Showing 69001 words to 72000 words out of 90573 words

Chapter 24 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8078

tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0


*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*


MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423



PAGE 20



*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso
kusa kar ayi* *babu ke*

*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*

*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*

*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*

*Iya adadin da kuke so muna turawa*

*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da
hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da
kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*

*Arabian oud*

*Lamsa oud*

*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*

*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*

*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*

*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*

*Adress ringi road, na dorayi, kano*

*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*

*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*


👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾


*08130902505*

Ganin haka sai ta ci gaba da karatun, burinta ta gama darasin lissafin ta fita. Jimmalo tana
zaune tana ta kallonta. Ko da aka kawo mata takaddunta da pencil kallonsu kawai ta yi ba tare
da ta ɗauke su ba, domin a ganinta basu da amfani don riƙe pensil ma ta iya ba ballantana
rubutu.

Wunin ranar ba za ta ce ta koyi komai ba, domin hankalin ta ba shi kan ta koyan, musamman
turanci da suke yi wanda yafi ɓata mata rai da tsanar bokon sosai.

Ko da aka fita break, ba ta fita ba saboda kayan da ta sanya da rayuwar da ta tsinci kanta sai ta
ji duk ta takura.

Umma tana son ta kawo mata abin break, amma ƙawayenta sun zura mata idanu so suke su
gane da gaske 'yar uwarta ne.

Ganin haka sai ta faki idanunsu ta kawai Auta ya kai mata.

A lokacin da ya kawo mata kular da sauri ta karɓa domin yunwa take ji sosai. Kallonta yaran
suke yi ganin yadda ta kai hannu za ta fi abinci ba tare da ta wanke hannu ba.

"Anty Safeeya, Anty ta ce ba a cin abinci ba tare da an wanke hannu ba, sannan ga cokali ki
sanya ki ci."

Ije kular abincin ta yi tana kallon Nadiya da take tsaye a gefenta.

"Ke! Karya ki xan yi in har kika shiga gonata. A Kauyenmu da maza na ke karawa, don haka
ban ga abin da zan samu a jikinki ba, domin ganin ki na ke kamar yanzu aka haife ki."

Jin abin da ta furta cikin zafi, sai ta matsa da sauri tana zare idanu. Jimmalo ta zabga tsaki ta
ɗauki abincin ta fara ci hannu baka hannu ƙwarya. Kafin ta gama cin abincin duk ta bata
hijabinta.

"Uncle Yahaya, ka ga Safeeya ta ɓata kayanta." Mudassir ɗan ajinsu ya je ya gaya wa Uncle
Yahaya, domin doka ce a makarantar duk wanda ya ci abinci sai an buge shi.

Cikin zafi ya isa gurin, ya yi mata bulalar da ya sanya ta miƙe za ta cakume shi. Da fari razana
ya yi, amma kuma sai ya dake ya tsula mata bulalar iya ƙarfinsa.

Ihu ta saka tana sosa bayanta. "Oya mu je gurin Principal sam ba ki da kunya." Ya furta tare da
kama hannunta yana janta.

Dukan da ya yi mata shi aka ƙara mata. Da fari zagi ta ƙunduma musu, jin hakan Principal ya
sanya sajen ya yi mata dukan tsiya. Duk dauriyarta sai da ta koka ganin yadda ya fasa mata
baya.

Kafin a tashi ta gama tsine musu, kuma ta rantse ba za ta ƙara zuwa makarantar ba.

Aliyu
Da ya koma gida Daddy faÉ—a ya yi mishi sosai."Cewa na yi ka kaita ayi mata rigista na islamiya

da boko."

"Daddy, ba zan iya dawowa da ita a cikin motata ba."

"Ya zama dole ka san yadda za ka yi ka É—auke ta a matsayin yar'uwa."

"Impossible dad, zan koma Abuja." Ya ce tare da miƙewa jin faɗan da yake masa.

Daddy haushi ya ji, ya haura sama Mommy ce ta kalle shi za ta yi magana ya riga ta."Please
mommy don't say anything, zan wuce ki yi mini addu'a."

"Allah ya tsare." Ta furta ganin yana musu da su.

Yadda ta amsa sam bai yi masa daÉ—i ba, amma tafiyar ya fi saboda yana in suna rayuwa a gida
É—aya, watarana zai kashe ta. ÆŠakinsa ya wuce ya É—auki Jakarsa.

