x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 25 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 72001 words
  • 75000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 749

07 Oct 2025
amince aje da ita.

LV Jogger da free size shirt dukka baƙaƙe sai GG sneaker ya yi sassanyar adonsa mai birgewa, don tafiya Airport.

Noorhan dake lulluɓe cikin Abaya kallon takunsa take yi zuciyarta na ƙara macewa Soyayyarsu.

Idanuwanta ta lumshe a hankali tunanin na zurfafa a cikin daƙiƙu, wai gasu sunyi aure har sun haifi yara kyawawa irinsu..

A gurguje Noorhan taje gida ta kwaso Kayan buƙatarta da Passport.

Sulaim bayason takura shiyasa shi da Noorhan kowa ya zauna a mabanbanta waje. Hakan ba ƙaramin daɗi yayiwa Malik ba, itama Noorhan bata wani damu ba tunda zata je Abyad ƴan uwansa su san da zamanta.

Ummi Aysha;

Ummu Malik da Simbi ne suka je dubata, laƙwas tayi kamar gaske, tana amsawa daƙyar don tasan Malik ne ya sanar da su.

Daganan su Ummu Malik da Simbi ɓangarensu Naila suka wuce don duba nata jikin, sai dai a tsaye suka samu Naila tana ciye-ciye haɗe da bawa Kaka labari.

Naila batayi rawar kan nuna murnarta ba kar su gwaleta, saboda wannan ne karonsu na farkon haɗuwa fuska da fuska tun bayan barin su Yankin Tudu.

Sai dai yadda suka rungumen Naila da Kaka kuma suka saki jikinsu yasa itama Naila nuna farin cikinta.

Bayan sun motsa baki da cookien da kaka ta gabatar musu Ummu Malik ta ce;

"Ashe ƙafa ya yi sauƙi Naila, ai a bayanin Malik ya ce Farheen ta kira tana kuka, wallahi sai muka ɗauka ƙafar karyewa tayi, Allah Ya kiyaye gaba, itama Ummi Aysha Allah ya tashi kafaɗunta"

Naila da Kaka wayancewa suka yi suka amsa da "Ameen" har da Simbi data ƙurawa Naila ido. Domin Ita bata yarda da jin ciwon ƙafar Naila ba wani abun take zargi daban.

Gaba ɗaya sai hirar ta su ya koma kamar na yaƙe domin daga Naila har Kaka jira sukeyi su Ummu Malik su tafi Naila taje ta tambayo Farheen abinda ya faru.

Fuskantar hakan yasa Ummu Malik yi musu sallama amma a nata ɓangaren gani takeyi baƙonta ce tasa suka kasa sakin jiki da su.

NAILA;

Suna fita kaka ta ce;

"Maza tashi kije kiji menene ya sameta"

Guntun light orange rigar da bai ƙarasa ƙasa bane sosai a jikin Naila Abaya mai maɓallai ta ɗauko ta ɗora akai ta ɓame maɓallan da sauri, bata damu da Ɗankwali ba tunda duk cikin gida ne, yasa ta yafa malulluɓin Abayar a kanta...

Ummi Aysha;

Bayan sun shirya faɗuwarta ita da Farheen da karyewar ƙafar Naila har sukayi nasarar Sulaim ya ce zai taho, sai ta rasa kuma ta hanyar zata nunawa Sulaim fuskar Naila ta hanyar bazatan da zai birgesa, don haka ta fara neman layin Malik, cikin sa'a tana kira ta samesa, ya shaida mata sun iso Airport ɗin Ƙasar Abyad.

Tana yunƙuri kiran Farheen domin samun mafita amintacciyar Hadimarta ta naimi izinin shigowa.

Tana jin ta ce Naila ce tazo gaisheta ta gyara zamanta tace ace ta shigo.

A ɗan gefen Couch Naila ta zauna ta gaisheta har ya sanar da ita shigowarsu Ummu Malik Sashensu amma kuma takasa tambayarta maiyafaru su Ummu Malik suka ce ta karye a ƙafa.

