Showing 72001 words to 75000 words out of 90573 words

Chapter 25 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

Advertisement

11 Sep 2025

8177

tashi makarantar ta yi mugun gajiya da zama, domin ita sam ba ta san a takurata. Sosai
ta ƙosa a tashi duk da zaman cikin gidan ba daɗi yake mata ba, amma ta gwammce ta koma ko
ta huta da gwalan-gwalan, yaren da ake mata tun da ta shigo cikin makarantar.

Ga wani azzabben yunwa da ya ke ƙwakwularta, saboda tun da Kaka Tani ta rasu ba ta samu ta
ci abinci sosai ba. A dalilin hakan sai gabakiÉ—aya hankalinta ba shi a makarantar. Tana takure
har lokacin tashi ya yi. Kallon makarantar ta yi a ranta ta yi mata kallon ƙarshe, domin ta saka
ko sama da ƙasa za ta haɗe ba za ta je makarantar ba.
Da aka tashi direba ya zo É—aukar su. Sosai yaran suke kallonta ganin yadda ta canza ta yi
fasali. Babu wanda ta kalla a cikinsu ballantana ta tanka musu tun da aka tashi. Motar ta shiga
ta kwantar da kanta, don yunwa take ji sosai.

Tun da suka doshi hanyar gidan sai kawai ta fashe da kuka. So take ta fara kuka tun yanzu
yadda za ta tunzura Mommy, don ta fahimci tana da saurin fushi.

Direba ya waiwayo ya kalle ta zai yi magana, sai dai kallon da ta yi masa ya kauda kansa ya ci
gaba da tuƙi, domin shi ma a zuciya yake ba shi da haƙuri kamar zawayi.

Su Umma suna jin kukanta, babu wanda ya tanka don sun san ba za ta kula su ba.

Ganin an buɗe musu get, bayan ya yi hon sai ta ɓare baki iya ƙarfinta. Mommy dake zaune da
Anty Amarya a falo suna hira jin kukan gabanta ya buga.

Dama tun da karfe biyu da rabi ya yi, ta É—an canza tana fargabar dawowarta.

"Ya Salam ta dawo! Kina jin ta da kuka za ta shigo cikin gidan nan kamar jariri ya. Ni kam Hajiya
ta haÉ—a ni da bala'i." Ta furta tana jin kukan har cikin ranta.

Anty Amarya, Mufida da Hanifa sai suka zuba ma kofar idanu suna son suga Jimmalo, da ta
zamar wa mutanen gidan ƙaya a maƙoshi, domin duk bayan minti sai Mommy ta kalli agogo ta
sako hirarta.

Jimmalo sai ta ƙara wage baki."Na rantse ko tsire ni za a yi, ba zan ƙara zuwa makarantar nan
ba. Shegu mugayen masu zuciyar arna." Abin da ta furta kenan lokacin da ta shigo falon.

Umma tsaki ta yi, burinta kawai ta shige É—aki ta je ta kwanta, kuma yau ta rantse sai dai a kaita
wani É—akin ta kwana.

Idanu suka zuba mata har ta shigo tana kukan. Anty Amarya mamaki sosai ta yi ganinta, domin
ta É—auka babba ce sosai, musamman ganin yadda Aliyu yake data jijiyar wuya in yana
maganarta.

"A mayar da ni Damagaran, saboda na gane ƙarya kike mini wayo kika yi mini aka kai ni
makaranta. Mugayen sun cire mini kayan da na gada gurin kakata, kuma sun yi mini wanka." Ta
furta cikin baƙincikin hakan tare da zubowar hawaye a fuskarta.

"Masha Allah! Ubangiji ya yi musu albarka, domin sun biya ni. Jimmalo kin ga yadda kin yi fasali
kuwa? Sam ba kya wannan warin, yau za ki yi kwanan daÉ—i?" Mommy ta yi mata tambayar tana
kallon ta.

"Ni kawai a kaini ƙauye na fi son rayuwar ƙauye, domin ba zan yi karatun bokon ba." Ta furta
tare da zama gefen kujera.

"Yanzu ina littafanki?" Mommy ta yi mata tambayar da son kauda zancen.

"A can na bar musu saboda ba shi da amfani a gurina. Na rantse ko na Muhammadiya ce ba
zan yi ba, ballnatana ta arna."

