*Labarin ZINARE ƙirƙirarren labari ne, gagaruwan ciki da wasu ƙasashen ciki duk ƙirƙirane, idan wani sashe na labarin ya yi kamaceceniya da rayuwar wata/ni to akasine*
*CHAPTER 1*
*"BA A RANAR DA MUKA SHUKA IRI ZA MU GIRBI AMFANINSA BA, DOLE SAI MUN JIRA, MUN YI HAƘURI, TARE DA YIN AIKI TUƘURU."*
Yara Matasa Maza da Mata ma su shekaru 15 zuwa ƙasa ne suka cika filin wasan.
Ɓangaren Maza daban na Mata ma daban.
A ɓangaren Maza, a tsakanin ƙungiyoyin biyu da suke gwabza wasan ƙwallon ƙafa kowa na ƙoƙarin nuna ƙwarewarsa, da zafin namansa. Wannan yasa ihu da tafi yake ta tashi daga kowani ɓangare, bakunan wasun su kamar zai yage saboda dariya da ihu.
Kujerarsa ba ta kusa da ta kowa, fuskarsa daban take data kowa, ba bu murmushi balle dariya. Ba ya tafawa kamar ragowar kamar ma dai bai san me ake yi a wajen ba, ko wanda aka tilastawa zuwa sansanin wasannin dole. Tsayayyen dogon hancinsa ya shafo ya na lumshe fararen idanuwansa, Kamar ance ya waiyawaya bangaren da Matan suke wasannin su. A daidai lokacin wata matashiya mai irin Shekarunsa ta kwaso ƙafar ƙaramar yarinyar da bata wuci shekaru 6 ba, mugun dariya ya kwashe da shi yana ƙara waiwayowa kansu dakyau, zaman ƴan borin da yarinya tayi ne yasa ya ƙara kwashewa da dariya.
Ya na son mugunta a rayuwarsa sai dai baya iya yiwa wani amma yana so yaga anyi a gabanshi, saboda daɗin da yake ji, musamman idan wanda aka kai ƙasan ba shi da gaskiya.
A hankali yarinyar ta miƙe fuskarta duk hawaye da majina, nan ma dariya ya ƙara kwashewa da shi, ya na jin daɗi a ranshi. Mai ya kaita cikin manyan da ba sa'anninta ba yin wasa, banda ga ƙananu Yara Ƴan uwanta suna na su wasannin? Miƙewarta tana karkaɗe ƙasar jikinta haɗe da zare idanuwanta da hawaye ya ɓata ne ya ƙara sashi sakin dariya kafin ya ɗauke kanshi yana sauke ajiyar zuciya nishaɗin da ya samu.
A take asalin fuskarsa da ba fara'a sam ta dawo yadda ta ke.
A can nesa da shi Sufyan yaron da bai wuce shekaru 11 ba ne ya zubamai ido, ya daɗe ya na kallon duk wa su motsinsa har hankalinsa ya bar wajen wasannin da ake yi gaba ɗaya. Maiyasa ba ya dariya sai ya ga mugunta? Maiyasa ba ya magana sai da ƙwaƙwarar dalili? Ya na son ya matsa kusa da shi ya yi masa magana kamar yadda Mahaifinsa yake umartarsa duk ranar da zai fito ire-iren waɗannan guraren da shi kaɗai yake iya sumun damar ganinsa kai tsaye, amma tsoro ya ke ji duk da ratar shekaru hudu ne kacal a tsakaninsu.
NAILA da aka kwashewa ƙafafu jikinta ta ƙarasa karkaɗewa har cikin ranta takejin takaicin abinda akayi mata, banda zafin da take ji a bayanta. Kalle-kallen wanda zata kaiwa ƙara ta fara yi har idanuwanta suka faɗa gurin dayake zaune shi kaɗai. Da gudunta na yaranta ta nufesa rabin fuskarta duk ƙasar da hannunta ya kwasa.
Gabansa ta zagayo ta tsaya batare jin tsoro ko shakka ba.
Da ƙaramin muryarta na yara ta fara koromasa bayani ta na sauke ajiyar zuciya.