Ummi Aysha ta gane ina Nailan ta dosa tunda ta sanar da ita shigowarsu Ummu Malik wajen su.

Cikin dabara da sanyi Ummi Aysha ta ce;

"Naila ɗan taimaka ki dafamin Noodles mana ɗazun Farheen ta dafamin sam banji daɗinsa"

Da sauri Naila ta ce "to" tana miƙewa.

Dakatar da ita Ummi Aysha ta yi ta hanyar cewa;

"rage wannan Abayar Naila karki samu matsala da wuta, ga scarf can ki ɗaure kanki"

Babu damar musu, don haka Naila cikin kunya ta ɓalle maɓallan Abayar jikinta, ta cire ta ajjiye a gefe da mayafinsa, sannan ta ɗauki ɗan Scarf ɗin da Ummi Aysha ta nuna mata.

Zata tafi Ummi Aysha ta ƙara dakatar da ita tana cewa;

" ɗaura mana mu gani Naila"

Cikin kunyar daya kasa sakin Naila ta ɗan ɗaurashi, kwantaccen sumar kanta ya bayyana agaban goshinta da bayan ƙeyarta.

Murmushi Ummi Aysha ta yi kafin ta bata umarnin tafiya.

Da taimakon masu Hidimar sashen Naila ta isa madafin Ummi Aysha.

Bayan fitar Naila ajjiyar zuciya Ummi Aysha ta sauke tana gyara kwanciyarta.

Sai dai kamar ana jiran fitar Naila, motsin Dhahab ya sauya saboda motsin motoci da ƙarin jami'an tsaron da suka fara mamaye kowani sashi na Dhahab.

Ummi Aysha murmushi ta saki lokacin da ta ji alamun kusantowar motocin sashenta, dalilin jiniyar da ke bawa Securities alamar buɗe ƙaramin gate ɗin da yayiwa Sashenta iyaka da ragowar sashen dake cikin Dhahab, tun kafin isowarsu kar Sulaim ya ɓata lokacin zaman daƙiƙu a cikin mota.

Farheen dake sama tanajin alamar chanjin da rabonta da jin irinsa tun shekarar da Sulaim ya ɗauke Naanah tayi wuf ta zura tsadadden abayarta, turare kuwa kamar zata juyeshi dukka ajikinta. Kamar zata faɗo haka take saukowa daga stairs da gudu kar ayi babu ita, domin tasan da zarar ya shiga to ma su tsaron lafiyarsa da zasu jirasa a living room bazasu barta ta shiga ba kuma ko sun kira Malik ba zai bari ba.

A hankali ƙarfin ƙamshin Sulaim ya fara mamaye living room ɗin Ummi Aysha kafin ya fara gangarawa ɗakunanan sashen da madafin abincin da Naila take ciki.

Ido Ummi Aysha ta lumshe ƙwalla na taruwa a cikinsu lokacin da tayi tozali da jarumin Ɗanta.

Bai yiwa kansa mazauni a ko ina ba sai gefen lafiyayyen tattausar katifar dake saman gadon da take kwance a kai, kafin ya gaisheta sai da ya fara rungumarta ya sumbaci goshinta da hannunta, sannan ya gaisheta Cikin taushin murya da Yaren ƙasar Abyad da sukafi amfani da shi. Kuka ta fashe dashi tana ƙanƙame hannunsa ta kasa amsawa.

Noorhan da Malik da suka zauna a Couch ɗaya Ummi Aysha ta kalla.

Cikin girmamawa suka gaisheta, da kai ta amsa kafin ta yafito Malik da hannu, raɗa tayimasa a kunne, kan ya yiwa Securities magana su bar Naila ta shigo.

Kafin Malik ya fita aiken Ummi Aysha suka gaisa da Farheen, Sannan Noorhan da take kallon komai dalla-dalla tana lissafa iya adadin dukiyar da aka kashe kafin mallakarsa ta gaishe da Farheen tana hura hanci.

Da Sulaim Farheen tayi gaisawar ƙarshe tana murmushin jiran ta inda Naila zata ɓullo.

