Showing 33001 words to 36000 words out of 90573 words
Chapter 12 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 10
Tallah
Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin
result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka
sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan
ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama
kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast
Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta
wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na
gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da
ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina
shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606
ina zaune a kano
"Tafi can ja'iri har yanzu ina jin haushin ka Aliyu. Ƙiri-ƙiri ka ƙi zaɓin matar da na yi maka."
"Hajiya ki kwantar da hankalin ki. Duk ranar da na kawo miki matata, sai kin ga amfanin jinkirin
da na yi."
"Jinkirin ba shi da amfani musamman ku sojoji, da wasu suke bibiyan mata, ko da ace ba ka da
wannan halin abokai za su iya koya maka."
Gabansa ne ya faɗi jin abin da ta ce."Ki kwantar da hankalinki sam ba haka jikan ki yake ba."
"Na yarda da kai Aliyu, ban taɓa ganin soja wanda ya kama addininsa yake riƙe kansa kamar ka
ba."
"Haka ne Hajiya in Sha Allahu zan ci gaba da kulawa." Ya furta cikin jin kunyar fuska biyu da ya
zama yana shafa kansa.
"Bari na kawo maka mutumin ka kamar nasan za ka zo, na yi kunun gyaɗa da yawa."
"Allah ya kyauta! Na sha wani abu wancan ƙazamiyar tana gidan. Zan tafi kawai, saboda ina
son na shiga Zariya, kuma duka kwana biyu zan yi na koma Abuja."
Kallonsa ta yi, ganin yadda ya gasganta abin da ya ce ba zai sha ba."Ok tom gara ka je ka yi
zumunci, musamman da an yi biki ba ka samu zuwa ba, sannan Lawan ma ya yi zazzaɓi."
"In sha Allahu zan je a yau. Muje ciki na yi hira da matata sai na tafi." Ya ce tare da kama
hannunta. Dariya ta yi suka shiga cikin bedroom ɗin ta.
Jimmalo tana zaune, tana tunanin abin da za ta yi masa ta baƙanta masa. Buɗe labulen ta yi sai
ta yi arba da motarsa mai kyau. Murmushin muguntar ta yi, sai ta fice daga cikin ɗakin ba tare
da ta kula da Kaka Tani da take cewa,"Ina za ki Jimmalo, kin ga ki bari wancan mai zuciyar
fir'aunan ya tafi, domin wallahi ya dukan mini ke rashin mutunci zan masa.
Ka tsaye kicin ta shiga, ta samu wuƙarta mai ƙaifi da ƙarfi. Gurin motarsa ta je ta samu ƙaton
dutse ta rinƙa bugawa tayar motar sai da ta sace masa tayar. Da sauri ta ruga cikin gidan, tana
murnan don ta san sai yaji haushi kamar zai kashe kansa.
A daidai falo suka haɗu Hajiya ta rako shi suna hira. Kallonta ya yi ganin yadda ta ɗan razana
na ganin shi
Ganin yadda ta yi, daga shi har Hajiya suka rakata da idanu. Wani wawan tsaki ya saki zai fice,
kafin ya fita ta mayar masa da nata.
"Don Allah kar ka rinƙa biye wa wancan yarinyar, saboda ba ta da hankali. Ni ban taɓa ganin
mace irin ta ba, wallahi Tani ta cuci rayuwarta yarinyar nan."
"Karki damu Hajiya, daga yau ba zan ƙara yarda na ƙara ganin ta ba, saboda na tsane ta bana
ƙaunar na rinƙa ganinta."
"Allah ya saka da alkahiri hidimar biki da ka yi." Ta ce tare da kawar da zancen.
"Amin, ya ba su zaman lafiya." Hira suke yi har suka isa gaban motar sa.
Hajiya na tsaye ya shiga bayan ya yi mata sallama."Don Allah in ka je Zariya ka gaishe mini da
su."
