ya faru da Abduh da Sulaim? Da gaske sun mutu? Wanene ya kashe su? Wanene ya yankewa Dattijo Junaid harshe? Wanene Abdallah kuma wanene ya ƙullamai sharrin fyaɗe? Da gaske Salman ya mutu, wanene ya kashe shi? Idan da gaske ya mutu to wanene Uzair?
Ya ya akayi Malik ya yi kuɗi?
ABDUH DHAHAB; tun da ya kalli fuskar Ɗayyib lokacin da ya je dubashi a Gidan Jalal, maganganun da Abokin Ɗayyib ya faɗamai a sirrince ya faɗomai na Ɗayyib yana son ganin bayansa ya shirya sayar da komai ya bar garin ya hana shi sukuni.
A take Abduh ya yankewa kansa shawarar tafiya amma ya yi alƙawarin ko ya tafi zai turo wakilin da zai kawowa Yankinsa cigaba, domin da wannan kuɗirin Iyaye da Kakanninsa suka rasa Ransu.
Tun bayan sayar da Tukwanensa ga Baƙin Turawa, ya je Iyakar Yankin Tudu ba tare da sanin kowa ba, ya kira Abokanan Kasuwancinsa da suke mutunci su Naima mai Matsuguni a ƙasar Abyad.
Tunda ya dawo a ranar yake tsammanin zuwan wani daga Masarautar amma ya ji shiru.
Bayan kwana biyu da wannan Mutanen Masarautar Yankin Tudu suka cimmai.
Baisan san da Sulaim ya tashi ba, amma ihun Sulaim na farko ne ya tashesa. Tsaf ya ke kallon yadda Ɗayyib yake yankarmai jikin Ɗa mafi soyuwa a garesa domin ta muryarsa ya gane Ɗayyib ne.
Bai motsaba domin bashi da ƙarfin yaƙar su saboda yasan bashi kaɗai bane dole akwai wasu. Sai dai cikin ikon Allah, hankali Ɗayyib ya kai kan Iyalinsa Mairam. Ɗayyib yana tafiya wajen Mairam Abduh ya sanɗa ya fara jan Sulaim a hankali dai-dai lokacin da Mairam take kallonsa, saɓa Sulaim ya yi a kafaɗa yana jan buhun kuɗin da yake rinjayarsa a hankali.
A hankali ya bi ta ƙofar baya ya isa gidan Mallam. Mallam da ya riga yasan da batun shirin Masarautar Yankin akan Abduh kamar yadda Abduh ya sanar mai a tsakar gidan yake sallar dare ba ya komawa cikin ɗaki har sai yayi sallar Asubahi ko Allah zaisa Abduh ya ƙwanƙwasa.
Don haka Mallam yana ji an ƙwanƙwasa ƙofa ya buɗe da sauri kafin ya nufi kekenunsa, da ƙarfin hali Abduh ya iso wajen Mallam da sauri.
Mallam shi ya ɗauki kuɗin Abduh ya goya a baya kekensa, shi kuma Abduh tuni ya nufi Asibiti da Sulaim da ɗaya keken.
Mallam saƙon Iyalinsa ta tafi Yankinsu ya bata idan Asubahi tayi, zai biyo bayansu idan ya dawo.
Bayan sun isa Mallam a gaggauce ya ɗaurewa Sulaim ciwo ya ce;
"Abduh ku tafi wataƙila su iso garemu, bana so su cimmana, In Shaa Allahu wata rana zamu sake haɗuwa ka ji" ya ƙarasa faɗa da rauni a muryarsa. Kuka Abduh ya fashe dashi yana ƙara saɓa Sulaim a kafaɗarsa. Suna tafiya suna kuka, sai da suka ɗanyi nisa kaɗan sannan Mallam ya ajjiye buhun kuɗin yana kallon Abduh kafin ya fashe da kuka, Abduh yana kiransa da magiyar ya dawo ya bashi kuɗi amma Mallam bai juyo ba sai hannu daya ɗagamai.
