Showing 36001 words to 39000 words out of 90573 words
Chapter 13 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
yi da karatun arna? Na addinin ma tun da na
iya na sallah Fatiha da Kulhuwallahu na daina wahalar da kaina."
"Kwantar da hankalinki Jikalle, babu uban da ya isa ya yi miki dole in dai ina raye. Ma za je ki
haɗa kayanki mu bar mata gidan nan, domin ba zan ƙara kwana ba."
"To Kaka Tani." Ta furta da sauri tare da shigewa cikin gidan.
Hankalin Hajiya ya tashi ganin yadda suka ɗauki zafi, tamkar wacce ta yi musu zagi. Hannu ta
kai za ta dafa Kaka Tani, amma sai ta fisge cikin muryar kuka ta ce,"Karki taɓa ni na tsane ki. Ki
manta kin san Ni a rayuwa, domin daga yau na goge duk zumuncin da yake tsakaninmu. Duk
wanda zai aibata jikata bazan ƙaunace shi ba."
Da sauri ta janye hannunta ganin yadda take kukan. Jikinta ne ya yi sanyi sosai har ta kasa
cewa komai. Lokaci guda yarda da maganar Daddy cewar ba za ta iya canza su ba, domin sun
wuce tunaninta.
Abinci da turamen zani ta haɗa musu sannan ta kawo musu falo.
"Ku yi haƙuri ban so haka rabuwarmu ta kasance ba. Na so ace na karɓi Jimmalo daga gurinki
na ba ta tarbiyya da ilmi, domin rayuwarta ta canza ta samu miji na gari, amma ga yadda abin
ya kasance. Aliyu ya yi kuskure kuma zan yi masa magana."
"Kar ma ki yi masa ki ƙyale shi, ba sai ya gammu zai shiga gonarmu ba. Ya je ya yi abin da ya
ga dama. Duniya ce ta ishi bagaruwa jima. Watarana in halinsa duka sai ya duki wacce da za ta
sanya a kulle shi."
"Eh Allah yasa kuma ɗan makullin ya ɓata ya mutu acan." Jimmmalo ta furta har cikin zuciyarsa
tana fatan hakan ya kasance, domin ta tsane shi sosai.
Hajiya dai kasa magana ta yi, ganin sam ba ta ganin laifin jikarta. Ƙosawa ta yi su tafi domin
kanta har zafi yake mata.
"Zo muje Jimmalo, ba za mu ɗauki komai daga gareta ba. Hatta kayan sawa ki bar mata ai ba a
tsirara ta gammu ba, sannan na raba zumuncin da yake tsakaninmu kar ki ƙara zuwa
Kauyenmu, domin in har kika zo ko wani na ki, sai na sanya an yi muku rashin mutunci."
Kayyasa ni kaina ban taɓa ganin rikitattun mutane irin waɗannan ba to ga shi dai sun yi
zuciya za su koma ƙauye. Anya Jimmalo kina da rabon kilewa? Ku ci gaba da bibiyar littafin da
kuma yin comments don ji an yadda za ta kaya. Wai ya ne da comments ina ga
tafiyarta hutu zan yi tun da bakwa comments
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/HKTsxAVvVlw2b9mPcAPKke
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 11
Tallah
Shin y’ar uwa, kin daɗe ana cin miki kuɗi saboda kina siyan maganin nonon da ba kyau ganin
result ɗin sa? Kina cikin matan da suke mafarkin ganin sun zama masu cikowar ƙirji, in suka
sanya kaya su yi kalar madara zubin ajebota? To maza ki garzayo kar ki ji ƙyashin siyan
ingantaccen maganin gyaran nono don daga yau kukanki ya ƙare, in sha Allah. Kin gama
kashe kuɗinki gurin maganin gyaran breast
Kizo kisamu ingantaccen maganin gyaran breast ɗinki a gurin Maman Sayyid collection, ta
wannan numbar 08063114606 kisha hankalinki kwance maganinmu herbal ne wato na
gargajiya bashi da side effects babu wani abun bature acikin maganinmu zallar saiwoyine da
ganyayyaki da tsirrai na gyaran nono wanda babu cutarwa saidai su inganta miki lafiyarki inkina
shayarwa yaronki zai samu isasshen ruwan nono maganinmu kowa na iya sha 08063114606
ina zaune a kano
Ganin sun kama hanya za su fita sai ta fara roƙon, su da su bari direba ya mayar da su, sannan
su tafi da kaya da ta basu, amma suka ƙi.
"Na dai gaya miki bana fatan ƙara ganinki da zuriyarki, don haɗuwarmu ta biyu sam ba zai yi
kyau ba."
