kansa bayan ya fito daga wanka ya na zura Soft Pyjamas ɗin da Malik ya kawomasa, tunda baya tafiya da kaya sai dai idan yaje ƙasa ko gari ya siya idan zai tafi ya barsu a can.
Yana shirin kwanciya bayan ya taɓa sassauƙar Abincin da Malik ya kawomai Ummi Aysha ta iso da Likita.
Yana son taji daɗi ya nuna mata itama Uwa ce data isa ɗanta kamar ko wacce Uwa don haka ya amince Likita ya dubasa haɗe da samai ruwa.
Noorhan;
tayi tunanin za'a kirata Dinner amma sai ta ji shiru, sai ɗaki da'a biyota da shi.
★washe gari ma tana sa ran zasu kirata shima ta ji, shiru. Wanka tayi ta shirya cikin kalar Abayar daya haskata tana girgiza ƙafarta tana jiran Sulaim zai turo a kirata ko bazai turo ba, ta kirasa ta WhatsApp baya ɗauka kuma ita bazata kira Malik ya fahimci halin da suke ciki ba.
Ummi Aysha da Farheen.
Ummu Aysha bayan ta dawo daga wajen Sulaim sun sha hira Farheen cikin farin ciki, musamman Farheen da har kwaikwayar kallon Sulaim takeyi.
★washa gari Ummi Aysha da kanta ta shiryawa Sulaim Breakfast, kuma ta ɗauka ta nufi Sashen.
A kwance ta samesa cikin Armani lounge wear jajayen da suka yi mai kyau, har lokacin ganinsa bai dawo dai-dai ba jikinsa a mace.
Shi ya fara gaisheta ta amsa tana yimai ya ya jiki?
Da kai ya amsa mata yana gyara zamansa.
Ɗagowa ya yi a hankali ya kalleta kafin ya ce;
"Tana zuwa Makaranta?"
Ummi Aysha da daɗi yasata sakin murmushi saboda gane ina ya dosa amma sai tayi fuska kamar ba ta gane ba ta ce;
"Wacece? Ai Farheen tuni ta gama Makaranta, ko su Simbi ƙanen Malik kake nufi?"
"Ummiiih" ya faɗa yana ɗage cikakkiyar girarsa ɗaya da murmushi kwance a saman fuskarsa.
Ummi Aysha wani irin daɗi takeji ɗanta ya saki jiki da ita a karon farko.
Saboda taga yadda zai yi sai ta ƙara cewa;
"To ai bangane ba, auuw! ohhh! Naila ka ke nufi😄?"
Juya mata baya yayi yana dariyar da ke motsa kafadunsa.
Itama Ummi Aysha dariya tasa kafin ta kira sashen Hadimai su sanar da Naila tana nemanta a sashen Sulaim idan bata gane ba su rakota.
Bata ajjiye wayar ba sai da ta kira Malik ya sanar da Securities su bar Naila idan ta iso ta shigo.
NAILA; lokacin da saƙon Ummi Aysha ya jewa Naila, daƙyar ita da Kaka suka daure Hadiman suka fita, suna fita Kaka tasa dariya tana dafa Naila dake juya idanuwa kamar zasu zazzago.
Ta ɗauko dogayen Riguna sufi kala goma tana nunawa Kaka, Kaka tace basu yi kafin ta zaƙulo Royal blue mai kyau.
Bata wani fesa turare sosai ba, kar ace sonshi takeyi da addu'ar sa'a Kaka ta rakata suna dariya...✍🏻
[9/5, 8:50 PM] Maman Amatullahi: SASAAL
11
SUFYAN; Tuna abinda ya ajiye a living room ɗin Sarki Hammam yasa ya ɗebi rabin abinci ya watsar a lungu, ya dai-daita zamansa amma har lokacin ya kasa tsaida hawayensa. Tun yana sa ran Ɗayyib har ya cire. ido buɗe ya kwana yana kallon inda Mahaifiyarsa take ciki.
