Duk da, da zazzaɓi ya kwana hakan bai hanasa yin mafarkai masu daɗi riskar barcinsa ba, sai ya ke jinsa kamar lokacin da Mahaifinsa yake raye suke rayuwar ƙere-ƙerensu a Yankin Tudu.
Ba iya son Abota yake yiwa Naila ba kamar na shekarun baya, son aure yake yi mata idan zata amince da alƙawarinsa..
Kafin gari ya yi haske zazzaɓin jikinsa ya sauka, Da abin karin Ummi Aysha ya karya. Ummi Aysha murmushin fuskarta ƙim ɗaukewa ya yi har ta bar sashen saboda daɗin yadda Ɗanta ya saki jiki da ita.
Bayan fitarta Malik ya ziyarceshi...
Da Muryar da zai fahimcesa dakyau Malik yake yimai bayani akan su Ɗayyib karon farko tun bayan haɗuwarsu, saboda Malik ya na ganin Yaƙine da bazai iyashi shi kaɗai ba.
Bayan Sulaim ya gama saurarar Malik kansa ya ɗago yana dangana wayar hannunsa ga ƙaramin table ɗin dake gefensa.. ya ce;
"Wa su burika ka taɓa sanar da ni Naila tana da su ma? sannan Menene hukuncin da kake ganin ya dace a yiwa Ɗayyib"
Sulaim ya tambaya yana kallon tsakiyar idon Malik.
Kai Malik ya ɗan sosa, a ganinsa bayaninsa ba shi da haɗi da burin Naila amma sai ya daure ya ce;
"Burinkanta biyu ne, cigaban Yankinmu da kuma samun tabbacin kana raye ko Dagaske ka mutu, ina ganin kuma ai muradanta sun cika, Ɗayyib kuma kasheshi shine hukuncin da ya dace da shi"
Kai Sulaim ya ɗan karkata gefe ya ce;
"A mayar da Ma'aikatar Tukwanen ZINARE tushen da aka ƙirƙiresa, duk wanda zai siya ya je har Yankinmu ya siya, Sufyan nake so ya zama GM sauran naɗe-naɗen yana hannunka, daga yau nakeson komai ya fara aiki. A filin da aka fara cinikin Tukwanen a filin za'a kafa Ma'aikatar. Ɗayyib kuma abarsa tukunna"
Sulaim ya ƙarasa faɗa yana miƙewa haɗe da ɗaukar wayarsa ya bar ƙwaƙwalwar Malik da lissafi.
Mayar da Companyn Dhahab na ɓangaren Tukwane na nufin burin Naila ya kammalu domin Yankin Tudu zai zama babban Yanki kuma kowa zai samu aikin yi Matasa Maza da Mata.
Bayyanar babban Maka'aitar Tukwanen Zinare da a yanzu a ƙasar Abyad ya fi rogowar shigowa da Sulaim kuɗi a Yankin Tudu da naɗa Sufyan a matsayin GM na nufin bugawar zuciyar Ɗayyib da Jalal... Idan ya fahimci Sulaim so yake yi su mutu da baƙin cikin abinda suka kasa kawo ƙarshensa..
Dariyar mugunta Malik ya saki har hawaye na tararwa gefen idonsa, Da zafin naman fara aiki nan take ya miƙe ya na zaro wayarsa ..
Misalin biyar na Yammaci Sulaim ya shirya cikin guntayen ƙananun kayan da suka dace da siffarsa, ƙafafuwansa sanye da Miami mule ɗin daya ƙara musu kyau.
Babu iso tsakaninsa da sashen Mahaifiyarsa, don haka ya fara shiga ya duba lafiyarta tare da shaida mata hukuncin da ya yanke a kan Ma'aikatarsa.
Ummi Aysha jin abin tayi banbarakwai yau Sulaim ya shaida mata wani yunƙuri nasa akan dukiyarsa, dariya ta saki tana nuna jinɗaɗinta, kafin addu'o'in nasara su biyo baya.
