Showing 3001 words to 6000 words out of 90573 words

Chapter 2 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8063

ba zan saɓa muku a garin nan, in har
kuka ƙara shiga sabgar wani sai na sanya an ko..."

Maganar ta katse sakamakon kukan da ya ji ta saka."Saboda zalunci sai ka yi mini barazana da
barin ƙauye da aka haifi iyayena da kakannina? Shikenan ina gani a doki jikata kuma a hana ni
na yi magana? Wa take da shi a duniyar nan da ya wuce ni." Kuka take sosai tana share
majina.
Ganin haka ta saka kukan ita ma." Ki yi shiru ki daina kuka kakata. Kin san hawayenki kawai
yake sanya jikinsa ya yi sanyi. Ki yi haƙuri tun kafin hawayenki, ya tunzura ni na cinna ma gidan
nan wuta."

Zare idanu su suka yi cikin mamaki, jin abin da ta ce, wanda sun san tsaf za ta iya aikata wa.

"Dole na yi kuka Jimmalo, kina gani ni da ƙauye mu ana mini barazana. To wallahi ƙauye nan
sai dai ina mutu akai kashewa bayan gari, don ko na mutu ban aminta akai gawata wani guri
ba."

"Ki share hawayenki ko an kaiki, sai na je ƙabarin na ƙwaƙwulo na cika miki wasiyar ki,
ballantana ba za ki mutu ba kakata."

Kuka suke yi sosai kamar su aka cuta. Mutanen cikin zauren sun kasa cewa komai sai kallon su
suke yi. Saboda takaici sun kasa magana.

Ganin sun yi shiru, kamar yadda suka saba, sai suka miƙe suka fice daga zauren

Bayan fitarsu Malam Sule ya kalli maigari da ya kasa cewa komai."Yanzu haka za mu bar su
suna taka kowa yadda suke so, kuma babu wanda ya isa ya tsawatar sai su rinƙa kukan
munafunci kamar su aka cuta?"

"To ya zan yi? Kawai na ba da umurnin duk wanda suka cuta in zai iya ya rama, in kuma ba zai
iya ba, sai a natsu da Allah."



Zariya birnin Shehu garin ilmi.

Babban gidane a cikin unguwar Juma, wanda daga gani ka ga ginin da, domin irin ginin nan ne,
mai ɗauke da ɗakuna sosai har da gidan sama. Saboda wadata da wasu daga cikin waɗanda
suka taso a cikin gidan, sai aka yi gyare-gyare aka ɗan sauya gidan har da tayas da kuma filista
a ka yi mishi, sannan kowa ya killace sashinsa, ya kewaye da kwano.
Tsakar gidan ya sha siminti mai kyau sosai. Kasancewar gidan ɗauke yake da matan yayyi da
kanni har ma da kawunnai, sai aka samu yawaitar 'ya'ya a cikinsu, domin akwai 'yan mata
kyawawa da kuma samarin maza.

Hanifah ce take sashin Anty Mariya, amaryar babansu tana kwalliya bayan ta fito daga wanka.
Hindatu ce ta yi sallama ta shigo da anko da ta karɓo daga gurin ɗinki.

Da sallama ta shigo cikin ɗakin bayan ta gaishe da Anty Mariya ta wuce ƙuryar ɗakinta. Turus ta
yi ganin Hanifah sai a lokacin take shafa hoda.

"Wai ni saboda Allah wane irin kwalliya kike yi? Tare muka fito wanka har na yi kwalliya na tafi
gidan A'isha Tela na karɓo kaya, amma har yanzu kina nan kina shafa hoda. Hanifah ko fuskarki
kike son canzawa sai haka."

Murmushi ta yi, tare da ɗaukar kwalli ta bayan ta ije soson hodan.

"Wai ba ki da labarin Ya Captain zai zo ɗaurin auren nan ba, domin har sun kamo hanya. Na ji
Baba Ɗanlami suna waya da Daddyn K.d, ya ce masa suna hanya, don haka yanzu na san sun
kusa."

"Eh zai zo ɗaurin aure sai kuma aka yi me?"

Murmushi ta yi tare da kashe nata ido ta ci gaba da gyara kwallin da ta saka ta ce,"Shi ka ke yi
wa wanna kwalliyar."

Wani uwar tsaki ta saki ta ce,"Amma iska na wahalar da mai kaya ƙara! Ke har yanzu Hanifah
ba za ki cire Ya Captain a ranki ba? Wallahi tun ranar da ya wanka mini mari na yi zuciya na ce
ko shi ne autan maza na haƙura da shi. Mutum sai wulaƙanci da girman kai sai kace shi kaɗai
ne soja kyakyawa mai kuɗi? Ni fa na haƙura da shi, domin na san ko mutuwa zan yi ba zai aure
ni ba."

