Showing 48001 words to 51000 words out of 90573 words

Chapter 17 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8086

Allah bai isa ba. Ki kwantar da hankalinki ki ci abinci ki huta ina nan zuwa
xan shigo, don na yi tafiya ni da Habibina. Kin dai san hanyar da na bi na riƙe shi. Ta baya ƙasa
za mu bi shi tun da ba shi da mutunci."
"Shikenan sai kin dawo."

"Yauwa kar ki damu ba zan daɗe ba. Na raka shi Legos za su yi seminer. Captain na ki ne babu
wata 'yar iskar da zai aura. Shi ma ya san yaudarar kansa yake. "

"Na gode Rauda sai kin dawo." Ta ce tare da kashe wayar hankalinta ya kwanta.

Iyayenta sun ɗauki fushi sosai da ita, ganin haka hankalinta ya tashi sosai. Da ƙyar ta samu ta
shawo kansu, bayan ta yi musu alƙawarin ba za ta ƙara kula shi ba, sannan za ta nemi wani ta
yi aure sannan suka haƙura, amma har lokacin haushinta suke ji.

Captain tun yana sanya idanun za ta dawo, amma har ya ga sun kwashi sata bata dawo ba.
Hankalinsa ya kwanta yana fatan ya yarda ƙwallon mangwaro ya huta da ƙuda. Tafiya zuwa
England ya kama shi hankalinsa kwance ya tafi.

Zariya
Mama Mufida zaune a gidan Anty Amina suna hira. Anty Amina ta waiwayo da take kwaɓa
kullum ɗan-gauda ta ce,"Wai yanzu kina nufin wannan turaren bitazaizai da ta shafa bai kalle ta
ba, mun yi asarar kuɗinmu kenan?"

"Hmmmmh! Ki bar ni da buhun takaici wallahi kallon banza ba ta samu daga gare shi ba, domin
ta ce mini gara Hanifa da yake kin san kishiyar uwarta ta san yadda za ta shiga fita a cikin
malamai, har kallon ta ya yi yana tambayarta karatu."

"Zai tambaya tun da yana zuwa an zuba masa a ruwa ya sha. Ni fa wannan Maryam ɗin tun da
na ji Sama'ila zai aure ta, na san cewar sai ta gama da shi da iyalansa."

"Wallahi ta gama da shi har ita mamata Hanifa, saboda ba ki ga ladabi da take mata ba, kaf
'ya'yanta in har Maryam ta yi magana ya zauna, har da waɗanda suke gidan auren."

"Duk za ta iya wannan 'yar gidan malaman zauren? Har yanzu ba ki ga sanin sunan mahaifinta
ba. Ita ma Maman Hanifah har da kwaɗayin ta sanya shi Aliyu, ya auri yarinyarta tun da kin ga
ya shaƙu da ita so take ta haɗa aurensu, ba tare da sanin ko da ta haɗa ba itace da riba, domin
haɗa auren amfaninta ne."
"Shi ya sanya tsani yarinyar nan, wallahi yadda na ke jin tsanarta, bana tunanin in Baban
Mufida ya ƙara aure na tsani kishiyata kamar haka. Yarinya ƙarama sai kinibibin tsiya, kowa
yanzu a gidan nan Anty Amarya dai."

"Iya makirci ne da kissa na mata, don ta zo daga baya ta mallake kowa a ciki, tun da bata
haihuwa ai dole ta nemi hanyar da za ta mallake kowa ta juya yaranku."

"Ai ba zai yiwu ba kuwa in har ina da rai. Kin san Allah yadda kaf yarana babu wacce ta auri mai
kuɗi kamar shi? To kuma babu yarinya da za ta samu mai kuɗi na zuba ido ayi auren ko da ace
Mufida ba ta son shi, sai na san yadda na yi na hana auren, domin ina gani ba za a rinƙa mana
iyayi da suruki mai kuɗi ba. "
"Ai gara ki miƙe wallahi in har Mufida ta same shi ta yi miji."

"Kin ga yanzu kuɗin da na ke juyawa na shinkafa na kwaso muje gurin Malamin nan, na fi son a
yi abun cikin sauri domin kin san da zafi-zafi akan buga karfe."