Domin ƙaramai ƙarfin gwiwa ta ce;
"Da Abduh yana raye, wannan yunƙurin naka sai ya zama babban abin alfahari a gareshi, Allah Ya kai rahama kabarinsa"
A hankali Sulaim ya ce;
"Amin"
Ƙwarin gwiwarta gareshi sun taɓasa don haka ya share sama da hour a sashenta, tana yi mai hira yana murmushi.
Ya yi godiyan tare da nuna jindaɗin yabonta akansa.
Ummi Aysha bata barshi ya tafi ba sai da ta shiryamai abu mai sauƙi ya sawa cikinsa.
Ummi Mairam; leɓunanta har rawa suke yi saboda maganganun da suka cika bakinta da zuciyarta, bayan surutun da take yi lokaci zuwa lokaci ita ɗaya.
Tana jin tsayuwar Motar da take kyautata zaton Sulaim ne ta miƙe da sauri.
Saboda rawar jikin tarbarsa har tuntuɓe ta yi, bai lura ba balle ya tareta don haka ta kife ƙasa.
Bata damu ba ta miƙe tana kama hannunsa zuwa ɗaya daga cikin Couch ɗin dayake parlon.
Babu cikakken nutsuwa balle karantar yanayin mutum ta fara zazzago abubuwan da suka daɗe suna damunta.
Bayan ta gama ta sako masa zancen Barirah kamar wacce ake kora..
Ɗan nisawa Sulaim ya yi sannan ya ce;
"Bansan mai irin sunan da kike magana akai ba, amma maganar ya tsaya a iya na yau, ba ni da muradinsa"
Da sakakken leɓunanta da yawu ke ƙoƙarin biyowa Ummi Mariam take bin Sulaim da kallo.
Ɗan raɓo jikinsa mai ƙamshi yayi ya ɗan rungumeta sannan ya bar sashen.
Mahaifinta da ke laɓe ya na jin komai da sauri ya fito, dalilin haka yasa tayi saurin shanyen yawun da yake ƙoƙarin zubowa gaban rigarta, kafin ta fashe da kuka..
SASHEN UMMU MALIK
Bayyanar Sulaim a ɓangaren Ummu Malik ya ƙara tsuma soyayyarsa a zuciyar Barirah, tare da bawa Simbi ƙarfin gwiwar ƙulla Abota da Naila..
Kamar yadda bai naimi iso a sashen Mahaifiyarsa ba haka ya nufi sashen su Naila.
Har bakin ƙofarsu Driver ya kaishi, kafin ya kaiga saukowa mai tsaron ƙofar har ya danna alamar zuwan baƙo...
Kaka ce ta buɗe, ta na ganin Sulaim ta saki fuskarta, har tsakiyar living room ɗin tayi masa Rakiya, kunyar jin sautin faɗuwar cokalinta da suka ji jiya na kamata, Naila da batasan da zuwansa ba, daga madafi ta fito hannunta riƙe da kofi mai kyau, haɗin kayan marmari ne a ciki tana sha, tana bawa Kaka labari..
Sauyin ƙamshin living room ɗinsu yasa ta fara raba idanuwanta, tana ganinsa ta tafi da gudu ta zauna a gefensa tana dariya.
Kaka dake kallon Talabijin da rabin ido ɗaya rabin a kansu dariya ta saki.
"Ina wuni" Naila ta faɗa tana kallon fuskarshi, lumshe mata ido ya yi alamar ya amsa.
Idon da ya amsa dashi ta kalla kafin ta saki dariya.
Naila har cikin zuciyarta ta ce;
"Idan ka tafi zan yi ƙewar idanuwanka"
Sulaim ƙara zaresu ya yi yana juyasu.
Dariya mai ban sha'awa Naila ta ƙyalƙyale da shi. Shima murmushin ganin farin cikinta ya saki yana karɓar kofin hannunta.
"You prepared the fruits yourself?" Ya tambaya ya na jiran amsarta.
Da sauri Naila ta amsa.
Ba tare da naiman wani cokalin ba ya kai cokalin ciki bakinsa..