Zariya
Anty Amarya riƙe da jakarta mai ɗauke da kayan kwana biyu. Sun yi shiri tsaf ita da Hanifa da
kuma Mufida. Dama sun shirya tafiyar za su yi wa Captain bazata. Tun da ya ce mata zai shigo
Kaduna, sai ta shirya zuwa Kaduna, don ta yi masa kyakkyawar albishirin ta samo masa yarinya
kalar wacce yake so.
Yarinya ce wacce ba za ta wuce shekaru sha bakwai ba. Hafizar Alqur'ani. Ita ta cinye gasar
Alqur'ani na wannan shekara na ƙasa da aka yi.

Dalilin da har ta yi masa hanyarta. Mahaifiyarta ƙawar ƙanwar Mamanta ne da take zama a
Suleja. Labarin yarinyar ta ji suna yi tana sha'awar tana da yaro ta aura masa, kasancewar
maƙota suke.

Jin yadda take sha'awar tarbiyartarta, da kuma yadda ta fasalta yarinyar har ta gaya mata
cewar burin yarinyar ta auri soja, duk da sanin wasu sojojin na su da natsuwa. Nan take ta
yanke shawarar ta yi wa Aliyu maganarta, amma sai ya yi mata alƙawarin zai daina kula matan
banza. Don haka take son su yi magana ta fahimta, kuma ba a cikin gidansu ba, don ka da wani
ya ji abin da take son yi, ya zama silar da mutanen gidan za su ƙara tsanarta, musamman
Hanifa da take ganin kamar kusancinta da Aliyu zai taimaka ta same shi.

Tun da Mufida ta ji za ta je Kaduna, sai hankalinta ya kwanta, ganin ta samu hanyar da za ta yi
maganinta ba tare da wahala ba. Don haka ana gobe ta je aka yi mata lalli da gyaran kai. Ganin
haka Hanifa ta cika da baƙinciki, domin ta san zuwan na ta ba ƙaramin cikas zai kawo mata ba.

Ba ta kira Aliyu ta gaya masa ba sai da suka kusa tasha. A lokacin da ta kira shi har ya shiga
cikin motar da ya sanya jakarsa. Ganin kiran na ta sai ya fasa tuƙa motar ya ɗaga.

Sallama ya yi mata sannan ya ce,"Antyna, na yi shirin biyowa ta Zariya, amma saboda wata
matsala ba zan zo..."

"Kwantar da hankalinka ka zo tasha ka É—auke mu."

Jin abin da ta ce, sai ya cika da mamaki domin ba ta gaya masa za ta zo ba." Anty ina fatan ba
yaran nan bane, suka sanyaki zuwa? Saboda wahalar da kansu suke yi. Gara ki gaya musu
gaskiya su je su samu wadanda za su iya auren su, domin in har ni suke jira za su mutu babu
aure."
Jin abin da ya ce, sai ta yi guntun murmushi tana kallon su. "Kwantar da hankalinka Aliyu. Na zo
maka da kyakyawar albishir da zai sanya ka yi mini kyauta."

Jin abin da ta ce sai ya yi murmushi."Anty, an samu kalar matar da na ke so ne?"

"Daɗina da kai ka cika ƙosawa, ka yi maza ka zo tasha ina jiranka." Ta kashe wayar kafin ya ce
wani abu.

Ganin ta kashe sai ya ije wayar, tare da kunna motar yana fatan Allah ya sa kalar matar da yake
so ne ta samu. Ba tare da ɓata lokaci ba ya tafi zuwa tashar. A lokacin da ya isa suna tsaye
suna jiran shi. Hon ya yi musu sannan suka fara tahowa zuwa gurinsa.

Kamar yadda gaban Hanifa ke dukan tara-tara haka na Mufida. Kowacce xuciyarta cike sonsa
da ƙaunarsa. Burinta ya yi mata tarba na musamman, amma sai dai kamar kullum don ba ta
canza zani ba.

Saboda girmamawa, fitowa ya yi daga motar ya karɓi jakarta. Fuskarsa ɗauke da murmushi ya
ce,"Gaskiya kin yi mini bazata kin san har na shiga mota zan koma Abuja?"

Mamaki sosai ta yi, domin ya ce mata kwana huÉ—u zai yi."Hala kiran gaggawa ka samu daga
gurin aiki?"

"Anty gara kiran aiki da tashin hankalin da na samu a gida."

"Subuhanallahi! Lafiya?"

Yatsina bakinsa ya yi, daidai lokacin da ya sanya jakarta a bayan mota."Za mu yi magana,
saboda in har zan yi maganar yanzu, wataƙila na kasa tarbarki da kyau."

"Komai dai ya yi zafi maganinsa Allah." Ta ce daidai lokacin da ta shiga gidan gaba.

Ba tare da ya ce mata komai ba ya kunna motar. Sai a lokacin suka samu ƙarfin iya gaishe shi a
tare.