"Yanzu kuwa domin ina ɗora tukunyar gaudar, kafin na shirya Karima sun dawo daga
makaranta, sai na bar mata muje mu dawo tun da babu nisa. Ki kwantar da hankalinki Mufida
bata da miji sai shi."

"Allah ya nuna mini haka, har na ga yadda zan shuka rashin mutunci a dangi. Kina ganin Anty
Hafsa daga yarinyarta ta auri miji mai mota yana aikin gwamnati, sai iskanci duk aka zauna
zancen suruki take yi, sai kace kanta aka fara auran mai mota."

"Mijin da ba ita ce ta farko ba mijin wata ta aura har take tutiya?"

"Za ta yi mana tun da yana basu abin duniya, kuma kin san ta itama da shige-shige ba zama za
ta yi ba?"

"Haka ne kuwa ta shi mu tafi bari na ɗauko mayafina tun da ta dawo." Anty Amina ta furta bayan

ta gama jera ɗan-gaudar a tukunya ta rufe.

Kasancewar babu nisa basu jima ba suka isa. Bayan sun yi mishi bayani sosai, ya shiga ciki ya
yi musu rubutu da magunguna ya ba su.

Suna tafe suna hira Anty Amina ta kalle ta ce,"Kin dai ji abin da ya ce, sai ta kula yadda za ta yi
amfani da su."

"In sha Allahu kin ga tun da suna shiri da ƙanwarsa Nufaisah, sai ta rinƙa tambayarta lokacin da
zai zo. Yana zuwa sai ta je hutu gidansu, yadda za ta samu ta yi maganin, tun da ya ce dole
wannan rubutun sai ya ci a abinci."

"Eh hakan ma ya yi shawara ma kyau. Allah dai ya sanya ayi a sa'a."

"Amin, bari na wuce gida kawai tun da samu abin da na zo nema."

"Na ɗauka za mu koma kici abinci Maman Mufida?"

"Gara na koma gida yanzu na san Mufida ta gama abinci."

"To shikenan Ubangiji ya bada sa'a."

Amsawa ta yi tana ƙoƙarin taran keke napep.

Cikin farinckin ta isa gida, ta yi sallama Anty Amarya ce zaune a tsakar gida tana gyara zoɓon
da za ta dafa.

Amsawa ta yi tana mata sannu da zuwa. Wani irin tsuka ta saki ta wuce ciki ba tare da ta amsa
ba. Kallo ta bita da shi tana mamakin kishin da take yi da ita, saboda kishiyarta suna zaman
lafiya, amma Maman Mufida abin da take yi mata ko miji suka haɗa sai haka. Ci gaba ta yi da
aikinta bakinta ɗauke da azkar domin tana kula da ibada, saboda ta san cewa tana da maƙiya
sosai musamman ita.

Mufida, da take raba shinkafa da wake da mai da yaji da ta gama. Sallamar Mama ya sanya ta
ɗago tana kallonta. "Sannu da dawowa Mama."

"Yauwa 'yar albarka maza ki gama ki shigo." Ta ƙarashe maganar tana washe baki tare da ije
hijabinta kan igiya.

Ganin yadda take farinciki sai ta kasa ƙarashe rabon. Ba ta zuba nata da na Mama ta rufe
tukunyar.

Shiga ciki ta yi ta zauna gefenta."Kina jina Mufida? Malamin yace ki natsu ki yi wannan aikin da

kyau, domin ya tabbatar mana da in kika yi yadda yace Captain Aliyu sai yadda kika yi da shi,
amma wannan rubutun dole sai kin zuba masa a abinci."

"Cikin abincin da zai ci, ina zan ganshi na zuba masa?"

"Dallah ja can kin cika tsoro. Kin san wane irin namiji kike son mallaka? Dole sai kin zama
jaruma sosai. Abu mai sauki tambayi Nufaisah lokacin da zai zo, in ta gaya miki sai ki shirya
zuwa Kaduna ki yi hutu, don kar a zarge ki ku tafi da Hanifa."

"Kuma haka ne Mama, domin na ji kamar Anty Amarya za ta je Kaduna, amma sai in ya zo."

