Showing 18001 words to 21000 words out of 90573 words
Chapter 7 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
tsalle zata cakume shi. Haka shi ma zuciyarsa ta tunzura, ji
yake in har bai canza mata kammanni ba yau, sam ba zai iya rintsawa ba.
Da ƙara aka samu aka hanata dabben da take son su yi. Shi kuma Mommy ta riƙe sosai tana
kuka. Ganin kukan da take yi, ya sa shi fasa abin da ya yi ninya, don ya ayyana hatta ƙashin
jikinta sai ya ɓaɓɓalla ya watsar.
Su Daddy sun cika da mamakin rashin kunyarta, ganin yadda take magana tana kama ƙugu
kamar za ta dake shi.
"Wannan wace irin yarinya ce babu tarbiya?" Daddy ya tambayi ka sa cikin tsananin mamaki.
"Please Aliyu, mu shiga mota kai kuma Daddy, ka shiga ku yi sallama." Mommy ta ce tare da
kama hannunsa, suka shiga motar tana huci tamkar mesa.
Dady kuwa cikin rashin ƙwarin jiki, ya bi bayan Kaka Tani, da take kwashewa Aliyu albarka, ko
kunyarsa ba ta ji.
"Zan tafi sai mun ƙara dawowa. Ku yi haƙuri da ain da ya faru." Ya ce tare da ciro kuɗi ya bata.
"In har za ka dawo, ka tabbatar da ba ka zo mini da fitsarraren yaronka ba, domin ba zan iya
ƙara lamunta ya dukan mini jika ba." Ya ce masa tare da amsar kuɗin cikin ɓacin rai kamar ya
bata guba.
Kasa cewa komai ya yi, sai dai ya bita da kallon mamaki. Jiki a mace ya shiga cikin mota. Ba
tare da ya kalli Aliyu da yake huci ba, ya cewa direba,"Ka ja mota."
"To ranka ya daɗe." Ya amsa tare da ba wa motar wuta.
"Wallahi in har zan ka yarinyar nan sai na yi ajalinta. Wannan dalilin ya sa ya tun farko na ce ba
zan biyo ka ba, saboda matan ƙauye jahilai ne, ba su da hankali dabbaci kawai suka sani."
"Kai kuma sai ka biye mata, kashe ta ka yi ninyar yi?"
"Haka na yi ninya maganin rashin kunyarta na so na yi." Ya ba shi amsa ba tare da ya tauna
maganar ba.
Cikin takaici daddy ya kalle shi. Ya san halinsa in har ransa ya ɓaci, sam ba ya tuna magana.
"Gaskiya matar nan ta ɓaci tarbiyyar yarinyar nan, dubi rashin kunyar da ta yi maka, amma ba
ta tsawata mata ba?" Mommy ta ce tana kallon Daddy.
"Abin mamaki ni kaina na yi mamaki ƙwarai."
"Hmmmmh! In dai haka rayuwarta za ta miƙe ina tausaya mata."
"Wallahi yarinyar ba ta da kunya. Na yi mamaki da ta iya ɗaya hannu za ta duki Ya Aliyu."
Cewar Nufaisah cikin ɓacin rai.
Ƙuta ya yi, ba tare da ya ce komai ba, amma har yanzu zuciyarsa tafasa take yi, tamkar za ta
fito waje.
Sun shigo cikin gari Daddy ya kalle direba ya ce,"Ka kaimu gidan Hajiya, na gaya mata na je
ƙauyen."
"To ranka ya daɗe."
"Please ya sauke ni a gida, a mood ɗin da nake ba zan iya zuwa gidan Hajiya ba, kun san
halinta ɓata mini rai kawai za ta yi."
"Sauke shi kawai." Daddy ya ce don ya san kowa ya je damuwa zai ƙara masa.
Da suka isa ƙofar gidan hon suka yi maigadi ya buɗe.
Hajiya jin sun dawo sai ta fito daga cikin ɗakinta zuwa harabar gidan.
"Sannunku da dawowa." Ta faɗa tana kallon Daddy da ya fito daga cikin mota, sai kuma ta juya
idanunta tana kallon Mommy, da rissina cikin girmamawa ta ce," Ina wuni Hajiya?"
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 6
"Sannunku da dawowa." Ta faɗa tana kallon Daddy da ya fito daga cikin mota, sai kuma ta juya
idanunta tana kallon Mommy, da rissina cikin girmamawa ta ce," Ina wuni Hajiya?"
"Lafiya lau, ya hanya." Amsawa ta yi tana ƙoƙarin shiga cikin gidan.
Jikokin nata suka gaisheta. Rungume su ta yi cikin so da ƙauna, sannan suka rankaya suka
shiga cikin gidan.