"Za ki yi ilmi shi ne gishiri zaman duniya, domin shi ne yake bambanta matacce da rayayye,
kuma wanda ba shi da shi. Misalin jaki ne aka É—aura masa dakon littafai."

Jin wata murya ta yi mata daban, sai ta ji muryar ta yi mata wani iri. Da sauri ta É—ago idanunta
tana kallon Anty Amarya da take kallonta cike da tausayawa. Ace kamar wannan ta rayu babu
sallah babu tsafta, duk da cewar ta yi wanka, amma da ka ganta kasan tana rayuwa ne cikin
ƙazanta da rashin kula. Dole Aliyu ya tsane ta, domin ko ita wani lokacin mamakin tsaftar shi ta
ke yi.

"Ke kuma ina...." Ta buÉ—e baki za ta yi mata rashin kunya, amma kuma idanunta da ta É—ora bisa
nata sai ta kasa. Wani irin ƙwarjini ta yi mata, har sai da ta cire idanunta sannan ta ƙara
mayarwa. Bayan Kaka Tani za ta iya cewa babu wanda take ƙauna a cikin duniyar, domin kowa
keta masa rashin mutunci take yi, amma yau ta haÉ—u da wacce ta ji ba za ta iya mata rashin
kunya ba. Wacce za ta iya mayar da ita 'yar'uwa. Wacce lokaci guda soyayyar jini ta haÉ—a su ta
yi mata ƙwarjini sosai. Har take jin za ta iya ba ta wani gurbi a cikin zuciyarta. Idan da ita za ta yi
rayuwa, tabbas za ta haƙura da kuka da ɓurari da take yi don a mayar da ita Damagaran. Sosai
shaƙuwar jini ya shiga tsakaninsu.

Addu'a ta fara yi Allah ya sa a gidan take rayuwa. Duk da cewar Anty Amarya ba wani girma ta
ke da shi ba, domin ko da ace tana haihuwa bai wuce babbar yaronta a aji na biyu a sakandiri
ba.

To fa Jimmmalo ki rasa wacce za ki ji ta yi miki sai yar gidan Aliyu da yake jin babu kamarta?
Hmmmmh lailai za ki tashi kan Aliyu. Comments kun san fa shi yake karawa marubuci karfin yin
rubutu.

Jimmalo za ta haƙura ta ci gaba da zuwa makaranta? Aliyu zai zauna a gidan sannan zai samu
damar auren irin macen da aka zaɓa masa? Ku dai biyo ni cikin littafin.Na gode da comments
da kuke yi Ah ya barmu tare.

Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruÉ—ani. RuÉ—anin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe

alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.


*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*


MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423



PAGE 21



*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso
kusa kar ayi* *babu ke*

*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*

*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*

*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*

*Iya adadin da kuke so muna turawa*

*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da
hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da
kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*

*Arabian oud*

*Lamsa oud*

*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*

*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*

*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*

*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*

*Adress ringi road, na dorayi, kano*

*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*

*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*


👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


*08130902505*


Addu'a ta fara yi Allah ya sa a gidan take rayuwa. Duk da cewar Anty Amarya ba wani girma ta
ke da shi ba, domin ko da ace tana haihuwa bai wuce babbar yaronta a aji na biyu a sakandiri
ba.

A karo na biyu, ta ɗago idanunta ta ɗora a kanta tana kallonta cikin ƙauna irin ta jini. Mommy sai
tsananin mamaki ya kamata, ganin yadda jikinta ya yi sanyi take kallon Anty.

"Ni fa makarantar ne bana son na yi, ko da zan zauna a birni, amma a cire ni a makaranta." Ta
furta hakan tana ƙoƙarin zama.

Mommy saboda tsananin mamakin ganin yadda ta yi, sai ta kalli Jimmalo da idanunta yake kan
Anty Amarya.

Murmushi Anty Amarya ta yi ta zama a gefenta, tana kallonta domin ita sam ba ta ga taurin kan
da ake faÉ—in tana da shi ba.

"Yanzu kin dawo, ma za ki je ki cire kayan makaranta ki canza sai ki yi sallah ki fito ki ci abinci,
domin an gaya mini ba kya sallah, na san ba ki yi a makaranta."

"Zan yi in zan kwanta, anan gidan kike?" Ta yi mata tambayar da ya cika su da mamaki.

"A'a amma ni 'yar uwar gidan nan ne, ina zama a Zariya."

