Showing 6001 words to 9000 words out of 90573 words

Chapter 3 - KIYAYYAR JINI Complete Hausa Novels by Humira Lawan Zango.pdf

11 Sep 2025

8088

zare idanu tamkar wacce ta yi kisa. "Ni
da yaushe na gaya haka?" Ta yi tambayar tare da fara hawaye.

"Au tambayata kike yi? Da kin tambayi wacce ta gaya mini Karime."

Karime jin an ambaci sunanta, kafin a sanya ta a ciki, sai ta tsaya a gabansu.

"Ki ji tsoron Allah yaushe..."

"Kin gaya mini mana ranar Attinin, da da zamu je sarin ayaba, ki tuna har kina cewa kar in gaya
mata."

Jin abin da ta ce sai hankalinta ya ƙara tashi, amma don ta ƙare kanta ta ce,"Ni fa ba ita ba ce
ba, Jimmalo na gidan Malam Balarabe na gaya miki."

"Ƙarya kike munafuka, kin faɗa hakan ai dama na lura da wani gani-gani da kike mini wai ke ga
ki mai tsafta, kuma wallahi yau sai jikin ki ya yi tsami." Ta ce tare da gaure ta da mari.

Kuka ta sanya domin ta ji shigar marin."Allah ya saka mini, ai na gaya miki ba ke na ke nufi ba."
Ta ce cikin muryar kuka.

"Tun da ba ki da kunya bari na yi maganinki, don sai na fasa bakin sai na ga gobe da wani bakin
za ki yi gulmar"Ta furta da fara kai mata duka ta ko ina tana kuka.

"Muguwa azzalumai, kin girma kin ƙi aure saboda ƙazantarki. Ai Innata tace duk kin girme mu,
shi ya sa kike cin zalincinmu yadda kika ga dama." Ta ce cikin kuka.

Jin abin da tace, sai ta zuciya ta ci gaba da dukan ta."Jira na ke yi Babanki ya saki mamanki,
sai na aure shi yadda zan koya miki tarbiyyar da aka kasa baki." Ta ce tana dukanta.

Da ƙyar aka samu aka hanata dukan sannan ta ƙyaleta tana huci.


Ukraine
Captain Aliyu zaune a katafaren hotel da yake birnin Ukraine, mai suna premier palace Hotel
Kyiv. Sanye yake da kayan sojoji, kayan sun yi masa kyawu matuƙar gaske! Daga ganinsa ka
ga namiji ingarma, wanda Allah ya yi wa tagomashi, da duk wani abun da ya kamata namiji ya
mallaka. Kallo ɗaya za ka yi masa ka gane mutum ne mara haƙuri da rashin magana. Sam
fuskarsa babu annuri Idanunsa lumshe, yana kallon abokinsa Kalim da yake gyara bindigarsa.

Aliyu ɗane ga Alhaji Abubakar mai gilashi wato Daddyn K.d. Mahaifinsa yana da kuɗi sosai.
Ɗan boko ne kuma ɗan kasuwa. Suna zaune a garin Kaduna, amma asalinsa haifaffen garin
Zariya, unguwar Juma. Alhaji Abubakar yara huɗu ya haifa da matarsa Hajiya Karimah. Wacce
take mai haƙuri kuma wayyayiwa 'yar boko. Ta yi sakandire a garin Kaduna da sannan ta yi
digiri ɗinta jami'a a Kasu. Bayan ta kammala sai ta fara koyarwa. Sun haɗu da Alhaji Abubakar
a sanadin Ƴaƴanta, da yake abokinsa kuma suna harkan cinikayya. Ganin ta yi masa ya
bayyana wa aminin nasa. Ba tare da ɓata lokaci ba aka sanya bikinsu. Hajiya Karimah da Alhaji
Abubakar suna da riƙo da addini. Wannan ya sanya duk tarin kuɗin da suke da shi, bai hana
bawa yaransu tarbiya na gari ba.