"Duk za su ji Hajiya." Ya ce tare da fara ƙoƙarin tuƙa motar. Da ya kunna sai ya lura ta yi ƙasa
gaban motar.
Gabansa ne ya faɗi sosai da sauri ya kashe motar ya fito, yana son duba abin da ya faru, domin
ya san motarsa lafiya take.
Hajiya kallonsa ta yi cikin damuwa, ganin yadda lokaci guda fuskarsa ta canza idanunsa suka
kaɗa, saboda ganin aika-akar da ta yi masa, domin ya tabbata ita ce kawai za ta yi masa.
"Lafiya soja?" Ta yi masa tambayar da sauri.
Saboda zuciyar da ta tiƙe shi kasa magana ya yi, sai kawai ya nufin cikin gidan yana huci.
A ɗakin Jimmalo take rawa cikin farin ciki, domin abin da ta yi masa ta san sai ya kusa kashe
kansa, saboda baƙinciki.
"Ina fatan ba wani abu kika ƙara yi masa ba? Kin ga ki fita harkar wannan mara
imani..."Maganar ta maƙale mata sakamakon ganinsa ya shigo yana huci kamar mesa.
Kai tsaye inda take ya je, ba tare da ya kula da Kaka Tani da take masa magana ba. Wani irin
wawan mari ya sakin mata, sannan kuma ya fara dukanta yana haurinta ta ko'ina. Saboda
kafiya da taurin rai, ƙoƙarin ramawa take yi, kuma bakinta bai mutu ba, sai zagi take auna
masa.
"Aliyu lafiyarka ɗaya kuwa don Allah ka daina dukanta." Cewar Hajiya tana riƙe shi, amma bai
kula ba so yake sai ya ƙaryata.
"Zuwana birni ya zamar mini masifa! Hajiya in har ya kashe mini jika wallahi sai mun yi shari'a."
Ganin dukan da gaske yake mata kuma ya ƙi dainawa, sai kawai ta fashe masa da kuka
sosai."Aliyu in har ni na haifi ubanka ka daina duka yariyar nan, domin zan iya masa baki."
Cak ya tsaya yana huci kamar mesa.Ganin haka ta fito da shi falo tana share hawaye.
"Na rantse ba zan yarda ba dole ki ɗauki mataki, kuma yau za mu bar gidan nan." Cewar Kaka
Tani tana girgiza. Ita kuwa ko hawaye sai ɗura masa zagi take yi, tana jawo masa bala'i, amma
kuma ta daku don ta ji jiki sosai.
"Hajiya ki fita daga rayuwarsu, saboda in har za su kasance dake zan daina zuwa inda kike, ko
kuma watarana za a kulle ni nayi kisa.. Yarinyar nan tayoyin motana ta sace saboda ba ta da
tarbiyya."
"Kai amma Jimmalo ba ta kyauta ba, na rasa yadda aka yi ta raina ka."
"Ok, goyon bayan jikan ki kike yi ko? Saboda ke kika haifi ubansa ba ki ga abin da ya yi mata
ba?" Kaka Tani ta furta tana jijjiga.
"Tani ya kamata ki fuskanci gaskiya, ki gane irin tarbiyyar da kike mata babu kyau. Jimmmalo
mace ce kuma uwa za ta zama nan gaba, in har baki canza ta kan tarbiyyar da kika bata ba,
walllahi za ki yi dana sani."
"Dakata Hajiya bana son rashin tsoron Allah. Jiƙanki ya duke ta kuma ki goyi bayansa kina
gaya mini jikata ba ta da tarbiyya?"
"Tana da shi ne? Ɗube ta tamkar jaka yarinyar nan ba ta da maraba da dabbobi, saboda wallahi
dana zauna da ita gara na zauna da kare."
"Aliyu karka ƙara magana ba sa'arka bace."
Jin ya danganta Jimmalo da kare, sai ta fashe da kuka ta ce,"Innnali wa inna ilahir raju'un!"
