x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 28 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 81001 words
  • 84000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 755

07 Oct 2025
wani dare ma a sashensu ta ce zata kwana, Naila ta yi yunƙurin kaita wani ɗakin daban amma ta nuna bata da matsalar kwanansu ɗaki ɗaya.

A tunanin Naila barci ya ɗauke Simbi don haka ta zubo abinci ta kira Sulaim video call.

Babu jimawa fuskarsa ta bayyana yana sanye da Pyjamas alamun ya shirya kwanciya.

Kamar kullum da ta gaisheshi bai amsa ba sai ido da ya Lumshe ya aikomata da sumbatar daya sata sakin dariya.

Tashi ya yi ya zauna, yanayin fuskarsa na sauyawa haɗe da buɗe dukka girman idanuwansa da bai fiyayi ba.

Dariyarta Naila ta gimtse tsoron sauyin da ban taɓa gani daga garesa ba na shiga zuciyarta.

kamar daga sama ta ji saukar maganar da banyi tsammani ba daga bakinsa;

"Ina jin idon mutum a kaina, wacece a ɗakinki Sa'aadati?"

[9/5, 8:52 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

14

Wani irin bugawa zuciyar Naila ya yi. Dariyar yaƙe ta ƙaƙalo kafin ta ce;

"Ido kuma bayan nawa?"

Bayason ya ƙarayin magana don haka yayimata sallama kamar komai bai faru ba.

Yana katsewa Naila ta juya gefen da Simbi take kwance da sauri, amma sai taga Simbi ba ma gefenta take kallo ba, kuma ba taji alamun motsin juyawarta ba.

Ajiyar zuciya ta sauke amma duk haka ta kasa cin abincin da ta zubo sai kitchen ta mayar da shi.

Har tsakiyar dare Naila ta kasa runtsawa, living room ta fito ta haɗa kanta da gwiwarta ta fashe da kuka. Tsoron gayawa Sulaim gaskiya take yi kar ya ce yarda da Simbi ne yasa ta barta har ta kwana a ɗakinta.
Kasa jurewa tayi ta koma ta kullo ɗakin ta waje sannan ta kira shi Video call ko Allah zaisa ya ɗaga.

Bai ɗaga ba, kuma bata daina kira ba, har barci ya ɗauketa.
Ba tafi hour uku ba ta farka, ƙara ɗorawa ta yi da kiransa, cikin sa'a ya ɗaga.

Yana zaune idanuwansa da barci sosai a cikinsu don haka ya rage girmansu kamar baya kallonta..

"Kayi haƙuri" Naila ta faɗa tana fashewa da kuka haɗe da dafe bakinta.

Bai ce mata komai ba sai wayan da ya kai saitin laɓɓansa ya sumbata sannan ya ɗan saki murmushi.

Ta yi tunanin zai tambayeta dalilin da yasa take bashi haƙuri har da su kuka, sai ta faɗamai gaskiya, amma sai ta ji bai tambaya ba. Maimakon haka da muryarsa da ya ɗan yi nauyi ya ce;

"Kalli yadda kike kuka Sa'aadati, matso daina kuka faɗamin menene?"

Ido Naila ta rintse tana jin soyayyarsa kamar ya yi mata yawa. Kai ta girgiza saboda ta kasa cewa komai.

Murmushi ya yi kaɗan yana shafa sumar kanshi kafin ya ƙara sumbatar wayar.

Noƙe kafaɗa Naila tayi alamar ba wannan take so ba.

Girarshi ya ɗage alamar tambayar "dagaske?"

Ɓata fuska tayi tana sosa hancinta.

"Babu laifin da zakiyimin, na kasa hukuntaki Sa'aadati, saboda ina sonki, son da babu rabuwa, amma karki bari ta ƙara kwana a Ɗakinki kinji"

Naila da sauri ta ɗaga kai, tana share hawayenta. Mamakin yadda yasan Simbi tana ɗakinta na kamata amma babu damar tambaya.