★har gari ya waye dare ya kuma sallace kawai take tashinsa ya kasa saka komai a cikinsa..
Yana zaune ya jiyo zafin takun Ɗayyib, miƙewa ya yi kafin ya shigo ɗakin ya riskesa. Domin da ga yanayin takunsa da jiyo ya fuskanci yaga abin ya ajjiye, don haka maganar ɓoye-ɓoye ya kau tsakaninsu.
Ɗayyib ya na shigowa Sufyan ya taresa da cewa;
"Don me zaka binnemin Uwa da rai! Na ce don me zaka binne min Uwa da rai!! Ka zo ka sareni da wuƙa ne? ka sare ni nima ka binne Ni? To ka sareni mana!!!"
Murmushi Ɗayyib ya yi yana cije haƙwaransa sai dai kafin ya zaro abinda ya yi niya Sufyan ya kai mai naushin daya sashi zubewa yana mayar da numfashi, kafin ya yunƙura ya miƙe, ihu ya karaɗe Daular gaba ɗayanta da kiran sunan Ɗayyib.
"Menene ya ke faruwa?"
WAIWAYE
Ranar da saƙon Malik ya isa ga Sufyan kafin ya shiga Yankin Tudu, A ranar Su Malik sauka baro Kahala.
Sanin hatsaniya zai iya biyo bayan zuwan Sufyan Yankin Tudu kamar yanda Sarki Hammam ya sanar mai yasa ya shirya tafiyarsa Iyakar Yankin Tudu bayan isarsa Kahala.
Malik da suka dawo Dhahab da Sulaim Bayan ya duba, Masauƙin Sulaim komai ya yi dai-dai ya miƙa masa abinci yayi sallar magrib ya kimtsa zuwa Iyakar Yankin Tudu ta ɗaya daga cikin jiragen da suke amfani da shi, sai dai da dirarsa waya ya riskesa daga Sarki Hammam Ɗayyib ya gano abinda Sufyan ya ajjiye, a wannan dare Malik da masu yi masa Hidimar sirri a Iyakar Yankunan suka isa Yankin Tudu har ɓangaren Jalal.
Da farko Jalal da ya ke kwance bai gane tsayuwar Malik ba saboda babu wadataccen haske, sai dai yankar da Malik yayiwa ƙwaurin ƙafarsa ne ya sashi miƙewa jikinsa yana rawa.
Cikin tsoro da ganin mutuwa muraran Jalal ya ce;
"wanene ya turoka? mai kake nema da n..."
Wani irin Yanka mai shiga jiki Malik ya ƙara yiwa rabin fuskar Jalal dayake kallonsa da shi ya na tambayarsa. Ihun azabar da ya amsa Masarautar ya saki yana lalube domin ko baiyi magana ba, yasan Malik ne ya riskesa.
Da ƙarfin Muryar da bai san yana da shi ba yake kiran Ɗayyib dake wajen Sufyan.
DAWOWAR LABARI
Da gudu Ɗayyib ya miƙe ya nufi Sashen Mahaifinsa Sufyan ma ya bi bayansa.
Babu wanda ya leƙa wajen Jalal saboda tsoro kowa laƙwas ya yi saboda suna kyautata zaton Malik ne ya bayyana a wajensa. Wa su dai sunyi ƙarfin halin fara neman Ɗayyib ta hanyar kiran Sunansa.
Malik tsayuwarsa ya gyara.
Ɗayyib yana Kunno kai ya yaye mayafin fuskarsa suna kallon juna.
Cikin kuka ga jinin da ke bin jikin Jalal da har lokacin yake yashe a ƙasa a gefen Malik yake cewa;
"Ka ceceni Ɗana Ɗayyib haƙiƙa Malik ya bayyana gare ni.."