ÆŠan waiwayo wa ya yi, ya watsa musu banzan kallo ya ce,"Kuna lafiya?"

Don takaici Mufida ba ta amsa ba, sai Hanifa ce ta amsa gwiyarta a sake. Mufida duk yadda
take jin xuciyarta na tafarfasa saboda ƙaunarsa, hakan bai hana ta watsa masa harara ba,
saboda ya cika ɗan wulaƙanci na ƙarshe.

Hankalinsa a tuƙi yana hira da Anty Amarya har suka iso.

A lokacin da suka iso, Mommy tana zaune xuciyarta cunkushe da damuwa, ganin ya yi fushi ya
tafi. Sosai take son É—an nata da damuwa da rashin sa a kusa da ita, amma kuma ga shi ya
samu hutu Jimmalo ta kore shi. Nan take ta fara ganin rashin adalcin Hajiya da ta jajibo musu
ita.
Tana wanan tunanin ta ji hon ɗin motarsa. Da sauri ta miƙe tare da yaye labulen falon. Ganinsa
sai mamaki sosai ya kamata.

Har ya shigo ya yi parking idanunsa na kan motar, sai kuma ta lura da mutane a cikin motar
kuma mata. Tana tsaye tana kallon su da tunanin su waye, Anty Amarya ta fito daga cikin motar,
sannan su Mufida da Hannifa.

Murmushi ya bayyanaa fuskarta, ganin baƙin da suka yi, domin yadda Anty Amarya take son
É—anta haka ita ma take sonta.

Fuskarta É—auke da farinciki ta fita zuwa harabar gidan. A lokacin Anty Amarya ta fito, sai kuma
Mufida da Hannifa da suke ƙoƙarin fitowa.

"Zuwan bazata amarya? Ai kya sanar da ni, duk da na san cewa ba don ni aka zo ba."

Murmushi ta yi tare da ƙarasawa gabanta. "Da gaskiyarki Mommy ba zuwanki bane, amma
kuma sai na kusa rashin sa'a don ya ce mini har ya shiga mota zai juya."

"Kin ga da sai ki yi zumuncin dole" Ta ce tana kallon su Hanifah da suke gaisheta.

"Lafiya lau kun iso lafiya?"

A tare suka haÉ—a baki gurin,"Lafiya lau."

"Masha Allah mu shiga daga ciki."


Mufida take bin gidan da kallo cikin birgewa, duk da cewar wannan ba zuwan ta na farko kenan
ba, sosai take son ta kasance surukar gidan, saboda ita a rayuwarta tana son rayuwar kuÉ—i

yadda za ta fantama ta yi rayuwarta cikin daula.

Suna hira suka shiga cikin falo da Mommy. Aliyu yana riƙe da jakar Anty Amarya ya kawo mata
kusa da ita.

Kallonsa ta yi tana dariya ta ce,"Na gode soja mazan fama. Da su Hanifah ka bar musu suka
shigo da shi."

"Kar ki damu Atyna kin san kin wuce haka a gurina. Ni dai na ƙosa da kika ce za mu yi wata
magana, saboda bacin zuwanki da yanzu ma yi nisa."

Da ido ta yi masa alamu da ya daina maganar za su yi sirri. Sai ta wayance da dariya tana
kallonsa ta ce,"Haka ne ai zuwan mai dalili ne, saboda faÉ—a na zo maka."

Gane abin da take nufi ya yi, domin duk 'ya matan sun zura mata idanu, ko wacce tana burin
ace ita za takura masa ya aura.

Mufida ta san ba ya wuce 'yar mijinta, amma duk ta ƙosa ta samu ta sanya masa maganin, don
haka ta fara tunanin yadda za ta shiga kofin É—in.

Aliyu hijira ya so ya yi mana, saboda mun É—auki yarinya muna son mu yi aikin lada."

Anty Amarya ta kalle shi lokaci guda fuskarsa ya sauwa, sai ta kalli Mommy da ita ma shi take
kallo ganin ya haÉ—e rai.

"Wannan yarinyar ce ko Captain?" Ta yi masa tambayar tana kallon sa.

"Ita ce suka kawo wai za su riƙe ta a gidan nan. Ni kuma in har za su riƙe ta, ba zan ƙara zuwa
gidan nan ba, saboda na tsane na. Wallahi ko tunawa na yi tana gidan nan sai na ji xuciyata
tana tashi."

Dariya mai sauti Anty ta yi, ganin yadda yake maganar da gaskiyarsa. Ta san cewa in har ya
tsani abu to ya tsane shi.