Dama kin ɗauko ni ƙauye, don ki wulaƙanta ni da jikata? Zumunci bai ce haka ba, saboda in da
kin tuna zaman da iyayenmu suka yi, bai kamata ki yi mini wannan rashin mutuncin ba, amma
babu komai yau zan bar gidan nan ba zan ƙara mintina ba. Kada ki ƙara tunanin kin san ni ko
zuwa gurinmu, saboda don kina kawo mini abu ba zai taɓa sanyawa na yarda ki rinƙa zagin
mini jika ba. Jimmalo ita kawai na ke gani na ji daɗi."
Hajiya sai ta rasa bakin magana, ganin yadda ta harzuƙa tana hawaye sosai. Jimmalo da take
cikin ɗakinta jin kukan Kaka Tani, da sauri ta ɗauko gwafan da ta zo da shi ta fito.
"Waye ya taɓa mini ke yanzu na sakar mishi harbi?" Ta ce tare da take gwafar tana zare ido.
Ganin ta saita shi sai ya zabura zai yi kanta. Hankalin Hajiya ya tashi sosai, domin ta san in har
ta ƙyale shi ba za a yi da kyau ba.
"Aliyu maza ka bar gidan nan." Ta furta da ƙarfi tana kallonsa.
"Hajiya ki barta na yi mata dukan da sai na gyara rayuwarta, domin wallahi tsaf zan iya kashe
ta." Ya furta tare da kai mata hauri.
"Na ce ka fita za mu yi waya." Ganin yadda ta yi maganar sai ya fita daga gidan.
Mai gyara ya kira, sannan ya ɗauki motar da ake fita da Hajiya ya tafi gidansu. A mota kuwa ji
yake kamar zai kashe kansa don baƙinciki. Ya so ace ta barshi ya karyata.
Da ya isa gida hon ya yi maigari ya buɗe masa. Daddy ne a tsaye da Mommy da suka fito za su
anguwa. Ganinsa farinciki ya kama su sosai.
"Soja mazan fama." Cewar Daddy lokacin da ya ƙaraso, ya durƙusa da makullin mota a
hannunsa.
"Ina wuni Daddy, da Mommy."
"Lafiya lau ya gurin aikin?" Suka haɗa baki a tare suka yi masa tambayar.
"Lafiya kau hutu na samu na ce bari na zo na yi kwana biyu."
"Allah ya yi maka albarka ya ƙara tsare mini kai."
"Amin, Daddy." Ya amsa yana miƙewa.
"Lafiya ka ganka da motar Hajiya? Ko ta jirgi ka zo soyayya ya tashi?" Ya yi masa tambaya da
ya sanya shi murmushi da Mommy.
"Motata tana gidanta. Wannan yar iska mara kunyar yarinyar nan da muka je ƙauye ta fasa mini
mota. Na gani a gidan Hajiya za ta yi mini rashin kunya na buge ta. Shi ne take ta yi mini faci."
Zare idanunta suka yi suna faɗin,"Jimmmalo, ba ta da kunya da hankali."
"Ni mamakin Hajiya na ke yi da take ganin kamar za ta shiryu. Ita tunanin yadda za ta yi ta
kwace yarinyar take yi, don ta canza mata rayuwa."
"Wannan yarinyar momi ai ba za ta taɓa shiryuwa ba, kina ganin ta sam ba ta da hankali. Hajiya
ko ta karɓe ta wahala za ta sha. Ga shi ta tsufa haka kawai ta sanya mata cuta."
"Ni ma abin da na yi tunani kenan, domin wanda yayi nisa baya jin kira. Ta ƙyale ta kawai,
saboda duk wanda ya ɗauki yarinyar nan ya ɗaukarwa kansa jaraba. Ga ƙazanta ga rashin
kunya da zagi kamar yar maguzawa."