"Ki barsu Allah ya sanya su yi gigin zuwa, sai na raka su da gwafata ina harbinsu." Ta ce tare da
saita gwafar tana dariya.
Ganin haka sai ta tsaya cikin mamaki tana kallon su har suka fita.
Zama ta yi jaɓar kan kujerar tana mamakin halinsu. Tun da take ba ta taɓa ganin rikatttun
mutane irin su ba. Hawaye suke zuba a ƙuncinta na tausayin Jimmalo, domin in har ta ci gaba
da rayuwa a haka, nan gaba sai ta yi kukan da za ta ci gaba har ƙarshen rayuwarta.
Mai aikinta ta kira ta ce,"Don Allah ki fito da kayan ɗakinsu a wanke dakin sannan a sanya
turare. Wallahi ko ina na gidan nan ji na ke yana warin jikinta."
"Kai Hajiya, ai wannan yarinyar ƙazamiya ce wallahi. Tun da ta zo gidan nan ba ta yi wanka ba,
sannan ba ta sallah ballantana ta samu rahamar alwalan da take yi. Shi yasa gata nan ta yi baƙi
ta fita hayyacinta. Inda za a sanya abu a kankari jikinta Allah sai kin ga dadti na zuba, sannan
inta matso ni kamar zan yi amai. Ni wannan kan nata bana tunanin ta taɓa sanya masa ruwa?"
"Bana tunanin haka, saboda yarinyar nan ta iya ƙazanta ga rashin tarbiyya."
"Gaskiya Kakarta ta cuce ta da sunan so."
"Hmmmmh! Allah dai ya kyauta domin sun gasa mini aya a hannu. Ni sai yanzu na ke jin daɗi
abin da ya faru suka tafi, saboda wallahi tun da ta zo gidan nan na rasa natsuwa, kullum cikin
bari-bari na ke yi kamar wata yarinya."
"Ai barnar da ta ke yi bana tunanin ɗan shekara biyu zan yi. Da gangan yarinyar nan ta lalata
gas cooker, wai tana son ta ga ko wutar daga kasa yake fitowa."
"Ɓanna ai ta yi kala-kala, bayin ɗakin da suke duk ta lalata famfunan saboda wasa da ruwa."
"Ruwan da ba za ta yi wanka ba. Kai yarinyar nan ƙarshe ce gurin ƙazanta."
Hajiya ta yi ajiyar zuciya ta ce,"Na huta ai da nayi ninyar tallafawa rayuwarta, amma Allah ya ba
ni ladar ninya, don tafiyarsu ji nake yi kamar an sauke mini kaya."
"Gaskiya yau za ki yi bacci har da munshari."
"Je ki gyara ɗakin gobe sai an yi wa gidan nan kwalema."
"To Hajiya Allah ya kyauta ya shirya su."
"Amin," Ta ce tare da ɗaukar wayarta ta yi ciki tana laluben numbar Daddy.
Bugu da ya ɗauka cikin girmamawa."Hello Abubakar, dama waɗannan mutane haka suke?"
Dariya ya yi jin da muryar da ta yi magana." Sun fi haka musamman Jimmalo, mai suka yi
miki?"
"Ai ita ma kanta Tani ba sauƙi, saboda duk abin da take yi, ita ta ɗorata kan turbar hakan. Da
ace ta ba ta tarbiyya mai kyau, da bata zama haka ba. Maraici hauka ne da za ta zauna ta lalata
yarinya."
"Hmmmmh! Aini ban taɓa ganin mutane irinsu ba."
Abin da ya faru ta kwashe ta gaya masa. Dariya ya ƙara yi ya ce,"Yanzu sun tafi?"
"Sun tafi Abubakar. Gara su tafi wallahi har sun sanya mini hawan ruwa ba jini ba, domin na
tabbata da za a duba jinina ya hau."
"Allah ya shirya su ai zama da su babu wanda zai iya. Hajiya ni fa tun da ta iya kallon Aliyu ta yi
masa rashin mutunci na tsinke da lamarin yarinyar nan."
"Yanzu ma ba ka ga rashin kunyar da ta yi masa ba, kuma abin takaici Tani ba ta gani ba, sai
zagi take yi wa Aliyu."
"Abin da ya faru kenan a lokacin da muka je ƙauyen su. Wallahi in kika ga yadda ta yi wa Aliyu
sai kin yi mamaki. Da ace ban tsawata masa ba, na rantse ko bai kashe yarinyar nan ba sai ya ji
mata rauni yadda ya fusata."