Captain Aliyu, ya yi makarantar kuɗi mai tsada a garin Kaduna. Sannan islamiya da hadda duk
na kuɗi ya yi. Bayan ya kammala mahaifinsa ya yi masa viser ya tafi America, don ya yi
karatunsa a can, musamman ganin yadda jarrabawar sa ta yi kyau, amma sai ya bijire masa
don a rayuwarsa soja yake son zama. Da fari sun ƙi aminta, ganin tun da ya taso yana da
tsananin fushi da rashin haƙuri. Sai dai, ganin ko da yaje America ya ƙi maida hankali ya yi
karatun. Wannan dalilin ya sanya kan dole ya dawo da shi, ya sanya shi a makarantar sojojin
N.D.A.

Sosai ya mayar da hankalinsa kuma ya tashi cikin hazaƙa, domin tun kafin ta girma ya samu
ɗaukaka fiye da sauran karatunsa. Yana kammalawa ya samu aka ba shi aiki.

Daddy ya yi namijin ƙoƙari, don ya ga ya tashi da tarbiyyar da ya ɗora shi a kai. Don haka ya sa
ya idanu sosai a kansa, tare da yi masa barazanar duk lokacin da ya ga ya yi abin da ba daidai
ba, zai cire shi kuma dole ya bi zaɓinsa. Saboda wannan sharaɗin yake matuƙar taka tsantsan
da halayen da ya koya, sai ya zamo fuska biyu, domin yana shan sigari duk da ba ta yi ƙarfi ba,
sai in an ɓata masa rai. Sannan mace ɗaya yake kulawa har yake mu'amala da ita.Giya ce
kawai ba ya sha, amma duk hali irin na sojoji yana yi. A gida yake zama mutumin ƙwarai, amma
da zarar ya dawo sai ya rikiɗe ya zama kura da fatar akuya. Abu biyu ne baya wasa da su
sallah da karatun Alqur'ani, wanda su suke sanya shi rage abin da yake yi, don wani lokacin
sam ba ya wannan harkar. Ba kamar sauran sojojin, da suka mayar da wannan rayuwar ya
zama jikinsu ba.

Kallonsa Kalim ya ƙara yi, daidai lokacin da ya juyo."I need to go back to Nigeria. Haƙiƙa am
missing my family a lot." Ya ƙarashe maganar, fuskarsa ɗauke da damuwar hakan.

"Ni kaina kewar gida ya ishe ni, ina buƙatar na ga ahalina." ya faɗa yana gyara zamansa.

Tautaunawa suka shiga yi, har zuwa wani lokaci. Yawancin hirar ta su, akan aikin su ne da
yadda suke takura.

Bayan sun gama hirar, ya miƙe yana gyara zaman belt ɗin wandonsa, yayin da idanunsa yake
kan wayarsa da kiran Lubaynah ya shigo.

Ƙaramin tsaki ya ja, wanda yake nuna takurar da mai kiran ta yi masa, ya fara taku ɗaya biyu,
sai kuma ya dawo da baya ya ɗauki wayar.

"Hello, Captain?" Ta ce cikin murya mai daɗi.

"Yes!" Ya furta a gajarce.

"Please, Captain.."

"Lubaynah, I will call you back." Ya kashe wayar, ba tare da ya ji amsar da za ta ba shi ba.

Fita ya yi zuwa harabar Hotel ɗin. Ya ƙarasa gurin swimming pool ya zauna a bakin ruwan.
Ƙafafuwansa ya zura yana lumshe idanunsa, jin yadda sanyin ruwan yake shigarsa.

A ƙalla sai da suka yi wata ɗaya, sannan ya dawo Nigeria. Daga filin jirgi gidansa ya wuce da
yake Barak na Abuja. Saboda cikin dare ya dawo wanka kawai ya yi ya kwanta.

Washegari da ya tashi, bayan ya je masallacin ya yi sallah, ya dawo ya kwanta. Bai ta shi ba,
sai da mai aikinsa Peter ya zo aiki. Motsin sa ya sanya shi tashi.

A hankali ya janye blanket dake lulluɓe a jikinsa. Jikinsa ya bayyana yana sanye cikin kayan
bacci, daga shi sai gajeren wando da wata rigar wandon mai kyau. Kayan suna da kyau kamar
yadda suka yi masa kyau. Ya na kwance yana kallon ɗakin da yake ƙamshi mai daɗi, kafin ya
zura ƙafafunsa ƙasa ya miƙe tsaye.
Kai tsaye bayi ya shiga, ya yi wanka bayan ya bata tsawon lokaci. Fitowa ya yi da ga shi sai
tawul, yana goge jikinsa da ƙaramin tawul dake hannunsa.