Noorhan zamanta ta gyara tana jiran Sulaim ya gabatar da ita ko su Ummi Aysha su tambayesa wacece ita, amma sai taji shiru har Malik dayake gimtse dariyar gano Plan aka shiryawa Ubangidansa ya dawo daga aiken Ummi Aysha ya zauna.

Naila ƙamshin turaren Sulaim har cikin siririn hancinta, jin alamun jiniya yasa ta matsu ta koma gurin Kaka taji menene yake faruwa.

A plate mai kyau ta juyo Noodles ɗin dayake tiriri da ƙamshi mai daɗi, Securities ɗin data gani yasa ta ɗan ja da baya, amma suka bata umarnin ta shiga inji Ummi Aysha.

Jiki a sanyaye Naila ta kutsa da Sallama.

Malik, Noorhan, da Farheen, idanuwansu kamar zasu zazzago wajen kallonta, musamman Noorhan da Malik.

Gaishesu Naila tayi Noorhan da Malik da kaa suka iya amsawa, saɓanin Farheen da ta amsa tana ɓoye dariyarta, da yaba basirar Ummi Aysha.

Sulaim bai damu da shigo ba tunda bai san wacece ba, hannun Ummi Aysha ya ƙara kamowa zai sumbata, jajayen siraran laɓɓansa suka maƙale a kai dai-dai lokacin da Naila ta ƙaraso ta ajjiye abincin hannunta a table ɗin dake gefen bedside.

Da tsoron ganin baƙin fuskar dayasa ta jin kunya tana ɗan zare ido ta kallesa da harshen ƙasar Abyad daya kama sassanyar muryarta ta ce;

"Ina wuni Sir,"

Sulaim ya kasa amsawa ya kuma kasa cire laɓɓansa daga hannun Ummi Aysha balle ya ajjiye hannun, lumsassun idanuwansa da zazzaɓi ya kama ya ɗago ya zuba mata....

😄
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

10

SUFYAN;
Zamewa yayi daga saman wajen yana kallon baƙin tiles ɗin da jajayen idanuwansa. dagaske Mahaifiyarsa Hindu ce a ciki. Kenan ba zai ƙara ganinta ba, ta yi wahala ta ɗorashi akan aƙidar gina kansa da kawowa Yankinsa cigaba ba zaman yin gasa ko kashe wasu ba. Ita ta fara tunamai, Sulaim da Abduh sun maƙale a zuciyar mutanen Yankin su ne saboda cigaban da suka kawo, don haka shima ya fita ya yi ilimin da babu mai irinsa ya kuma kawo cigaban da zai zama abun yabo wa mutanen Yankinsa, kuskurenta ɗaya don zuciyarta akan kowa matsawar zai zama abinda take buri, saɓanin Mahaifinsa da burinsa ya tusa masa aƙidar da suka taso akai na kashe-kashe da ramuwar gayya.

Da ace idan ya fasa ramin domin bazai kirasa kabari ba, zai samu masu tsayamasa su karesa daga Ɗayyib ya ciro Mahaifiyarsa da ya cirota ya yi mata wanka ya kaita Maƙabarta ya binne kamar kowa, amma ba shi da wannan damar.

Tuna irin azabar da ya san dole zatashashi a hannun Mahaifinsa, wanda kuma ita kaɗaice zata iya basa labari amma bata raye yasa ya fashe kuka. Tsanar Mahaifiyar da ta yi masa ƙarya saboda duniya na mamaye ko ina nashi.

Ɗayyib har ya yunƙura zai miƙe idanuwansa suka sauka kan ɗan na'urar da Sufyan ya ajjiye, kallon Sarki Hammam ya yi yana nazartar yanayinsa kafin ya ce ;

"Sufyan ya shigo nan ne?"
Sarki Hammam cikin Basarwa,dakiya da shariyar da ya ɗauki tsayin shekaru yanayi ya ce;
"Ya shigo ya gaisheni bai jima ba ya miƙe, da alama sauri yake yi."