Ɓata fuska ya yi yana girgiza kai alamar babu daɗi, a haka ya shanye yana girgiza kai, Naila da ta gane wasa yake yi mata, madubi ta mayar da shi tana murmushi.
Kaka tuni ta daina fahimtar abinda take kallo, gaba ɗaya hankalinta da rabin idonta yana kansu..
Naanah ya kira Video call, ya kamo hannun Naila ta dawo kusa da shi sosai.
Naanah murmushi take yi tana kallonsu.
A hankali ya ce tayi guessing wacece wannan ya faɗa yana nuna Naila.
"Naila??" Ta ambata da sigar tambaya. Ɗaga mata kai ya yi yana dariya.
Tsananin kamanceceniyar Sulaim da Naanah yasa Naila ƙura mata ido, cikin kokwanto Naila take tambayar wacece ta haifesa "Naanah ko Ummi Aysha?" Dariyar mara sautin da Naanah ta jima ba tayi ba tasa, son Naila da burin aurensu da Sulaim na ƙara samun matsuguni a ranta.
Sun ɗan jima suna waya don har da Kaka suka gaisa kafin su yi sallama.
Da ya tashi tafiya har ƙofa Naila ta rakoshi. Sallamarsu taƙaitacciya ce, don haka Naila ta dawo ciki ranta fari fes...
★washe gari saƙon sabon waya da saƙon farin Takarda ya riski Naila.
Da mamaki take kallon wayar da farin envelope ɗin, a tunaninta zamani yasa an daina rubutu a takarda sai ta hanyar waya da sauransu.
Daƙinta ta shige ta kullo kanta. Saboda Yadda ta matsu da sanin abinda takarda ya ƙunsa bata wayar da aka aiko tare da shi ba.
Ga abinda wasiƙar ta ƙunsa
"WASIƘAR ALƘAWARI
Amintata ƙalilan ce, saboda da Aminta ake kai mutum ƙasa. Inajin nutsuwa a raina tun ranar da na ganki Naila! Amma nutsuwata ba zata tabbataba har sai kinyimin alƙawari!
Ba na ci ko sha daga kowa sai Naanah da Mahaifiyata, sai kuma Malik, da ke dana yarjewa. Bazan rabaki da Kaka ba, amma kiyimin alƙawari bayan Kaka bazaki Aminta da kowa ba, har ƙarshen rayuwarmu.
Rashin Aminta ba yana nufin yanke zumunci ko ƙin kyautatawa amma yana nufin tsantseni da kiyaye sirri.
Na koma da ƙewarki da sonki mara iyaka a cikin zuciyata Naila! ba kuma zan dawo ba har sai kin ɗauki alƙawari, domin ki fahimci girman alƙawarin da zaki ɗauka yasa na rubatashi da alƙami, ki kiranta har iyakar yadda zaki fahimta..
Idan baki gamsu ba, ki sanar da ni, hakan ba zai dakatar da ni daga kula dake ba har bayan rayuwarki da Ahalinki.
SULAIM ABDALLAH"
Naila ta maimaita karanta saƙon Sulaim ya fi sau uku, da ta rasa yadda zata yi sai ta nufi wajen Kaka.
Kamar Kaka zata ƙumeta haka take kallonta kafin ta ce
" da wacce dama Sartaj ya samu hanyar ciyar dake sihiri?"
"Da damar amintar da mukayi da shi" Naila ta bawa Kaka amsa muryarta a sanyaye.
"To ba Sulaim ko ni saikin ɗaukarmin wannan alƙawarin Naila"...✍🏻
Gobe Asabar hutu In Shaa Allah 🤗
[9/5, 8:52 PM] Maman Amatullahi: SASAAL
13
ƊAYYIB;
kwanan su biyu aka sallamo Jalal da ɗauraren ciwo, domin ya ce shi ba zai yi zaman jinya a Asibiti ba.
Har Jalal da Ɗayyib suka iso Gida zuciyar kowannensu a ƙuntacce cike da ƙudirin ramuwar gayya ko ta halin ƙaƙa.
