Showing 66001 words to 69000 words out of 90573 words
Chapter 23 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da
kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*
*Arabian oud*
*Lamsa oud*
*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*
*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*
*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*
*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*
*Adress ringi road, na dorayi, kano*
*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*
*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*
í ½í±‡í ¼í¿¾í ½í±‡í ¼í¿¾í ½í±‡í ¼í¿¾í ½í±‡í ¼í¿¾
*08130902505*
"Mommy, ta ce ki zo ki tafi." Umma ta ce sai kuma ta tsaya dariya na son kubce mata ganin
shigar da ta yi.
"Dallah gani nan zuwa kike kallona kamar ba ki san ni ba." Ta daka mata tsawa, tana watsa
mata harara kamar idanunta zai faɗo ƙasa.
Da sauri ta koma falo tana dariya."Mommy, kin ga shigar da ta yi kuwa? Yadda kika san wata
tsohuwa."
"Ni dai kawai ta zo su tafi, na gaji da yarinyar a kwana É—aya."Mommy ta ce kamar za ta yi kuka.
Daddy na saukowa daga sama da nufin ya kira Aliyu, sai ta murɗa ƙofa ta fito.
Dariya sosai ta kama su."Jimmalo, don Allah ki daina shigar nan. Ki kawo kayan nan a ƙona,
mutane na gaya miki dariya za su rinƙa miki."
"Babu wanda zai ƙona mini kaya, kuma ba zan daina sawa ba." Ta ce cikin rashin kunya.
Mommy kallonta ta yi, domin ta gwammace da ba ta yi wankan ba, duba ga yadda ta taso da
datti.
"Don Allah Daddy ku je kawai, wannan kafaffiyar yarinyar ba za ta canza kayan ba."
"Ok, Umma da Nufaisah ku taso ku tafi."
"Ok," Suka ce tare da fara tafiya.
Ganin haka suka bi bayansa, har da Jimmmalo da take ta yanke shawarar yadda za ta gudu ta
koma Damagaran.
Aliyu na zaune a falonsa yana huci, kamar mesa Daddy ya yi masa sallama ya shigo. Tun
lokacin da ya tura masa tsaƙon, ya fito yake jin kamar ya kashe kansa.
Jin sallamar Daddy ya sanya shi fitowa yana huci."Je ka kai ƙanwarka makaranta, in ka gama
mata rigister ka kai ta islamiyar su Nufaisah."
Ganin da su Umma za a je sai ransa ya ɓace sosai, domin ya shirya sai sun fita ya ce ta bar
garin, bayan ya wahalar da ita a mota, domin wani irin gudu ya shirya zai yi da ita.
"Mu je amma ba zan iya ɗaukar mahakaciyar nan a mota..." Maganar ta maƙale masa ganin
shigar da ta yi
"Daddy, kana ganin shigar mahaukatan da ta yi? Su kansu masu makarantar ba za su É—auke ta
ba, ganin shigar haukar nan. Wannan yarinyar makarantar mahaukata ya kamata a sanya ta."
"Kai ne mahakacin ba ni ba." Ta ce masa cikin gatsali.
Ganin yadda ya harzuka sai Daddy ya ce masa,"Don Allah Aliyu ku je na riga na yi magana da
mai makarantar. Kuma kar na ji ka kai hannu jikinta, innba haka ba su na yi mummunar saɓa
maka." Daddy ya ce cikin ƙosawa.
Nufaisah da Ummu suka shiga gaba sai Auta a gaba. Daddy ya nuna wa Jimmalo gefen Umma
da take ta addu'ar Allah ya sanya gefen Nufaisah za ta shiga, amma sai ta ga addu'ar ta ba ta
karɓu ba, ganin haka ta yi dubarar juya mata baya ta toshe hancinta, domin har yanzu wari take
yi.
Aliyu kafin su tafi sai da ya ƙarar da kwalbar turare, domin tana shiga ƙamshin motar ya canza.
Maigadi ya buÉ—e masa get ya fara tafiya cikin takaici. Yana fita daga gidan ya kashe motar ya
fito.
Buɗe gefen da take ya yi, tare da fincikota ya watsa a boot, sannan ya shaƙi numfashi mai daɗi.
"Banza ƙazamiya mara kunya. In har zan fita dake sai dai ki rinƙa zama a Boot." Ya ƙarashe
maganar tare da rufe boot É—in da karfi.
Mamaki sosai su Umma suka yi, amma sai suka hankalinsa kwance ba tare da tunanin komai
ba yake tunkinsa bayan ya ƙara fesa turare, domin wani irin wari take mishi. Jin zata dame shi
da buga Boot ɗin ya sanya waƙa har suka isa.
