x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 763

07 Oct 2025
rayuwa, duk da suma nasu Gidan ba laifi da kyansa dan yafi na dubban mutane a Yankin, yasa ta ke ƙoƙarin yi mata ƙara tunda batasan abinda ya kawota ba.

Cikin sanyi hali da na murya da kuma sanin girman na gaba Naila ta buɗe matsakaicinta bakinta mai ɗauke da siraran laɓɓa ta ce;

"Barka da Rana Ranki ya dade, da kin turo har gida zanzo nayi miki ba sai kinzo ba" murmushi mai kyau Hindu tayi tana dafa kafaɗarta saboda sanyi da daɗin muryarta da ya yi matuƙar birgeta ta ce;

" Karki damu ɗiyata gaba idan zan ƙarayi sai kizo Gida kiyimin" Kai Naila da gyaɗa itama da kyakkyawar murmushi a saman fuskarta.

Hindu da dabara take kallon duk wa su motsin Naila har aka fara yimata kitson da tace guda goma take so.

Kuɗi mai yawa kwatankwacin wanda Iyalan Sarki Hammam suke bawa Naila idan taje Gidan yi musu ƙananan kitso ta bata. Daƙyar ta karɓi kuɗin don sai da Kakarta ta saka baki.

Yanayin Naila da dabi'unta sun matuƙar burge Hindu, don da ba dan burin auren Mace ƴar Babban Birnin da takeyiwa Sufyan kwaɗayi ba, da ta amince Naila ta zama Surukarta ta din-din.

09132403788
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥



SASAAL
https://www.arewabooks.com/dashboard/info



08

ƊAYYIB.
Da ranar cin Kasuwa ya ƙara zagayowa, Harajin da zai kai iya adadin kuɗin gidan hayar da ya yi alƙawarin biyawa Sufyan na Shekara ɗaya a Babban Birnin Abyad ya tsawwalawa Ƴan Kasuwar Tukwanen Zinare. Wasun su har da kuka su na magiya amma ba bu wanda aka saurarawa. Sai bayan an tattara kuɗin ya zo yake basu haƙurin In sha Allahu Kasuwa mai zuwa hakan bazai faru ba. Dubban mutane ne suka koma Gida ransu a ƙuntace.

Ko da Ɗayyib ya tattara kuɗaɗen basu kai adadin abinda yake nema ba har sai da ya haɗa da wanda ya jima ya na tarawa.

Tun kafin zancen neman Auren Naila yaje ga kunnen Danginta da ita kanta da Mutanen gari Dangin Ɗayyib suka nuna sam basu amince ba. Ta ya ya Naila ƴar Gidan Mahmoud da yake Madinki talakan fitik zata shigo zuri'arsu? Hakan zubar da ƙima da mutuncin Masarautarsu ne don haka sam su basu yarda ba.
Da labari yajewa Jalal murmushi ya yi a zuciyarsa tare da bada Umarnin a nemawa Sufyan Auren Naila ba tare da jinkirtawa ba.

A ɓangaren Mutanen gari, ba su yi mamaki ba saboda sunyi zargin haka tun zuwan Hindu Gidan. A ɓangaren ƴan uwan Mahmoud da suke Uba ɗaya jiki na rawa suka amince ba tare da sanin Kakar Naila ko amincewar ita kanta Nailan ba.

KAKAR NAILA;
Da labari ya riske Kakar Naila tsabar zabura sai da miƙe bakinta yana rawa take ambaton Sunan Allah don tasan ruwa baya tsami banza kuma tun a zamanin Budurcin Babbar Ƴarta Yayar Mahaifin Naila tasan wacece Hindu da makircinta. Itace silar rushewar auren Ɗan uwanta da Yayar Mahaifin Naila saboda kawai ba su da kuɗi. Baƙin cikin rushewar auren ne ya yi sanadiyyar mutuwar Ƴarta.