"Shikenan, sai ki ce za ki bita kin ga ai ba za ta ce a a ba, tun da za ta da Hanifa."

"Amma ina jin tsoron yadda zan sanya maganin, kin san ko a gida abincin Mommy kawai ya ke
ci?"

"Wannan kuma shawara ya rage wa mai shiga cikin rijiya, sai ki rinƙa abu kamar ba mace ba.
Ke ko irin fim ɗin nan da ake kallo ake sumun dubara ai kyayi yi tunani. In kin kasa sanya iya
abincinsa, ki sanya a cikin abinci kowa duka kin ga shi an yi don soyayar aure, sauran mutanen
gidan sai su ƙaunace ki."
"To Mama, zan gwada duk yadda zan yi sai na sanya masa, domin ba zan iya haƙura da shi
ba."

"Yauwa haka na ke son ji."

Damagaran
Jimmalo zaune a gaban Kaka Tani ta tasa ta kamar za ta yi kuka. Kallonta ta ƙara yi tare da
ɗauko jiƙaƙƙen magani ta miƙa mata,"Don Allah Kaka Tani kisha maganin nan, kin ga tun jiya
kika fara janta har yanzu jikin ya ki sauƙi."

"Na sha Jimmalo, sauƙin ne dai Allah ba kawo ba."

"To ki ƙara sha, yanzu zan je gurin Lado mau kyamis ko Audi ya haɗa mini maganin janta." Ta
ce tana ƙoƙarin kai mata ruwan maganin baki.

Kurɓa sau uku ta yi sannan ta koma ta kwanta. "Yauwa Kakata sanyin idaniyata. Bari na ruga
na siyo miki sai na tafi sarin ayaba."

"Sai kin dawo jikalle, Allah ya yi miki albarka." Ta ce tana kallonta.

"Amin," Ta amsa sannan ta fita da gudu.

Ba ta jima ba ta karɓo mata maganin, ciwo takwas da boska sai na ulser. Sai da ta tabbatar ta
sha sannan ta ɗauki tiren ta yi mata sallama ta fice.

Bayan fitarta Kaka Tani ta durƙushe a ƙasa tana maleluwa, saboda wani irin zafi da cikinta da
kirjinta yake yi. Sosai ulser ta taso mata. Haka ta yi ta maleluwa har ta samu ta lafa. Da ƙyar
take numfashi saboda ƙirjinta da yake mata zafi sosai. Tana da ciwon ulser, amma ba ta yi mata
haka.
Tun ranar da suka dawo cikin dare ta kasa bacci, domin da ta rufe idanu maganganun Hajiya
suke mata kuwwa a kunninta.

"Da gaske ne na ɓata tarbiyar Jimmalo?" Ta yi wa kanta tambayar domin ita gani take gata ta
bata. Duk da ta san cewar ba ta da tsafta. Abin da take ganin kawai za ta iya cewa shine
naƙasunta, amma tana ganin masifa da rashin kunya sai mutum ya taɓa ta, kuma wannan a
gurinta sam ba damuwa bane. Shi kansa jikanta da take ganin ta yi masa rashin kunya ai ba shi
da kunyar.

Duk yadda ta so ta kare lamarin kar ta ga laifinta, amma zuciyarta ta gaza hakan, domin
zuciyarta hutuma da zarginta take yi. Ta kasa bacci kullum cikin tunanin maganganun take yi,
musamman da ciwo ya rufe ta lokaci guda. Cikin ƙanƙannin lokaci ta gane tabbas gaskiya
Hajiya ta gaya mata, domin ta zauna ta auna lamarin rayuwarta, duk sai ta ga hakan ne. Duba
ga har yanzu da take shekar goma sha huɗu babu wanda ya zo yana sonta, kasancewar daga
shekara goma ake fara aurar da 'yan matan ƙauyen. Tsananin tsoro da firgici ya kamata ganin
ciwon na son ya fi ƙarfinta. Tunanin in ta mutu a hannun wa zata bar Jimmalo ta fara, wanda ya
ƙara rikita jikinta. Tunawa da duk 'yan'uwanta babu su.