Da gudu Mallam ya ƙaraso Asibitin sai dai yana buɗe ofishin likita ya samu ƴan shaye-shayen wasu Yankin su uku maza a zaune wai suna neman likita, yana zuwa Mallam ya ce musu ya nufi hanyar fita domin zuwa Gida. yana fitowa yayi cikiɓus da su Ɗayyib.
Zage-zage da neman da suke yiwa su Abduh yasa ƴan shaye-shaye neman maɓoya gudun karsu kashe su, sai dai tura Mallam ciki tare da sanyawa Asibitin wuta ne yayi ajalinsu dukka.
Wannan dalilin yasa aka samu gawar mutum huɗu.
Nannaɗewar Ɗayyib cikin abun rufa na da alaƙa ne da ƙarfen da Sulaim ya cakamai gudun Iyalinsa da mutanen gari su sani, dama kuma ya ƙirƙirarwa kansa ciwo ne, don kawar da hankalin Mutanen Yankin daga kansa, Surutai da Kukan da yake yi duk don ya kawar da zargin mutanene a kansa tunda kowa yasan shi ɗin Aminin Abduh ne.
Tun lokacin da Dattijo Junaid ya ɓullo da zance bincike aka waɗanda suka sakawa Asibitin Mallam wuta, Bashar ƙani ga Jalal uwa ɗaya uba ɗaya ya fara shirin kawo ƙarshen Dattijo Junaid. Sai dai sun tsayar da shawarar kashesa ba mafita bane, Bashar da kansa ya kawo shawarar a cirewa Dattijo Junaid harshe, kuma ya jagoranci Ƙattin matasan da suke yi musu aiki har gidan Dattijo Junaid. Bayan matasan sun banƙare Dattijo Junaid, Bashar da hannunsa ya yankemai harshe. Tare da gagargaɗin idan ya bari kowa ya sani ko ya ƙara tsoma baki akan mutuwar su Abduh kansa zasu cire.
Abduh ya ci baƙar Azaba shi da Sulaim. A jeji suka kwana, sai da gari yayi haske suka samu amalanken daya fitarsu da su Iyakar Yankin tudu.
Ba su yi minti biyu da zuwa ba Abduh ya naimi mai maganin gargajiya domin duba ciwukan Sulaim, saboda duk azabar dayake ji baya magana sai rawa da jikinsa yake yi.
Duk irin jan da Abduh yake yiwa ƙaton buhun hannusa babu wanda ya kawo zunzurutun kuɗi ne a ciki.
A lokacin babu masu musayar kuɗi a Iyakar Yankunan balle ya canza su zuwa na Ƙasar Abyad, kuma tsoron kai kuɗin Ɗan ƙaramin Bankin da ke gurin yake yi kar wani ya cucesa. Cikin ƙasa da hour biyu Sulaim ya samu Barci a rumfar mai maganin da suka raɓe. Shima mai magani bai san kuɗi bane a ƙaton ɓakin buhun wajen Abduh har yamma tayi suka samu Motar Kayan da zai tafi Birnin Abyad.
A bayan mota Abduh da Sulaim sukayi tafiyar kwanaki. Ko da suka isa, a bayan garin Abyad suka naimi matsuguni.
Washe gari da tambaya Abduh ya samu addireshin Abokin kasuwancinsa daya kira a waya.
Harun ɗan asalin Abyad ne da ƴaƴansa biyu Abdallah da Bushra.
Bayan sun haɗu da taimakon Harun suka kai Sulaim asibiti. Har suka gama hidimar Asibiti Abduh bai nunawa Harun tarin kuɗin da ya zo da su ba saboda tsoron kowa yake ji.
A lokacin Abdallah babban ɗan Harun saurayine daya yi karatun likitanci yake kan naiman aiki Bushra kuma tana ƴar mitsisiya.
Bayan kwana biyu
Abduh ya kasa daina tunanin mutanen Yankinsa da su yake kwana yake tashi. Cikin girmamawa Abduh ya roƙi alfarmar Abdallah yaje Yankin Tudu ya koyamusu aikin likitanci da zasu dogara da kansu, ya yi alƙawarin biyansa duk wata.