"Ki je wani ɗakin ki kwanta" ya faɗa yana jingine wayar a saitin fuskarsa

Fara buɗe Simbi Naila tayi Sannan ta shiga wani ɗakin ta kulle har lokacin Sulaim yana kan layi.

Kwanciya tayi ta duƙunƙune cikin abin rufa tana kallon yadda yake kallon wani waje daban da alama labarai ko wani abun yake kallo mai muhimmanci. Yanayin fuskarsa da babu wasa sam sai yana kallonta na matuƙar birgeta, takan ji a ranta kamar tafi kowacce ƴa mace Sa'a.

"Na gama" Naila ta faɗa tana kallosa

hankalinsa ya maido kanta.
Maimakon ya yi magana, sai ya yi mata alamar da hannu ta matso.

"Ta ina zan matso" Naila da faɗa tana dariya.

Shima murmushi ya yi, kamar yadda ya saba ya kai wasu daƙiƙu yana kallonta, sannan yaƙara sumbatar saitin inda goshinta ya bayyana a tasa wayar.

A kunnen Sulaim Naila tayi addu'a kafin ya mata alamar ta jingine wayar tayi barcinta.

A kan Bedside lamp ta jingine wayar. Sanin waya ɗaya ne a tare da ita yasa ya kunna karatun Abdurrahman Bin mus'ad ta ɓangarenshi haɗe da rage sautin labaran da yake ji.

A hankali sanyin sautin karatun Alqur'anin yake shiga kunnen Naila yana sanya mata nutsuwa a cikin zuciyarta, tun tana ɗan buɗe ido tana kallon gefen fuskarsa idan tayi sa'a ya juyo suka haɗa ido ya aiko mata da sumba har barci mai daɗi ya ɗauketa. Sai da ya tabbatar barcinta yayi nisa sannan ya katse kiran.



SULAIM
Tun bayan komawarsa Kahala Noorhan ta fara ziyartarsa babu dare babu rana.
Bai ɓoyemata ya rabu da ita ba, amma sam ta nuna wallahi bai isa ba, ita zai rainawa hankali ko ya ɗauko ita irin Matannan ne da Namiji zai so a lokacin dayaga dama kuma ya rabu da su a lokacin dayaga dama?. Ko don yaga yana da kuɗi? Ita babu inda zata je idan zai dawo hankalinsa ma ya dawo.

Duk mitar Noorhan da kalamanta masu kama da nuna iyaka ko gadara Sulaim bai taɓa kulata ba.

Lamarin su yayi ƙaramari ne data fara binsa har office da duk wani wajen taro da zai je sai ya ganta a harabar wajen, hatta Asibiti wajen Naanah zuwa takeyi ta zauna a harabar wajen. Kuma duk haɗuwar da zasuyi sai ta biyosa har jikin mota tana mita. Bai taɓa sawa a wuƙantata ba.

Noorhan anata ganin Sulaim ya ƙyaleta tana cimai zarafi ne don yasan ba shi da gaskiya kuma itama Mahaifinta ai mai kuɗine.

Ranar da ta kaishi ƙarshe ta biyoshi har cikin office tana zage-zage, kai tsaye ƙararta ya shigar kan shiga haƙƙinsa, cin zarafi, takura da ɓatamai suna.

Abu kamar wasa Sulaim ya nuna mata ikonsa da dukiyarsa da take ganin kamar zasu aunu a ma'auni ɗaya da na Mahaifinta.

Da kuka da magiya tare da alƙawarin ɗauke Noorhan su mayar da ita Lebanon Iyayenta suka shawo kan Sulaim ya janye ƙarar da ya shigar..

Wannan ne sanadiyyar fitar Noorhan daga cikin rayuwarsa.

Al'amarin Naila gareshi babba ne, domin ba iya kallon Matar da zai aura yake yi yiwa Naila ba, harda kallon aminiya ƙanwa kuma uwar ƴaƴansa yake mata.