Haka ta wuni cikin ciwo da tunani, wanda yake ƙara rikitar da jikinta. Gani take kamar mutuwa
za ta yi, saboda yadda numfashinta yake ɗauke wa in ciwon ya taso. Kafin Jimmalo ta dawo
daga tallah ta fita hayyacinta. Hawaye tausayin Jimmalo take yi, domin gani take kamar
mutuwa za ta yi ta barta a cikin duniyar da bata da kowa, kuma duk ta hayyaci kowa. Ta san
cewa in har wa'adinta ne ya yi, tabbas rayuwarta ta shiga gararin rayuwa. Ita kaɗai za ta ci gaba
da rayuwa a cikin gidan? Wannan tambayar yake ƙara tayar da hankainta matuƙar gaske!

Jimmalo tana gurin sarin ayaba, amma hankalinta na gurin Kaka Tani. Da sauri ta samu ta siyar
da ayabar, sannan ta siyo musu awara da rogo. Bata jira abokan tallarta ba, ta yi musu sallama
ta dawo gida.

Halin da ta ganta ya tsorata sosai, domin ta yi tunanin za ta zo ta ga jikinta ya yi sauƙi."Kaka
Tani, har yanzu jikin?" Ta yi mata tambayar cikin rauni murya tana kallonta, saboda tun da suke
rayuwa, bata taɓa ganin ta yi jinyar kwana biyu ta galabaita haka ba.

"Jikata kin dawo?" Ta furta da ƙyar tana jawo numfashi.

"Na dawo Kaka Tani. Ki tashi ga rogo da awara ki ci." Ta ƙarashe maganar tana ƙoƙarin zaunar
da ita.

"Ba zan iya cin komai ba Jimmalo, ji nake jikina kamar ana mini lalas na wuta, sannan ga wani
irin zafi da ƙirjina yake mini. Ki ba ni ruwa mai sanyi na sha."

Ganin yadda take maganar sai hankalinta ya tashi sosai. Da sauri ta kamata ta kwantar, sannan
ta ɗauki kofi ta ibo ruwan randa ta kai mata baki bayanta ɗago ta.

"Bari na je na kira Innar Salame ta yi miki kamun ƙirji." Ba tare da ta ji abin da za ta ce ba, ta fita
daga cikin gidan cikin tsananin tashin hankali.

Tana zuwa gidan ta faɗa babu sallama. Innar Salame tana gaban murhu tana ƙoƙarin ɗora
abinci."Don Allah ki je ki yi wa Kakata kamun ƙirji ba ta da lafiya."

Juyowa ta yi da sauri don ba ta ji lokacin da ta shigo ba. Kallonta ta yi ganin yadda ta bayyana
rauninta.

"Ba zan zo ba, sai yanzu da kike son na yi miki abu za ki bayyana fuskar tausayi? Duk yadda
kike ƙawance da 'yata bai hana ki gurza mini rashin mutunci ba. Shekaranjiya allasarata kika
ɗauka kan Fatahu yana tallah ki ce Salame ko uwarsa ta ƙwatar masa. Don haka ki je ki yi mata
da kanki tun da ita ma bata da mutunci, in an kawo mata ƙarar ki sai ta goyi bayan ki. Shi ya sa
kike abin da kika ga dama."

Jin abin data ce sai hankalinta ya tashi sosai, musamman tuna yadda ta bar Kaka Tani cikin
mawuyacin hali.

"Don Allah Innar Salame kije kar kakata ta mutu. Wallahi zan haɗa zan biya har da kuɗin kamun
ƙirjin, kuma na rantse daga yau ba zan ƙara miki rashin kunya ba."

"Ba zan ji daɗin bakinki ba, ki tafi ki ba ni guri mara kunya da rashin tarbiyya fitsarrarriyar banza
kawai."

Da ace lafiyar Kaka Tani ƙalau ta faɗi haka. Ta san cewa a rashin kunyarta sai ta yi ƙoƙarin
marinta, amma sai ta yi mamaki ganin ta kara duƙawa ƙasa ta ce,"Ki taimake ni kar Kakata ta
mutu don Allah."

