Showing 42001 words to 45000 words out of 90573 words
Chapter 15 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
kular.
"Is so bad that I can't eat it."
"Yanzu ba za ka iya ci ba?" Ta yi tambayar cikin damuwa.
"In zan tilastawa kaina zan yi amai, an so sorry for the inconvenience."
"Babu komai." Ta ce tare da ɗauke dambun cikin mamakin ƙazantar da ya gani a jikinta har ya
hana shi cin dambun sanin yadda yake so.
"Anty bari na miƙe zan shiga cikin gari, yanzu haka Ya Auwalu sai kirana yake a waya, don ma
ban gaya musu zan zo ba."
"Ok tom sai ka dawo."
"Ina ga zan wuce daga can ga wannan sai mun yi waya." Ya dunƙula kuɗi masu yawa ya bata.
"Aliyu na gode Allah ya tsare hanya."
"Amin," Ya ce daidai lokacin da Musa yar shigo cikin ɗakin yana faɗin,"Ya Captain ashe ka
shigo gari?"
Hannu ya ba shi suka yi sallama sannan suka fita suna hira. Rabon kuɗi yayi wa mutanen gidan
sannan ya yi musu sallama ya tafi. Musa ya raka shi Ƙwarbai ya gaida Gwaggo Mariya, sannan
ya bata kuɗi ya yi mata sallama ya tafi.
Ana kiran sallar isha'i ya isa Kaduna. Ya yi parking daidai lokacin da Daddy ya fito don zuwa
masallaci, don haka ya bishi suka tafi tare.
Bayan sun dawo Aliyu ya kalli mahafinsa. "Yanzu Daddy kana gani Hajiya ta ɗauko mutanen da
za su kashe ta tun kafin lokacinta ya yi?"
Dariya ya yi yace,"Ai yau sun koma ƙauye ta kira ni tana ta murna, har cewa ta yi na kira likita
ya gwada jininnta."
Jin abin da ya ce sai hankalinsa ya kwanta ya yi dariya ya ce,"Waɗannan mutanen mahaukata
ne, duk wanda ya zauna da su tsaf zasu haukata shi."
"Sosai kuwa ai ta ce ta haƙura da zumunci."
Dariya ya yi sannan Dady ya ce,"Ya mutanen Zariya?"
"Lafiya lau suna gaishe ka. Na je na gida Gwaggo Mariya ashe ba ta ji daɗi ba?"
"Eh, wallahi mantawa nayi na gaya maka, tun da ka je ka yi aikin hankali."
"Na je kuma ta ji daɗi sosai, har take gaya mini bikin jikarta na gurin Ya Sarki."
"Na ji Mommynku tana maganar bikin. Allah ya ƙulla alkhairi."
"Amin," Sun ɗan yi shiru suka tafiya. Daddy ne ya kalle shi ya ce,"Kai ma fa ya kamata ka fara
maganar aure, na yi shiri ne saboda yadda na ga har yanzu kana nan da natsuwata da
hankalinka, amma duk da hakan kana buƙatar ka ije mace tun da ka kai munzalin aure."
"In sha Allahu kwanan Daddy."
"Allah ya kaimu ya baka ta gari. Ina jin daɗi sosai yadda ka kama kanka bai ruwanka da bin
mata ko shaye-shayen da wasu sojojin suke yi. Kowa a family yabon ka yake yi. Yana gaya mini
in har za auri yarsa ya ba ka, duk wannan ya faru ne saboda riƙe tarbiyyar da na ɗora ka akai.
Ko bayan rayuwata Aliyu karka canza. Ban taɓa zina da yar wani ba, kuma ina roƙon har na
mutu kar zuriyana su yi ko ayi da su."
Jikinsa e ya kama rawa lokaci guda hankalinsa ya tashi."In sha Allahu Dady addu'ar da kake
mini ina ganin amfaninta, domin ko da abokan aikina masu irin wannan halin sun ja ni, sai ka ga
Allah ya tsare ni." Ya ƙarashe maganar cikin rawar murya zufa na keto masa.
"Ƙarfin addu'a ce ka ci gaba da ƙoƙarin kare kanka. Zina musifa ce da take shafan har waɗanda
ba su aikata ba. Zina alfasha ne daga cikin manyan zunubin da Allah ba ya so, amma abin
takaici da jimami har ma da zaman makoki al'ummar zamanin mu mun ɗauki zina ba a bakin
komai ba. Namiji mai aure yana zina, matar aure tana zina samari da 'yan mata duk suna zina
har da zawarawa, shi ya sa musifa ta yi mana yawa. Abinci yana gagarar wasu. Mutane an
mayar da kashe su ba komai ba, dabba tafi mutum, domin sai ta yi yawo ba a taɓa lafiyarta ba,
amma mutum har gida ake zuwa ake kashe shi. Wannan duk yana faruwa da irin manyan
zunuban da muke aikawa ne."