Kai Ɗayyib ya jinjina ya wayance ya durƙusa ya ɗauke na'urar.

Da yake dare ya yi sosai Ɗayyib sashensa ya wuce da Na'urar bai nemi Sufyan ba. washe gari da sassafe
yana fita kai tsaye wajen mutumin da ya taɓa bincikamai wayar Naila ya nufa da kansa. Tabbacin na'urar naɗar sautin da ake amfani da shi don naɗar sirri ya tabbatarmai, tare da shaidamai dole wani ne ya taho dashi daga wata nahiyar, Sarki Hammam ba shi da ikon mallakarsa ta daɗin rai.

Kamar zai huda ƙasa haka Ɗayyib yake taka sawayensa, zuciyarsa kamar ana gobara saboda yadda ko ina nasa ya ɗauki zafi.
Dakewa ya yi, ya cije bayan ya dawo Gida har sai da ya bari dare ya yi sannan ya nufi wajen Sufyan.
Kaifaffen wuƙar ƙugunsa ya shafa yana lumshe fararen idanuwansa kafin ya buɗe su, sun koma jajaye. Babu sallama ya kutsa sashen Hindu....

UMMI MAIRAM;
Tun ranar da hatsaniya ta haɗasu da Naila take kuka, Mahaifinta mai son zuciya da fifita farin cikin nasa akan na wani, sai mita yake yi yana kwashewa Naila albarka, acewarsa bai san uban daya kawosu Dhahab ba. Dama daga gani Malik baƙin ciki yake yi da zamansu. Ban da haka tayaya zai marawa Naila baya kai tsaye ba tare da bari a yankemata hukunci ba?

Kukan da Mairam ta dage tanayi kamar ƙaramar yarinya da zugata da Mahaifinta yakeyi ne yasa Mahaifiyarta ta magantu;

"Kina ba ni mamaki Mairam, mahaifiyar yarinyarnan tun kafin Mijinta Mahmoud ya mutu take hidima da ke, Mijinta ya mutu ta dawo kula dake gaba ɗaya, sanadiyyar haka ta rasa ranta, a tunanina duk ranar da kikaga Naila sai kin fi kowa farin ciki, amma son zuciya na neman makantar da ke, Yaron nan da kike kwaɗayin abinda ya tara yana da Uwa kuma ko ya mutu baki da gadonsa, yana kyautata miki dai-dai iyawarsa, amma ke burinki ya manta uwarsa ya nunawa duniya ke ce kika haifesa tun da shi mahaukaci ne ko? Ko Barirah kinsan ba halin ƙwarai gareta ba, amma duk kin toshe jinki da ganin ki burinki kawai ya aureta ki samu fada a wajensa, ai sai mu ga idan kina da ikon auramai son ranki, sha-sha-sha mara tsayawa iyakarka kawai"

Kaf maganganun Mahaifiyarta Mairam bata ɗaukesu da muhimmanci ba, a ganinta ai Ummi Aysha guduwa tayi mai zai sa a yanzu ta dawo Sulaim yafi fifitata a kanta?

Ummi Mairam bata ƙara birkicewa ba, sai da Barirah ta kirata a waya ta sanar da ita ai tuni ma Sulaim yasan da zaman Naila tunda har Malik ya naima mata tsadadden Makaranta da matsuguni na musamman ɗin da ko ita da ta zauna da shi bayan Mahaifiyarsa ta gudu ta barshi bata samu ba.

Tana cikin jinyar zamansu Naila a waje na musamman a Dhahab, sauyin Dhahab alamar Sulaim ya dawo ya ƙara hargitsata. idanuwanta har zurma sukayi ciki kamar zasu faɗo saboda zarensun da takeyi tana jiran Sulaim ya fara shigowa Sashenta ya gaisheta kafin ya isa ga Mahaifiyarsa.


SASHEN UMMI AYSHA;
ido Naila ta ɗan zare tana kallon laɓɓansa da ya kasa ɗaukewa da ga kan hannun Ummi.