Da farko Harun bai amince ba amma dayaga Abduh ya lissafo kuɗin wata biyar ya bawa Harun ya canza zuwa na ƙasar Abyad, a take suka shirya tafiyar Abdallah.
A wannan lokacin ne Abdallah ya bayyana a Yankin Tudu a matsayin jami'in jinyar da Gwamnati ta turo.
Ɗayyib da kansa yayiwa Yarinya fyaɗe ya ajjiyeta a bayan ofishin Abdullah.
A wacce lokacin Harun Abokanan hulɗarsa na bakin Iyakar Yankin ya tura suka ɗauko Abdullah a Yankin Tudu, domin tun a daren da abun ya faru bayan Abdallah ya dawo hayyacinsa ya kira waya ya sanar.
Bayan Abdullah ya tsira daga Mutanen Yankin Tudu
Daga lokacin Harun Mahaifin Abdallah ya tattara komai nasa ya bar su Abduh batare da ƙara waiwayarsu ba.
Jin mutuwar Mallam a bakin Abdallah yasa jikin Abduh ƙara rikicewa kullum ba shi da aiki sai kuka..
Sulaim baya magana, komai Mahaifinsa ya yanke dai-dai ne, sai dai a gaɓar da mutanen Yankin Tudu suka ƙullawa Abdallah sharri suka kashe Mallam Sulaim ya cewa Mahaifinsa ya kamata ya manta da al'amarin mutanen Yankinsu su fuskanci rayuwar da take gabansu, domin komai yawan kuɗin da yake tunanin ya tara wata rana zai ƙare.
Tunanin halin da mutanen Yankin Tudu suke ciki da wanda Mallam yake cikine ya kwantar da Abduh ciwo duk da nasihar da Sulaim ya yi masa, sannan Bautar da ya kwashi shekaru ya na yi ba tare da hutawa ba ya taka rawar ganin kwantar da shi jinya mai tsaho.
A lokacin Sulaim ya fara fuskantar rayuwa, ya kuma tsaya tsayin daka domin gina Dhahab ɗin da Jamil yayi alƙawarin rusawa.
Da farko buhun kuɗin Mahaifinsa ya ɗauka zuwa kasuwar canjin da suke yawan zuwa da Harun, saboda kaɗan-kaɗan Abduh yake canza kuɗin har Harun ya gujesu bai taɓa sanin akwai dukiya mai yawa a tare da Abduh ba.
Wuƙa Sulaim ya soke a ƙugunsa. Su kansu masu canjin sai da suka tsorata da irin kuɗin da Sulaim ya kawo a buhu, bayan sun canza masa ya ƙara ɗuresu ya taho gida. Ashe wasu sun biyosa sun ga Gidan.
A wannan dare ƴan daban da aka turo daga kasuwar canji suka farmaki Sulaim ya kawo kuɗin da ya canzo.
Sulaim ya yi yanke-yanken daya ƙara gusar da imaninsa a wannan dare domin bai barsu sun tsira da ko sisi ba. Duk Abduh yana kwance jikinsa babu ƙarfi sai kuka da yake yi.
Sulaim sai da ya share sama da sati baya barcin dare na ranar ma na lokaci ƙalilan yakeyi, suma ɓarayin haka suka share kwana uku suna zuwa su yayyaki juna da Sulaim, ƙarshe su gudu babu ko sisi.
A fuska Sulaim sai ya koma kamar Ɗan daba saboda ƙaton Yankar da ke tsakanin kuncinshi da idonsa.
Mai mota ya nemo suka tattara kayansu zuwa cikin Birnin Abyad, a ranar Sulaim ya binciki ofishin dillacin gidaje suka kama gida mai sashe-shashe.
Washe gari da tambaya Sulaim ya samu Banki bayansa ɗauke da Abduh a goye. Bayan ya buɗe komai ya wuce da Babansa Asibiti.