Ba ya wasa da yara, balle ya ce ya taɓa wasa da ita a wani wajen ne yasa ta zo har gabansa ta tsaya. Tsaf yake sauraronta, a bayanin na ta da yanda take kame-kamen dole sai ya bi mata haƙƙinta yasan itace bata da gaskiya amma take so a rama mata, rabin fuskarta ya kalla tare da tuno yadda aka kwashe mata ƙafafuwa tayi zaman ƴan bori, sai ya kwashe da dariyar mugunta
Ya kai wasu daƙiƙu ya na yi kafin ya gimtse fuskarsa yana ɗauke kallonsa daga kan fuskarta. Tsayawa Naila tayi ko zai ce mata ta zo su je ya rama mata amma sai taji shiru. Ƙasar fuskarta ta ƙarasa karkaɗewa da kyau. Sai a lokacin ta gane wajen wanda ta zo. SULAIM ne ɗan gidan ABDUH DHAHAB ɗin daya zama ƙashin bayan Yankin su kuma Abokin Mahaifinta. Indai shine Dama bazai kulata ba, dan da tasan ma shine da bazata zo ba.
Barin wajen ta yi tana tunano abinda zatayimai tunda yaƙi kulata dama kuma tasan kurma ne baya magana.
A haka wasannin ya ƙare kowa ya fara haɗa kayan wasanninsa don tafiya Gida.
NAILA; Sanyin iskar da yake busa ta ne yake ƙaramata ƙaimin tunanin abinda zata haɗamai lokacin da take kallon takun sawayensa shi kaɗai, saɓanin ragowar da suka jero da Abokannan su.
★washe gari ƙarfe bakwai na safiya a harabar gidan Abduh Dhahab ya yi mata, sanye cikin Uniform ma su tsafta, kafaɗarta rataye da jakar buhu shima a wanke ƙal.
Baki Malik Mai share harabar gidan ya saki, lokacin da ya yi ido biyu da Naila, tambayarta dalilin zuwanta ya yi yana ajjiye tsintsiyar hannunsa.
Dariya ta fara ƙyalkyalewa da shi sannan ta ce;
"ina kwana Malik, dama Sulaim ne yace na biyo ya kaini Makaranta a kekensa"
kai ya girgiza mamaki da wayon ƙaramar yarinyar na kamasa uwa uba ƙarfin halinta. Kafin yayi magana Sulaim ya fito da Kekensa shirye cikin Uniform ɗin daya bambanta da nata color.
Sulaim kallo ɗaya ya yi wa Naila ya ganeta, duk ɓacin ran daya fito da shi sai ya nemi gushewa;
"Anata tunanin zata iya ƙuntatamasa kenan?" Ya tambayi kansa.
Kai kawai ya jinjina ya na karkata Kekensa mai kyau da tsada ta gefen da take tsaye. Dasauri ta ɗane tana sakin dariyar nishaɗi haɗe da ɗagawa Malik da ya saki baki hannu.
Gudun dayasa Naila sakin kuka da majina Sulaim ya ke yi da ita a kan keken. Duk inda suka gifta sai an kalleta ma su dariya na yi. Kafin su isa Makaranta mazaunanta har ƙaiƙayi su ke mata. Bai ce mata komai ba bayan ta sauka ya bar wajen.
Naila takai minti goma a tsaye tana kuka kafin ta shiga aji.
Bayan kwana biyu
Sulaim ya ɗauka Naila zata gajiya amma sai ya ga kullum sai tazo. Tun hankalin mutanen Yankin ba ya kansu har kowa ya fara Ankara haka ma Mahaifinsa sai dai bai ce komai ba.
Tun ƙarfin halin Naila baya birge Sulaim har ya fara birgesa, ya dawo kullum da kansa yake tsayawa a ƙofar Gidansu ya ɗauketa.
A ɗan kwanakin da suke zuwa Makaranta tare Naila ta fahimci Sulaim ba kurma ba ne Selective mutism ne. Tun yana yaro har ya kai shekaru huɗu bai iya maganar arziƙi ba, kuma a haka sai ya wuni baiyi magana ba musanman a cikin mutane. Ya na jin nauyin yin magana a wasu lokutan da ma wasu guraren. Da farko yawon kaishi Asibitocin wa su Yankunan Matar da Mahaifinsa ya aura bayan tafiyar Mahaifiyarsa ta yi-ta yi saboda son da takemai. amma duk inda taje amsa ɗaya ne ba sauyi.
SULAIM;
Rayuwar neman kuɗi da kafawa zuciya ra'ayin riƙau na tsayuwa kan matsaya ɗaya tare da aikin ƙarfi tuƙurun Mahaifinsa ya horar da shi a kai, wannan dalilin ne ya yaƙara duƙufar da maganarsa, saboda shima Abduh mahaifinsa ba gwanin surutu ba ne kuma tare suke wuni su na aiki, idan ya dawo daga Makaranta.