To idan zata hana Yayanta auren Yayar Mahaifin Naila saboda talaucisu tun a waccen zamanin wani dalili ne zai sa yanzu ta amince Ɗanta ya auri Naila tunda su dai sunanan a Talakawansu ba bu abinda ya sauya?

Naila da take gyara dogon gashin kanta mai cika da tsaho a gefe ba tace komai ba, sai ƙwallar da yayiwa ganinta yana. Ba ta da abin cewa, tunda burinta macaccen burine a zahiri, amma a baɗini rayayye ne a cikin zuciyarta tunda da shi zata mutu.

Tasan ko da Sulaim ya na raye ba lallai ya so Mace irinta ba. Sai dai Mutuwarsa ya sa tanajin ƙwarin gwiwar da wataƙila ya na raye da zai iya auranta suyi rayuwar farin cikin da take hasashe.

Tasan dole wata rana, irin wannan ranar zata zo domin bazata dawwama a haka ba tayi aure ba, shiyasa tayi alƙawarin sawa kanta jarumtar amsar duk Namijin daya zo mata a matsayin Mijin aure, tunda son Sulaim a cikin zuciyarta ba Ɗan adam ba ne irinta balle ta yaƙeshi.

Kusa da ita Kakarta ta zo ta zauna tana kamo dukka hannayenta daga tazar gashin da takeyi.

Cikin tausayin jarabawar da yake samun Nailan akai-akai ta ce;

" karki kiyi kukan zuci ke kaɗai Naila ki fito da shi sarari muyi tare"

Naila tanajin haka ta saki Kukan daya maƙalemata tuntuni. Sun kai minti Talatin a haka kafin Kakarta ta jata Ɗaki. Manne da juna suka zauna kan Naila kwance a samar Kafaɗarta.

A hankali Kaka ta ce;
"Ba na jin tsanar Sufyan a raina duk da labarin ɗabi'unsa marasa kyau da nake ji a bakin mabanbanta Mutune, sai dai ina tsoron wani irin ƙulli Hindu ta ƙulla da har zaisa ta amince ki auri Ɗanta. Hindu Ƴar masu rufin asirce a Yankinsu, dalilin haka ta ƙulla makircin da ya haramtawa Habeebah yayar Mahaifinki auren Yayaanta saboda talaucinmu, domin sana'ar Ɗinki muka gada daga Iyaye da kakanni, dalilin wannan baƙin cikin Habeebah ta rasa ranta. Babban burin Hindu a waccen lokacin shine ta auri Ɗan babban Gida, Allah Kuma ya cika mata burinta. Babban Ɗa ga Ƙanin Sarki Yankin Tudu na wacce lokacin Ɗayyib ya nuna yana sonta, har sukayi aure. Abinda yake bani mamaki da tsoro shine idan har Hindu zata guji Ɗan uwanta ya auri Habeebah saboda Talaucin mu tun a waccen zamanin, wani dalili ne zaisa yanzu ta bari Ɗan da ta haifa a cikinta jinin Sarautar Yankin Tudu a wannan zamanin da burika suka yi yawa ya aure ki duk da ƙin amincewar da mutanen Masarautar suka nu na kamar yadda na samu labari?"

Naila ba tace komai ba sai ƙara ƙanƙameta da tayi da dukka hannayenta, a haka barci ya fara ɗaukarta.

Sai da aka kira Sallar la'asar sannan suka miƙe, kowannen su zuciyarsa ba daɗi.

Har dare ya raba Kakar Naila ta kasa runtsawa, sai kai da take girgizawa lokaci zuwa lokaci saboda zuciyarta dake hasaso mata ai gara Halayyar Hindu da Halayyar mutanen cikin Masarautar Yankin Tudu.
Hannuwanta ta sarƙe waje ɗaya, Allah Ya ɗauki ran Mahmoud da Mahaifiyar Naila a tsakankanin Shekaru kaɗan kuma Allah ya jarabceta da mugayen Ƴan uwan uwa da na Uba gaba ɗaya idan aka cireta ita kaɗai ba bu wanda ya ke son Naila ko ya raɓeta sai domin buƙatar kanshi. Idan har ta zuba Ido Naila ta auri Sufyan to tabbas taci amanar Naila ba kuma zata yafewa Kanta ba, dole ta samo mafita ko da kuwa zai kaita ga gaban Sarki Hammam ne, don Masarautar Yankin Tudu tamkar Masarautar Uƙubane ga baren cikinta har ma da Ƴaƴan cikinta.