Saboda ba ta san Zariya ba, sai ta taɓa bakinta lokaci guda fuskarta ta canza, domin ta so a ce
a gidan nan take.

Miƙewa ta yi, za ta nufi cikin ɗaki don ta cire kayan jikinta, saboda sam ba ta ƙaunar ganin
kayan a jikinta.

Mamaki sosai ya ƙara kama Mommy."Wonder shall never ends. Jimmalo ce ta yi magana da ke
ta fahimta? Laillai na yi mamaki ƙwarai, ke kuwa wane irin farinjini kike da shi? Domin tun da ta
zo gidan nan take shuka rashin kunya, hatta Daddy ba ta ɗaga masa ƙafa ba.

Dariya ta yi ta ce,"Ikon Allah kenan! A cikin duniya ba ka rasa wanda za ka ji maganarsa. Ba
kya ganin wani lokaci mukan yi tarayyar da mutanen da suke gaya mana magana mu ji kuma
mu ɗauka, ba tare da mun bi na iyayenmu ba. Wasu yaran ko sanar da iyayensu ba sa yi. Ƙawa
sai ta canza rayuwar danka, ta kuma ba shi muguwar shawara ya É—auka."
"Na yarda da hakan domin ga zahiri nan. Ni kam zuwan ku babu abin da zan iya cewa, sai dai
na yi miki godiya."

"Ba komai ai yaro na kowa ne. Har yau ina jin damuwar rashin haihuwa da bana yi, domin babu
abin da ya kai haihuwa farinciki da yaye damuwa." Ta ƙarashe maganar hawaye yana zuba a
ƙuncinta.

Ganin haka sai hankalinta ya tashi, ta ƙarasa gurinta tare da kama hannunta."Ki yi haƙuri Allah
yana tare da ke, kuma in ya so sai ya ba ki a lokacin da kika cire tsammani. Na sam cewa babu
bin da yafi haihuwa daÉ—i, amma kar ki manta Ubangiji ya ce yana jin kunyar macen da bai ba ta
haihuwa ba, sannan akwai bin da ya tanadar musu ranar gobe kiyama wanda ya barwa kansa
sani."

Ta numfasa sannan ta É—ora ganin har yanzu da damuwar a fuskarta. "Akwai haihuwar da Allah
zai ba ki, sa kin gwammace da ma ba ki haihu ba. Yaran da ake haifa suna lalacewa suna

zamar wa duniya annoba. Kin ga da irin waÉ—annan yaran, gara mutum ya mutu ba tare da ya
haife su ba. Sannan akwai yaran da su za su kai iyayensu wuta."

"Haka ne Ubangiji ya bani yaro domin da ciwo, don na samu kishiyar da ba ta mini ido kan
yaranta, amma da yanzu xuciyata ta gaza da girman ƙaddarata, sannan ina son na haihu nima
na ga sayin idaniyata, akwai ciwon da mutum zai yi dole sai jininka zai yi jinyarka."

Haka ne za ki samu haihuwa ki ci gaba da addu'a lokaci ne bai yi ba." Mommy ta ce mata cikin
tausaya.

"Ina fatan lokacin ya yi. Har ga Allah ganin Jimmalo ta shiga raina sosai. Tausayi sosai ta ba ni
domin duk abin da take yi ba laifinta bane. Shi yaro yana tasowa ne da irin tarbiyyar da ya ginu
a kansa. Duk wannan sakarcin da take yi laifin kakarta ce da so ya rufe mata ido, amma tun da
ta rasu, sai mu yi mata addu'a, sannan kuma mu yi ƙoƙarin gyara kuskure da ta yi."
"Haka ne Allah ya bamu ikon gyara, tun da kin zo don Allah ki shiga ciki na iban mata kaya
sosai a cikin na Umma, kafin na samu na shiga da ita kasuwa a siya mata duk abin da take
buƙata."

"Ba matsala zan ji da ita." Ta ce tare da miƙewa ta shiga cikin ɗakin.

Ajiyar zuciya mai ƙarfi Mommy ta yi, sai ta ji zuwanta kamar an sauke mata dutsen da aka ɗora
mata a kai.