Aliyu shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba. Ganin haka Daddy ya ɗora da cewa,"Ka ga ko karya
alƙawari da mutum ya zama fuska biyu? Shi ma yana matuƙar sanya Allah yayi fishi sannan ni
kaina Aliyu in har mutum zai zama fuska biyu a gareni zan iya yafe shi har cikin rayuwata. Na
tsani haka domin babu kyau."
"Eh, Daddy Allah ya tsare mu da aikata zina." Ya yi ƙoƙarin sauya muryarsa ya furta hakan.
"Amin shi ya sa na ke alfahari da kai. Har gobe ina bugan ƙirjina a cikin abokai na yabe ka,
saboda kyawawan halinka. Dangi damu kanmu muna alfahari da kai. Ubangiji ya yi maka
albarka."
"Amin Daddy." Ya ce hawaye na zuba a ƙuncinsa, domin ya san cewa duk lokacin da ya sani
akwai matsala. Ya zama dole a yau ya rabu da Lubaynah ya daina shan sigari.
"Daddy bari na kwashi kayana na kai mota zan shigo." Ya ce masa don ya keɓe.
"Ok, ba matsala sai ka shigo bari na gaya wa Nufaisah ta haɗa maka abinci." Ya ƙarashe
maganar tare da shiga ciki.
Sashinsa ya shiga buga kansa kasa da bango. Sosai ya ke jin ya tsanar kansa, saboda
yaudarar mahaifinsa da ya yi. Ganin yadda yake alfahari da shi, sai ya ji hankalinsa ya tashi. Da
sauri ya ɗauki wayarsa ya shiga cikin chatting da suka yi da Lubaynah na batsa da hotunanta
marasa ɗa'a ya goge.
Goge numbarta ya yi, yana fatan ya zama shi ne na ƙarshe da zai yaudari mahaifinsa. Saboda
tashin hankalin da ya shiga jin abin da Dady ya rinƙa cewa, domin ya ɗauka ko asirinsa ne ya
tonu. Wanka ya shiga sannan ya canza kaya, ya tafi zuwa sashin iyayensa.
Mommy na zaune a falo da remote ɗin tibi a hannunta ya yi sallama ya shigo. "Yauwa ma yanzu
na ke son na tura Umma, ta je ta yi kiranka mu yi dinner."
"Wanka na yi shi ya sa na daɗe." Ya furta tare da wuce dinning yana gaishe ta.
"Lafiya lau ya mutanen Zariya?"
"Duk suna lafiya Anty Amarya ta ba ni tsaƙo na kawo miki, na san bai wuce abin da ta saba. Su
daddawa da kuka da barkono."
"Ba ta gajiya duk wani ya je sai ta yi hidima."
Murmushi ya yi sannnan ta zauna yana faɗin,"Anty Amarya tana da kirki sosai."
Bismillah suka yi sannan suka fara cin abincin. Kwana biyu Captain Aliyu ya yi ya koma aikinsa.
A ranar da ya koma washegari suka yi tafiya, don haka Lubaynah ba ta samu damar ganinsa
ba.
Jimmalo.
Cikin tsananin takaici suke tafiya suna tsinewa Hajiya da Captain Aliyu, domin inda ace zagi na
fitowa a jikin mutum tabbas da ya yi musu tabo. Zagi kam sun zagu. Suna tafe suna zaginsu har
suka isa Damagaran.
A lokacin da suka isa sai kunya ta kama jimmmalo, da ta fara haɗuwa da mutane ana kallonta
ana tambayarta, dalilin da ya sanya ta dawo da wuri, sannan ta gama cika baki cewar za su
dawo da abubuwa, amma sai ga shi duk dawo daga su sai kayan jikinsu kamar wasu korarru.
Mutanen ƙauye da suke haɗuwa, don su suka ci gaba da kallonsu suna gulma, cewar sun yi
halin su an kore su. Kafin su isa gida labari ya cika ko'ina Jimmalo ta dawo birni babu abin
arziki.
Da suka isa ƙofar gidansu Kaka Tani ta buɗe suka shiga. Zama suka yi sannan ta ibo ruwa ta
sha."Allah ya tsinewa mutanen birni gabakiɗaya. Kaka Tani ni da birni har abada, saboda ba su
da mutunci. Ki ga irin tozarcin da suka yi mana. Na gama cika gari ina gaya musu zan dawo da
abin arziki, amma ko tsarabar biskit ban yi ba."