Tsayawa a gaban mirror yayi, ya shirya tare da gyara fuskarsa. Kamar mace haka yake akwai
gyara jiki da ɗaukan wanka, sannan sam ya tsani ƙazanta. Shi mutum ne wanda za a iya ce
masa tsafta ta yi masa yawa. Saboda duk yadda yake da mutum ba zai iya cin abinci ya rage ya
ba shi ba, sannan in ba iyayensa ba ko ƙanninsa bai taba cin abinci da su ba. Ko iyayen na sa
tun da ya girma ya daina. Baya son ƙazanta don ko a hanya baya ƙaunar ya haɗu da ƙazami.
Wannan dalilin ya sanya kaf 'yan aikin gidansu suke taka tsantsan. Shi ya sa kodayaushe
gidansu yake cikin gyara. A lokacin da ya mallaki nasa gidan, saboda tsafta komai nasa fari ne
na kayan gidansa. Hatta kujerunsa fari haka kayan kicin ɗinsa dinning ɗin sa. Gidansa babu
abin da babu, domin kamar na mai aure gidan, saboda yadda ya tsaftar shi, yana da son ado da
ƙyalƙyali. Wani lokacin da kansa yake zama yana gyara gidan. Masu aiki kuwa an sha kawo
masa yana korarsu sai Peter kaɗai ya iya da shi, don shi ma yana da tsafta kuma ya iya abinci,
saboda abin da ya karanta kenan.

Bayan ya gama shirya ya saka wando da riga masu kalar kayan sojoji, amma suna da taushi

sosai ya fito. Zama ya yi kan kujerar da wayarwa a hanunsa daidai lokacin da Peter ya fito daga
kicin ya nufi dinning da kular abinci.

Bayan ya ije ya zo inda yake. "You are highly welcome sir." Ya ce masa cikin girmamawa tare
da ɗan duƙawa.

"Peter how doing?" Kawai ya ce masa ya ci gaba da kallon wayarsa.

"Fine sir, how was the trip?"

"Successful."Ya furta a takaice.

"We thank God, breakfast is ready."

"Ok," Ya ce masa ganin haka ya koma kicin ɗin.

Sai da ya ɓata lokaci, sannan ya mike zuwa dinning inda aka shirya abincin. Ruwan Lipton ya
haɗa masa, sannan ya soya masa doya da source, sai kuma farfesu da ya yi masa, sanin halin
ogan nasa ya son albazaranci kuma ba ya cin abinci da yawa.

Ba wani sosai ya ci abincin ba, ya miƙe ya fita daga falon. Inda karensa Bindo yake ya nufa
bayan ya ɗauki abincinsa.

Ɗakin da yake ya ƙarasa tare da buɗe ƙofar ya fito. Wani irin baƙin kare ƙatoto da shi. Sai kaɗa
bindinsa yake yi yana zare harcensa. Daga ganinsa kasan ana kula da shi, saboda yadda yake
cikin tsafta.

Karen ya ci gaba kaɗa bindinsa, yana taɓa jikin Captain Aliyu, tare da rawa na murnan
dawowarsa. Murmushi sosai yake yi masa ya kama kansa ya riƙe. Sosai yake son karen, domin
zai iya wuni da mutane ba tare da sun ga fara'arsa ba, amma ko kallon karen ya yi sai ya
murmusa.
Ya ɗauki tsawon, lokaci yana kula da karen ya kuma yi wasa da shi, ya wuce zuwa lambun shi.

Iskar da take kaɗawa ta saukar masa da nishaɗi sosai. Zuciyarsa ta raya masa ya kamata ya
kira Lubaynah don ta rage masa kewa.

Ba tare da dogon nazari ba, ya ɗauki wayarsa tare da danna mata kira.

"Hello babyna," Ta furta cikin muryarta na son jan hankalinsa.

"Ki kwaso kayanki kamar na wata na dawo Nigeria."

Jin abin da ya ce mata, ya sanya ta ji matuƙar farinciki. Fuskartar ta bayyana murmushi sabanin
da, da take cikin damuwa."

"Amma shi ne ba ka gaya mini ba?"