Sai da ya mula baya sun gama fitowa kalli Nufaisah."BuÉ—e mahaukaciyar can." Da sauri ta
ƙarasa tun kafin ya gama maganar saboda tausayinta, domin ta ƙara tabbatar da ba shi da
imani.
Tana buÉ—e ta ta saka kuka, ta fita da sauri tana sauke numfashi. "Mugu azzalimi sai na rama
abin da ka yi mini."
Ba tare da ya kalle ta ba ya wuce ofishin Principal. Jimmalo sai ta nemi guduwa, amma babu
hanya kan dole ta bi bayan su Umma, tana É—ura masa ashar da jawo masa jifa'i.
Umma aji ta wuce da sauri, don kar ƙawayenta su ganta da Jimmmalo. Auta ya shiga na shi
ajin. Nufaisah ce ta bi shi zuwa ofishin Principal É—in.
A lokacin da ta fito, kallonta É—aliban suke yi cikin tsananin mamaki. Ba tare da ta damu da
leƙenta da 'yan ajin suke yi ba, ta bi bayan Nufaisah.
Captain kuwa tuni ya shige ofishin Principal É—in"Mahaukaciyar ce innta yi abu duka ake mata
sannan take natsuwa. Da zarar ta yi muku hauka ku sanya sajen ya yi mata dukan tsiya.
Ya cewa Principal É—in da yake kallon ta cikin mamaki ganin shigar da ta yi.
"Ok bari na gama mata interview sai na san inda zan sanya ta, domin yarinyar ta yi girma
kamata ya yi a sanyata a aji uku."
"She is illiterate ba ta san komai ba. Ku sanya ta a nursery one." Dariya sosai ya yi jin abin da
yace.
"Ta yi girma sosai, domin ko primary six aka sanya ta ta girma, amma dole haka nan za mu
sanya ta in ya so sai ki É—aukar mata tuitor a gida."
Tsaki ya yi don,' wannan ba shafe shi ba, saboda a gurin shi in ta so ta mutu a jahila.
Ganin haka ya juya gurin Jimmalo da take ta raba idanu.
"Ke what is your name?" Ya yi mata tambayar yana kallonta.
Jin turanci ya yi mata ba ya gane ba, domin inda an tambaye ta bata san yaren da yi yi mata ba.
"A mayar dani kauyen damagaran, saboda ba zan yi makarantar arna ba." Ta furta a gatsale
tana kallonsa.
"I said what is your name? Kina gaya mini makarantar arna. An gaya miki ni arne ne? Musulmi
ne ni sunana Muhammad."
"Amma ka yi asara kana arne ka sanya sunan Annabinmu." Ta furta cikin takaici tana kallonsa.
"Ke! Ni ba arne bane." Ya daka mata tsawa yana faÉ—in haka.
"To amma kake shigar arna?" Ta furta hakan ganin suit ne a jikinsa.
Komawa ya yi ya zauna yana huci. Don ya rasa amsar da zai bata.
"Ka gani ko? Na gaya maka mahaukaciyar ce. Dole ku dage in ta yi muku haka ku yi mata
shegen duka."
"Gaskiya na ga alama za mu yi aiki."
"Sosai ma kuwa." Ya ce tare da miƙewa domin so yake ya bar Kaduna da zarar ya koma gida.
"Za ki iya karanta mini A.B.C da kuma 1.2.3.4?"
"Kai ka sansu, don ni ko karatun allo da na iya na sallah na yafe wa kaina, saboda ba zan
wahala ba. Haka kawai wani gardi ya duke ni."
Mari Aliyu ya kawo mata."Uban waye gardi?"
Da sauri ta matsa tana ƙunkunai."Kana ji ko? Ba zan koma da ita ba, saboda zan iya amayar da
kayan cikina. A nan zan barta sai ka yi mata tambayoyin, amma da za ka ji shawara ku sanya ta
a nursery one"
"Shikenan babu matsala, zan yi magana da mahaifinka duk da ya tura mini kuÉ—in komai, amma
gaskiya bayan na makaranta dole a tura mana da wasu kuɗi, domin tana buƙatar proper care.
Nanny's É—in mu za su kula da ita, yau dole ayi mata wanka sannan ayi kitso ta canza ka..."
"Wanne me? Na rantse babu wanda ya isa ya taɓa mini jiki, duk wanda ya yi kuskure taɓa ni,
sai na ragije masa kai." Ta furta tana ƙoƙarin ficewa.
Aliyu ya sanya kafa ya taÉ—iyeta sannan ya ce,"Good, ku yi duk abin da ya kamata. In kun kasa
wanke gashin ku aske kawai." Yana gama faÉ—in haka ya fice.