"Bari na kira Hafsatu mai aiki ta kawo muku abinci, na ga kamar da ga ƙauyen, kawai wutowa
nan ku ka yi?"
"Eh wallahi Hajiya abin mamaki na tarar a ƙauyen."
"Mamaki kuma ta mutu ne?" Ta yi masa tambayar cikin tsoro.
"A'a tana nan cikin ƙoshin lafiya, kuma ta amshe mu hannu biyu-biyu, sannan ta ce na gaishe ki
sosai. Sai dai fa yarinyar da take riƙo ta ce mana jikanta ne, iyayenta sun mutu sakamakon
kwalara da ta kama su. Yarinyar da suka bari sam ba ta da tarbiya. Ga ta ƙazamiya mara kunya.
Kin ga rashin kunyar da ta yi wa Aliyu? Wallahi har dabbe ta so su yi, ta kuma fasa mana
gilashin mota."
Tsananin mamaki ya kamata jin abin da ya ce, sai kuma ta ɗaure fuska tana kallonsa.
"Shi Aliyu ɗin uban me ya yi mata? Ai ni dama ban so tafiyar da shi ba, saboda na tsani baƙar
zuciyarsa, ace yaro saboda ɓakin rai da zuciya sam ya kasa samun matar aure? Ato wacce
matar za ta aure shi yana wannan zuciyar, domin tsaf a rashin imaninsa zai iya sanya bindiga
ya harbe ta."
"Hajiya soja ne shi fa, kuma dole ya kasance yana da zuciya da mazantaka, kina sane da 'yan
da masu garkuwa da mutane suka damu ƙasar mu. Shin in ba shi da zuciya, ya zai yi ya ɗauki
hukunci a kansu?"
"Oh kenan kai kake ɗaure masa gindi? In ya yi zuciya a gurin daga, sai kuma ya yi a cikin
danginsa? Ni ban san kinibibin da ya sanya ka tafi da iyalinka ba, na so ka je kawai ka ga wuri
ka kai ni."
"Ki yi haƙuri in na ɓata miki rai, dama na so na ƙarfafa zumunci."
"Zumunci? Ai ga shi wancan mai baƙar zuciyar ya ɓata, tun da ya je ya dukan mata jika."
Jin ya yi shiru ta kalle shi ta ce,"Yanxu yaushe za mu je ka kai ni ƙauye na gansu, kuma na
ɗauku su su yi mini kwana biyu?"
Zare ido ya yi jin abin da ta ce yana kallonta."Eh mana ya kamata na je mana, ko saboda jikarta
ba ta da kunya ba za mu yi zumunci ba. Abubakar kar ka manta cewar duk wanda ya yanke
zumunci Allah ba ya tare da shi. Da irin mugun halinka yanxu da kake nunawa, in har na kwanta
dama za ka yi zumunci kuwa? Ko don ka ga su 'yan ƙauye ne?"
Kallonta ya yi yana mamakin abin da ta ce. "Haba Hajiya, sai bai kamata ace kin yi mini wannan
tambayar ba. Tun da kika gaya mini na je na ga inda suke, hankalinsa bai kwanta ba sai dai na
je."
"To da ka tashi zuwa mai ya sa kake da Aliyu? Kana sane da yaron nan ɗan banza ne. Sam
rayuwarsa ba ta yi mini ba, tuntuni na gane ya tsani ƙauye da mutanen ƙauye. Arzikin sunan
mijina, da aka sanya masa kawai nake raga masa bana gurza masa rashin mutunci duk da
halina bane."
"Ki dai yi masa uzuri amma bana tunanin haka. Ƙauye ai tushen kowa ne."
"Ina zai san hakan tun da ya ga an haife shi a birni. In da ace Allah bai sanya na auri
mahaifinka ɗan birni ba, wallahi Kaunyenmu ko girki da icce ba a yi sai turoso, sannan yanzu
ya aurar da 'ya'ya." Ta ce masa fuskarta a ɗaure.
Ganin ƙorafin ba zai ƙare ba, sai ya kalle ta ya ce,"Am Hajiya ina ganin bari mu wuce gida."
"Abinci fa? Daga tafiya kuka dawo ya kamata ku ci abinci." Ta ce sai kuma ta ƙwala kira tana
faɗin,"Hafsatu, ki kawo musu abinci."
"Hajiya, da kin barshi in muka koma gida sai mu ci."
"A'a bari ta kawo ai mun gama." Ta ce tare da miƙewa ta nufi kicin ɗin, ganin ba ta ji kiran ba.