Sannan Abduh Dhahab ya keɓancesa daga Abota da kowa musamman da ya ga sunfara tsokanarsa da kurma. Tun Sulaim yana jin ƙiwiya da nauyin yin aikin ƙarfin ƙera Tukwanen da sukeyi har ya haƙura ya saba.
Sulaim ya fi jin daɗin saurarar maganganun mutane a kan ya yi. Daga Makaranta ba ya zuwa ko ina sai wajen sana'ar Mahaifinsa, sai kuma filin wasannin ƙarshen Mako.
Sauraran hirarrakin mutane ba tare da ya tofa ba, ya taimaka ƙwarai wajen mayar da shi Yaro na daban a cikin dubban Yara ƴan uwansa saboda basirarsa.
Matsowar ƙarshen watan cin Kasuwar babban Yankin ne yasa ko ina ya ɗauki harama don kusan dukka mutanen Yankin kowa da abinda yake siyarwa don samun kuɗin shiga daga baƙin da suke shigowa.
Haka yake a Gidan su Sulaim da suke ginshiƙin Kasuwar gaba ɗayanta. Ba ji ba gani suke ƙera Tukwanen dake ɗaukar idon duk wanda ya kallesu tare da kwaɗaituwar son mallakar su.
A gidan su Naila ma haka zancen yake. Mahaifiyarta kayan wasan Yara take ƙerawa na laka, irin su kwano, murhu, cokali, da randar ruwa ƙananu gwanin ban sha'awa, dukka na wasan Yara. Kuma da yawan gaske takeyinsu amma baya kwantai duk sai an siyeshi.
Zuwan Naila Makaranta tare da Sulaim ya ƙara farfaɗo da zumunci a tsakanin Mahaifiyarta da Matar Mahaifinsa, tun da dama can akwai alaƙar jini amma Abduh Dhahab ya datsesa saboda hana Iyalinsa shiga wajen kowa da ya yi.
A tsakanin kwana huɗun da ya rage aci Kasuwar Zinare, Ɓakin fuska a manya motocin da ya zama abin kallo ga Mutanen Yankin su ka bayyana a Daular Sarki Hammam.
A fadar Sarki Hammam baƙin fararen fatar su ka shaida abinda ya kawosu, wato siyan Tukwanen Abduh.
Har gidan Abduh Sarki Hammam ya sa akayi musu rakiya.
Bayan sun kai, ƙememe Abduh yaƙi fitowa balle su gana, haka suka haƙura suka ƙara dawowa Fadar Sarki Hammam ya taimaka ya yiwa Abduh magana, ya siyar mu su da Tukwane.
Sarki Hammam da kansa ya tura a kirawo masa Abduh.
A ɓangaren Ɗayyib Ɗan uwa ga Abduh Dhahab kuma Aboki, Mahaifi ga Sufyan.
Bai samu nutsuwa ba, har sai da aka bincikamasa dalilin zuwan Baƙin da kuma wajen wanda su ka zo, ta hanyar Aminansa da baƙin suka shigo Fada akan idanunsu.
A ranar bayan Sallar Magriba labarin Faɗuwar Ɗayyib ya riski Abduh Dhahab. A dai-dai lokacin da kiran Sarki Hammam ya riskesa.
Ɗan jim Abduh ya yi, yana sauraran ɗaya daga cikin Aminan Ɗayyib da yasa su ka bincikamai zuwan ɓaki da kuma dalilin zuwansu da wajen wanda suka zo, bayannan kuma ya yanke jiki ya faɗi. Wanda ko shakka ba ya yi akwai abinda Ɗayyib ɗin ya shirya.
A tsarin Abduh baiyi niyyar Aminta da ɓakin da suka zo ba, don ko ganinsa bai bari sunyi ba ne saboda ba zai siyar musu ba.
Tayaya zai kwashe dukka Tukwanen ZINAREN da mutane suke baro Yankunan su da jahohinsu don siya, ya siyarwa da mutane ƙalilan bayan yasan bazai iya ƙera wa su Tukwanen ba kafin zuwan ranar? Bayason Darajar Yankinsa da Kasuwar da ya sha gwagwarmaya kafin kafuwarsa ya yi faɗuwar Tasa, amma yana ganin lokaci ya yi, da ya kamata ya sallama komai. Godiya ya yiwa wanda ya kawo masa labari, sannan ya ɗauki hanyar zuwa ganin Sarki Hammam.