"Ai Hajiya ta ba ni mamaki sosai tun da ta fifita jikanta a kaina. Na rantse ko mutuwa ta yi ba
zan je gaisuwa ba, kuma tsakanina da ita na yanke zumunci, sannan ni ma ko mutuwa a yi kar
ta zo."
"Allah ya kawo su ma suga rashin mutuncin da zan yi musu, domin duk ranar da suka kuskura
suka zo gurinmu na rantse da duwatsu zan raka su."
"Ai ba za su yi kuskuren zuwa ba." Cewar Kaka Tani tana ƙoƙarin miƙewa ta shiga cikin ɗakinta.
Jimmalo na tsaye a waje tana jijjiga, ji take yi kamar ta koma ta shaƙi wuyan Captain Aliyu ta
kashe shi. Wani irin tsanarsa take ji yana zagaye ilahirin jikinta.
Tana zaune tsahare ta yi sallama ta shigo tana washe baki. Mugun kallo ta watsa mata tare da
tamke fuskarta.
"Jimmalo ashe kun dawo? Lauratu ta gaya mini cewar ta ganku a da zaku dawo?"
"Ko ba ta gammu ba na san kece za ki fara zuwa, saboda kaf garin nan babu munafuka kamar
ki."
"Laa! Jimmalo ba haka bane cewa nayi bari na maza na zo na karɓi alkawarin taliyar birni da
kika ce za ki zo mini da shi?"
"To jikar mayu ban zo da shi ba, sai na ga uban da zai yi mini dole na baki."
"Ko kin zo da shi ba lailai ki ba ni ba, dama na san alƙawarin ki ba kya cikawa, musamman kan
abinci ɓakin rowa ne dake."
"Ke Tsahare fita a gidan nan kafin yanzu jininki ya yi tsami."
"Dama ko baki ce na fita ai zan fita, alƙawari dai kaya ne duk wanda bai cika ba, Allah xai
hukunta shi, kuma duk wanda ya ci shi kaɗai shi kaɗai zai mutu."
"Da na gaya miki da gyatumarki zan mutu?" Ta ce tare da fara tafiya da sauri za ta shaƙota,
ganin haka ta ruga da gudu ta fice daga gidan.
Ba ta zame ko'ina ba, sai dandali ta sanar musu da cewar Jimmalo ta dawo daga birni, babu
abin arzikin da ta rinƙa musu ƙaryar za ta dawo da shi. Kafin dare ya yi an gma yayata maganar
wasu suna faɗin mugun halinsa da rashin mutunci suka yi aka ƙoro su. Maganar har da gishiri
da magi, aka ƙara mata cewar koro su aka yi har da duka.
A lokacin da maganar ta dawo kunnen Jimmalo ranta ya ɓaci. Ɗanmara ta sha ta je har ƙofar
gida ta samu Tsahare ta yi mata duka.Mahaifiyarta ta biyo ta, amma babu wani matakin da aka
ɗauka.
Bayan dawowarsu suka ci gaba da rayuwarsu. Sun gwammace irin rayuwar da suka saba.
Jimmalo tun safe take zuwa talla, da ta siyar za ta tafi sarin gwaiba ko ayaba, sai ta siyar
sannan take dawowa. Bayan magariba ta ɗauki talla ta wuce dandali. A haka suke samun
abincin da za su ci.
Wata ɗaya Captain Aliyu ya yi sannan ya dawo. Hankalin Lubaynah ya tashi matuƙar gaske
ganin ba ya ɗaukar wayarta, sannan in ta yi chatting ɗin da ta Whatsapp ba ya reply. A cikin
lokacin ta rame ta fita hayyacinta. Ita kanta mamakin wani irin so take yi masa kamar za ta
mutu.
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGA 13
Wata ɗaya Captain Aliyu ya yi sannan ya dawo. Hankalin Lubaynah ya tashi matuƙar gaske
ganin ba ya ɗaukar wayarta, sannan in ta yi chatting ɗinsa ta Whatsapp ba ya reply. A cikin
satin ta rame ta fita hayyacinta. Ita kanta mamakin wani irin so take yi masa kamar za ta mutu.
Ganin halin da ta shiga sai Hannah ta kira gida ta sanar. Duk abin da take ɓoyewa ta sanar
musu har zuwa kwanar da take yi gidansa. Hankalin iyayenta ya tashi sosai, inda duk suka
ɗauki laifin suka ɗora mata, domin da ace tuntini ta sanar da sun yi wa abin tufka hanci.