"Daddy, ina zargin tana fitsarin kwance saboda wani irin xarni da karni na ke jin tana yi."
"Zai iya yiwuwa, domin yarinyar nan sakalta da sangarta ya yi mata yawa."
"Allah ya kyauta wallahi ina baƙincikin da ta fito a 'yar'uwarmu, saboda ƘIYAYYAR JINI na ke yi
mata." Cewarsa ya miƙe.
"Ya za ka yi tun da Allah ya haɗa jinin." Cewar Daddy.
"Bari na shiga ciki, na yi wanka na shirya kafin Abdullahi Bakanike ya gyara mini motata. Yau
zan shiga garin Zariya in sha Allahu."
"Gurin mutuniyar ta ka ko? anty Amarya." Cewar Daddy ya ce yana kallon sa.
"Eh amma zan je na gaishe da su Baba Ɗanlami na yi murnar biki."
"Yana da kyau zumunci abu ne mai kyau, duk dacewar na san dai dalilin zuwan ya karfafa don
Anty Amarya."
"Haka ne Daddy kwana biyu ban je gurin ta ba."
"Ai shi da Anty Amarya ba a jin kansu. Ko ranar bikin ana ta yi mishi tsiya sai kare shi take yi.
Yarinyar tana da hankali sosai, domin Ya Audi ya samu mace mai natsuwa da hankali.
"Gaskiya kin ga ai ta yi karatu sannan tana da tarbiya. Shi kansa yana yabonta. Na tabbata da
ace tana da yarinya babba a yadda Aliyu yake mugun shiri da ita, zai iya auren yarta."
Kallon su ya yi yana murmushi domin zai iya ɗin. Tana da hankali da natsuwa. Kamar yayansa
haka yake jin ta.
"Bari na shiga ciki ina Nufaisah, Umma da auta?"
"Umma, ta je ɗauko shi a makaranta." Cewar Mommy.
Cikin ɗakinsa ya shiga, ya ije jakar goyon da ya zo da shi, da kaya kala biyu suke ciki, sai turare
da ɗan tarkacensa.
Ajiyar zuciya ya saki cikin ɓacin rai. Ya so ace Hajiya ta barshi ya cire mata haƙori.
Wanka ya shiga ya yi ta dirzan jikinsa, domin ganinta ya sanya shi ƙyamar kansa. Sai da ya
ɓata lokaci gurin yin wankan, sannnan ya fito ya shirya cikin shigan manyan kaya ya sanya
hula. Ya yi kyau sosai kamar ka sace shi ka gudu.
Wayarsa ya ɗauka don ya fito falo ya ci abinci. Nufaisah ce a falon tana shirya masa abinci, sai
Adnan da yake falon yana kallon cartoon.
Ganinsa da sauri ya tashi ya rungume shi."Auta ya kake?"
"Lafiya lau Ya Captain, where is my promise?"
"Yana ɗakina ga makullin ɗakin kai da Nufaisah ku ɗauki tsarabarku."
"Thanks brother." Ya furta cikin tsannanin farinciki.
"Sannu da zuwa Ya Captain?" Cewar Nufaisah tana kallonsa.
"Yauwa ya kike ya karatu?"
"Alhamdulillah mun yi hutun semester za mu shiga two hundred level."
"Da kyau ayi karatu sosai ban da kula samari da ƙawaye."
"In sha Allahu ya Captain." Ta ce masa tana kallon sa.
Dinning ya wuce don ya ci abinci, amma sai kawai ya rinƙa tuno fuskarta da haƙoranta. Da sauri
ya miƙe jin amai yana taso mishi. Mamaki yake yi yadda Hajiya ta iya surviving tana cikin gidan.
Wayarsa ta yi ƙara alamun ana kira. Ganin Abdullahi Bakanike ne, sai ya miƙe ya fito ba tare
daya ɗauki wayar ba, saboda ganin an buɗe masa get ya shigo da motar.