A Asibiti Sulaim yake kwana, har Abduh ya yi sati biyu suka tattaro suka dawo gida ba don ƙarfin jikin Abduh ya dawo gaba ɗaya ba, sai lallaɓawa da yake yi.
A ranar da Sulaim ya ƙarasa kai dukka kuɗaɗensu Banki tunda kaɗan-kaɗan yake kaiwa, a ranar ya yi fafutar neman maƙera a Birnin Abyad.
Ƙaramin ma'aikatar ƙera Tukwane na Salman Ɗan asalin ƙasar Abyad mai ƴaƴa ƴan biyu Maza Zubair da Uzair Sulaim ya samu. Sai dai bai ɗaukesa aiki ba ya ce yaje ya dawo.
★washe gari da Sulaim ya koma, Salman ƙin kulasa ya yi acewarsa Sulaim kama yake yi mai da Ɗan daba kar ya zo ya kasheshi ya kashe mai ƴaƴan da yake ji dasu....✍🏻
[8/8, 8:36 AM] nafisaaliyusasaal: SASAAL
4
Haka Sulaim ya haƙura ya dawo Gida.
Bai haƙura ba, kullum ya na gama hidimar Mahaifinsa sai yaje gaban ma'aikar maƙeri Salman ya zauna.
Tun maƙeri Salman bai amince da Sulaim ba har ya haƙura ya bashi dama.
A ranar da Sulaim ya fara yi musu Tukwane Salman ruɗe ya yi yana tambayarsa daga ina yake, Sulaim bai iya surutu ba don haka amsoshinsa sam basu gamsar da Salman ba, wannan dalilin yasa yace yana son ganin Mahaifinsa da ya ce suna tare.
Sulaim bai musa ba, ya kaishi har Gidansu.
Cikin bayanin da Salman zai gamsu Abduh da damuwa da ciwo suka ramar da shi yake bashi labari. Sosai Salman ya tausayamusu ya kuma ɗauki nauyin abincin cin su kullum, domin Abduh bai sanar da shi akwai tarin dukiya a tare da su ba.
A zaman wata ukun da Sulaim ya yi da Salman da ƴaƴansa Zubair da Uzair ya gane mutane ne masu amana da dattako, don haka Sulaim ya samu lokaci ya tattauna da Mahaifinsa Abduh kan jan Salman a jiki su ƙirƙiri Ma'aikata mai girma da dukiyarsu da ke ajjiye.
Kai kawai Abduh ya ɗagawa Sulaim alamun ya amince, Sulaim yakai minti biyar yana kallon Mahaifinsa shima yana kallonshi, kowannen su yana kallon iri lalacewar da Ɗan uwansa ya yi, ba su da kowa ba su da kwanciyar hankali, Harun da suka sani ya gujesu.
Kukan da ba kasafai Sulaim ya cika yi ba, ya saki yana rungume Mahaifinsa.
Shima Abduh kuka yake yi yana cewa ;
"Allah Ya zama gatanka Sulaim yasa maka albarka a duk abinda ka sawa hannu, duk tsananin karka manta da mutanen Yankina idan ka samu sukunin rayuwa ka naimi Kakarka da Mahaifiyarka ka faɗa musu irin ƙewarsun da na yi, idan Allah Ya ƙaddara haɗuwarku da Mairam ka roƙamin yafiyarta. Iyalan Mallam suma ka nemesu ka ji halin da suke ci. Gwargwadon samunka gwargwadon kyautarka Sulaim karka gajiya, Allah yana tare da Kai, ko bayan raina inaso ka kafa Dhahab ka raya mutanen Yankina a cikinta, kayi aure ka hayayyafa, sannan ka faɗa musu har bayan barowata Yankinmu ban daina son su da begen su ba, na roƙeƙa Sulaim, idan da hali ka tura Yankin Tudu wani ya koyamusu ƙera Tukwanen da zasu dogara da kansu kayimin alƙawari!" Sulaim wani irin juyi yayi da Kansa yana zaro Mahaifinsa daga jikinsa, laƙwas Abduh ya yi yana kallonsa da fararen idanuwansa da suka ƙara haske alamun alƙawarinsa ya ke jira.