Wani irin ɗauka Malik yayiwa Jalal kamar tsumma, ya ɗaga wuƙar hannunsa ya Chaka mai a saman kafaɗarsa yana kallon tsakiyar idon Ɗayyib ta ɗan hasken da Malik ɗin ya kunna da kansa..
Ihun azaba Jalal ya saki..
Cikin kaushin Muryar dake nuna zafin kan Malik da haushinsu daya rayu da shi ya ce;
"Bayan tasha uƙubar watanni daga gareka yanzu awoyinka hamsin da huɗu da binneta, ka je ka cirota da hannunka Ɗayyib! a wanketa a kaita Maƙabarta idan ba haka ba, wallahi! Wallahi!! Sai na tafi Babban Birnin Abyad da kawunanku" Malik yaƙarasa faɗa yana murza wuƙar da bai cire ba a saman kafaɗar Jalal da azaba ya jima da sumarwa.
Tsayawa Ɗayyib ya yi yana jin kamar ya taro ƙarfin duniya a jikinsa ya kashe Malik da Sufyan nan take, amma abin taƙaicin ko Bafade ɗaya babu, kowa yana gudun ransa.
Ganin Ɗayyib ya ƙame a tsaye yasa Malik ya ce;
"Iya adadin mintocin da ka ɓata iya adadin jinin Ubanka da zai salwanta har ya rasa ransa, kaga ka rasa Shaiɗanin Uban daya horar dakai yake kan tayaka ɓarna" Malik ya ƙarasa faɗa yana watsar da Jalal a gefe..
Gane gaskiya Malik ya faɗa kuma babu abinda ya isa yayi mai idan Jalal ya mutu, ya sa Ɗayyib fita da sauri, waɗanda suka tayasa binne Hindu ya nemo da Gatari da komai da sukayi amfani suka fasa da sauri, sai gashi sun cimma gawar Hindu da ya karaɗe ko ina da wani wari...
Sufyan wajen Malik ya je ya ɗurkushe ƙasa yana kuka haɗe da haɗa hannayensa da suke rawa waje ɗaya alamar godiya domin tsoron Malik ba zai barsa ya yi magana ko ya iya kallonsa ba.
Ɗayyib suna tono gawar Hindu ya komo wajen Mahaifinsa sai dai babu Malik babu Sufyan. Da sauri ya ɗaukesa zuwa cikin Mota da taimakon abokan ɓarnarsa suka nufi Asibiti da shi.
A wannan dare Sufyan ya dinga bi gidajen Dattawan Yankin yana kukan su taimakamai, tunda Malik tuni ya bar Yankin.
Jin abinda Ɗayyib ya aikatawa Hindu ya sa suka tausaya mai, duk suka ɗaure hancinansu suka dumfari gawar Hindu..
Da taimakon Matar Babban limamin Masarautar da ma'aikatan Jinya aka suturta gawar Hindu iyakar yadda zasu iya..
★washe gari Dandazon Mutanen Yankin Tudu ne suka yiwa gawar Hindu rakiya zuwa makwancinta.
Sufyan ya yi musu godiya yana kuka. Bayan ya tsaya a kabarin Mahaifiyarsa ya yi mata addu'a ko minti biyar bai ƙaraba ya koma gida ya ɗauki jakarsa da bai taɓa komai a ciki ba ya bar Yankin Tudu zuwa Babban Birnin Abyad. Tare da sawa zuciyarsa ya tafi kenan har abada.
NAILA;
Da taimakon Hadiman sashen Ummi Aysha Naila ta isa sashen Sulaim.
Ƙofar Sashen a buɗe yake don haka tana zuwa Securities suka barta ta shige.
Ƙamshin sashen da tsaftarsa yasa Naila ƙara nutsuwa. A zaune ta samesu shi yana Breakfast Ummi Aysha kuma tana danna waya.
Gaisuwar Naila kawai Ummi Aysha ta amsa da fara'a a kan fuskarta ta miƙe tana kafa waya a kunnenta alamun amsa kira.