Bayan sun gana cin abinci sun mike ta kalli Daddy."Ina son ka samu lokaci sai ka kaini ko,
domin so na ke na ɗauko su su yi kwana biyu, yadda Allah ya yi ma 'ya'yana arziki, dole su ci
gajiyar haka tun da su kaɗai na ke da su.?"
"Hajiya karki ɗauko mutanen nan wallahi tsaf za su sanya miki hawan jini, domin in har tana
gidan nan ba za ki iya shaƙar iska mai daɗi ba."
"Sai kuma na kyale 'yan'uwana su ci gaba da rayuwa a haka? Zuwa zan yi na ɗauko su, sai na
gyara musu rayuwarsu na samu lada."
Ganin yadda ta yi maganar a xafafe ya ce,"Shikenan Hajiya, yadda kika ce haka za a yi." Ya ce
cikin biyayya.
"Allah ya kaimu kuma ya yi maka albarka."
"Amin," Ya amsa cikin farincikin.
Ko da suka koma gidan hirar Jimmalo suka rinƙa yi. Har lokacin da za su kwanta, sannan aka
kashe wutan gidan suka kwanta.
Captain Aliyu da tun da suka dawo ya shiga cikin ɗakinsa ya kulle ƙofa. Zuciyarsa tafasa take
yi. Tun da yake ba a taɓa wulaƙanta shi irin na yau ba. Wulakancin ma wata yar ƙauye kucama
ƙazama da ita.
"Yarinyar nan da ace babu zumunci. Wallahi sawa zan yi a harbe ta, sannan a ƙona gidansu."
Ya furta tare da zaro sigari ya kunna yana shafa.
Kwanciya ya yi, sai kuma ya ɗauki waya zai kira Lubaiyna, amma sai ya fasa ya yi wurgi da
wayar cikin takaici. A haka ya kwana cikin tsanannin takaicin abin da ta yi masa, domin ko
abinci bai nema ba sai ruwa da ya rinƙa banka ma cikinsa. Ga shi yana gida ballanatana ya sha
maganin damuwarsa. Cikin dare kasa bacci ya yi yana ta juye-juye har zuwa uku da rabi,
sannan bacci ya yi nasarar sace shi.
Jummmalo zaune a baƙin ƙofar ɗakin Kaka Tani. Kaka Tani take gasa mata inda Aliyu ya haure
ta. Ƙuta ta yi tare da jan tsaki."Na rantse wannnan ɗan iskan ɗan birnin da na sani da na karya
masa muƙamuƙi, tun da ba shi da mutunci. Da wata fuskarsa kamar alalar da ba ta nuna ba."
"Ke ma jikalle kin cika rikici, daga ganin mutum sai ki hau neman shi da rigima?"
Ɓata fuska ta yi tare da kwaɓa-kwaɓa za ta yi kuka."Kaka Tani, kamar goyon bayansa kike yi,
ko saboda sun kawo miki abin arziki..."
Bige bakinta ta yi cikin ɓacin rai,"Ja'irar banza kina ganin har akwai abin da za a kawo mini ya
sa na goyi bayan wani? Ba kya gani takanas daga Kaduna suka zo gurina, amma na rufe
idanuna na yi musu kashedi?"
"To ai ke ne ba ki ga ciwon da ya ji mini ba kike ƙorafi." Ta ce tana kallonta a sakalce.
"Ina miki ƙorafi saboda ki daina ƙoƙarin gwada ƙarfin ki da maza. Inda ya ji miki rauni ya kike so
na yi? Kin san ke kaɗai ba ke gani na ji daɗi."
"Hakan ma ba zai faru ba, saboda kin san ina da ƙarfi. Ni fa kamar soja na ke, domin da ace a
birni na ke na yi karatu, aradu soja zan zama na yi ta dukan masu laifi, ina harbinsu da bindiga,
kuma ko ciwon da ya ji mini ai shammatata ya yi, wallahi da sai na kai ƙato ƙasa. Tsaf zan
wawuri ƙafarsa na danƙarashi da ƙasa, amma ko yanzu a juri zuwa rafi, watarana fili zai fashe,
domin na ratse duk lokacin da Allah ya haɗa ni da shi sai na kai gardi ƙasa."
"Kar na ƙara jin haka saboda ɗan'uwanki ne, kuma ba kya ganin irin abincin da suka kawo
mana, duk garin nan wa kika ga 'yan'uwansa sun taɓa kawo musu haka?"
Ƙara ta saki tana birgima a ƙasa."Dama na faɗa kwaɗayin abin da suka kawo kike yi, shi ya sa
da ya naushe ni, ba ki sanya taɓarya kin ragije shi."