Babu rabuwa da ita a tsarinsa amma ya lura Naila sam bata da wayo, kuma ita mutum ce da zata iya sadaukar da farin cikinta don na kusa da ita yaji daɗi, da wannan damar Simbi take neman shiga jikinta.

Tun zuwanta Simbi sashen a ranar farko labari ya riskesa, ba shi wani makusanci da ya yarda da shi ɗari bisa ɗari, domin ko Malik akwai wanda kawai aikinsa lura da motsin Malik ne , ba tare da shi kanshi Malik ɗin yasan da zamansa ba sai manyan Securities ɗin Dhahab, domin a matsayin mai bawa shukoki ruwa yake rayuwa a Gidan.

Saukar numfashin Simbi da yasan tana fitarwa ne da gan-gan ya bashi tabbacin tana ɗakin kamar yadda aka bashi rahoton tunda ta shiga sashen bata fito ba.

Idan ya yiwa Naila kashedi akanta har sau uku bata ji, to zai yimata hukuncin daya dace da ita...

SIMBI.

Tana sane ta dinga fitar da numfashinta da ƙarfi saboda tasan waye Sulaim, ba zai taɓa son kwanciyarta a ɗakin Naila ba, kuma gaskiya ya faɗa lokacin daya bayyana akan screen ɗin wayar Naila, idanuwanta ƙuri suke akansa sai dai dayake bata saitin Camera shiyasa bata fito ba, a hankali ta juya domin tasan dole Naila ta waiwayota bayan ya katse kiran.

Da Naila ta kullota a ɗaki dasauri ta miƙe ta ɗauki ɗayan wayar Naila da ta bari.

Babu password babu komai sai Apps ɗin karatun Alkur'ani kala-kala har ta gama bincikenta bata ga komai ba, asalima babu layi akan wayar.

★washe gari bata tsaya jiran tashinsu ba ta tattara ta bar sashen.

Tsaf ta zauna ta karya da Iyayenta har tana tsokanar Barirah da take cika tana batsewa.

Bayan ta shiga Ɗaki Taswirar Dhahab da aka yiwa ado da kaloli ta manna shi a bangon ɗakinta take kallo. Zama tayi tana tunano irin dukiyar da Sulaim ya mallaka a iya ƙasar Abyad, amma ace Naila ita kaɗaice ta samu zama a cikin zuciyarsa. Mai zai hana ya ɗauko bare haɗiɗɗiya ƴar manyan mutane mai kyau da aji daga wata nahiyar ya aura? Naila fa? Naila ƴar Mahmoud madinkin da bai taɓa ɗanɗanar arziƙi ba har ya bar duniya.

Ina laifin ma ya zaɓi Barirah tunda tafi Naila ilimi da wayewa..

Banbancin kishin Barirah da Simbi. Barirah mace ce mai faɗa saurin fushi lokaci, ɗaya da son cin zalin yara ta hanyar Dukansu tun tana yarinya ƙarama, son girma da mulki tun bata san zasu riski kansu a Babban Birnin Abyad ba. Amma bata da baƙin ƙishin cutar da wani ta hanyar sharri ko asiri, barta da masifa da ƙunci. Saɓanin Simbi bata da hayaniya amma wani irin kishi ne da ita daya haɗe da hassada, kuma akan cikar muradinta bata ƙi tayiwa mutum sharri ba, a baya hassada yasa take ganin wawtar ƴar uwarta akan son Sulaim duk da itama dama ne bata samu ba, amma yanzu da yake son Naila sai take ganin gara kawai ya je ya ɗauko bare.

Naila da Barirah ba su dace da shi ba, ko kuma dai ya ɗauki Barirah ya rabu da Naila. Simbi har ta gama Makaranta bata yarda kina ƙawance da ita kiyi da wata ba, da zarar ta ganki da wata musamman wacce ta fita sai ta fara kishi, waɗanda ba su fuskanceta ba sai suke yimata kallon wata manufa daban..