Ganin haka ta saka kuka za ta bishi."Wayyo ba zan yi karatun arna ba, kuma babu wanda ya
isa ya aske mini kai. Ba zan yi wankan ba. Wayyo Kaka Tani ki taso daga ƙabari za a kashe
jikarki." Ta saki ihu tana faÉ—in haka.
Principal ɗin fitan Aliyu sai ya yi masa daɗi. Da sauri ya miƙe bayan ya kira nanny guda biyu.
"Mene ne sunanki?"
"Jimmmalo jikar Tani." Ta furta tana harararsa.
"Sunanki na gaskiya nake magana da na mahaifinki."
"Sahiya Audi." Ta furta tare da murguÉ—a baki.
"Ok, Safeeya Abdullahi kenan?"
"A ɗan dakata kar ka ɓata mini sunana, saboda Sahiya Audi nake, kuma Kaka Tani da Jimmalo
take kira na, saboda ta ce ranar sa a aka haife ni. Ranar Juma'a don haka Jimmalo za ka kira
ni."
"A makaranta dole sunan yanka za a kira ki da shi."
"Ni wallahi duk wanda ya kira ni da wani suna ba Jimmalo ba, sai ba gurje bakin mutum da
yashi."
"To sai ki fara ta kaina mara kunya fitsarrarriya kawai." Ya ce yana harararta
Kafin ta yi magana nanny's suka shigo"Sir gamu." Suka haÉ—a baki girin faÉ—in haka.
Kallonsu ya yi ya ce,"Ku kira mini sajen Saminu, sannan wanna yarinyar ku kamata ku yi mata
wanka, ku duba kayan da zai shige ta na uniform primary one za a sanya ta."
Zare idanunsu suka yi "Primary one sir? Yarinyar da ta girma haka?"
"Yar ƙauye ce ku yi abin da na ce."
"Ok sir." Suka haÉ—a baki gurin faÉ—in haka a tare.
Kallonta suka yi da take zare idanu."Na rantse duk wanda ya taɓa ni, saina sanya Kakata ta yi
masa fatalwa ta lashe shi." Ta ce cikin rawar murya ganin kashedin bai sanya su fasa ninyar su
ba.
"Kai this girl is smelling ke wace irin ƙazamiya ce bakya wanka?"
"Gyatumar ki ce ƙazamiy..." Kafin ta ƙarashe maganar ta ji an wanka mata mari.
"Kul! ba a zagi a makarantar nan, saboda ba za ki koya wa É—alibanmu rashin kunya ba."
"Alllah ya isa mugu azzalimi."Ya ji tace kafin ya ƙarashe maganar.
"Please ku je ku yi mata wankan ku tsaftace ta."
Ihu ta saka za ta fita, amma sai sajen Aminu ya ɗauke ta cak zuwa bayi, saboda wani irin ƙato
ne murÉ—adde.
Ihu ta cika makarantar tana kiran Kaka Tani, amma ba su kula ba har sai da suka danganata da
bayi.
A cikin class É—in su Umma, tana zaune ta gefen windo tana kallonta."Umma, wancan yarinyar
ba 'yar uwarsu bace? Saboda kamar a motar Yayanmu ta zo?"
"Ba 'yar uwata bace ban san ta ba." Ta ce don bata son mutane su san suna da 'yan'uwa a
ƙauye '.
Aliya komawa ta yi ta zauna, don ba ta yarda ba, musamman da ta nuna rashin gaskiya.
Tana kuka tana ihu, amma basu kula ba sai da suka fara mata wanka. Ihu da zagi kam ta yi shi
har sai da muryarta ya rushe. Da ta san abin da za ayi mata kenan, da ba ta yarda da maganar
Mommy ta zo makarantar ba.
Kanta kuwa, bayan sun sanya mishi mai, sai da suka yanke gashin da ya dunƙule, duk da kuwa
gashin irin mai tsantsi da warwara ne, amma saboda rashin tsafta da kula ya sanya shi fita
hayyacinsa. Abin takaici gashi tana da gashiin sosai, amma duk wanda ya kalli gashin sai ya yi
mai. Da suka zo goge bakinta sai da suka ji kamar ba za su iya ba, saboda suna dirjewa jini
yana zuba. Makilin kusan ɗaya ya ƙare, amma bai yi hasken da suke so ba, saboda ya riga ya
dafe. Ga abinci da ya zama gansa kuka.
Sun samu sun yi mata wankan, don babu dauÉ—a jikinta, sai dai ba ta yi haske ba. An dai cire
datti. Kayan makaranta suka É—auko mata bayan sun shafa mata mai da karfin tsiya.