Ƙara maimaita gaisuwarta ta yi da harshen nasara ko Yaren ƙasar Abyad ne baya ji.
Still bai amsa ba sai kallon fuskarta da yake yi kafin ya gangaro da kallonsa kan kyawawa ƙafafuwanta da take tsaye a kai.

Ido Naila ta ƙara zarowa, Ummi Aysha da daɗi yakama kamar ta tashi ta rungume Naila, a hankali ta ce;

"Zaki iya tafiya Naila, ki ce ina gaishe da Kaka"

Sulaim hannun Ummi Aysha ya zame a hankali daga kan laɓɓansa, sai dai bai ajjiye hannun ba mannawa ya yi a gefen fuskarsa yana lumshe idanuwansa. Kunya ce ta mamayesa son Mahaifiyarsa na ƙara kamashi.

Don ya gane plan ta shiryamai tunda ga Naila tsaye akan ƙafafuwanta kuma saboda ta nunamai Naila a lokacin da zai fi birgesa sai tasa ta dama mata Noodles domin ya yi tozali da ita.

Ƙara buɗe idanuwansa ya yi ƙaɗan yana kallon yadda Naila take yunƙurin ɗaukar Abayarta da sauri, ba tare da ta zura ba ta nufi hanyar fita.

Kamar wanda ya ƙware haka ya ƙirƙiro tarin dole.
Ummi Aysha da sauri matse dariyarta tana ce wa Naila;

"Naila tsaya ki nutsu ki lulluɓe jikinki kinji"

Malik da Farheen kamar jiran fitar Naila sukeyi. Tana fita suka saki dariyar da babu sauti haɗe da dafe bakunan su.

Sulaim hannun Ummi Aysha dake gefen fuskarsa ne fara motsawa, alamun dariyarsa takeyi.

Cikin taushin Muryar dake fita da sautin mai sanyi ya ce;

"Ummiih, kinsa na ji kunya, wani iri nake ji, dama wayo kikayimin"

Ummi Aysha miƙewa ta yi zaune tana dariya haɗe da rungumoshi, shima ƙaramin dariya ya saki yana ɓoye fuskarsa a bayanta.

Noorhan hannunta da ƙafafuwanta ne suka fara rawa, wayarta da ta riƙe tana dannawa kamar batasan abinda suke yi ba, shima yafara rawa.

"Wacece wannan yarinyar, Sulaim bai sanar da ni yana da ƙaramar ƙanwa ba, maiyasa yake kallonta irin haka?" Noorhan ta tambayi kanta tana satar kallonsu Malik da har lokacin suke ɓoye dariyarsu...

NAILA;
Tana isa Sashensu ta ƙwalawa Kaka kira
"Kakaaa!!!"
Kaka da sauri ta fito tana tambayar "menene ya faru Naila?".

"Kaka wani mutum na gani tare da su Malik a sashen Ummi Aysha, Kaka kinganshi,?"

"A'a Naila banganshi ba, maiyasa sameshi" Kaka ta tambaya da son jin zance.

"Kaka yana da kyau, kinga yadda yake kallona, Ni kuma na ɗan zaro ido, kai Kaka ya ruɗarni wallahi"

Kaka da labarin yake yiwa daɗi dariya tasa ta ajjiye cokalin hannunta haɗe da cewa;

"sai ya ce miki me? Yana sonki?"

Tsabar yadda zancenta yayiwa Naila daɗi sai da ta saki dariya tana juya idanuwa ta ce;

"Kaka ko fa magana baiyi ba, kinga bakinsa hmmm😄!"

"Bakinsa me?? Ke ki saki jiki ki bani labari mai ya samu bakin na sa?" Kaka ta faɗa tana dariya.

"Kaka fa tsabar kyawuna da yake kallo kasa cire bakinsa ya yi daga hannun Ummi Aysha, ga idanuwansa masu kyau, shiyasa fa nima na ɗan zaro nawa idon, saboda ya ƙara ganin kyansu, yasan nima kyakkyawa ce. Ko da yake ni fa bai wani birgeni ba, kamar zai yi tsaho da yawa"

A wannan karon Kaka garin dariya har cokalin gefenta ta wurga, da salon ƙara zurma Naila tunda tuni ta samu labarin zuwan Sulaim ta bakin Hadimansu ta ce;

"Kuma baiyi miki kama da wani wanda kika sani ko kika taɓa gani ba?"