ƊAYYIB
Ko ina na jikinsa rawa yakeyi, sai da ya share mintuna goma bai dawo nutsuwarsa ba. Gumi kuwa kamar an watsamai ruwa suna zubowa yana sharcewa.

Da sauri Nurse ya fito don kiran babban Likita kar Ɗayyib ya mace ba tare da yayi yunƙurin komai ba

Fargaba yasa jinin Ɗayyib ya yi mugun hawa bayan likita ya gwadashi dole suka bashi gado.


Da dare yayi Ɗayyib fitik-fitik ya yi sai sun sallamesa ya koma Gida saboda bayaso Jalal yaji labari ko ya ga fuskarsa balle yasan gaskiyar abinda ya faru.

Bai nufi sashen Jalal kai tsaye ba sai da ya fara tsayawa a nashi sashen yayi wanka tukunna.

Jiki a sanyaye ya nufi Sashen Jalal fargabar sunan da Malik ya rubutamai a kuncinsa har lokacin bai gama sakinsa ba, duk da yasan ba'a mutuwa a dawo.

Ko da ya isa wajen Jalal ya tambayeshi game da aikin filin daya fara shiru yayi kamar bai ji sa ba, har sai da ya ƙara maimaita tambayarsa.

Sannan Ɗayyib da har lokacin jikinsa yake a sanyaye, ya sanar da Jalal abinda Malik ya ce akan filin ya kuma saka an rushe komai.

Shiru Jalal ya yi, yana runtsewa idanunsa, irin azabar da Malik ya ganamai na dawomai.
Hukuncin da yake ganin shine mafita Jal ya sanar da Ɗayyib, na zuwansa wajen Bokan Tsaunin da shi kaɗai ya rage musu.

A wannan dare Ɗayyib ya yi sallama da Jalal, ya koma sashesa ya shirya kayansa.

★washe gari da Asubahi ya saɓa jakarsa domin tafiya ƙasar Abyad, wajen ƙasurgumin Bokan Tsaunin da Jalal ya kwatantamai, a wajen wasu tsaunuka bayan garin Birnin Abyad...

NAILA;

Bayan ta idar sallar Asubahi alfijir ya fara ketowa ta kira wayar Sulaim kamar yadda ta saba.

Ya ɗaga amma bai buɗe idanuwansa ba, jingine wayar yayi ya barta tana kallon fuskarsa.
Naila kallonshi take yi tana murmushi kamar wacce ta samu matsalar kai.

Farin hannusa ya miƙo, Naila ta na dariya da tai kai bakinta kan wayar dai-dai saitin inda hannun yake ta sumbata, shima murmushi ya saki yana gyara kwanciyarsa.

Naila tana kallon Sulaim da idanuwansa suke kulle har ta koma kan gado ta jingine wayar, a haka Barci itama ya ɗauketa, wayar da kanta ta mutu bayan chajinta ya ƙare.

Wannan shine daily routine ɗin Sulaim da Naila..

Da gari yayi haske, Kaka ta umarci Naila ta taso Simbi suyi Breakfast.

Wayam ta samu ɗakin. Daga ita har Kaka basu wani damu ba, saboda kai tsaye tunaninsu kan wataƙila dan Kar ta takura musu ne tayi tafiyarta.

Da yammaci sai ga Simbi ta ƙara dawowa, hirar tana son yin wani cos a makarantarsu Naila take yi musu, dan haka ta roƙi dan Allah idan zata je tayimata waya su fita tare..

Naila bata kowa komai ba a ranta, washe gari bayan ta kimtsa ta kira Simbi ta layin wayar da ta bata.

Da Simbi ta fito Kai tsaye Driver ta hana shiga, ran Naila babu daɗi takeyiwa Drivern ƙorafin ɗaukar Simbi ai ba wani matsala ba ne, tunda Makaranta ɗaya zasu je.