Naila shafa gefenta ta yi taji ba bu Kaka. A hankali ta miƙe, a tsakar gidansu ta hangota ta na zarya. Da sanyin tafiyarta ta ƙarasa bayanta. Cikin taushin harshe ta fara magana;

"Lokacin da na wayi gari ba bu Sulaim ya ƙone, na ji raɗaɗi a raina, da na zo na rasa Mahaifi sai na ƙarajin raɗaɗi amma ba irin wanda naji lokacin da na rasa Sulaim ba. Da rasa Mahaifiya sai na ƙarajin raɗaɗin da sam ba shi da haɗi da irin waɗanda na ji a baya. Abin nufi zafin rasa abu a zuƙatan mu na da alaƙa ne da yanda matsayin abun yake a wajen mu, saboda haka nasan abinda kike ji Kaaka, amma karki bari hukuncin Ubangiji ya hanaki barci wajen tunani har ki kasa neman mafita a wajen Shi. Zuciyata mai kaushi ce akan abinda ba na so Kaaka. Auren Sufyan ba ya nufin komai gareni balle har ya hanani barci, abu ɗaya na sani, idan abu mara daɗi ya sameni kuma na jure na yi haƙuri to tabbas Ubangiji Zai musanyamini da mafi alkhairinsa."
Naila ta ƙarasa faɗa da siririn kuka tana ƙanƙame Kakarta.
Itama Kakaa da rawar murya ta ce;
"Hakane Naila, amma ki sani zanyi iya yina don samar miki mafita domin nasan Hindu dole ta na da wata manufa, Naila ba na son rasaki, ke kaɗai nake gani na ji daɗi"
dukkansu kuka suka sa, su na ƙara ƙanƙame juna a haka Naila ta jata suka koma ɗaki.

Sun ɗauki tsahon mintina a haka kafin Naila ta ce;
" Maiyasa ki ke tsoron Masarautar Yankin Tudu, ko saboda kashe-kashen da akayi shekarun baya ne?"