"Mai zai sa Ɗayyib ya yanki jiki ya faɗi mai hakan yake nufi" Abduh ya tambayi kansa, lokacin da ya kutsa Fadar Sarki Hammam.
Bayan Sarki Hammam ya gama koro masa jawabi bai ja da nisa ba ya ce ya amince, don haka Sarki Hammam ya ce yaje Sashen Baƙi suka ƙara tattaunawa da su.
Kafin Abduh ya shiga wajensu sai da ya fara shiga Sashen Ɗayyib, yanayin yadda ya gano makirci ƙarara a ciwon nasa ne yasa kai tsaye bayan ya shiga wajen baƙin Fararen Fatar ya ce mu su;"Gobe su kawo kuɗi ku kwashi Tukwane"
Jikinsa a sanyaye, ya yi musu sallama ya nufo gida.
Bayan ya dawo gida, pillow da abin lulluɓarsa ya ɗauko ya dawo ɗakin Sulaim, rauni da tsoro na shigarsa akaron farko tun fara gwagwarmayasa...🏻
SULAIM;
★washe gari da Safe. A shirye yake tsaf cikin Uniform fuskarsa a turɓune, da zafin nama ya ke yunƙurin fito da kekensa, kalaman Mahaifinsa na ƙara sukar zuciyarsa, kullum ya tambayesa kuɗin kashewa sai ya ce masa;
"Ba a ranar da mu ka shuka iri, za mu girbi amfaninsa ba, dole sai mun jira kuma mu yi haƙuri, tare da yin aiki tuƙuru. Ka je Makaranta yau ma ba ni da kuɗin da baka"
Waɗannan kalamai su Mahaifinsa yake yawan nanata mai, duk lokacin daya miƙamasa hannu da sunan ya ba shi kuɗin da zai siyi abu a Makaranta ko yin wa su uzururrukan da ba su zama tilas ba. Duk da ga kuɗin ya na ganin su muraran amma sisi ba zai ba shi ba.
Kamar kullum da haushin hanasa kuɗin da ya yi ya yaƙarasa fito da kekensa ya bar Gidan, ƙofar gidansu Naila da ke kusa da na su gidan ya ja ya tsaya. Yana kaɗa kararrawar, ta fito a guje, Ta na hawa ya fige keken ko gaisuwar da take masa bai amsa ba.
Yanayin yadda ya ke tsala gudu a kan keken kwatankwacin ranar da ya fara ɗaukarta ne ya sa ta ƙanƙamesa da siraran hanayenta da ko kusa ba su ratsa rabin cikinsa ba.
A haka suka isa dogon ginin da ke kewaye da ajujuwan karatu. A hankali ya kwanto da keken duk da ba wani ƙato ba ne ta sauko. Idanuwanta ma su kalar tausayi ta ɗago ta kallesa, sannan ta ɗagamai ɗan ƙaramin hannunta. Kamar yanda ya saba bai ɗaga mata na sa hannun ba kuma bai ce mata komai ba, sai kanshi daya ɗan karkata gefe yana lumshe fararen idanuwansa haɗe da jinjina mata kai.
Murmushi da ya bayyana ƙananun haƙoranta ta saki, kafin ta nufi ajinsu da ɗan gudu tana ƙara waiwayarsa.
Shima murmushin da shi kaɗai yasan yadda ya ke yin kayansa da salo mai birgewa ya saki ya na juya kan kekensa ya bar wajen.
GIDAN ABDUH DHAHAB
Tarin Tukwane sababbun ƙerawa ma su kala mai kyan gani a ido da ƙwari a hannu ne jere a ƙaton filin da yake ƙerasu, Lokaci ɗaya ido bazai iya ƙirga su ba saboda yawansu, Ƙira mabanbanta akayiwa tukwanen. Gefe guda Abduh Dhahab da siffarsa ta fi kama da na tsoho, ko mai rangwamen hankali, a tsaye, duk da fuskarsa ta ɗan ƙuruciya kan gani kasan ba wai tsufar shekaru ba ne, tsufar bautar da ya ke yi ne, da kuma rashin tsaftace jiki.
Fararen Fatar da suka zo Daular Sarki Hammam ne a gefensa, su na cinikin Tukwanen da ya jera da harshen nasararsa da ke fita fes kamar ba shi ba.