"Mu kanmu, bisa tursasawar Hajiya ya sanya ta zauna a gidan nan, amma wallahi da na zauna
da Jimmmalo, gara a haɗa mini jarirai biyu na riƙe, gabakiɗaya babu wanda ya isa ya sanya ta
ta yi ko ta ji magana. Kakarta ta yi mata wani irin tarbiyya mara kyau. Ga ƙazanta ga rashin jin
magana babu sallah ba salati."
"Innnalilahi! Wannan wace irin yarinya ce?" Anty ta yi tambayar da mamaki.

"Hmmmmh! Za ki ganta sun kusa dawowa makaranta, saboda yau aka sanya ta a makaranta.
Na rantse duk bayan minti sai na kalli agogo xuciyata ta buga."

"Ikon Allah gaskiya tana da rigima." Ta furta ganin yadda damuwa ya bayyana a fuskarta.

Aliyu ƙaramin tsuka ya ja, ya kalli 'yan matan da suke kallonsa kamar za su cinye shi, sai kuma
ya kalli lokaci ya sanya idanunsa a fuskar Anty.

"Na ba su zaɓi ko ta bar gidan nan ko na daina zuwa. In har suna son ganina sai su biyo ni
Abuja. Anty bari na je na watsa ruwa sannan na shigo." Ya ce mata kafin ya jira amsa ya wuce.

Mommy ta yi ajiyar zuciya, daidai lokacin da mai aiki ta fara kawo musu ruwa da drinks." Humh!
Na kasa yanke shawara game da lamarin. Na cika ki da surutu ga ruwa kusha." Ta ƙarashe
maganar tare da ɓalle murfin ruwan tana zuba musu.

"Ba komai kan É—an gidana ne dole na tsaya da komai na ji."

"Haka ne kuma, ko wannan zuwan na san wani abu za ku ƙulla, domin ban yarda da ku ba,
amma ya kamata ki yi masa faÉ—a a samu ayi aure a bar magana, yadda mutuwa ke wuf da
mutane, ya tsaya ruwan ido ko wace mace ya ce bata yi masa ba."

"In sha Allahu, zai yi lokaci ne domin aski ya zo gaban goshi." Anty Amarya tace tare da karɓar
ruwan.

"Mommy ina Nufaisah, ko tana school?" Hanifa ta yi tambayar ganin bata ganta ba.

"Yau ba su da lecture, tana cikin bayi wanka ta shiga, domin ba ta jima da shiga ba."

"Ok," Ta ce tare da mayar da hankalinta kan wayarta.

Ba ta jima da maganar ba Nufaisah ta fito daga cikin É—akinsu da tawul É—auke, sai kuma hijabi da
ta sanya. Cikin farinciki suka hada, sannan ta koma ciki don ta sanya kaya.

Duk da Mommy ba ta san da zuwan su ba, amma ta yi musu tarba ta musamman domin kafin
su gama shan ruwa da drinks aka cika gabansu da snacks, sannan ta miƙe ta ce musu." Bari
na shiga na bayar da odar na abin da za a dafa, ga shi na ga lokaci ya ƙure gab da 'yan
makaranta su dawo."
"Ok, mu je na ta ya ki." Cewar Anty tana ƙoƙarin miƙewa.

"Kai haba kar ki damu, akwai mai aiki da ga zuwanki sai ki kama aiki. Ki zauna ki huta zuwa
yamma sai ki yi mana gudun kurna tun da kin zo."

"Ok, tom shikenan." Ta ce tare da komawa ta zauna

Murmushi Mommy ta yi ta shiga kofin É—in. Sosai jininsu ya haÉ—u da ita, domin akwai hankali da
natsuwa.

Abin ka da aikin da gas, babu jimawa aka gama abinci aka kawo musu. Suna zaune suna ci
Aliyu ya shigo cikin shirin fita.

"Anty Amarya zan fita, amma ba zan jima ba, wataƙila kuma na kai dare. Kar ki yi bacci domin
yau za mu yi maganarmu."

"To shikenan, babu matsala É—an gidana sai ka dawo, amma abinci fa?"

"Ni Allah ya kyauta! Ko ruwan cikin gidan nan ba zan iya sha ba in har tana cikin gidan."

Dariya ta yi ba tare da ta ce komai ba. Mufida da Hanifa sai suka ƙosa suka ganta ganin yadda
ya tsane ta.

"Kallon Mommy ya yi da take cin abinci."Mommy, sai na dawo."

"A dawo lafiya Allah ya yi maka albarka."

"Amin,"Ya ce tare da fita yayin da 'yan matan suka raka shi da kallo suna faÉ—in,"Sai ka dawo Ya
Captain."

Sun so su ji ya amsa ba ko bai amsa ba, domin ya tsinci maganarsu, daidai lokacin da ya kai
ƙofa


Jimmalo
Kafin a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login