Da harshen nasara Naila ta gaisheshi tana yin ƙasa da kanta.
Da kaa Sulaim ya amsa mata yana nuna mata gefenshi, wajen da Ummi Aysha ta tashi.
Ƙafafuwan Naila su na harɗewa ta taso ta zauna, gaba ɗaya sai take jin saman kanta kamar an ɗora mata duniya saboda girma.
Kofin hannunsa ya ajiye yana gyara zaman da ya bashi damar fuskantarta da kyau.
"Naila" ya faɗa yana kallonta.
Still Naila da zuciyarta take bugawa da sauri-da sauri bata ɗago ba.
"Ki ɗago ki kalleni ko zaki ganeni, tunda kin kasa tuna muryata" ya faɗa a hankali kamar mai tsoron magana.
A hankali Naila ta ɗago, ƙwaƙwalwarta ya shiga lissafin kyansa amma har lokacin kai tsaye ta kasa gano wani abu ɗaya na shi. Domin fuskar waccen Sulaim ɗin da ban da wannan, shi waccen aikin wuta ne sana'arsa, ga rayuwar ƙunci da kaɗaici da yakeyi saɓanin na yanzu da yake rayuwarsa cikin raɓa dare da rana, iyayensa da danginsa duk su na kewaye da shi, kowa gudun ɓacin ransa yake yi, dai-dai da muryarsa ya canza yaƙara zama mai sanyi da daɗin sauraro, irin sanyin da kuɗi da nutsuwa ne kawai suke iya samar da shi.
Ganin da gaske Nailan ta kasa tunashi sai ya ɗan motsa laɓɓansa tare da buɗe muryarsa kaɗan yadda zata ji shi da kyau..
"Yankin Tudu! Daular Sarki Hammam, sassanin wasannin ƙarshen mako, gidan Abduh Dhahab maƙerin Tukwanen ZINARE! Sulaim mai kaiki Makaranta a keke"
Sulaim yaƙarasa faɗa yana ɗage dukka girarsa murmushin yadda Naila ta zaro dukka idanunta na ƙara faɗaɗa a saman fuskarsa.
Da sauri, ƙwaƙwalwar Naila yake ƙara lissafa mata komai na fuskar Sulaim, kafin idanuwanta suyi juyewar da tayi baya zata kife ƙasa.
Da sauri ya kamota ya gyara mata kwanciya.
Bayan wani lokaci
Lokacin da Naila ta farfaɗo babu mutumin da ya ce mata shi Sulaim ne, sai Ummi Aysha. Da taimakon Ummi Aysha ta koma sashensu.
Tana kwance Kaka ta shigo da Dinner a hannunta, kafin ta karɓi abincin ta ce;
"Kaka da gaske ne?"
"Da gaske me? Tunda ke babu nutsuwa a lamarinki"
Kaka ta faɗa kamar zata kai mata dukka.
"Kaka to kiyimin bayani, ni fa gani nakeyi kamar na daina gane komai, Yasar ya taɓa faɗamin Muhammad Dhahab shine ya kafa Dhahab kuma babu wanda ya san Asalinsa amma wa su sunce ɗan asalin ƙasar Abyad ne, Ni fa kamar ma na ƙara manta fuskarsa" Naila ta faɗa da iyakar gaskiyarta.
Abincin Kaka ta dangwarar mata tana jan ƙaramin tsaki, haɗe da cewa;
"idan zaki nutsu ki nutsu domin da gaske Sulaim kika gani, idan ya shigo dubaki mutuwa zaki yi ba suma ba, tunda kuɗi da raɓa sun sa kin zama fara🦗, daga ganin mutum ya ce miki Yankin Tudu sai ki Sume, kuma a haka ki ishi mutane da daa Sulaim yana raye da shine kaza da shi zaima kaza, Ni ce ma shi ina zan kulaki na zama mai arziƙi"
Kaka taƙarasa faɗa tana taɓe baki
kafin ta bar daƙin Naila ta miƙe da sauri tana sha gabanta..
