana wani tarairayar sa kamar za ta zauce.
Ga shi yana mata magana a tsaye tsaye cikin isa. Irin wannan ko sun yi auren, ba zaman lafiya
za su yi. Yadda wasu sojojin suke ɗaukar mace ba a bakin komai ba, sannan ta haɗu da mai
zuciya."

"Ita ta sani, wannan karon zam gaya wa Mommy , saboda babu ruwana tun da ta ƙi ji." Ta ba shi
amsa tare da shigewa ciki.

Shiga ta yi tana kwance ta yi rub da ciki, kuka take yi sosai har da sheshsheƙa. Har yau in ta
tuna wahalar da tasha a lokacin da ya rabata da mutuncinta, sai ta ji kamar za ta yi hauka, duk
wahalar da tasha sai ya ce ba zai aure ta ba? Wannan tunani yake sanya ta ji ba za ta iya
haƙura da shi ba.
"Wahallalliya mara sanin darajar kanta! Sau nawa na gaya miki Aliyu ba auren ki zai yi ba?
Tsotse ƙwallon mangwaro zai yi, yar ya huta da ƙuda. Kina ganin dama zai aure ki ne?"


"Wallahi Anty Maryam dole ya aure ni, saboda in har ya bijire hakan sai na hana shi zaman
lafiya da ita. Ba zan taɓa yarda ya yi aure ya bar ni ba, in har kin ga ya auri wata ki tabbata ba
ni a cikin duniyar."

Hattara 'yan mata masu bawa maza kansu kafin aure, domin duk namijin da kika amince ya
sanki a 'ya mace ba zai taɓa aurenki ba, sannan shi ne mutumi na farko da zai fara goranta
miki. In kunne ya ji.....

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242


Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci

guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban.

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg



*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*


MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423


PAGE 4

"Wallahi Anty Hannah dole ya aure ni, saboda in har ya bijire hakan, sai na hana shi zaman
lafiya da duk wacce ya aura. Ba zan taɓa yarda ya yi aure ya bar ni ba, in har kin ga ya auri
wata ki tabbata ba ni a cikin duniyar."

"Sai ki je ki yi ta wahala har ki kashe kanki. Duk wanda bai ji bari ba, ai ya ji hoho. Ki ta biyewa
daɗin bakinsa sai ranar da kika ji ɗaurin aurensa, sai ki yi nadama a lokacin da ruwa ya ƙarewa
ɗankada."

"A ranar kuma zan yi nadamar yaudarata da ya yi, saboda in har ban yi nasarar kashe shi ba,
sai na kashe matar daya aura."

"Shikenan kin yi maganin matsalar da kanki. Ya je ya auri wata ki ƙare rayuwarki a kurkuku." Ta
ƙarashe maganar tare da ficewa cikin takaici.

Kwanciya ta yi, ta ci gaba da kuma har sai da ta yi mai isarta, sannan ta shi ta yi sallah ta fito
falo don ta ci abinci.

Anty Hannah, tana zaune ganinta ta saki tsaki ta miƙe ta bar falon.

Zama ta yi kan dinning ɗin xuciyarta na suya. Sosai take ganin son zuciyar Aliyu da ya kasa
gane tsananin sonsa, ba ita ta ɗorawa kanta ba, saboda da ace za ta iya cire soyayyarsa tuni ta
rabu da shi, duba ga irin wulaƙancin da yake mata.

Iya ƙoƙarin da ta yi, na kwana uku ne ta rinƙa danne ƙaunarsa da kamar yanzu ake mata
wahayinsa. Anty Hannah tana lura da ita,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login