Babu wani mutum ɗaya da Jalal ya lamuncewa zuwa dubashi ciki harda Sarki Hammam. A ganinsa Sarki Hammam ba shi da wani amfani shi da fadawansa da mutanen gari baki ɗaya, tunda suka kasa kawo masa ɗauki ko ɗaukar mataki cin zarafin da Malik ya yi masa har cikin Gidansa.
Sufyan kuwa sunyi masa mummunan shirin da duk ranar da Allah Ya ƙaddara haɗuwarsu sai dai wani ba shi ba.
Bayan kwanaki
Harajin da ya tashi hankalin kowa Ɗayyib ya ƙaƙabawa Kasuwar Tukwanen Zinare. Mutanen gari har gaban Sarki Hammam suka kai kokensu. Sarki Hammam haƙuri yasa aka ba su tare da yi musu alƙawarin duba kokensu.
Da dare yayi Sarki Hammam ya buƙaci ganin Ɗayyib a keɓantaccen wajen hutawarsa.
Ba a matsayin Ɗan uwa ya bashi Umarni ba a matsayinshi na Sarkin Yankinsu ya bashi umarnin ya janye harajin da ya ƙara ƙaƙabawa Mutanen Yankin.
Ɗayyib bai cewa Sarki Hammam komai ba, har ya tashi daga gurin, ɓakar zuciyarsa na suya.
★washe gari gaggamin ɓata garin wasu Yankunan Ɗayyib ya gayyato suka zo suka shafe duk wasu rumfuna na Kasuwar.
A take suka kewayeshi da guntun langa-langa, aka fara fitar da ɗakuna a ciki.
Dattijawan Yankin ne suka yi gangami har cikin filin, Ɗayyib yana zaune fuskarsa a ɗaure kamar an musanyoshi.
Cikin Taushin harshe Dattijon da ya jagoranci gangamin ya ce;
"Ka tuna wannan filin magajinsa Abduh Dhahab tuni ya sadaukar mana da shi a matsayin Kasuwar da zamu gina Yankinmu ta hanyar samun kuɗin shiga, nuna iko da kangeshi domin buƙatar kanka kai kaɗai rashin adalci ne Ɗayyib, kuma zaka tauyemana rayuwarmu har da na Ƴaƴanmu da jikokinmu da zasu so nan gaba."
Ɗayyib gyara zamansa ya yi, yana jin kamar ya zaro wuƙar jikinsa yayi gutsi-gutsi da naman jikin su.
Muryarsa babu alamar tausasawa, haka kalaman da yake shirin furtawa kalamai ne masu tsananin kaushi da ya tane da su ga duk wanda ya ƙalubalanci kuɗirinsa ya ce;.
"Na yi muku uzuri, amma ku sani daga ranar irinta yau duk wanda ya ƙara yunƙuri dakatar da ƙudirina ko ƙalubalantar hukuncin da na yanke wallahi sai na yi ajalinsa na rantse bazanyi kaffara ba. Sannan ku sani wallahi ko da Abduh zai dawo a raye bai isa ya ƙwace wannan filinba"
Ƙosassun Motocin Malik da aka yiwa ƙira mai ƙwarin hawa tsaunuka ne suka kunnawa Yankin kai.
Ɗayyib na cikin surutansa na cin mutunci ga Dattijawan Yankin, Motocin suka biyo takan langa-langar da dama tsofaffi duk sun ji jiki.
Da gudu Ɗayyib ya miƙe ganin Motocin sunyo kansa gadan-gadan.
Dai-daita parking Drivern Malik ya yi, ragowar suma suka dai-daita nasu a gefen na Malik.
Baƙin gilashin fuskarsa Malik ya ɗan zame.
Yana tafiya ya na faɗin;
Waɗanda yasaka aikin su rusheshi da kansu a cikin daƙiƙu, su kuma koma Yankunan su kafin na juyo kansu.
Babu gardama tunda Ɗayyib ɗin da ya gayyatosu ya fisu tsaurin ido ya zabura balle su, dasauri suka fara kwashe komai.
Malik da har tsakiyar kan Ɗayyib yake kallo lokacin da ya matsa kusa da shi, dariyar mugunta ya saki yana shafa kan haɗe da kamoshi. Wata mitsitsiyar wuƙa mai ƙaifin gaske Malik ya zaro daga aljihun gefen wandonsa.