Ɗan jim Naila tayi kafin ta ce;

"Ai Sulaim ne kawai da ya girma a raye ya samu kuɗi zai yi irin wannan kyan, wai Kaka kinga idanuwansa kuwa? Sak irin na Sulaim idan yana kallona a Yankin Tudu, amma wannan sai wani iyayi ko gaisuwata fa bai amsa ba"

Kaka da dariyarta yaki yankewa miƙewa tayi tana hasaso duk ranar da Naila ta gane Sulaim yana raye yaya zata ji??..

Kamar sakarya haka Naila ta koma lokaci zuwa lokaci sai ta zaro ido ta ƙyaƙyale da dariya.

A living room ta zauna tana roƙon Allah Ya sa Ummi Aysha ta aiko kiranta, amma har wajen goman dare bata turo ba don haka ta haƙura ta kwanta barci.

A SASHEN UMMI AYSHA
Farheen ce ta fara miƙewa tana yiwa Noorhan maganar ta zo ta kaita masauƙi, kafin Malik ya bi bayansu, don duba gyaran da aka yiwa Masauƙin Sulaim.

Bayan sun fita zame jikinsa Sulaim ya yi, ya zauna da kyau sannan a hankali ya furta;
"Na gode"
Kai Ummi ta janjinamai haɗe da cewa;

"Nasan ba lallai ka ziyarceni ko da kaji ina halin jinya ba, saboda girman laifina daka kasa mantawa, amma idan na haɗa da ni da ita, nasan dole ka ziyarcemu, ba ni da abinci mai daɗin da zan gabatar maka ko wani abu da zan shiryamaka da zai birgeka sama da nuna maka fuskar masoyiyarka da ka manta tun zamanin ƙuciya.

faɗamin ya ya kaji da ka ganta? Ka ganta kyakkyawa ko? Tun da gashi hannuna har maƙalewa ya yi"

A karon farko Sulaim ya saki dariyar da ya bayyana jerarrun haƙoransa yana miƙewa saboda kunya.

Itama Ummi Aysha haƙoranta ta ƙara washewa ranta fari fes, zata iya rantsewa tun bayan sanin Sulaim yana raye bata ƙarajin daɗin da ta ji irin na yau ba.

Ta ji zafin jikinsa ba kamar na mai cikakken lafiya ba don haka bayan fitarsa ta lalubo wayarta ta kira Malik.

Malik Bai ɓoyemata zazzaɓin da Sulaim ya kwana biyu yana yi ba.
Likintanta tayiwa waya, bayan sun gama tattaunawa ta miƙe ta ɗauki Noodles ɗin da Naila ta ajjiyemata, ai ko babu daɗi dole ta ci, balle daɗinsa abin a yabawa Nailan ne da tukwaici mai tsoka.

Ƙaramin Sashen dake jikin na Ummi Aysha aka gyarawa Sulaim, masu tsaron lafiyarsa zagaye da ko ina na sashen da Dhahab gaba ɗaya.

Noorhan; tana wanka tana Kuka, kenan Sulaim ya kawota ƙasar Abyad ne domin ya nuna mata matsayinta, suma mugayen ƴan uwansa suna kallonta amma ko su tambayesa wacece ita? Wallahi dole Sulaim ya sanar da su matsayinta idan ba haka ba ita ta sanar da su da kanta...

SULAIM;
Yana wanka fuskar Naila da yadda ta zare ido tana gaishesa da muryarta da ya sauya daga na ƴan yara zuwa na ƴar budurwa na kai kawo a cikin idanuwansa, kunnen da zuciyarsa.

Nailarsa da zama ƴan mata ta girma, to maiyasa bata gane shi ba?

Ya tambayi