A haka Sulaim ya dawo da kekensa ya same su. Hannu ya ɗaga musu haɗe rusunar da kansa alamar gaisuwa kafin ya wuce aihinin cikin gidan su.
Yana ƙoƙarin sa ke fitowa cinikin su ya faɗa a kan idanuwansa su ka ajjiyewa Mahaifinsa kuɗi ma su yawan gaske a cikin jaka.
Mamakine ya kama Sulaim, maiyasa Mahaifinshi zai siyar da Tukwanen da saura kwana uku a ci kasuwar su? mai zai cewa mutanen da za su taso da ga maƙotan Yankunan su da mutanen Birni ma su zuwa sara? Dole yasan wata sabuwar wahalar zai ɗora mu su, su sake ƙera wa su Tukwanen, amma ta yaya hakan zai yiwu?
Ranshi a ɓace ya ƙara komawa cikin Gidan. Matar Mahaifinsa ya samu a ɗaki. Da hannu ya tambayeta ta san dalilin da ya sa Babansa ya siyar da Tukwanen da za su fita kasuwa da shi jibi ba? Alamar ba ta sani ba ta yi masa. Agogon ɗakinta ya kalla ya na fita da sauri ya bar Gidan gaba ɗaya.
ABDUH Dhahab
Bayan Fararen Fatar sun sa an ɗebe musu Tukwane,
Ƙwalla ne ya tararwa idanunsa da su ka zama jajayen ƙarfi da yaji, saboda bauta da neman kuɗi da ya ke yi tsayin shekaru ba tare ya mora ko ya bari Iyalansa sun mora ba, shi dai kawai burinsa cigaban Yankinsa.
Ɗakinsa ya wuce da tarin kuɗin. Yanayin yadda ya samu fuskar Ɗayyib jiya da ya shiga dubasa na ƙara dawomasa.
A baya Zuciyarsa babu ɗigon rauni ko tsoro sai burin kafuwar Yankinsa, amma a wannan karon zuciyarsa tsoro ne fal a cikinta, a ransa ya yanke ya zama dole ya bar Yankin a wannan karon ya haƙura saboda ba shi da zaɓi ko don ginuwar rayuwar Sulaim da shi kaɗai Allah Ya mallakamai, bayan ya adana kuɗin ficewa ya yi ba tare da ya sanar da Iyalinsa inda zai je ba.
SULAIM;
Bayan ya baro gida Makarantarsu Naila ya wuce, kasancewar su sun rigasu tashi saboda jarabawar da suka fara.
A bakin makaranta ya sa mu Naila da jakarta na buhu saƙale a kafaɗarta. Bai ce mata komai ba ya kwanto da keken ta hau. Har suka ƙaraso ƙofar Gidansu da ya ke maƙota da na su Gidan bai ce mata komai ba. Ya na sauketa dasauri ta sa ɗan ƙaramin hannunta tana lalubar jakarta, kwandala biyu ta fito da shi ta na miƙamai.
"ga shi ka siya wani abun"
Ta faɗa da ƙaramin muryarta na Yara, ta na jiran amsarsa. Saboda sarai tasan ya na magana.
Ɗan mitsitsin hannunta ya kalla da kuɗin sannan ya girgiza kai alamar a'a ya na karkata kan kekenshi alamar tafiya zai yi. Ƙin matsawa ta yi daga gurin ta na kallonshi. Har ya fara tafiya ya kasa jurewa ya juyo.
Hannunshi ya miƙa mata alamar ta kawo kuɗin. Da sauri ta miƙamai ta na dariyar da ya bayyana jerarrun ƙananun haƙoranta. Shima murmushin bazata ne ya tahowa laɓɓanshi wannan dalilin ya sa yabar wajen da zafin namansa.
Har ya rage saura kwana biyu aci kasuwa, Sulaim bai ji mahaifinsa ya yi misa zancen ƙara ƙera wa su tukwane ba, kuma bai ga alamun ya na da niyyar yin wasu ba, wannan dalilin yasa yafara zargin abubuwa dayawa har ya kasa runtsawa, musamman daya ga Mahaifinsa ya tattara duk uban dukiyar da ya ɗauki shekaru yana tarawa a cikin ƙaton buhu ɗaya.
★Washe gari jikinsa sam ba bu ƙwari ya yi shirin Makaranta ya hau kekensa ya nufi ƙofar Gidan su Naila. Tana tsaye ta shirya tsaf