Jimmalo tana tafiya, xuciyarta cunkushe da takaicin jin ba a gidan take ba. Har ta isa zuwa cikin
ɗakinta jefar da hijabin da ɗan-kwallinta suka ɗora mata a ƙasa. Takalminta kuma ta yi jifa da
shi a saman gadon. Ta miƙe ta shiga cikin bayi, saboda wani irin fitsari da ya matse ta. Da ta
shiga bayin ta yi fitsari. Har ta murɗa ƙofar za ta fice, amma sai ta dawo sakamakon ganin kanta
a madubi. Da sauri ta janye gashinta ta buÉ—e bakinta. Tabbas ita kanta ta ga canjin da ta yi,
domin za ta iya cewa ba taɓa ganin ta yi kyau irin haka ba.

"Ashe ina da gashin haka?" Ta furta tana fincike lobalin da suka É—auke mata da shi, sai dai duk
kyan da ta yi ba ta jin za ta iya cigaba da tsafta, domin ita takurar ce ba ta so a rayuwarta.

Daidai lokacin da ta fito sai Anty ta shigo. Tsintar kanta ta yi da sakin murmushin da bai wuce
iya leɓe ba, a maimakon ɗauke kanta da ta so ta yi.

Ba ta ce mata komai ba, ta ƙarasa kan gadon ta zauna, wanda ganin hakan Anty ta zauna a
gefenta.

"Yauwa ga kaya Mommy ta ce ki canza."

"Ni bana so na sanya wasu kaya in ba na Kakata ba." Ta furta tare da janyo kayan ta É—auki wata

riga da sani da take zama a tsakar gida.

Da mamaki ta kalle ta, ganin yadda kayan sun yi tsufan da ko goge-goge ba za ta iya yi da su
ba."

"Jimmalo, waÉ—annan kayan za ki saka? Kin san kuwa a gidan da kike rayuwa?" Ta yi mata
maganar cikin zallar mamaki.

"Ni ina ruwana su na ke son na saka." Ta ce tana ƙoƙarin ɗaukar zani.

"Ƙona su za a yi, daga yau ba za ki ƙara sanya su ba." Ta ce tare da fisge kaya ta miƙa mata
doguwar riga mai kyau kalar pink.

Kallon kayan ta yi, cikin damuwa kuma ta kasa musu da ita. Ganin haka ya sanya ta miƙe, tare
da ƙarasa gurinta kamar za ta taimaka mata ta cire kayan.

"Wai mene sunan ki? Saboda Jimmalo sunan rana ne?"

"Jimmalo Jikar Tani na fi son a rinƙa ce mini, bana son Sahiya da wannan mai kama da arnan
ya ce dole shi za a sanya mini."

Dariya ta yi jin wautarta. "Ok, sunan ki Safeeya kenan? Wow kina da sun mai daÉ—i, kuma
ƙanwata sunan ku ɗaya da ita, amma ana kiranta da Surfy."

"Hmmmmh, ita ma kun mayar mata da sunan arna." Ta ce lokacin da ta cire rigar makarantar, ta
sanya doguwar rigar tana yi wa kanta wani irin kallo.

"A'a suna ne da zamani ya zo da shi." Ta ce mata lokacin da take duba chatting É—in Aliyu, da
yake gaya mata yana hanya, don bai samu wanda ya je nema ba.

"Wow, kin ga yadda kika yi kyau?" Ta yi mata maganar tana gyara zaman rigarta.

"Ban gani ba saboda na tsani shigar birni ba ta mini kyau."

"Daga yau ita zaki rinƙa yi, don kin zama 'yan birni, ga shi har kin shiga makaranta. Surfy zan
rinƙa kiranki da shi." Ta ce mata lokacin da ta miƙe ta kwashi kayan.

Ganin ba ta tanka mata ba sai ta kwashi kayan ta ce,"Ƙona su za a yi saboda ba su da amfani
a gurinki."

Kama kayan ta yi ta ce,"Don Allah kar ki ƙona mini kaya, saboda su kawai na ke gani na tuna
da Kakata." Yadda ta yi maganar sai ta ba ta tausayi.

"Kin yi alƙawarin ba za ki ƙara sawa ba?"

"Eh na yi." Ta tsinci kanta da faÉ—in haka cikin rawar murya.

"Ok, tom shikenan ki fito ki ci abinci."

"To," Ta furta mata daidai lokacin da za ta fita, domin har ta kama ƙofa sai ta tsinci muryarta
tana faÉ—in,"Don Allah ki zauna a gidan nan, ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login