Kan Ɗayyib ya saki ya koma fuskarsa da hannunsa ɗaya ya matse, nan take farar fuskarsa Ɗayyib ta yi jajir.
Karon farko kenan da Ɗayyib ya ji tsoron da fitsari ya zubomai nan take a tarihin rayuwarsa.
Sai da Malik ya kuma sakin dariyar mugunta, sannan ya rubuta mai sunan Sulaim ɓaro-ɓaro a gefe da gefen kuncinsa a rarrabe.
Jini ne ya fara tsatsafowa yana biyo har gaban rigar Ɗayyib, su dama Dattijawa da suka tsaya da farko tuni suka gudu tunda suka fahimci Malik ne.
Murmushi Malik ya yi ya ce;
"Nasan baka da ilimin nasara, amma kaje wajen shaiɗanin da yake duba maka wayoyi da na'urorin mutane ya sanar da kai abinda na rubuta maka, zaka tuna wanene yakeson yi maka iyaka da ƙudirinka" Malik ya ƙarasa faɗa yana sakinsa haɗe da kama gefen rigar jikinsa ya goge wuƙarsa.
Ɗayyib kuka ya saki yana jin fuskarsa kamar an watsamai wuta, shi da kanshi yasan shi mungune amma sai yake ganin kamar Malik ya fishi iya mugunta.
Maimakon ya yi gida Asibiti ya wuce don yasan idan Jalal ya gansa a haka zuciyarsa ce zata buga ya mutu.
Duk da azabar da yake ji bayan ya isa Asibiti mudubi ya ce su bashi, sanin matsayin Ɗayyib ɗin yasa suka naimomai Mudubi a gaggauce.
Fuskarsa ya kalla kafin ya cewa Nurse ɗin;
" karantamin abinda aka rubuta a gefe da gefen kuncina".
A rarrabe Nurse ɗin ya ce Sul-aim, dukka da Nurse ɗin bai faɗa dai-dai ba, sai da gilashin hannun Ɗayyib ya suɓucewar da yayi kwatsa-kwatsa a ƙasa....
SUFYAN; walwalarsa gaba ɗaya ta ɗauke wasu lokutan sai ya ji kamar wayarsa tana yimai gizon Hindu Mahaifiyarsa tana kiransa. A haukace zai fara neman inda ya ɗora wayar sai ya ɗauko sai ya ga babu wanda ya kira shi.
Wasu lokutan kuma sai yayi ta mafarkin ga su Ɗayyib da Jalal nan sun zo zasu kasheshi.
Baya samun hutu ko sukunin zuciya ta kowani ɓangare, ga Sumaya da ta nace da kiransa. Shi kuma ya riga yayiwa kansa alƙawarin babu zaman aure tsakaninsa da ita, saboda Hindu Mahaifiyarsa tasha faɗamai Sumaya morarshin da take yi ne yasa take son shi, ba zai yarda da maganarta ba sai ranar da Allah Ya jarabceshi da Talauci..
Shirmen da ya farayi a wajen aikin ne yasa ya yiwa Kansa faɗan ya nutsu ya kula da aikin saboda shi kaɗai ne abinda ya rage mai.
Wata rana bayan ya dawo daga wajen aiki saƙon Malik na mayar da Companyn Tukwanen Zinare tushen da aka ƙirƙiresu ya riskesa. Sam bai fahimta ba sai da Malik ya turomai dogon saƙo mai ɗauke da bayani dalla-dalla da ƙarin matsayin da ya samu.
Rabonsa da farin cikin da zai bayyana dariyar dake fita tun daga ƙasar zuciyarsa har ya manta sai da ya karanta saƙon Malik.
Ya murmusa ya dara yayi surutai shi ɗaya tunda bashi da abokin gayawa.
Ƙewar Mahaifiyarsa, da tuna burin kafuwarsa da yayi sanadiyyar ajalinta yasa shi fashewa da kuka.