Jikinta ya kama rawa ganin jin abin da take cewa."Haba Jimmalo, ki tashi a ƙasa kin ga kina
ɓata kayanki, kuma na san ko sama da ƙasa za ta haɗe, ba za ki yi wanka ba. Ki je ki ƙara
ganin kayan da suka kawo mana, na tabbata za ki yarda da abin da suke cewa."
Ƙara ta yi sai kuma ta kalle ta tana satan kallon inda kayan suke. Ganin haka ta kama hannunta
tana faɗin,"Yauwa Jimmalo jikar Tani, ma za ta shi kin ji jikalle."
Kamar wata 'yar ƙaramar yarinya ta miƙe tana tafiya, sai ka ce yar kaciya ta isa gurin.
Zama suka yi suna duba kayan. Kayan abinci sosai suka kawo musu, da sabulu man-shafawa
da kuma kilin."Kin ga kaya sosai har da man-shafawa na 'yar birni? Da ace ke wata ce sai ki yi
wanki kuma ki yi wanka."
Ɓata fuska ta yi jin abin da ta ce,"Aradu ba zan yi wanka ba sai bikin Tasallah ya zo, ko ranar da
kika sanya ni dole na yi haka na yi ta soshe-soshe, don haka ba zan cutar da kaina ba."
Zare ido ta yi cikin mamaki jin abin da ta ce,"Sai nan da sati biyu za ki yi wanka Jimmalo? Kin
san irin ƙarnin da kike yi?"
"Ni fa ki daina cewa ina wari saboda babu ƙarin da na ke yi." Ta ƙarashe maganar tana sunsuna
hammatarta da ya cika da gashi ba ta askewa."Kaka Tani shi shima ki ji wallahi ba ya wari."
Da sauri ta matsa nesa da ita tare da toshe hancinta."Ba kya dai jin warin, amma ko wucewa
mutun zai yi sai ya gane ba kyau wanka. Ga kayanki can na wanke, amma ba za ki yi wanka
ba?"
"Ba zan yi ba, sai lokacin bikin shi ma don kawai ina son na gurzawa Badaru rashin mutunci
ne." Ta ce tare da ɗaukar ledar biskit. Ɓarewa ta yi ta kai bakinta."Kai 'yan birni suna morewa
wallahi. Kaka Tani dole mu kai musu ziyara mu je mu ci yo daɗi." Ta ƙarashe maganar tare da
miƙa mata ledar biskin ɗin.
"Ah'ah, wai ba dai daɗi ba, kin ji yadda kunnina yake zut!zut? Dole mu je birni, amma kuma kina
ganin za su dawo, bayan kin fasa musu gilashin mota?"
"Za su dawo mana, in kuma ba za su dawo ba, sai mu tafi nemansu a birni. Ni fa na so na yi
masa mutunci kar na nuna masa kalata, shi ne kawai ya nuna ƙyamata kamar ya ga kashi. Ni
kuma haushin hakan ya sanya na fasa masa gilashin motar, saboda ya san ba a ja da ni, kuma
kin ga ko dawowa suka yi zai ji shakkata."
"An gaya miki birni ƙauye ne da za mu je nemo su? Kuma na rantse ba na jin zasu dawo."
"In ma ba su dawo ba sai na je nemo su in kina jin tsoro."
"Ke ma kin san duk inda za ki ƙafarsa ƙafarki."
"Haka ne kakata." Ta ce sai kuma ta farko kwalin indomie ta fara iba tana ci.
"Allah ya isa domin Ubangiji kawai zai saka mana, yadda 'yan birni suke cutarmu, suna cin
kayan daɗi. Kaka Tani ji wannan kalar biskit ɗin mai gishiri."
Karɓa ta yi ta kai bakinta tana lumshe idanu."Kut! Gaskiya Allah sai ya saka mana, domin garin
daɗi na nesa. Shi ya sa kika gansu kamar an ɓaro su a kwali, musamman wannan mara
mutunci ba dai gayu ba tsafta ba." Ta ce suna ta cin indomie suna santi.
"Ni fa ban ga kyan shi ba saboda dana kalle shi lokacin da ya mare ni, wai yana amai saboda
warin jikina da biri yake kama."
Kaka Tani bata bata amsa ba, Salame ta yi sallama da tirenta na satin ayaba. Ganin ta a zaune
ta yi turus! Sai kuma ta ƙarasa."Lafiya Jimmalo, ba za ki je sarin ayabar ba?"
Kallonta ta yi tana shirin ɓoyewa indomie ɗin, domin Jimmalo ba dai rowa ba. Kowa ya sanya
da shegen rowa, da kuma son abun wani. Ko gidansu ƙawayenta suka zo tana cin abinci, babu
kunya za ta cinye