"Kaka dan Allah to kiyimin bayani, yanzu Ni ce fara🦗?" Naila ta tambaya tana marairaice fuskarta.
Domin sauƙaƙawa Naila saboda an turo neman izinin Sulaim zai shigo dubata Kaka ta zaunar da ita. Bata rage mata komai ba a labarin da Malik ya bata, sannan ta ɗora da nasihar Nailan ta kula, saboda daga yanzu komai zai iya sauyawa.
Naila bata motsa ba, a hankali komai yake warware mata, irin kuɗin da Malik yake kashewa da irin girman da yake ba su ashe da dalili, Dagaske kamar yadda take ji ajikinta ashe Sulaim bai mutu ba ya na raye.
Naila bata kawo zuwansa kusa ba tunda ba'a daɗe da yin sallar magrib ba, living room ta fito ta zauna, Kaka da bata yarda da Mai hidimar dafa abinci ba tana madafi tana shirya kayan tarbar Sulaim duk da tasan ba lallai ya ci ba.
Ana knocking Naila ta tashi da kanta ta tafi buɗewa.
Tana buɗewa da fuskarsa tayi tozali babu kowa a bayansa, jikinsa sanye da kaya masu kauri baƙaƙe, sai hular sanyi mai taushin daya rufe rabin girarsa. Hannayensa zube cikin aljihun wadonsa, da alama sanyi yake ji.
kallonta Sulaim ya tsaya yi yana karantar yanayinta, ganin zasu jima a haka ba tare da ta iya cewa komai ba sai ya kamo hannunta suka dawo living room ɗin tare, a gefen Couch ɗin da ya zauna, ya zaunar da ita.
"Ina wuni" Naila ta faɗa a hankali tana kallon dogon hancinsa ta gefen fuskarsa.
Hannunta dake cikin nasa ya matse alamun ya amsa.
"Ka yi haƙuri" shima bai amsa ba still hannunta ya ƙara ɗan matsawa alamun ya ji.
Waiwayowa ya yi yana kallon fuskarta da ta sunkuyar, cikin sanyin muryar daya haɗe da zazzaɓin dayaƙi barinsa ya ce;
"Na dawo Abyad ina murnar zan ganki har ciwo nake yi amma kin ganni kin suma, kin daina son abotarmu ko?"
Naila da daɗi ke neman gusarwa da nutsuwa dasauri ta ɗago kanta tana girgizashi.
Daɗin muryarsa da yadda kai tsaye yake nuna kulawarsa akanta ya sata sakin murmushi kafin kuka mai sanyi ya biyo baya.
Yau ga ta ga Sulaim sun girma sun zama manya kuma a raye ba a mace ba.
"Na tafi bakyason ganina?" Ya tambaya kamar ba Sulaim ba.
Kai Naila ta girgiza da sauri tana ƙanƙame hannunsa.
"Ki kirata mu gaisa zan tafi tunda kuka kikeyi bakyason gani na" Sulaim ya faɗa da wasa.
Naila da take jin kamar su dawwama a haka kai ta ƙara girgizawa da sauri.
" Kiyimin magana Naila, ki kalleni a waccen Sulaim ɗin, ba wannan ba, ( ya faɗa yana nuna ƙirjinsa) kiyimin hirar da kika saba, ki bani labari, Kinyi kuka da ake ce na Mutu?"
Ya tambaya idanuwansa na kai kawo a saman fuskarta..
Naila da daɗi yayiwa yawa har ta rasa wajen zuba extra kuka ta fashe da dashi mai tafe da dariya lokaci ɗaya...