Mahaifinta ya yi fushi sosai, cikin tsananin ɓacin rai ya zabga mata mari."Irin tarbiyyar da na
baki kenan Lubaynah? Ko da kika ga na ƙyale ki kina rayuwa yadda kika dama, ban taɓa
tunanin za ki iya, zuwa gidan namiji kina kwana, a tunaninki hakan da kike mishi zai sanya ya
aure ki?"
"Daddy Anty karya take mini, Captain Aliyu sona yake yi, ban taɓa zuwa na kwana a gidansa
ba, kuma zan tabbatar maka da hakan da zarar ya dawo zan sanya ya turo iyayensa."
"Ƙarya za ta yi miki kenan? Mene ne ribarta don ta yi miki karya?"
"Eh na san cewa ina zuwa gidansa na taimaka masa da aiki, amma Captain Aliyu bai taɓa riƙe
ko da hannuna bane."
"Wallahi Daddy yarinyar nan ƙarya take yi, ko Daddyn Fadil ya san abin da take aikatawa, kuma
shi yace na sanar daku tun kafin lamarin yafi ƙarfinmu."
"Ki barta tun da ta ƙaryata na ba ta izinin ya turo iyayensa, sannan ba za ta ƙara zuwa Abuja
ba."
Kuka ta fashe da shi, jin tsautsaurar hukuncin da ya yanke mata. Ta san cewa da wuya Captain
ya turo iyayensa. Wayarta ta ɗauka ta shige cikin ɗakinta.
Layinsa ta fara kira, amma kamar kullum ba ta shiga. Sai ta yi jifa da wayar tare da fashewa da
kuka. A zuciyarsa tana jin ba za ta iya bin umurninsa na hana ta zuwa Abuja ba, domin ya zama
dole ta je gurin sa, don ta ji dalilin ƙin ɗaukar wayarta.
Tana cikin damuwa har tsawon sati bai ɗauki wayarta ba, sannan an sanya mata tsaro sosai
domin idanun mahaifiyarsu yana kanta. Zazzabi sosai ya kamata har sai da aka kaita asibiti.
Ita da Mommy suka je sibiti. Tunanin hanyar da za ta gudu take yi. Tana cikin wannan tunanin
likita ya ba Mommy takadda ta je ta siyo magani. Da sauri ta miƙe ta fice daga asibitin.
Bayan ta dawo ta neme ta sama da ƙasa ta rasa. Hankalinta ya tashi sosai ta kalli
likitan."Please Petient ɗin da na zo da ita fa?"
"Ta ce za ta je bayi." Ya ce mata hankalinsa a kan laptop ɗinsa.
Cikin sanyin jiki tafiya tana duba ko'ina, amma ba ta ganta ba. Ganin ta duba kaf asibitin babu
ita, sai hankalinta ya tashi ta ɗaga waya tana kuka ta kira Daddy.
Hankalinsa a tashe ya iso asibitin, amma sun duba ko ina ba su same ta ba. Mommy ce ta
fashe da kuka tana faɗin,"Lubaynah na da hankali kuwa? Namiji ne za ta gudu ta je gurin sa?"
"Lailai bata da hankali kuwa, amma ki barta in har ta dawo sai na ɗauki mataki a kanta."
Cikin ɓacin rai suka koma gida. Mommy sai kuka take yi Daddy yana bata haƙuri.
Hannah suka kira ko ta san gidan Captain, amma sai ta gaya musu ba ta sani ba. Fushi sosai
suka yi da ita, suna jiran ta dawo sai sun ɗauki mummunar mataki a kanta.
Lubaynah na fita daga asibitin ta shiga cikin napep ya kaita tasha. Sai da ya kaita sannan ta cire
kuɗi a p.o.s, don transfer ta yi musu saboda ba ta zo da ATM ɗin ta ba.
Kuɗin mota ta biya zuwa Abuja. Ba ta iso Abuja ba sai bayan magariba. Kanta ne ke ciwo sosai
ga wata uwar yunwa da take ƙwakularta. Tun a hanya ta kira shi yafi sau nawa, amma baya
shiga. A mota tana kuka sosai domin ta san son Captain jarrabawar ta ne.
A lokacin da ta isa gidansa tana addu'ar yana nan.Cikin sa'a Solo ya sanar mata yana nan,
amma ya ce kar su ƙara buɗe mata gidan. Hankalinta ya yi mummunar tashi ga yunwa ga
zazzaɓi a jikinta."Mai Captain yake nufi?" Ta yi wa kanta tambayar cikin tsananin tashin hankali.
Ganin yadda take daga ganinta ka ga mara lafiya, sai Solo ya shiga cikin gidan. Yana zaune
daga shi sai gajeren wando yana ta aiki a Laptop ɗinsa..
Solo ya nemi izini ya shiga."Sir,