Showing 90001 words to 90573 words out of 90573 words

Chapter 31 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8089

hawaye.

Murmushi mai ciwo ya yi yana kallon sa."Yadda ka aikata mini, haka sai na rama kwatankwacin
abin da ka yi mini, don sai na sanya ka kuka da idanunka. Ba zan aura maka yarinyar nan ba,
saboda bana son na haɗa ka aure da ita, domin za ka iya zama da ita nan gaba. So na ke
zuciyarka ta yi ƙuna kamar yadda nawa take ƙuna. Ni nake da iko da kai da Safeeya wallahi ka
ji na rantse a yau zan aura maka it..."

Da sauri suka ɗago idanunsu, suna kallonsa cikin tsannanin tashin hankali.

"No, Daddy please no! Zan iya fuskartar duk hukuncin da za ka yi mini, amma ban da aura mini
wannan ƙazamiyar yarinyar! Ko da ace hukuncin barin aikin soja ne, za iya haƙura domin na
gwammace na rayu babu aure da na rayu da ita!"

"Hmmmmh! Ta yaro kyau take bata ƙarko. Wallahi a yanzu zan kira Zariya na sanar da aurenka
don ba zan jirga daga asibitin nan ba sai an ɗaura."

"A'a Alhaji kar ka yanke hukuncin da za ka yi dana sani! Ka taɓa ganin inda zafi da sanyi da zafi
suka haɗu. Babu yadda za a yi Jimmalo da Aliyu su yi zama aure, in har ba so kake yi su kashe
kansu ba." Mommy da take cikin tsanannin tashin hankali jin hukuncin daya yanke ta ce.

"Na riga na gama yanke hukunci, kuma ba zan saurari kowa ba." Ya furta tare da ciro wayarsa
don ya kira waliyan Aliyu. Baba Ɗan- Lami da Sa'idu.

To masu karatu ya kuke tunanin wannan ma'aurata za su zauna? Tun da Daddy ya furta dole

sai an yi auren.

Shin kuna ganin za a yi zaman lafiya?

Jimmalo ya za ta ji in aka gaya mata za ta auri maƙiyinta? Kar ku manta aure bashi a cikin
lissafinta, sannan ta tsani mazinaci.

Mufida za ta haƙura da Captain in ya auri Jimmalo?

Ina Hanifa baiwar Allah?

Captain zai iya amincewa da ita a matsayin matarsa? Bayan ya gama zaga duniya yana faɗin
matar da zai aura daban take a cikin mata?

Ta ya ya za a yi su yi zaman auren har Captain ya ɗauke ta a matsayin mata a sh soyayya shi
daina ya ganta yake jin amai?

Ku hango mana gidan Captain da yake komai fari idan amarya ta tare

Ni kaina zan so na ga rayuwa da waɗannan ma'auratan za su yi a a gida ɗaya. Kun dai san tun
da Daddy ya furta babu fashi, domin ran yan maza ya ɓace, dole Aliyu ya girbi abin da ya shuka
na auren Jimmalo Capacity.

To duk kusha kurumin ku domin amsoshin ku yana book 2 wanda za a fara posting ba da
jimawa ba.

A book two taku din nan haziƙar marubuciya ta tanadar muku duk amsar da kuke bukata.

Ba fa a yi komai ba domin labari yanzu aka fara. Kun san dai somin tabi aka ba ku, ainihin
labarin yana cikin book two.

Wacce take buƙatar cigaba da karanta labarin sai ta biya naira 600 kacal don shiga cikin paid
group. In kuma aka kammala za ta biya naira 800

Ga masu buƙatar payment sai a biya ta wannan asusun

8144072423
Jamila lawal opay


A kuma tura shaida ta wannan numbar
0707 297 1093

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login