Cikin kuka Sulaim ya ce; "na yi alƙawari amma dan Allah karka tafi ka barni Baaba ba Ni da kowa"
"Ka na da Allah Sulaim! Sannan ka tuna Naila? ƴar gidan Abokin Mahmoud?" gane wayo yake son yimai yasa ya girgiza kansa yana kamo hannunsa.
A wannan rana daƙyar Sulaim ya fita aiki.
Ko da ya je wajen aiki yakasa yin komai balle su tattauna da Salman kan zuba jarin da sukayi magana da Mahaifinsa. Yamma na yi ya taho gida bayan ya biya ya siyowa Babansa kayan marmari.
A kwance ya samesa kamar kullum, sai dai daya mirginasa ya gane dagaske wannan Baaban daya rainesa da izinin Allah ya wahala kan bauta da ƙera Tukwane don cigaban mutanen Yankinsa ya yi barcin da ba zai ƙara farkawa ba anan gidan duniya ba.
Hannunsa dayake wani irin rawa yasa ya kamo farar Fuskarsa Mahaifinsa daya koma ɗan siriri ya bushe. Rayuwarsu na Yankin Tudu ne yake dawomai da yadda Mahaifinsa yake bugun ƙarfe dare da rana, yau gashi ya mutu bai mori ko sisinsa ba, Sulaim hawayensa basu gusheba har sai suka jiƙa gaban rigarsa.
Bayan mintuna Sulaim ya saɓa Abduh da jikinsa ya saki gaba ɗaya, zuwa Asibiti ko zasu ce mai dogon suma ya yi.
Da gaske Abduh ya mutu ya bar Sulaim cikin maraici!
Sulaim ya yi kuka irin kuka da har duniya ta tashi bayajin zai ƙarayin irinshi. Da taimakon Salman da mutanen Ma'aikatarsa aka binne Abduh.
A tsakanin kwanakin da Sulaim ya rayu shi ɗaya ya fuskanci kuɗi suna gaba da komai a rayuwar wasu Mutanen, na wasu Mutanenma muninsa ya yi yawa. Kamar Salman tunda ya turo su Zubair sau ɗaya bai ƙara turosu ba balle ya zo da kansa acewarsa aiki ya yi musu yawa a Ma'aikata.
Idan har kuɗine sune gishinƙin da zai cika masa burikansa mai zai hana ya neme su?
Cikin tsanani da wahala Sulaim ya fara gwagwarmayar kafa kansa da zuciya da ƙwanjinsa bai bi takan komawa Makaranta ba tukunna har sai komai ya dai-daita.
Garin shiga can faɗa nan Sulaim ya samu mutumin da zai taimakamai ba tare da yaƙarabin takan Salman ba. Cikin ƙanƙani lokaci tunda da kuɗi masu yawa a ƙasa Sulaim ya fara kafa Ma'aikatar Sarrafa shinkafa.
A kwai mabaratan da suke yawan zuwa bakin ma'aikatar tun kafin gininsa ya yi nisa, wata rana Sulaim ya taho da Baturen da aka haɗashi da shi zai taimakamai, ya gane ashe su Malik ne.
A yadda ya tsani duk wani jinin Yankin Tudu baiyi niyyar kulasu ba, sai dai tuna wasiyyar Mahaifinsa yasa ya isa garesu.
Da farko sun tsorota tare mamakin dama basu mutu ba suna raye?
Mahaifin Malik da suke Bara tare yayi kuka da yaji labarin mutuwar Abduh, shima Sulaim ya tausayamusu jin tsahon lokacin da suka ɗauka a Birnin Abyad suna Bara tare da kwana dukkansu a ɗaki ɗaya. Daga wannan rana su Malik suka samu muhalli mai kyau.
Malik da Iyayensa sun san halin Sulaim tuntuni balle yanzu da yake jinsa shi kaɗai a duniyarsa, dalilin wannan yasa suka zaunar da jununsu suka yiwa kansu nasihar riƙon amana da riƙo da gaskiya komai ɗacinta.