Barkanmu da dare🍜
[9/5, 8:51 PM] Maman Amatullahi: 🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥🔥
ZINARE
2
BY
NAFISA ALIYU SASAAL
CHAPTER 2;
*WASIƘAR ALƘAWARI*
12
NAILA;
Bansan yadda zata misalta daɗin hirarsu a wannan dare ba, amma ya tunamata da abubuwa da dama, sai take jinta kamar lokacin da take yarinya ƙarama a Yankin Tudu. Sulaim bai bar Sashensu ba sai 11:00pm.
Barcinta na wannan rana na musamman ne mai cike da mafarkan cikar muradi, domin Sulaim da ta rayu da soyayyarsa a cikin zuciyarta a matsayin matacce ya bayyana a zahiri gareta matsayin rayayye, sam bata hasosa dukiya ko girman Dhahab da ƙawarsa a matsayin abinda zai zama linzamin Soyayyarsu ba, kulawarsa da mutuntawarsa garesu ya fiyemata komai.
Noorhan; tun tana sa ran Sulaim zai biyota masauƙinta ko ya turo aka kirata har ta cire rai.
Tana kuka ta kira Mahaifinta ba tare da bin ba'asi ko sanin gaskiyar abinda ya haɗasu ba, Mahaifanta ya ce ta turamai number Malik don bazai iya kiran Sulaim kai tsaye ba.
Ko da ya kira Malik kai tsaye Malik ya shaidamai wannan lokacin na Ahalin Sulaim ne kuma itama Noorhan tasan da haka shekararsu nawa suna tare bai ziyarci Gida ba? Idan zata jure to, idan kuma bazata jure ba zai sakota a jirgi ta dawo Gida.
Bayanin Malik ya soki zuciyar Mahaifin Noorhan, a ganinsa ƴar sa abar da za'a tattalace duk uzurin da Sulaim zai gabatar ya zamana tana gefensa.
Batare da Shawara da Noorhan ba, ya ce wa Malik su sako ɗiyarsa a jirgi ta dawo Gida.
Gajeran Saƙo Malik ya turawa Sulaim, tabbacin ya gani kuma bai ce komai ba, yasa ya naimi tikitin tafiyar Noorhan nan take.
★washe gari Noorhan tana gama Breakfast Malik ya tura mata saƙon ta kimtsa Jirgin karfe biyun Rana zata bi, da mamaki take kallon saƙon kafin ta kira Mahaifinta. Da yake bawani tarbiyya aka horar da ita a kai ba, kai tsaye bayan ta ji shi ya yanke hukuncin tafiyartata ba tare da naiman shawararta ba ta fara yimai rashin kunya da faɗar maganganun masu kaushi.
Tasan bata isa ta jawa dukiyar Sulaim asara ba tare da wani dalili ba don haka ta shirya kayanta tana kuka.
Ummu Malik;
duk da Sulaim bai shigo gaishesu ba tukunna taji daɗin aiken kuɗin da ya yi musu, hatta Barirah da ƙunci ya hana sukuni ta ji daɗin kyautar kuɗin.
Bayan sunyi Dinner Ummu Malik take yiwa Simbi da Barirah faɗan su ja Naila a jiki, kishi tsakaninsu ya kau, su tuna Yankin ɗaya ne ya samar da su, kar su bari son duniya ya makantarsu, su yi biyu babu.
Barirah kai tsaye ta nuna sam bazata iya mutunci da Naila ba, saɓanin Simbi da take ganin hakan kamar wani dama ne na sanin halin da Naila da Sulaim suke ciki, idan ta ja Naila a jiki dole duk zurfin cikin Naila tasan wani abu akan Soyayyarsu.
Ummi Mairam;
Duk kyautan kuɗin da Sulaim ya yi musu bai birgeta ba sam, burinta ya zo gareta ta gabatar masa da Barirah ko Allah zaisa ya amince mata.
Gaba ɗaya bata sa abincin kirki a cikinta ba har zuwa washe garin da aka sanar da ita Sulaim