Ga shi zai zama mutumin da kowa zai so ya dama da shi, zai zama abin kambabawa a Yankin Tudu kamar yadda ya jima yana buri, amma mai tayashi kokawar cikar muradin nasa ƙasa ya lulluɓe idanuwanta, inama da tana raye.. ya faɗa yana tuno Fuskarta.
NAILA;
"Na yi alƙawai Kaka" Naila ta faɗa jikinta a sanyaye.
Hannunta Kaka ta kamo, itama cikin sanyin da ya haɗe da tsoron rayuwar da za su iya fuskanta anan gaba tace;
"Allah Ya baki ikon cikawa Naila, shima ki turamai saƙon kinyi alƙawari, ba iya na baki ba har cikin zuciyarki, Allah Ya na tare mu kinji"
A hankali kamar mai raɗa Naila ta ce;
"Kaka kina ganin alƙawarin bai yi tsauri da yawa ba, kar wata rana ya canzamin bayan na guji kowa"
"Wa kike da shi bayan ni Naila? Wa zaki aminta da shi bayan ni? Ba fa zumunci ya ce karkayi ba, bai ce karki kyautatawa kowa ba, to me kike nema? mai kike yiwa fargaba?" Kaka ta faɗa tana kallon Naila da tayi ƙasa da kanta.
A hankali Naila ta girgiza kanta alamar babu komai.
A jiyar zuciya Kaka ta sauke ta ce; "maza tashi kije ki turamai saƙo".
Ɗaukar alƙawarin Naila shi ne mafarin soyayyar mai ƙarfi tsakaninta da Sulaim.
A hankali ta fahimci Sulaim wani irin so yake yiwa abu da iyaka yardarsa da dukiyarsa da kuma zuciyarsa.
Wa su lukutan haka zai kirata ya yi ta kallonta ba tare da yacemin komai ba.
Ciwonsa, damuwarsa farin cikinsa duk Naila ta karance su, maganganunsa ƙalilan ne, amma kulawarsa gareta ba shi da iyaka.
Yana yawan tunamata har yanzu bai daina jinsa a matsayin Maraya ba, duk da Ummi Aysha tana raye amma rashin samun kulawarta tun farko da rayuwar gwagwarmayar da yayi bayan mutuwar Mahaifinsa, yasa yake jin kansa a wannan yanayin. Amma idan yana kallonta ko yana saurarar muryarta sai ya ji kamar Mahaifinsa ya na raye a kusa da shi bai mutu ba, dalilin raɓar rayuwarsu da tayi lokacin da babu wani abin nishaɗi a cikinsa sai kaɗaici.
Bani da matsala da Ummi Aysha duk ƙarshen sati sai ta aikomin da kyaututuka na musamman.
Motoci daban-daban da Driver Mace Sulaim yasa ake kai Makaranta a ciki masu kyau da tsada.
Komai na daya dangi Naila ƙarara Sulaim yake nuna muhimmancinsa ga kowa.
Cikin watanni su Naila suka yi wani irin kyau ita da Kaka.
Tsakanin Naila da Yasar sai dai su gaisa da ƴan uwansa da Iyayensa domin duk yadda ta kaiga ƙoƙarin dawo da zumuncinsu na baya sam Gasar bai bata haɗin kai ba, acewarsa ta fi ƙarfinsa yana tsoron kar yin waya da ita ya kawowa aikinsa matsala. Ba don Naila t so ba haka zumuncinsu ya yanke da Yasar, kamar bamu taɓa sanin juna ba a baya.
Wata ranar sati Simbi ta kawowa su Naila ziyara.
Basu wani saki jiki da ita ba har ta tafi.
★washe gari ta ƙara dawowa, yadda ta saki jiki da fuskarta abin ya ƙayatar da su Naila, har hirar Yankin Tudu ya fara shiga tsakanin su.
A cikin wannan satin kullum da daddare Simbi a sashensu takeyin dare, su na hira da Kaka wasu lokutan har da Naila.
A cikin sati biyun da suka biyo baya shaƙuwa ya fara shiga tsakaninsu da ita, a kwai