Karɓar makullin ya yi, bayan ya yi masa godiya ya shiga cikin motar.
Bayan fitarsa Hajiya sai ta rasa yadda za ta yi da su. Ta kalli Kaka Tani da take ta kuka tana
face majina, sannan ta jiya kallonta ga Jimmalo da take aika masa da zagi buhu-bubu. Kanta ya
kulle har ta yi dana sanin gayyato su gidanta.
"Wallahi Hajiya kin nuna mini jika ya fi ɗan'uwa. A gaban idanunki ya duki jikata, amma da yake
ita ba mutum ya haife ta ba, sai kika kasa ɗaukar mataki."
"Haba Tani, yaron nan fa magidanci ne ba ƙaramin yaro da zan kama shi da duka ba. Ke baki
ga rashin kunyar da ta yi mishi ba? Bayan zagin da ta yi masa har da yi masa faci."
"To don ta aikata haka ai ba sata ta yi masa ba, da zai sanya ƙafafunsa yana haurinta tamkar ta
yi mishi sata."
"Da kin ƙyale ni na sakin masa gwafar nan. Aradu sai ya yi fitsari a wando.Mugu azzalumi mai
idanun doki." Ta ce cikin zallar rashin kunya.
"Tani, zan gaya miki gaskiya ko da ba kyau so. Tarbiyyar da kike ba wa yarinyar nan cutarta kike
yi. Wallahi in har baki gyara ba, har kika bari Allah ya ɗauki kwananki ba ki canza mata
rayuwarta ba. Kin cuce ta kuma nan gaba sai ta yi dana sani sosai."
Sautin kuka Kaka Tani ta ƙara, saboda gani take kamar wulanƙanci Hajiya take mata don tana
da kuɗi.
"Na gode da rashin mutuncin da kika yi mini. Yau zamu koma ƙauye ba zan ƙara zama a cikin
gidanki ba, domin tozarcin da kika yi mini ya isa. Kin kira jikata mara kunya, bayan jiƙanki ne
mugu azzalumi mara kunya. A gabanki ya dukar mini jika kuma ya gaya mini maganganu mara
sa daɗi, amma ba ki ce komai ba tun da shi yana da kuɗi. Ni kuwa ba mu da komai dole ki
wulaƙanta ni."
"Ba wulankanci bane, gaskiya na ke ƙoƙarin gaya miki wallahi tarbiyyar da kika ba a ba mai
kyau bane, kuma kin cutar da rayuwarta. Za ta yi kuka ko da babu ke a rayuwa."
"A'a Hajiya, zan yi miki rashin mutunci wallahi in har kika ƙara faɗin Kaka Tani tana cutata. Kin
san wahalar da ta yi ta ciyar da ni har na girma? Kaka Tani har aikin ƙwadigo ta yi don na samu
abinci, amma saboda kin shigo cikin rayuwarmu jiya nan, don kin kawo mana abinci sai ki kalle
ta gaya mata haka?"
"Jimmalo, gaskiya na ke gaya miki kuma dama ɗaci ne da ita. Idan akwai abin da yafi cuta tayi
miki. Don da take miki da maraicin ki ya sanya ta yi miki tarbiyya mara kyawu. Rayuwa ba haka
take tafiya cikin haukar da ƙazanta da rashin kunya ba. Dole ki fuskanci rayuwa ki yi ilmi in har
kina son rayuwarki tayi kyau. Na yi miki alƙawarin zan kula da rayuwarki na ba ki ilmi in har za ki
zauna da ni. Zan canza miki rayuwarki Jimmalo. Zan sanya ki a makarantar kuɗi, na kuma ɗauki
ɗawainiyar rayuwarki har sai kin zamo wata aba"
"Allah Ubangiji ya tsare ni da wahalar da kaina gurin yin karatu. A yadda nake rayuwa haka ya
yi mini, kuma babu wanda zai yi mini dole. Mai zan