Abinda Naila bata sani ba Simbi bata da mai biyamata irin jami'ar da take zuwa, kawai tayi hakane saboda tasan labari zaijewa Sulaim, kuma ƙorafin Nailan akan lallai sai an ɗauketa tamkar Sulaim tayiwa tunda da yawunsa Drivern take magana.

Driver zuwa tayi ta dawo, ba tare da ta ƙaracewa komai ba tace Simbi ta shiga su tafi.
Har sun yi nisa Simbi tafara lalubar jakarta, tsaki ta saki tana faɗin;
"Subhanallahi wallahi na manta takarduna a gida Please Driver ajjiyeni anan"

"A'a mai zai hana mu koma ki ɗauko" Naila ta faɗa da zuciya ɗaya

"Karki damu zan fita da motata kawai"

Simbi da fuskar alhinin manta takardun da tayi a gida, acewarta sukayi sallama da Naila.

Murmushi Simbi ta saki bayan ta sauka, tana ƙoƙarin lalubo wayarta don kiran Drivern su, Mota mai kyau ya tsaya a saitinta.

Kyakkyawan matashine, farinsa har kashe mata ido yakeyi, yana tsayawa ya sauko ba tare da ɓata lokaci ba yana yi mata sallama.

Fuskarsa take kallo har zuwa takalmin ƙarfarsa baƙi wuluk, baƙin har wani irin gizo yake yimata.

Amma da yake taga alamar tarin dukiya a tare da shi, sai ta amsa sallamarsa tana ɗauke kai, amma zuciyarta cike da farin cikin babban kamun da tayi, wayancewa tayi da kiran Driver kamar bata damu da Mutumin da ya tare ta ba
[9/5, 8:59 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

15


SIMBI

Cikin salo da iyayi take sanar da Driver ya taho mata da Motarta, haɗe da kwatantamasa inda take.

Cikin ɗan kame fuska ta dawo da hankalinta kan Matashin da ya tsaya jiran ta gama amsa waya.

"Barka da safiya Hajiya Simbi, ina fatan ban dameki ba ko?" Matashin ya faɗa yana kallon fuskarta.

Daɗin muryarsa da daɗin da take ji acikin zuciyarta yasa ba tayi tunanin ina Matashin yasan sunanta ba.

"Sunana Ɗayyib amma zaki iya kirana da Dee, ni mazaunin Babban Birnin Abyad ne, mamallakin kamfanin sarrafa shinkafa na D&J a Birnin Abyad, na ji daɗin haɗuwa da ke, ina fatan kema haka?" Matashin ya yi bayanin kansa a taƙaice yana karantar yanayin Simbi.

Wani irin fari tayi da ido tana ƙaremai kallo, kafin ta saki murmushi tana miƙamai hannu alamun ya kawo wayarsa.

Wayar hannusa ya miƙa mata yana murmushi.

Ƙirar wayarsa da kyanta sam ba irin manyan wayoyin ƙasar Abyad ko ta ce na duniya gabaki ɗaya data Sani bane, "kenan ƙera mishi tashi akayi daban? Gaskiya na yi babban kamu, yau na fito a sa'a yaushe rabon da wani ya tare ni da sunan yana so na, hmm! gaskiya Allah Ya na so na"

Simbi ta faɗa a cikin zuciyarta lokacin da take jujjuya wayar Dee a hannunta kafin tasamai Number wayarta.

Tana samai, ya karɓi wayar ya juya ya shiga Mota. Simbi tayi tunanin tafiya zai yi sai taga ya fito da abu a nannaɗe a cikin takarda mai tudu da kauri. Sai da ya miƙa mata yana murmushi sannan ya ce;

"Ga wannan kisha Ice cream babu yawa, sai na kiraki ko?" Ya ƙarasa faɗa yana yimata alamar kira da hannunsa.

Kuɗin Simbi ta shafa, wani irin kuɗi ne dashi haka, da zai yimata kyautar kuɗi irin wannan daga haɗuwa?,

"gaskiya na yi babban kamu" ta faɗa ƙasa-ƙasa tana murmushi

Bayanshi tabi da kallo tana shafa kuɗin hannunta har ya shige mota ya tasheta yabar wajen.