"Dole ya fusata ko ni na ga rashin kunyarta. Yanzu dai sun tafi kuma ba zan ƙara bibiyar
rayuwarsu ba. Zumuncin ma na haƙura Allah ya gani na yi iyakan yi na."
"Haka ne Hajiya Allah ya ba ki lada."
"Amin, don Allah in zaka koma gidan ka biyo da likita ya duba ni."
"To shikenan Hajiya yau za ki yi bacci mai daɗi."
"Har da munshari Jimmalo ko hawan jini."
Dariya yayi sanan ya yi mata sallama ya kashe wayarsa. Mommy da take zaune a kujerar mai
zaman banza tana saurarensu.
Dariya sosai ta yi ganin ya kashe wayar. Shima dariya yake yi.
"Dama na san ba za ta iya da su ba, domin Waɗannan mutanen sai Allah."
"Wallahi kuwa lamarin su kam babu wanda zai iya jurewa."
"Haka ne."Ya ce suka ci gaba da hirarsu.
Captain Aliyu
Awa ɗaya da minti goma daidai ya ɗauka zuwa Kaduna. Duk da yau yake son ya dawo, amma
cikin natsuwa ya yi tuƙin har ya isa.
Dama ya sanar wa Anty Amarya. Tun da ta tashi ta fara shirin tarbarsa. Hanifah da ta ga ta aika
kasuwa an yi mata cefane har dasu hanta nama da za ta sanya a cikin dambun, sai ta kalle ta
lokacin da ta shigo ɗakinta tana zaune tana gyara tsaki.
"Anty Amarya, na fara zargin kamar mutumin ki zai zo?" Ta yi mata tambayar cikin tsananin
murna.
"A'a Babanku ne yace na yi masa dambu." Ta faɗi hakan don bata dan su san zai zo, su zo
suna masa kwarkwasa ya yi musu rashin mutunci.
"Gaskiya Anty ban yarda ba, saboda wallahi in ya Captain ne kawai zai zo kike irin wannan
dambun. Don Allah ki gaya mini wallahi ina son Ya Captain. Ta ƙarashe maganar cikin hawaye
tare da kama hannunta.
Tausayi sosai yarinyar ta ba ta, domin da akwai abin da za ta iya yi don ya aure ta, da tuni ta yi
hakan. Ta sani sosai take son shi. Ba wai don ɗiyar mijinta bane, amma duk cikin 'yan matan tafi
ƙaunarsa, saboda ta sha yi mata kuka kan ta sanya Captain Aliyu ya so ta, amma ta kasa
fahimtar Aliyu ba irin mazan da za'a yi masa cushen mace, ko kuma a bashi shawarar ya
aureta. Yana da ra'ayinsa kuma duk kusancin da mutum yake da shi, sam ba ya ɗaukar
shawararsa. Har yau da suke ganin kamar asiri ta yi masa yadda yake kula da ita ya shaƙu da
ita, amma ba ta da hurimin da za ta iya ba shi shawara ya ji. Abin da Captain ya so shi yake yi.
Ko zaɓin da ya bata na matar da yake so, ai sai daya jero mata abubuwan da yake so.
"Hanifah, Please ki cire Aliyu a ranki yana da kalar zaɓin matar da yake so. Kina da kyau da ilmi
za ki samu namiji na gari. Don Allah ki cire wa ranki son maso wani. Aliyu ba zai aure ki b.."
"Don Allah Anty kar ki mini mugun baki. Ba zan iya cire ƙaunarsa ba. Anty na yi kuka na yi
addu'a da sadaka, amma har yau ƙaunarsa ƙaruwa take a cikin zuciyata." Ta ƙarashe maganar
cikin muryar kuka.
Sosai ta ba ta tausayi domin ta san tana son shi. Da ace akwai abin da za ta iya yi, za ta
taimaka mata don ya aure ta, kuma shi kansa ya dace mata. Sam ba ta da makusa she is fine
and looking dashing, amma Captain murɗaɗɗen mutum ne kuma ba a yi masa dole."
Ganin yadda ta ke kuka sai ta koma hannunta ta ce,"Ki bar kuka shi ne zai zo, zan yi ƙoƙarin yi
masa magana, amma don Allah Hanifah ki rage son shi kar ki yi abin da zai cisga ki."
Wani ihun tsalle ta yi ta rungumeta."Na gode Anty, bari na je na shirya idanuna dakunnuwa cike
suke da ɗokin jin muryarsa da ganinsa." Ba tare da da jira abin da za ta ce ba, ta ruga da gudu
don ta yi wanka.
Anty girgiza kanta ta yi, cikin haushinta ta ci gaba da gyara tsakin.