"Ba zan yi ba sai ki je rashin kunyarki ya yi mata."

Miƙewa ta yi cikin hawaye za ta fice da gidan, sai ga Salame ta shigo da sauri, saboda an gaya
mata jimmalo ta je gida su. A tunaninta rashin kunya ta je ta yi wa innarta.

"Yauwa Salame ki taimaka ki roki innarki ta je ta kama ta kirji, kin san duk ƙauyennan ita ce ta

iya kamun ƙirji."

"Ba za ta je ba ai dama na gaya miki, akwai ranar da zan rama rashin mutuncin da kika yi mini.
Sai ki je ki nemi wata, amma Innata ba za ta je ba mara mutunci kawai."

Jin abin da ta ce sai ta fita cikin damuwa, ba tare da ta ƙara cewa komai ba.

Salame da uwarta suka rinƙa zaginta suna ala ƙara.

Cikin sanyi ta koma gida, sai dai ganin jikinta ya ƙara riƙewa sai ta sanya kuka sosai ta koma
gidan.

Duƙawa ta yi cikin muryar kuka ya ce,"Ku taimaka mini Kakata za ta mutu numfashinta sai
ɗauke wa yake yi."

Jikin Salame ne ya fara sanyi ganin Jimmalo tana kuka sosai. Za ta iya cewa tun da take karon
farko da ta ga zuciyarta ta karaya tana kuka.

Salame sai tausayinta ya kamata, kallon Innrta ta yi da take ta tuƙin tuwonta."Inna, don Allah ki
je ki dubata. Ki yi saboda Allah daga ganin yadda ta yi Kaka Tani tana jin jiki."

"Yanzu kin manta rashin mutuncin da take miki? Kaf ƙauyen nan wa suke gani da mutunci. Ai
dama muna jiran wannan lokacin da za su nemi taimako a kai musu, sai su san ana yin mutunci
saboda gobe."

"Ki je ki dubata saboda Allah ba don halinsa ba. Allah yasa hakan ya zama silar shiriyarsu."

Shiru tayi tana tunanin kamar kar ta je. Ko mai ta tuna sai kuma ta figi gyalenta ta ce,"Ki kwashe
tuwon ki raba."

Jin abin da ta ce sai Jimmmalo ta kalli Salame ta ce,"Na gode da kika sanya ta je. In sha Allahu
ba zan ƙara miki rashin mutunci ba."

Ba ta amsa magabata wuce murhu don ta kwashe tuwon. Ganin haka ta ruga da gudu ta bi
bayan Innar salame.

Suna shiga cikin gidan ta ɗago Kaka Tani da take nishi da ƙyar."Yanzu Innar Salame zata yi miki
kamun ƙirji za ki warke sannu Kakata." Ta ce tana ƙoƙarin tayar da ita.

Innar Salame, duk haushin su da take ji sai da ta tausaya mata ganin halin da take ciki. Da sauri
ta fara kamun ƙirjin tana mata sannu.

Bayan ta gama ta kalli Jimmalo data yi zuru tana kallon ta cikin tausayawa. "Jimmalo ki kira

Audi mai kyamis ƙila sai ta sha ruwa, saboda ta yi yaushin sosai."

Miƙewa ta yi jin abin da ta ce ta fita. Bayan ta yi mata kamun sai ta kasa tafiya ganin halin da
take ciki.

"Wash! Jimmmalo mutuwa zan yi ki zo mu yi bankwana." Haka Kaka Tani take faɗi hawaye
yana zuba ƙuncinta tana tausayin rayuwar Jimmalo.

Audi mai kyamis ya shigo ya sanya mata ruwa, sannan ya yi mata allura. Kallonta yake yi ya
ce,"Yaushe ta fara wannan ciwon?" Ya tambaya yana kallonta yadda ta koma.

"Shekaranjiya ne kuma na bata bauri."

"Ina ganin in dai ruwan nan bai yi ba dole kaita asibitin birni, saboda gaskiya tana buƙatar kula
da magunguna."

"Na shiga uku! Kaka Tani ciwo lokaci guda? Kar dai mutuwa za ki yi?"

To Kaka Tani Allah ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login