"Why do you ask? It is as usual." Ya furta mata a ɗan zafafe.

Jin ransa ya ɓaci ya sanya ta ce,"Ok, my Captain. I will be on my way. I Love you."

Kashe wayar ya yi, sannan ya faɗa swimming pool, ya rintse idanunsa. Duk ya ƙosa ya koma ya
ga family ɗinsa. Ya daɗe a cikin ruwan, domin yana son wanka a swimming pool sosai, sannan
ya fita ya shiga ciki don ya cire kayansa.

Kamar yadda ta yi masa alƙawarin zuwa. Ba ta ɓata lokaci ba, yana zaune a cikin falonsa sai ga
kiranta.

"My Hearthrop, I'm outside the get?" Cikin harshen Nasara ta yi masa maganar.

"Ok," Kawai ya ce tare da kashe wayar.

Mikewa ya yi, bayan ya ɓata lokaci yana zaune, sannan ya ɗauki wayar da ya fita.

"Solo, open the get." Ya ce tare da komawa ciki.

"Ok, sir." Ya faɗa sannan ya tashi cikin hanzarce ya buɗe mata.

Janyo trolley ɗinta ta yi, ta shigo cikin gidan. Tana sanye da doguwar riga baƙa, sai ƙaton
recommenden glass da ta sanya.

Captain Aliyu ya da fuska biyu? Ke kuma Lubaynah na miji kika amince da shi har ya maida ke
kamar matarsa? Makaranta wannan salon daban yake. Kici gaba da bibiyar labarin da kuma
zafafan comments.

FOR WHATSAPP: 07072971093
CALL: 00814407242


Ƙiyayyar jini tsuke yi wa junansu tun kafin haɗuwarsu, domin sun kasance tamkar mage da
ɓera, saboda bambancin rayuwar da suke ciki. Haƙiƙa rayuwa tana zuwa da ababen al'ajabi da
ruɗani. Ruɗanin da yake sanya mu cikin wasu wasiku abin da zai faru a gibenmu. Duk da cewar
akwai wasu burika da kuma sirrin da yake ɓoye a xuciyoyinmu, wadanda Ubangiji kawai ya
sansu, sai mu da muke aikatawa. Haka ya kasance ga rayuwar Captain Aliyu, da ya ɓoye sittin
da ya saya shi zama fuska biyu, wanda bayyanuwar sittin ya canza linzamin ƙaddarar

rayuwarsa, daga farar takadda zuwa baƙa. Shin kun taɓa ganin inda aka haɗa zuma da maɗaci
guri ɗaya, ko kuma kun taɓa ganin inda mage da ɓera suka yi rayuwa a guri ɗaya? To duk ya
faru a cikin littafin "Ƙiyayyar Jini!" Wanda faruwar hakan ya sanya zuciyoyi cikin dana sani da
alhini. Akwai wani irin rikitacciyar soyayya, da kuma tsana, cin amana, yaudara har da ban
dariya da sanya nishaɗi. Maribuciya duk ta yi shiri ta wasa ƙwaƙwalwaarta kuma ta feƙe
alƙalaminta don ta nishaɗartar, fadakar har da sanya zuƙata cikin tausayi. Ka da ku sake a baku
labari domin wannan tafiyar salon sa daban ne.

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/E9kBdqbI0Yf2hsCTaxPVjg

*ƘIYYAYYAR JINI!*

NA

*JAMILA LAWAL ZANGO*

(Jamsy)

*FIRST CLASS WRITERS*


MARUBUCIYAR
Sakacina ko halin maza
Kura da fatar akuya
Ranar wanka...
Wasu mazan

And now

Ƙiyayyar jini!


08144072423



Don karanta Ƙiyayyar Jini ku bi link ɗinnan, sannan karku manta ku yi following ɗina
arewabook
https://www.arewabooks.com/chapter?id=68641a0d7c887833ecc9b10d. Check it out!

Ga link na channel ɗina shi ma ku yi joinning don samun labarin tun daga farko.Follow the
ƘIYAYYAR JINI channel on WhatsApp:
https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xqsd72WTrg772JU2P



PAGE 3

Cikin yauƙi da yanga take tafiyar, kamar yana gabanta ta shiga cikin falon. Ganin ba shi a falon
ta fara tafiya zuwa ɗakinsa.