Babu laifi sai ta fito 'yar makaranta da ita. Kallon kanta ta yi cikin kuka saboda gani take babu
tozarcin da ka yi mata yafi wannan. Jikinta kuwa zafi yake mata, saboda dirzansa da suka yi.
"In sha Allahu wuta za ku shiga mugayen azzalumai." Ta ce daidai lokacin da sister Lami ta
miƙa mata sandal da sock.
"Rufe wa mutane baki mara kunya. A makarantar nan sai na koya miki hankali. Maza sanya
sandal da sock ki je ofis."
Ganin ta ƙi sanya wa tana murxa bakinta da ta buge, sai ta janyota ta faɗi kasa ta fara ƙoƙarin
sanya mata. Ganin haka Sister Ani itama ta janyo É—ayan kafar suka sanya mata.
Janta suke yi da ƙarfi har suka isa ofishin. Principal ya kalle ta ya ce,"Dubi ki kin ɗan yi fasali
mai ake yi da mutum ƙazami?"
Harara ta aika masa da shi saboda ba ta son magana, domin bakinta da suka gurje zafi yake
mata, sannan da ta yi magana sai jini.
"Ku je zan kaita primary one."
"Ok sir." Suka ce tare da juyawa suka tafi.
"Ki biyo ni." Ya daka mata tsawa yana faÉ—in haka
Binsa a baya ta yi tana ƙunkunai har suka shiga primary one.
Yana shiga yaran suka miƙe suka haɗa baki gurin faɗin,"Good morning sir."
"Morning how are?" Ya ce musu yana kallonsu.
"Fine thank you sir." Suka ce suna kallon Jimmalo da ita ma take kallonsu.
"Sit-down you have a new mate sunanta Safeeya Abdullahi."
"A'a ni fa sunana Jimmalo, ku kira ni Jimmalo jikar Tani, domin na rantse duk wanda ya kira ni
da Sahiya sai na karya mutum."
"Safeeya, za ku kira ta sannan ku rinƙa koya mata karatu, a jinku za ta zauna"
Zare idanunsu suka yi, jin abin da ya ce."Sir wannan sa'ar Addata Hafsat ce a kaita ajinsu,
saboda ta yi girma a nan. Za ta zama maman aji" Faisal ya ce su suka kwashe da dariya.
"Kai ni ne zan zauna da waɗannan ƙananan yaran? Hahaha, wasa kake yi na rantse, in ba so
kake yi na rinƙa ɗaukar su na maka su da ƙasa ba, don tsaf zan kashe yaro in har sun mini
dariya."
"Ke Safeeya, ki natsu don wallahi kika cutar da wani sai na sanya an miki duka."
"Ni fa ka daina kirana da Sahiya Jimmalo dai." Ta ce tana harararshi.
"Kuna ji ku rinƙa koya mata karatu Anty don Allah ki sanya ido, sannan ki rinƙa koya mata
karatu."
"Ok, sir." Malamar ta ce tana kallonta da take ta kumburin tana zaginsa.
"Na rantse duk yaron da ya yi kuskuren cewa zai koya mini karatu suna karya shi."
"Ki taɓa yaro a makarantar ki gani." Ya ce mata tare da tsaki ya fita.
Ganin za ta bishi Anty ta ce,"Ke Safeeya, come and sit down."
Tsayawa ta yi ganin ya rufe kofar sai ta dawo ta É—age saman windo tana faÉ—in."Na rantse duk
sai na yi maganinku, har ke da kike ji da ƙiba kamar doya."
Dariya aka kwashe da shi malamar ta yi musu tsawa."Ba zan lamunci rashin kunya ba, kuma
zan mugun saɓa miki."
Ƙunƙunai ta yi ta haye zaman windo tana mamaki wai yau ita ce a makarantar boko?Gaskiya
mutuwar Kaka Tani ya kawo mata cikas a rayuwarta.
Ganin haka sai ta ci gaba da karatun burinta ta gama darasin lissafin ta fita. Jimmalo tana
zaune tana ta kallonta. Ko da aka kawo mata takaddunta da pencil kallonsu kai ta yi ba tare da
ta ɗauke su ba, domin a ganinta basu da amfani don riƙe pensil ba ta iya ba ballantana rubutu.
To Jimmalo Jikar Tani an fara shiga wata rayuwa. Daga Jimmalon yau mun ji ainihin sunanki
Safeeya. Sai na ce ɗaliba Safeeya Allah ya sanya ki tsaya ki iya karatu. Yau dai kawo ƙarshen
kan Jimmalo da rashin wanka. Shi za ta goge ta waye ta zama student ko za ta ci gaba da
gidadanci? Ku ci gaba da bibiyar labarin da zafafan comments.
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruÉ—ani. RuÉ—anin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan