Showing 57001 words to 60000 words out of 90573 words
Chapter 20 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf
iya zama da ita
ba. Su da Allah ya ƙaddara wa kazar wahala suna da sauran karfi sai su ɗauki ƙaddara, amma
ita kam tana gama wanka za ta tafi, saboda ko muryarta ta ji tana kuka sai kanta ya buga.
"Zo mu shiga cikin gida Jimmalo." Mommy ta ce, ganin Daddy ya kuma hanyar shiga ba tare da
ya kalle ta ba.
"Babu inda zani sai dai a mayar da ni Damagaran."
"Kin zo kenan domin ba ki da kowa a ƙauyen. Hatta gidan da kike zama an siyar, don haka ki zo
ki shiga cikin gida ki karɓi canjin rayuwar da kika samu."
"Ni fa babu inda zani a yanke mini kai. Wayyo Kaka Tani ina ma tare muka mutu." Ta furta tare
da sakin razanannen kukan da sai da ta toshe kunninta.
"Hajiya, ki barta ta zauna a nan tunda ita shashasha ce ba ta san rayuwa a cikin daula ba. Ana
miki tayin shiga cikin aljannar duniya kina wani zancen ƙauye wai shi Damagaran. Kawai tun da
bata da rabo a duniya a kai ta b.q sai ta zauna a can."
Cikin takaici ta rarumi karfe ta yi gurinshi zata kwaɗa masa."Ba ka san wace ce ni ba a ƙauye
ko? Na yi faɗa da mutane masu ƙiba duk ba su samu nasara ba, ballantana kai kana ji da
siranta kamar tsinke. Wallahi a gidan nan sai na karya maka wuya." Ta ƙarashe maganar, tana
nuna alamun karya wuyar da hannunta.
"Ke ba ki da tarbiyya jakar ƙauye kawai!"
"Don Allah Hassan biye mata za ka yi? Ke Jimmalo zo mu shiga cikin gida." Ta ce tana miƙa
mata hannu.
"Babu inda za ni, kuma wallahi tun da ka kira ni da jakar ƙauye, zan nuna maka jakanci, domin
sai na zame maka kaɗangaren bakin tulu."Sai kuma ta noƙe ganin Mommy ta ƙara miƙa mata
hannu.
Kallonta ta yi, sai kawai ta girgiza kai ta shiga cikin gida. Tunanin yadda za ta yi ta gyara ta take
yi.
"Yarinyar nan ta ƙi shigowa tana waje sai ɗurawa Hassan zagi take yi."
"Please ki ƙyamar ta dole ta shigo. Yunwa da dare zai sanyata dole."
"Yanzu ya ya za mu yi da ita?"
"Shine nake ta tunani. Dole na kaita makaranta boko da islamiya, sai na sanya Umma ta rinƙa
koya mata."
"Aikuwa ka haÉ—a umma da aiki yarinyar nan ba ta da kunya, domin bana tunanin zata yarda."
"Ni kaina Hajiya ta haÉ—a ni da aiki wallahi. Tun da muka je kaina yake ciwo saboda ihu da ta
rinƙa yi."
Zama sukayi suna tautauna yadda za su gyara ta, musamman yadda za su yi ta fara wanka da
sallah.
Jimmalo, tana harabar gidan riƙe da kayan Kaka Tani da take ji a yanzu sun fi mata komai
mahimmanci. Da sun haɗa ido da Hassan, sai ta yi masa daƙuwa tana murguɗa masa baki.
Kallonta kawai ya yi, saboda ya fahimci tafi ƙarfin tunainsa. Shiru suna tunanin za ta shigo,
amma har ka kira magrib ba ta shigo ba. A lokacin Hajiya ta yi iyakan ƙoƙarinta, don ta shigo ta
kama kanta.
Ganin Hajiya bar gidan, sai ta rushe da kuka ta ɗauki ƙullin kayanta tabi motar tana
faɗin,"Gidanki zani ba zan zauna a nan ba..." Kafin ta ƙarashe maganar motar ta fice
Ajiyar zuciya Hajiya ta saki ta kalli Daddy."Jihadi za ku yi don Allah, ka san yadda za ku yi ta
zama mai hankali."
Ajiyar zuciya ya saki kawai ba tare da yace komai ba. Hajiya ce take ta yi masa nasiha, da irin
alkhairin da yake cikin riƙe maraya.
Bayan ya dawo ya ƙara lallabarta, amma ta ƙi shigowa, domin har da tsoro gidan yake bata,
saboda a kyawu gidan Hajiya ba komai ba ne.
Mommy ganin an kira sallar Isha, kuma bata ci duk abincin da aka ka mata ba, sai ta miƙe ta fita
zuwa gurin ta. Kuka take yi tana ta kiran sunan Kaka Tani.
"Jimmalo tashi mu shiga ciki gobe xan kai ki ƙauyenku." Jin abin da ta ce su ta kalle ta da sauri.
"Da gaske nake yi tun da bakya son zama damu."
"Eh, na fi son na yi rayuwa a ƙauye bana son rayuwar birni."
"Shikenan, ki shiga ciki ki yi wanka da sallah, sannan ki ci abinci zan mayar dake gobe."
"Zan dai ci abinci na yi dakatsami, amma ba zan yi wanka ba, sannan sallah sai gobe zan yi da
safe saboda a gaji."
Galala ta yi tana kallonta, cikin tsananin mamakin abin da ta ce, amma da ta tuna rarrashinta
take yi dai ta ce,"Ok, mu shiga ciki to."
Ƙullin kayanta ta ɗauka tare da maƙe su a hamma. A tsanake take tafiya tana kallon gidan
sama mai kyau. Mamaki sosai take yi irin kyau da tsarin gida. Ba ta ƙara tsoratar da tabbatar da
cin kai suke yi ba, sai da ta shiga cikin falon. Duk halin da take ciki sai ta saki baki da hanci.
"Zo mu je ki shiga cikin É—akin 'yan'uwanki, ki kwanta kafin gobe." Hajiya ta ce mata tana kallonta
ganin yadda take a firgice.
Saboda tsananin kyawu da girman, gidan sai ta kasa musa mata, don tana tsoron ta kwana ita
kaÉ—ai cikin dare a su kashe ta, domin har ga Allah tunaninta su suka kashe mata Kaka Tani.
Nufaisah da Umma, suna zaune a kan makeken gadonsu. Nufaisah ce take yin assignment, sai
Ummah da take zaune da wayarta tana kallon TikTok. Ganin sun shiga duk suka mayar da
hankalinsu kan Mommy.
"Ga 'yar'uwarku nan, za ta kwana gobe zan mayar da ita ƙauye."
A yadda ta yi maganar sun É—auka da gaske ne. Sosai suka ji daÉ—i duk da cewar ba su da
wulaƙanci, amma sam ba sa son ta rayu da su, saboda abin kunya ne a kalle ta a matsayin
'yar'uwarsu.
"Ok ga gadona sai mu yi amfani da na wa."
"No Mommy, a haÉ—a ta da Baba mai aiki mana."Umma ta furta tana mata wani irin kallo, saboda
tun da ta zagi Captain take jin haushinta.
"Kul! Matsayinta ya wuce haka. Ƴar'uwarku ne don haka ke Umma ki koma gadonta."
"To," Ta ce da sauri tare da É—auke filo za ta koma.
Nufaisah kallon ta ta yi sai ta kalli Mommy da idanunta yake kanta, don haka ba ta ce komai
ba, sai ta ci gaba da assignment É—inta.
Jimmmalo kuwa, ganin wani kallo na ƙaskanci da suke mata sai ta watsa musu nata. Ta so ace
za ta iya zama ta gurje bakin duk wacce ta yi mata rashin kunya, domin ko yayansu mai kama
da zabiya ba ta jin shakkarsa ballantana su ƙananun ƙwari, amma saboda tana son komawa,
sai ta zauna a gefen gadon tana kallon tsaruwar É—akin.
"Jimmalo bari na sanya a kawo miki abinci, amma in kina son ki tafi da wuri sai kin yi wanka da
sallah."
"Ni fa ba zan yi ba kaina ciwo yake mini." Ta ce tare da kwanciya tana shaƙar ƙamshin dauɗar
jikinta.
Wani irin kallo suka watsa mata, har da auta da ya shigo lokacin. Sai kauda fuska suke yi,
saboda tun da ta shigo É—akin ya canza.
Fita Mommy ta yi, tana tunanin yadda za ta shawo kanta ta zauna.
Lafiyayyen tuwon shinkafa da miyan agushi, sai farfesun nama Baba ta kawo mata. Duk daÉ—in
da abincin ya yi bai ɗauki hankalin Jimmalo ba, domin ta ƙosa gobe ta yi ta koma Damagaran.
Sosai suke kallonta, ganin duk halin da take ciki sai data share malmala biyar. Mugun kallo ta
watsa musu ganin yadda suke mata kallon raini. Miƙa ta yi sai ta miƙe kan gadon ba tare data
wanke hannunta ba, ballantana su yi tunanin ta É—auke kwanon.
"Anty Nufaisah, She is dirty girl. Ta ci abinci ba ta É—auke kwanon ba, kuma ba ta wanke hannun
ba. All her body is looking dirty."
"Kai xagina kake yi? Don wallahi ina yi maka ƙubula ɗaya sai ka sume!" Ta daka matsa tsawar
tana faÉ—in haka.
Tsoro ta ba shi da sauri ya matsa gurin Umma. "Cewa na yi ki É—auke kwanon da kika ci abinci
sannan ki yi brush ki wanke baki, saboda Malaminmu ya ce in har ba ka yi brush ba, ka kwanta
abincin zai rufe ya sanya maka ciwon haƙori, sannan kwanuka da kika ci abinci ki ɗauki saboda
ƙananan ƙwari za su iya zuwa."
"Rufe mini baki bana wanke baki, amma har yau ban taɓa ciwon haƙori ba, ka kalli haƙorana ka
san ba ni da ciwon haƙori." Ta ƙarashe maganar tare da wage musu baki haƙoranta suka
bayyana.
Da sauri suka kauda fuskarsu, saboda ganin yadda haƙoran suka yi babu kyan gani, domin za
su iya rantsuwar da abincin da ya maƙale tun na shekaru.
Komawa ta yi ta kwanta tana harararsa. Ta so ace za ta iya zama ta gyara musu zama, saboda
tsaf sai ta yi maganin tsaftansu.
Jin abin da tace su suka daina mamakinta. Satan kallon ta suke yi. Wani irin gyatsa ta saki mai
ƙarfi har sai da suka jiyu. A maimakon ta yi hamdala sai ta shafa cikinta ya ce,"Kwanta naman
kaza da tuwon birni."
Sosai suke mamakin rayuwar da take yi. Ba su cika da mamaki ba sai da suka ji tana jan rago,
domin har da gayya take yi, don su ga cewar ba za su iya ba su mayar da ita.
Munshari da take yi ya ƙara ƙular dasu, har suka fara tunanin dole su yi wa Mommy boren ba za
su iya kwana da ita a É—aki É—aya ba.
Ba su yi shirin kwanciya ba sai ƙarfe sha ɗaya. Bayan sun gama abin da za su yi, sannan suka
É—auro alwala. Sai da kowa ya yi tilawar hadda, sannan suka canza kayan bacci suka kwanta
suna karanto addu'a.
To Hajiya Jimmalo a birni ko ya zaman birni zai ci gaba? Ko kuma za ta yi nasarar a mayar da
ita Damagaran?
Tsokaci
Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruÉ—ani. RuÉ—anin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar
rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I4eCFpcg1htLIH4Iavlhw0
*ƘIYYAYYAR JINI!*
NA
*JAMILA LAWAL ZANGO*
(Jamsy)
*FIRST CLASS WRITERS*
MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan
And now
Ƙiyayyar jini!
08144072423
PAGE 17
*Nace Wai baki da labarin S D Y COLLECTION AND KITCHEN bane Hajiya to maza maso
kusa kar ayi* *babu ke*
*Domin kuwa S D Y COLLECTION AND KITCHEN tazo muku da duk akan abinda kuke so*
*ba anan suka tsaya ba suna siyar da data akan farashi me rahusa*
*MTN 1gb 650*
*2gb gb 1300*
*Iya adadin da kuke so muna turawa*
*"" Ina mata 'yan gayu masu san ƙure kwalliyar su da mayafai na 'yan gayu, muna siyar da
hijabai na 'yan gayu muna sai da yadin Hijabi din mutum yana so, akwai kuma takalma da
kayan kitchen duk akan farashi me rahusa*
*Arabian oud*
*Lamsa oud*
*Black oud*
*Da Duk wane oud da kake nema*
*Muna siyar da data, muna bada sari ga masu siyarwa*
*Duk wandan abubuwan zaki. Same su a gurin*
*S D Y COLLECTION AND KITCHEN*
*Adress ringi road, na dorayi, kano*
*muna tura kayanmu kowane gari da yardar Allah*
*Karki samu damuwa, tun tube a wanan layin ta whatssap*
í ½í±‡í ¼í¿¾í ½í±‡í ¼í¿¾í ½í±‡í ¼í¿¾í ½í±‡í ¼í¿¾
*08130902505*
Ba su yi shirin kwanciya ba sai ƙarfe sha ɗaya. Bayan sun gama abin da za su yi, sannan suka
É—auro alwala. Sai da kowa ya yi tilawar hadda, sannan suka canza kayan bacci, suka kwanta
suna karanto addu'a.
Saboda canjin gurin kwanciya mai daÉ—i, sai ta yi baccin da ta ci bashi tun rasuwar Kaka Tani. Ba
ta tashi ba har sai ƙarfe bakwai. Yaran gidan tun asuba suka tashi suka yi sallah, sannan suka
yi karatun hadda. Bayan sun gama suka yi na boko, har suka gama suka kwanta, Jimmalo tana
sharan bacci.
Mommy ta ninyar tashinta, amma tsoron rikicin ta ya sanya ta ƙyale ta, domin ta san ko ta tashi
ba sallar za ta yi ba.
Ƙarfe bakwai ta buɗe idanunta, saboda alarm da Auta ya kunna ya ɗora mata kusa da kunni.
Da sauri ta buɗe idanunta tana zare idanu. Babu salati ta zabga miƙa tana hamma. Ba tare da
ta kulle bakin ba, sai ta miƙe tana zare ido tuna inda take.
Falo ta fito kai tsaye ba tare da ta yi sallah ba. Ganin babu kowa a falon, sai tibi da aka sanya
karatun Alqur'ani suratul Tauba ƙira'ar Mishawi.
Jin motsi a kicin sai ta nufi kicin É—in tana zare ido, tamkar makauniyar da ta warke daga
makanta.
Mommy tana tsaye da Asibi mai aiki suna ƙoƙarin dama kunun gyada. Babu sallama sai dai
suka ganta a tsaye tana soshe-soshe. Asibi har ta tsorata ta dafe ƙirjinta.
"Haba jimmmalo kyayi sallama kin ga kin tsorata ta." Mommy ta furta tana kallon ta.
"Gari ya waye ki mayar da ni Damagaran." Ta furta a maimakon ta ba ta amsa.
Mommy gabanta ne ya faɗi tuna alƙawarin da ta yi mata, domin ta ɗauka da gaske take yi. "Zan
mayar dake amma ki je ki yi sallah, sannan ki yi brush da wanka. Na sanya Umma, ta haÉ—a miki
kayanta, kafin a siyo mi.."
"Ni fa ba zan zauna ku cinye ni, kamar yadda kuka cinye Kakata ba, saboda aradu wannan
dukiyar da kuke da shi mutane kuke cinye wa."
Murmushi Mommy ta yi, ganin yadda ta haƙiƙance kan gaskiyar maganarta."Ki je ki yi sallah
lokaci yana wucewa." Ta furta mata daÉ—an tsawa.
Amma ko gezau ba ta yi ba ta ce,"A matar dani Damagaran don ba zan zauna anan ba."
"Shikenan, zan mayar da ke, amma yanzu ma sai kin yi wanka kin canza kaya."
Har ta buÉ—e baki za ta musu sai kuma ta juya tana gungunan.
"Hajiya, kamar zaginki take yi fa? Wannan yarinyar an yi mahaukaciyar ƙazama."
"Ya xan yi haka nan zan daure na canzata. Wallahi tun jiya da ta zo kaina ya fara ciwo, saboda
ban san ta inda zan fara ba."
"Gaskiya ga shi ba ta da kunya kallon mutane take a tsaye."
"Hmmmmh! Hajiya ta haÉ—a ni da aiki."
"Babba ma kuwa, saboda wannan yarinyar canzata matsala ne." Asibi ta furta tana juya kunun
gyadar a wuta.
Mommy cikin É—aki ta koma don ta ci gaba da karatun da take yi. Xuciyarta cunkushe da tunanin
ta inda za ta fara.
A maimakon ta yi wankan sai ta yi daka tsami. Ta lafka mai É—aya daga cikin kayan Kaka Tani
riga da zani ta É—aura.
Sai kawai ta fashe da kuka ta rungume sauran kayan."Kaka Tani mai ya sa kika mutu kika
barni?" Ta yi tambayar tana kuka.
Falo ta fito tana jin a zuciyarta dole su mayar da ita Damagaran, saboda zaman gidan shine zai
É—ebe mata kewa ta ga kamar za ta dawo.
A lokacin da ta fito fili duk suna kan dinning. Daddy ne yake saukowa daga bene hanunnsa riƙe
da carbi.
Ganinta sai suka zuba mata ido cikin mamaki. Da fari sun É—auka ko mutuwar ya haukata ta,
ganin shigar da ta yi, amma sai da ta ƙaraso ta kallo Mommy ta ce,"Na shirya a mayar da ni."
Umma, Auta da Nufaisah suka kwashe da dariya.
"Mommy, wannan wane irin kaya ta sanya?" Cewar Umma tana nuna ta.
"Ita kanta Mommy daurewa ta yi, saboda dariyar da take son cin ƙarfinta."
"Jimmalo, lafiyarki kuwa? Da gaske kike za ki rinƙa sanya wannan kayan?" Daddy ya yi mata
tambayar cikin takaici.
"Kayan Kaka Tani ne, wanda su kawai suka rage mini na ke gani na ke jin daÉ—i. Daga yanzu su
zan rinƙa sanyawa har ƙarshen rayuwata."
"Hakan ba zai faru ba, saboda mahaukaciya za a mayar dake, duk inda kike je da kayan nan
dariya za