Daa Simbi tasan Ɗayyib ɗin Yankin Tudu lokacin da yake Matashi kamar yadda su Malik suka sanshi, da ganin fuskar Matashin da ya tsayar da ita kaɗai sai ya sata yin gudun da bata taɓayi ba, ko zuciyarta ta buga nan take.

Amma maimakon wannan tsoron tunda ba sanin Ɗayyib tayi yana Matashi ba, sai tayi ta sakin murmushi har Driver ya zo ɗaukarta..

MALIK
A ɓangaren Malik tun safiya yayiwa Yankin Tudu tsinke, domin duba yadda aikin Ma'aikatarsu ya ke gudana.

Bayan ya yi sallar Magriba yana ƙoƙarin kimtsawa domin tafiya Masauƙi, kwatsam ya ji Muryar mutum a gefensa.

Malik bai zabura ba, saboda bashi da tsoro ko ƙanƙani sai tsayuwarsa da ya gyara yana waiwayo gefensa.

Sarkin tsafin Yankin Tudu ne ya bayyana a idon Malik.

Malik bai ce komai ba sai tsayuwarsa da ya ƙara gyarawa haɗe da ƙara matse fuskarsa, cikin ƙasa-ƙasa da murya ya ce;

"Mai kake nema? Mai ke tafe da kai yi bayani a gaggauce"

"Yau kwana biyu da tafiyar Ɗayyib wajen Bokan Tsauni, ɗaya daga cikin Bokaye mafiya hatsari a Ƙasar Abyad, zai iya bayyana ba iya wajenku ba har a cikin Dhahab, Zai shafe Tarihin Dhahab da wanda ya kafata idan har ya bayyana a cikinta ba tare da an dakatar da shi ba, lokaci ƙalilan ne ya rage, ƙarin haske na wajen Simbi ƴar uwarka" Sarkin Tsafin Yankin Tudu yana gama faɗa ya ɓace.

Motsi biyu Malik yayi shine ɗauko wayarsa da turawa Sulaim bayanin komai nan take.

Idan Malik ya ce bai ji tsoro ba ya yi ƙarya, amma babu wani Mahaluƙi daya isa ya rusa Dhahab matsawar su na raye..

Tsoron da ke neman mamaye zuciyarsa ya fatattaka ya dannawa Driver kira.

Cikin mintuna ƙalilan Driver ya ƙaraso.

Bayan Malik ya shiga Mota saƙon Sulaim ya shigo wayarsa, gumin da rabonsa da yin irinsa ne ya shiga tsatsafomai mai yana sharcewa, hannunsa yana rawa ya dannawa Sulaim kira...


NAILA

A ɓangaren Naila bayan sun tashi, bata tsaya wani ɓata lokacin biyawa wajen cin abinci ba Driver ta dawo da ita Gida..

Kamar yadda ta saba bayan ta iso gida ta huta, wayar Sulaim tafara kira, amma har sau uku bai ɗaga ba.

Tasan bazai wuce fushin tafiya da sukayi da Simbi Makaranta tare ba, ita gaskiya ta gaji, to so yake yi ta dinga wulaƙanta su tana nuna musu ita tafisu, gaskiya bazata iya ba.

Kasa riƙe zancen tayi, ta fara bawa Kaka labarin ko ƙarasawa Makarantar fa basu yi ba Simbi ta sauka amma shine zai yi fushi har ya ƙi ɗaga kiranta..

Kaka bata tofa ba, a ganinta faɗan masoya ne zasu shirya daga baya.

Naila har ta gama cin abinci bata daina mitar
"gaskiya ni bazan jurewa wannan ƙa'idojin nasa ba"

SIMBI
A ɓangaren Simbi har takai gida bata daina murmushin babban kamun da ita yi ba.

Tana isa cikin sashensu kai tsaye