"Saboda wulaƙancin da ya yi miki sai ki haƙura? Wallahi ina nan kan bakana, sai abin da ya
turewa buzu naɗi. Idan yana taƙama da kyau ai ni ma ina da shi, sannnan ilmi shekarar ƙarshe
na ke a digiri."

"Ki daina wahalar da kanki kawai ki haƙura da shi, saboda Ya Captain ƙila balarabiya zai aura.
Yadda yake ji da kansa, ba na tunanin zai iya auren bakar fata."

"Wannan faɗan ki ne, amma ni ina jin zai aure ni."

Wata 'yar iskan dariya ta saki mai haɗe da shewa."Ashe kuwa za ki mutu ba ki yi aure ba."

Kafin ta amsa kyawawan 'yan mata su huɗu, kusan kansu ɗaya suka yi sallama suka shigo.

Kallon su ta yi ta ce,"Kuma duk kwalliyar kuka yi wa Ya Captain?"

"Ke dai ba kin sare da wuri ba, amma mu kam muna nan kam bakanmu. In sha Allahu sai ya
auri wata a cikinmu. Ina fatan nine."

"Ku zauna kuna yaudarar kanku za ku mutu ba ku yi aure ba."

Anty Mariya ce ta shigo ciki tana jin hirar da suke yi. Murmushi ta yi saboda ta san duk a cikinsu
babu wacce zai so. Ta san kalar macen da yake so, duk dacewar shi ba haka yake ba. Tasan
zaɓinsa da rayuwar da yake so. Zata iya cewa yana gaya mata sirrinsa wanda iyeyensa ba su
sani ba, domin ta san Aliyu da sirrin da yake ɓoyewa a rayuwarsa wanda ba ta fatan su sani,
domin sanin zai iya kawo wargajewar farincikin rayuwarsu da kuma yardar da suka yi masa.
Aliyu fuska biyu ne yana da wani hali, wanda take tunanin daga ita sai shi suka sani. Har yau
tana fatan Ubangiji ya ci gaba da ɓiyo sirrin har ranar da zai daina. Ihu suke yi bayan hari domin
duk cikinsu babu wacce take da criteria, da yake son wacce zai aura take da shi. Yana da wani
zaɓi da buri ga matarsa, duk da cewar shi ba haka yake ba.

Zama ta yi tana kallon su, da suke ta hayaniya suna zuzuta kyawunsa kowacce tana fatan ace
ita zai so.

"Ni wallahi na ƙasa su zo na ga shi, saboda ya daɗe bai zo family ba. Ko rasuwar da aka yi na
Kaka Naninna. Daga Hajiya sai Mommy da Daddy suka zo."

"Ai lokacin baya ƙasar fa." Cewar Hanifah da ta gama kwalliya tana ɗaura ɗankwali.

"Yanzu ma baya ƙasar. Yana Yukrain. Har da shi aka zaɓa a cikin waɗanda za su kai wa Ƙasar
Ukraine taimako."

Jikinsu ne ya yi sanyi, kamar za su yi kuka jin abin da ta ce.

"Kai innalillahi! Wallahi har da bashi na ci na sayi kaya don kawai na burge shi." Ummita tace
tana kwance ɗaurin ɗankwalinta, da ta bata kusan rabin awa tana ɗaurawa.

"Aiko dai dai ku yi haƙuri domin zai yi wata biyu ko fiye."

Kamar za su yi kuka, haka suke kallonta jin abin da ta ce.

Murmushi ta yi musu ta miƙe ta fita ganin ya kira ta a waya. Tamkar ƙawarsa ya ɗauke ta,
saboda sai ya gaya mata abu, ba tare da ya sanar wa abokinsa.

Masoya, wannan labarin da wani irin salo na musamman ya zo. Kar ku sare ku bibiyi labarin
tare da yi mini xafafen comments domin akwai cakwakiyar gaske da ruɗani. Kun dai san
comments na ku yake karfafa mini gwiya. Ku yi following channel, arewabook, da kuma
Whatsapp ɗina.
FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242


Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiwasin abin da zai faru a gobenmu. Duk da
cewar akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, waɗanda Ubangiji kawai
ya sansu, sai mu da mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya
ɓoye sirrin da ya sanya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sirrin ya canza linzamin
ƙaddarar rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma
da maɗaci guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya?
To duk ya faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana
sani da alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da
ban dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg

*ƘIYYAYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*



Don karanta Ƙiyayyar Jini ku bi link ɗinnan, sannan karku manta ku yi following ɗina
arewabook
https://www.arewabooks.com/chapter?id=686289d4e9cb75389b9d68c8. Check it out!