Kai Kaaka ta girgiza tana lumshe idanuwanta labarin asalin Masarautar kamar yadda Marigayi Mijinta babansu Mahmoud ya bata labari na dawo mata, fuskantar Naila ta yi ta ce, "kinsha tambayata wanene Abduh Dhahab su wanene ƴan uwansa ban taɓa baki labari ba, amma yau zan baki ko don ki fuskanci gaba"

```MASARAUTAR YANKIN TUDU```

Sarki Musa shine Sarki na farko da ya kawo sauyi mai girma a Yankin Tudu lokacin Mulkinsa. Daga wannan lokacin mutanen Yankin suka samu ƴanci da sauƙin abubuwa da dama, da shigowar gwamnatin sama-sama cikin lamuransu. Sarki Musaa yana da ƴaƴa da yawa Maza da Mata daga Uwaye daban-daban amma wanda ya yi zarra a cikin su kuma ya fi ƙarfin arziƙi shine ABDULYASAR MUSA DHAHAB, Abdulyasar su biyu Mahaifiyarsu ta haifa, kafin Allah Ya ɗauki ranta. Matsi daga Kishiyoyi da asirce-asirce kala-kala da har ya yi sanadiyar mutuwar ƴar uwarsa, shi kuma yake fuskanta azaba daga ɓangaren kishiyoyin Mahaifiyar su bayan ranta ya sa Mahaifinsa Musaa ɗaukeshi daga cikin Ƴan uwansa zuwa Babban Birnin Abyad wajen Abokanan Kasuwancinsa don yin ilimin zamani dana Addini.

Anan Babban Birnin Abyad Abdulyasar Dhahab ya yazama Babban Ɗan kasuwa.

Kasuwanci Zinare yakeyi da taimakon Bature Francis Ɗan Aminin Mahaifinsa da ya ɗorasa a hanya har yazama hamshaƙin mai Arziƙi.
Dalilin wannan Kasuwanci na Zinare da ya ɗauka da matuƙar muhimmanci sama da Abokanan Kasuwancinsa ya sa suka sauya mai Suna daga Abdulyasar Musaa zuwa Abdulyasar Dhahab.

Bayyanar Abdulyasar Dhahab a Yankin Tudu a matsayin hamshaƙin ɗan Kasuwa babban abin alfahari ne a wajen Mahaifinsa Sarki Musa. Bayan dawowar Abdulyasar, babu wanda yasan dalili Gaba mai ƙarfi ya sarƙe a Masarautar tsakanin ƴan uwa biyun da suke aminai wato Sarki Musa Jamil Kakan-Kakan Ɗayyib Mahaifin Sufyan.

Abdulyasar bai jima da dawowa ba Allah Ya amshi ran Mahaifinsa Sarki Musa. A waccen lokacin anso naɗa Abdulyasar a matsayin magajin Mahaifinsa ko dan ƙarfin arziƙinsa amma ya nuna bayaso da suka takura ya tattara ya gudu na ɗan lokaci. Dole aka naɗa Yaya ga Sarki Musaa Mahaifin Sarki Hammam.
Ƙarfin arziƙin Abdulyasar Dhahab da taimakon shi ga Talakawa Yankin sai ya shafe sunan kowa a Masarautar su kamar shine Sarkin Yankin. Lamarin ya na sosa ransu matuƙa, wannan dalilin yasa suka fara kaiwa dukiyarsa hari ta kowacce siga tare da alƙawarin kaishi ƙasa ko ta halin ƙaƙa.

Su na cikin wannan yanayin matar Abdulyasar Dhahab ya aura bayan dawowarsa ta haifa ɗa Namiji Ubaidullah. Da taimakon Iyalinshi bayan ta haihu saboda kwaɗayin abin duniyar da sukayi alƙawarin za su ba ta na kaso maiyawa, ta taimaka musu suka kai Abdulyasar ƙasa, duk da haka Abdulyasar Dhahab bai bar rayuwar Ɗanshi Ubaidu ya lalace kamar yanda suka so ba, ya miƙa amanarshi hannunshi abokannan kasuwancinshi suka tafi da shi can wata nahiyar, shi kuma ya cigaba da gwagwarmaya da azzaluman Masarautar su.

Ubaidu bai tashi dawowa Yankin Tudu ba sai da kowa ya fara mantawa da shi, da kyakkyawar Matarsa da Ɗansa mai kama da shi Abdullah(Abduh Dhahab) ya dawo, lokacin Abduh har zama ƙaton saurayi, har da ƴar Yayar Matarshi Aysha da Mahaifiyarta ta mutu suka dawo Yankin Tudu. Ga dukiya mai tarin yawa da Ubaidu Dhahab ya dawo da shi.