Labarin kafuwar Ma'aikatar Sulaim ne yasa Salman naimansa da kansa, ya kuma baiwa Sulaim haƙuri. Sulaim bai manta halaccin Salman ba kuma ya yi masa uzuri tunda da ma'aikatar suke ci suke sha, sakaci dashi kan damuwarsa shi kaɗai zai iya rusa masu kasuwancinsu.
A cikin wannan tsukin Harun ya ƙara dawowa, daƙyar Sulaim ya sauraresa suka dai-daita shima da yaji mutuwar Abduh har da kwanciya a gadon Asibiti.
Har Yankin Tudu Sulaim ya tura Malik ya sirrince, ya kwaso rahoton halin da Yankin yake ciki. Malik ya dawowa da Sulaim mummunar labarin irin talaucin da mutanen Yankin suke ciki.
Kamar yadda Mahaifinsa ya roƙesa kafin ya bar duniya Sulaim ya samu Salman da batun tura wani Yankin Tudu ya koyawa Mutanen Yankin ƙera Tukwanen da zasu dogara da kansu.
Cikin kasada Salman ya amince Ɗansa Zubair ya je ya koyamusu ƙera Tukwanen da Abduh yake yi kamar yadda Sulaim ya koya musu tuntuni. Sai dai Uzair ne zai fara zuwa tunda yafi Zubair iya tsara kalami, idan yaso idan suka bashi masauƙi sai ya dawo Zubair ya zauna.
Zubair shine ya rayu a Yankin Tudu da sunan Mahaifinsa Salman, yawancin maganganun Abduh da yake yi Malik ne yake faɗamai ta ɓoyayyiyar wayar da ya tafi da ita.
Bashar da muƙarabansa har da Jalal su sukayi ta'asar kashe Zubair da Dattijo Junaid, wuƙa suka ɗan sokawa Ɗayyib gudun tonuwar asirinsu.
A daren da abun ya faru labari yajewa Malik ta hanyar waɗanda ya saka gadin lafiyar Zubair.
Dama kuma a daren suka iso iyakar Yankin domin tafiya da Zubair, kafin labari ya isa kunnen Sulaim da baya ƙasar Abyad Malik ya yanke nasa hukuncin akan Bashar .
Lokacin da gawar Zubair ya isa ga ɗan uwansa Uzair da mahaifinsu Salman sunyi kuka, tare da tsanar Yankin Tudu da mutanen cikinta.
ƊAYYIB
Baƙin cikin bayyanar hannun Bashar a cikin kisansu Abduh maimakon ya nuna bai san wanda ya yanke masa harshe ba ne ya tunzura zuciyar Ɗayyib, har ya shaƙawa Bashar gubar daya tanada tuntuni a aljihunsa lokacin da suke yunƙurin kaishi Asibiti. Dama ya tana de shi ne idan har ya tabbata da gaske bayanin ɗaya daga cikin iyalin Abduh Bashar yake kwatantawa, Gara ya mutu daya tona musu asiri.
Mairam Matar Abduh Dhahab a ranar data fara magana ɗan leƙen asirinsu ya kai musu labari, a daren ranar ya tura ƴan daba su kashe Mariam, fitowar Mahaifiyar Naila kama ruwa ne yasa suka ɗauka Mairam ce, don haka suka farar sararta ta ko ina har sai da ya daina numfashi, Iyayen Mairam da sukayi laƙwas a ɗakunansu, ƴan daban suna tafiya suka fito suka tattara kayansu suka bar Yankin.
Ɗayyib Babu irin bincike da naiman da baiyiwa Sarah Matar Mallam ba, amma babu wanda yasan duniyar da suke.
Menene burinsu Ɗayyib? Su kashe sunan Dhahab su kuma samu ɗaukaka da dukiya ko da jinin dukka mutanen Yankin zai salwanta, su dasa tsoro a ran Mutane yanda zasuci karansa babu babbaka ba tare da