Ga link na channel ɗina shi ma ku yi joinning don samun labarin tun daga farko.

Follow the channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P




MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423


PAGE 2

Jin Captain Aliyu ba zai zo bikin ba, gabakiɗaya jikinsu ya yi sanyi, domin kowaccen su ta ci

burin ya zo ya ga kwalliyarta.

Da misalin sha biyu Hajiya, Daddyn K.d da Mommyn K.d har da Nufaisah, Umma da auta Farid
suka iso cikin. Zariya.

Ƙofar gidan cike yake da mutane sosai a ciki da waje. Hajiya da ta fito daga cikin motar tana
miƙa. Da sauri mutanen da suke zaune suka taho gurinta don kwasar gaisuwa.

Farar mace dattijuwa, wacce daga ganinta ka ga naira ya zauna, domin duk tsufan da ta yi,
hakan bai ɓoye kyau da take da shi ba.

Tana sanye cikin riga da zani na atamfa, kasancewar mace wacce ta yi riƙo da shigarta na
Hausawa.

Ɗaga gilas idanunta ta yi, cikin tsananin so da ƙaunar ɗanta, da kuma iyalansa suka ƙarasa
inda suke.

Cikin mutunci take amsa gaisuwar na su, bayan sun gana gaisawa sannan suka shiga ciki.

Baba Ɗahiru wanda shi zai aurar da yarinyar ya bi ta suna tafiya."Hajiya, mun ga tsaƙo Ubangiji
ya ɗaukaka ke da iyalanki. Sosai kun yi ƙoƙari har da soja, don ko jiya ya kira ni in akwai abin
da ba a gama siye ba, ya turo kuɗi bayan abin alkhairin da ya yi."

"Ai wai Aliyu ai dama ban so ya zo bikin ba, ka san yanayin aikinsa, ni dama ko ba aikin ya
tsare shi ba, gara da bai zo ba. Ya raba hali da wannan shegiyar ɓakar zuciyarsa."

"Soja ne dole ya yi zuciya, kuma baya haka kun manta halin mai sunan da ya gado? Yaya Aliyu
har na haihu yana kai mini duka ina ɓata masa rai." Ya ƙarashe maganar yana dariya.

"Da wannan, amma kuma marigayi mijina ai zuciya bata hana shi aure ba, amma shi kuwa fa?
Inda ya aminta da haɗin da na so na yi da yanzu matar ta haihu."

"Lokacin auren ne bai yi ba, kuma yadda yake da zafin zuciya bana son a yi masa auren dole.
Mu bari ya zaɓi matarsa da kansa, saboda in har muka yi kuskuren masa auren dole mun cuci
yarinyar. Soja ko shi ya ga mace yana so wallahi sai tayi haƙuri."

"Ni fa na tsame hannuna kan lamarin da ya je ya auri kaki. Ai duk abin da yake yi ɗaurin gindin
ubansa ya samu. A lokacin dana ce ayi auren shi da Ameera ya ƙi, idan da ubansa ya yi masa
dole ai zai karɓa."

"Zai yi lokaci ne Allah ya haɗa shi da mata ta gari."

Hajiya shiru ta yi ba ta amsa ba sai ƙuta da ta yi, domin sosai yake ba ta haushi.

Daddyn k.d shiru ya yi yana jin ta bai ce komai ba, domin ba ya son ya tanka ta raba masa abin
faɗe ana taro, amma shi ya san dalilin da ya sanya shi bai aminta da auren ba. Sam ba ya son
abin da zai ɓata zumuncin su. Ya san wane ne ɗansa da kuma in ya kafe ba ya son abu. Sam
ba shi da matsala da rayuwarsa aure lokaci ne, kuma saboda zafin ransa dole ya tsaya ya nemi
matar da za ta iya shanye duk halinsa. Jin daɗin da ɗaya da ba ya aikata abin da wasu sojojin
suke yi. Yana alfahari dashi sosai, tun da ya shiga aikin soja bai taɓa ko shigar banza ba. Har
yau yana alfaharin da ya riƙe alƙawarin da ya ɗaukar masa.

Ciki suka shiga, nan mutane suka taho gurinta cikin murna. Bayan an gaigaisa sannan Mommy
ta shiga ciki ɗakin uwar bikin, Nufaisah kuma da Umma suka shiga cikin 'yan mata.

An yi taro cikin rufin asirin Allah, an kai amarya gidanta. Su Daddy sun dawo Kaduna lafiya.