Kamar yadda Hanifah ta zargi zuwansa haka sauran 'yan matan. A tunaninsu Anty Amarya ta
ɓoye musu, don Hanifah ta yi kwalliyar da za ta sace zuciyarsa. Tun ba yau ba su da iyayensu
suke zargin tana son haɗa su, saboda ita 'yar mijinta ne.
A dalilin wannan tunanin ya ƙara mata tsana a cikin gidan, amma sam bata damu ba tun da
suna zaman lafiya da kishiyarta, sannan ƴaƴanta suna yi mata biyayya, domin biyayya da
Hanifah take yi mata tamkar ita haife ta.
Tana wanke tsakin, ta ji sallamarsa shi da Yaya Sama'ila da yake ta tsokanar sa.
"Soja mazan fama." Dariya ya yi yana shafa kansa.
A tare suka shigo tsakar gidar, kusan duk mutanen gidan suna waje don shan iska.
Jin sallamarsa gabakiɗaya gidan ya ruɗe da murnarsa. 'Yan matan da suka ci kwalliya suka
ƙyafe suna jiran zuwansa, zarginsu ya tabbata. Wani irin tsanar Anty Amarya ya kama su.
Mufida da uwarta yadda take jin sonsa, in har ya zaɓi Hanifa ko da Malamai sai ta raba shi da
ita, domin in har Captain bai aure ta ba, yi babu wacce za ta aure shi a cikin 'yan matan gidan.
Anty Amarya da take tsaye, da gayyen zogale a hannunta za ta tsinke. Sosai ta yi murnar
zuwansa.
"Soja marmari daga soja mazan fama." Anty ta yi masa kirarin da ya faɗaɗa murmushinsa.
"Anty Amarya na same ku lafiya?"
"Lafiya lau Captain Aliyu, ya hanya da su Hajiya Mommy K.d da auta?"
"Duk suna lafiya suna gaishe ku." Ya ƙarashe maganar, tare da shiga cikin gidan don ya gaida
iyayensa maza.
Ɗakin Baba Audi ya shiga, mahaifin su Mufida domin shi ne kawai take gida bai fita kasuwa ba,
saboda janta da yake yi.
Bayan sun gaida shi, sannan ya zauna a gefensa yana masa ya jiki.
"Jiki da sauki soja. Na ɗauka za ka zo bikin, amma Ya Abubakar ya ce kana Yukrain?"
"Eh wallahi ai mun dawo duka bai wuce wata ɗaya ba."
"Da kyau, Allah ya yi albarka ya kuma tsare ku ya ba da sa'a. Kuna ƙoƙari sosai domin kune
kuke tsaron rayukanmu da kuɗaɗen mu."
"Haka ne Baba Audu. Bari na shiga gurin Anty Amarya, na bar ka ka huta."
"To shikenan kafin ka tafi za ka je ƙwarbai ka gaida Goggonka Mariya ita ma ba ta ji daɗi ba,
domin har sai da aka ƙara mata jini. Mahaifinka ya zo shi ma.Wataƙila ya gaya maka ciwon?"
"A'a ya manta ne duk da ban jima da zuwa ba na taho nan."
"To ya kamata ka duba ta, ta yi jinya sosai."
"Zan je Allah ya ƙara sauki."
"Amin, Allah ya yi maka albarka ya ba ka mata ta gari."
"Amin," Ya ce sannan ya miƙe zai fita.
Gyaran murya ya yi, jin haka ya dakata ya tsaya don ya san magana zai yi masa.
"Aure Aliyu sai yaushe? Ya kamata kayi aure, musamman aikin ka kana hurɗa da sojoji bata
gari. Kai kanka Allah ne ya tsare ka, saboda shigarka soja bai sanya ka ɓata tarbiyar daka
samu ba."
Jim ya yi sai ya ce,"Zan yi har yanzu ina dubawa ne. Matan ne dole dai mutum ya duba wacce
za ta tarbiyartar da yaransa."
"Kuma haka ne dole a tsaya ka zaɓi mace ta gari, domin tarbiyyar zuriyar ka, musamman a
wannan zamanin da muke ciki na tafiyar biri a yashi, amma kuma soja tun da har ka gaza samu
a waje, muna da yaran mata kyawawa kuma sun sauke Alqur'ani da hadda. Ka dai san tarbiyar
da suka tashi da shi. Duk yarinya da za ka samu a bayansu take. In har ba Zariya ka zo ka
nema ba, sanin kanka ne yaranmu muna ƙoƙarin ba su ikon da hadda." Bance matan Zariya
sun fi ilmi ba, amma kun san akwai ruwan shi boko da Muhammadiya lol
"Haka ne zan yi tunani."