Fitowarsa ya sanya ta miƙe da sauri ta isa gareshi. Jikinsa ta faɗa tare da rungume shi. Hot kiss
masu zafi ta sakin masa.

Janye ta a jikinsa ya yi, ya zaunar da ita gefensa, tare da zama kusa da ita yana wani kasalalen
murmushi, wanda yake iya leɓe.

Har ranta take kallonsa, tana jin yadda zuciyarta ke bugawa." Ba shi wani kiss ɗin ta yi, amma
sai ya kauda kansa yana sakin ƙaramin tsuka.

"Hearthrop, you called me for this, and you are avoiding it?" Ta yi masa tambayar cikin
shagwaɓa.

Miƙewa ya yi, ya rage kayan jikinsa, ya rage da ga shi sai gajeren wando na sojoji. Kallonsa
take tana ji kamar ta lashe shi. Ji take kamar ta rungume shi, amma ta san tun da ya nuna
wannan mood ɗin, in ta aikata hakan, sai ya yi mata wulaƙancin da ba za ta so ba. Sanin hali,
ya fi sanin kama. Wannan dalilin ya sanya ta haɗiye maitarta.
Bayi ya shiga don ya watsa ruwa. Ya jima sosai ya fito, domin a lokacin har ta gaji da jiransa, ta
ɗauki wayarta, ta hau yanar gizo.

Ganin ya fito ya sanya ta kashe wayar tana kallonsa. Kai tsaye gurin kayansa ya nufa, wanda
ganin haka ya sanya, ta kama hannunsa da sauri tana masa wani irin kallo.

Kallon da ya sanya shi fasa saka kayan. Hannunta ya ja ta faɗa ƙirjinsa tana maida numfashi.
Fuskarsa ya haɗe guri ɗaya, yana jin yadda numfashinsu ke sauka a kan fuskokinsu. Ba tare da
ya ce mata komai ba, ya jata suka faɗa kan gado.

Ba su tashi bacci ba, sai da lokacin sallah ya yi. Captain Aliyu ya fara tashi, saboda duk abin da
yake yi, sam ba ya wasa da sallah.

Janye jikinsa ya yi, tare da ture ta da ta ƙara rungume sa."Ki tashi ki yi sallah." Ya ce mata yana
buga filon da take kwance da ƙarfi.

Buɗe idanunta ta yi tana kallonsa."Please, I need to rest, zan yi sallar zuwa anjima, saboda jiya
ka hana ni bacci."

Jin abin da ta ce ya sanya shi ɓata rai, tare da daka mata tsawa yana faɗin,"Ki tashi ki yi sallah."

Babu musu ta miƙe ta wuce bayi, ba tare da ta yi ƙorafi ba, domin tana mugun tsoron shi, duk
yadda yake sonta in ya ɓata rai, ba ta sha da daɗi a Captain Aliyu kenan namijin zuma ga daɗi
ga harbi.

Bayan ta yi sallar ta koma ta kwanta, ba tare da ta ci abincin da aka kawo musu ba.

Da ya idar da sallar fita ya yi, domin za su je je training da Kamil

Bayan sun dawo, ya ci abinci sannan ya fita zuwa gurin Kamil. Hannu ya ba shi suka tafa.

"Na ga mutuniyar jiya ta zo, ina shirin fita da motata na ganta. Na hange ta za ta shiga gidanka."

"Eh, ni na kira ta." Ya faɗa a gajarce yana buɗe lemun da yake gabansa.

"Lubaynah, tana matuƙar sonka, domin duk ta bambanta, da sauran matan da muke yin hurɗa
da su. Why not ka aurenta, domin tana da kyau.."

"Oh please, no! Kar ka yi mini baki." Ya katse shi yana faɗin haka.

Mamaki ya sanya shi kallonsa ganin haka ya kurɓi lemun, sannan ya ije ya kalle shi ya
ce,"Kasan kalar macen da na ke so na aura kuwa? Mace zan aura tsarkaka wacce ba ta taɓa
sanin ɗa namiji ba. Uwa ta gari zan zaɓawa 'ya'yana, bana fatan Ubangiji ya jarrabce ni da
aurar mace mara kamun kai kamar Lubaynah."
"Ok, wanzami ba ya son jarfa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login