x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 30 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 87001 words
  • 87720 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 751

07 Oct 2025
ta zauna tana janta da hirar da ba wani amsar kirki take samu ba.

Kaka dama Ɗakinta ta wuce, bata zauna ba.


Naila surutun Simbi ne yake hawa kanta, sam bata son hayaniya tafison ta zauna shiru ko zata samo mafitar bawa Sulaim haƙuri.

Naila tunanin tayiwa Ummi Aysha wani abu mai daɗi ta kai mata ne yazo zuciyarta, daganan sai ta sanar da ita abinda yake faruwa ko zata taimaka mata.

Da ƙwarin gwiwarta ta miƙe ta nufi Kitchen, Simbi tayi wuf ta rufamata baya.

Simbi tana maƙale a gefen Naila tana yimata hira, Nailan tana amsa mata sama-sama tare da cigaba da abinda take yi.

Da salon dakar ciki Simbi ta ce;
"Me kike haɗawa haka da safenan, ayi dani nima zanci"
"To " kawai Naila ta ce ta cigaba da aikinta.

Naila ji tayi kamar wayarta da ta bari a parlor yana ƙara, da sauri ta saki aikin tana addu'ar Allah Ya sa Sulaim ne.

Bayan fitar Naila ta wannan damar Simbi tayi amfani, kafin ta biyo bayan Naila tana faɗin;
"Yau na ga bakyason kulani, bari na koma Sashenmu sai anjima"

Haushinta da Naila take ji yasa ko gefenta bata kalla ba ta cigaba da amsa kiran Abokiyar karatunta.

Bayan Naila ta koma Madafi ta gama aikinta, wanka tayi ta shirya, har ɗaki tabi Kaka ta sanar da ita zata je ɓangaren Ummi Aysha ta dawo.

Addu'ar a dawo lafiya Kaka tayimata.

Yadda Naila ta samu sashen Ummi Aysha anata hidima ne ya sanyaya jikinta, bayan ta miƙa mata Snacks ɗin da ta nannaɗe da foil paper sai ta kasa faɗar abinda ya kawota.

Ummi Aysha, da farin ciki ta karɓi kyautar Naila, tana ɗan janta da hira. Amma bata yimata hirar Sulaim ko abinda ya dangacesa ba har Naila ta bar Sashen.

UMMI AYSHA Batasan akwai matsala a tsakanin Naila da Sulaim ba, don haka ta ajjiye abinda Naila ta kowamata domin nunawa Sulaim idan ya iso.

SULAIM
A ɓangaren Sulaim duk kiran da Naila takeyi baisan tana yi ba, saboda wayar a Silent take, batun barinta da ya ce yayi, ya faɗa ne, don ta dawo hankalinta saboda ya lura son dayake mata na naiman kawo rashin girmamawa a tsakaninsu.

★Da Asubahi aka sanar da shi ansamu Malamin daya ce a naimomai, kai tsaye ya haɗa Malamin da Malik. Bayan gama wayarsa da Malik ya ankara da tarin kiran da Naila tayi mai, maimakon ya amsa kiranta data cigaba da kira da Asubahi sai ya kashe wayar gaba ɗaya.

Kamar yadda ya tsara bayan gari ya yi haske ya kira Mahaifiyarsa ya sanar da ita zuwansa.

Ummi Aysha tayi mamakin zuwansa a irin wannan lokacin tun da bai jima da tafiya ba, sai da yayi mata bayanin uzurine zai kowasa.
Da wasa da dariya take tsokanarsa ko dai Naila zai zo gani?
Sulaim murmushi kawai ya yi bai ce komai ba har sukayi sallama.

Shirye-shiryen tarbarsa Naila ta samu anayi a ɓangaren Ummi Aysha.

Kafin Sulaim ya isa Dhahab, Malik da Mallamin da daya je ya ɗauko sun rigasa isowa.

A ɓangaren Malik bayan sun iso Dhahab da Mallam, a sashensa yayiwa Mallam masauki.
Mallamin ko hutawa baiyi ba ya ce akirawomasa Simbi.

Ko da Malik ya je, Simbi ta kulle kanta a ɗaki da sunan tana barci, da Malik ya dawo ya gayawa Mallam Simbi tana barci cewa yayi su tasheta, idan taƙi tashi su kirasa..

Lokacin da Sulaim ya iso ƙasar Abyad a sirrince aka ɗaukosa zuwa Dhahab babu chunkoson jami'an tsaro da yawan Motoci.

Ɓangaren Ummi Aysha ya sauka kamar waccen karon.

Ummi Aysha bakinta ya kasa rufuwa sai fara'a takeyi, tana jansa a jiki.

Abincin data shiryamai da kanta ta gabatarmai har da Snacks ɗin da Naila ta kowamata masu kyan gani a ido ta jera a gefe.

Maimakon ya ɗaibi abinda yake gabansa, sai ya kai hannunsa kan Snacks ɗin da sukayi matuƙar burgesa.

Ummi Aysha dariyarta ta ƙunshe tana jiran yakai bakinsa sannan tayimai tsiyar wato Naila ta gayamasa ta kawo mata Snacks shine zai ajjiye nata girkin ya fara dana Naila.

Ya na kaiwa baki ya gutsira ya tauna ya haɗiye.

Dariyar Ummi Aysha ta saki tana yi mai tsiya ba tare da ta lura da sauyinsa ba.

A hankali ya jingine bayansa da kujerar dayake kai, Fuskarsa ya sunkuyar ƙasa, kafin wuyar ya karye kamar wanda barci ya kwashe a zaune.

Dariyar Ummi Aysha ne ya ɗauke lokaci ɗaya, ta miƙe ta nufosa tana faɗin;

"lafiyarka Sulaim menene haka ka karya wuya, kayimin magana mana!"