Ƙauyen Damagaran.
Bayan fitarsu Malam Sule ya kalli maigari da ya kasa cewa komai."Yanzu haka za mu barsu
suna taka kowa yadda suke so, kuma babu wanda ya isa ya tsawatar, sai su rinƙa kukan
munafunci kamar su aka cuta?"

"To ya zan yi? Kawai na ba da umurnin duk wanda suka cuta in zai iya ya rama, in kuma ba zai
iya ba, sai a barsu da Allah."

Washegari da safe, tana zaune bayan ta tashi ta yi sallar safe, sallar da in aka tsareta ba za ta
faɗi abin da ta karanta ba. Shi ma don Kaka Tani ta tsare ta ne, amma inta ga dama dai ta wuni
har kwana ba ta yi sallah ba. Karatun allon ba zuwa take yi ba, duk yadda Kaka Tani ta so ta je
haka ta haƙura ta zuba mata na mujiya, domin da ma ba wani tsaurarawa ta yi mata ba, a
cewar ta tun da ta iya karatun sallah shikenan.

Kwalliya take yi, duk ta ɓata fuskartar sai kallon kanta take yi a magani. Tana son kwalliya sai
kace mairo 'yar kwalliya ta shige ta.

Kaka Tani ta fito daga cikin ɗaki da kofin koko a hannunta. Ki sha ruwan kokon nan, ki yi maza
ki je mana tallah, yau kin san akwai kasuwa zan je na tsinto miki kayan ɗaki.

"Wai Kaka Tani, ba za ki daina wahalar da kanki gurin siyen kayan ɗakin, da kin kwana da sanin
ba aure zan yi ba?"

"Subuhanallahi! Ki daina ma kanki fatan hakan. In sh Allahu, sai na ga aurenki kafin na mutu."

"Ashe kuwa za ki yi gadin duniya, saboda babu ɗan iskan da zan iya aure a duniya yana sanya
ni aiki."

"Aure shi ne daraja da cikar ƙimar 'ya mace. In har na mutu ba ki aure ba, wa kike son ya kula

da ke in kika tsufa?"

"Ai ni ba yarinya ba ce zan iya kula da kaina, amma ni da aure mun yi hannun riga."

"Anya ba aljanu suka kama ki ba? Ace kin girma ba kyau son aure. Babu fa sa'ar ki a ƙauye nan
Jimmalo?"

"Babu aljanin da ya kamata ni. Auren ne ba zan yi ba."

Ta buɗe baki za ta yi magana, Ladidi ta kwaɗa sallama da sanda a hannunta tana wasa da ita
ta shigo.

"Yauwa Ladidi, zo ki riƙe mini tirena na gama kwalliyar nan, kin san yau in mun sai da kaya a
kwai rawa a dandali. Sannan ina son na koya wa Karime karatu."

"Karime ta ba ki haƙuri fa don Allah ki ƙyale ta."

"Malama ban son gulma! Ba ke kika gaya mini tana ta yamaɗiɗi dani wai ina da ƙwarkwata ba?"

"Eh, amma ta ba ki haƙuri kuma ta ce Salame ta gaya mata."

"Ina ruwan ko uwar Salame ce, wallahi sai na koya mata hankali." Ta ce tare da gyara
ɗammararta ta fice daga gidan.

"Ba za ki sha ruwan kokon ba?"

"Sai na dawo ki sayi rogo ki haɗa mini."

"To shikenan, dawo lafiya." Ta ce tare da juya ta shiga cikin ɗakinta.

Tana fita ta cire gyalenta ta sha ɗanmara. Ganin haka hankalin Ladidi ya tashi ta kalleta."Don
Allah Jimmalo, ki bar maganar nan ki bari ayi rawar nan lafiya a tashi lafiya."

"Kin ga Ladidi ki fita daga idanuna, in har ke ma ba munafuka bace, ki barni na yi maganin
munafukai." Ta ƙarashe maganar cikin fusata.

Ganin haka ta kama bakinta ta yi shiru suna tafiya, yayin da zuciyarta ke cike da damuwar abin
da zai faru.

Da suka isa dandalin, tsaya ta yi tana zare idanu tana son ganin inda Karime take. Cikin sama
ta hangeta tana kasa mazaƙwailar da take siyarwa."Yauwa ga munafukar can." Ta furta tare da
yin wani sufa sai ga ta a gabanta. Ba tare da tunani ba ta ciyo kwalar rigarta, daga duƙe har sai
da ta miƙar da ita.

"Ta shi munafukai algunguma, da kike je kina gaya ina da ƙwarkwata kanki ko nawa?" Ta yi
mata tambayar bayan ta cikwikwiye rigarta, ta hanata shaƙan numfashi.

Tsoro da firgici ya kamata jin abin da ta ce, sai ta shiga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login