Dawowar Ubaidu Dhahab da dukiya da kuma zankaɗeɗiyar Matar da babu ma su irin siffarta a Yankin Tudu ya yi matuƙar sosa ran maƙiya Masarautar. Maimakon su yaba sai suka hau kushewa da aibata Ubaidu Dhahab ya auro bare mai kyan da zata kashe shi ta kwashe dukiyar da ya tara. Duk Abdulyasar na sane da su sai dai bai ce komai ba, sai jikansa Abdullah da yaja a jiki.
Sanin matsawar Abdulyasar ya na raye ba zai barsu su kai Ubaidu ƙasa kamar yadda su ka kaishi ba, ya sa suka fara shayar da shi guba a sirrince ta hanyar amintacciyar hadimarshi. Cikin ruwan sanyi suka kashe Abdulyasar ba tare da kowa ya ankara ba, sai daga baya Mutanen gari suka ji ƙishin-ƙishin.

Mutuwar Abdulyasar ba iya Ubaidu da Iyalansa kawai ya taɓa ba har da mutanen gari, saboda alkhairinsa.

Bayan wani lokaci suka dawo kan Ubaidu. Duk da sun kashe Abdulyasar sun kasa kai Ubaidu ƙasa ta cikin ruwan sanyi kamar Mahaifinsa, sun tusawa ɗanshi Abdullah ƴaƴansu ya aura yaƙi yarda, saboda alƙawarin auren da ke tsakanin Abdullah da ƴar Yayar Mahaifiyarsa Aysha da suka taho tare da ita. Babu yadda su ka iya, haka suka haƙura Abdullah ya auri Aysha. Daga wannan lokacin ne suka ƙara duƙufa wajen ganin bayan Ubaidu ko ta halin ƙaƙa, da suka ga sun kasa, sai suka bishi har Gida suka yi mai kisan gillar da ya tashi hankalin mutanen Yankin.

A lokacin Iyalinshi Mahaifiyar Abduh Dhahab Nanaah tayi ƙururuwar abi mata haƙƙinta amma babu wanda ya saurareta sai ɗanta Abduh Dhahab da ya tayata fafutuka, sai dai shima a lokacin ba shi ƙarfin yin komai.

Baƙin cikin hakan yasa ta tattara kayanta ta bar Yankin Tudu aka nemeta aka rasa. Shima Abduh tattara komai nashi ya yi ya bar masaurata zuwa Gidan ɗaya daga cikin gidan da Mahaifinsa ya gada a wajen Abdulyasar Dhahab tsakiyar Talakawa.

Daga wannan lokaci Abduh Dhahab ya barrata kansa da masaraurar Yankin Tudu, ya dawo kamar kowanni ɗan gari. Ba bu tsinke daga dukiyar Ubaidu da ba su ga bayanshi ba. Duk da wannan abubuwan da suka faru Ɗayyib da yake nunamai tsananin ƙauna ya na tare da shi. A sabuwar Unguwar da Abduh ya dawo ya yi sababbun Amanai, Mallam, Mahaifin Malik da kuma Mahaifinki Mahmoud, duk da sun girmewa juna a shekaru hakan bai hana amintarsu saboda hali da ya zo ɗaya.

Abduh ya na da buri mai zurfi, da kuma kishin Yankinsa, ya na son ya kawowa Yankinsa cigaba, kamar yadda Kakanshi da Mahaifinshi sukayi yunƙuri Allah bai ƙaddara ba. Wannan dalilin yasa ya fara tunanin mai zai ƙirƙiro sabo da zai kawowa Yankinsa cigaban da kowa zai amfana???


Abduh ya share sama da wata ya na tunanin abinda zai ƙirƙiro amma ya kasa samun mafita. A wani dare Ubangiji ya sanya masa tunanin ƙirƙirar Tukwane. To amma ai akwai mutane ma su ƙera Tukwane da yawa, ƙirƙirarsu kaɗai ba zai zama wani sabon abu da zai ja hankalin mutane ba, dole sai ya haɗa da wani sabon abinda mutane ba su san da shi ba. Har ya gama saƙe-saƙensa a wannan rana bai samu mafita ba.

★washe gari har Iyalinsa Aysha da ke ɗauke da tsohon ciki ya tuntuɓa itama ba bu wani basirar da ya zo mata.

A haka Abduh ya ƙara shafe wata ya na tunanin abinda zai sa Tukwanensa su zama ma su jan ra'ayi da kwaɗayin mallakar su a wajen Mutane. Ya na cikin wannan tunanin sana'ar Kakanninsa na Zinare ya faɗo mai. Mai zai hana ya yi wa nashi Tukwanen laƙabi da Tukwanen Zinare, ya tambayi kansa, hakan zai zama sabon abu a wajen mutane, kuma abin rububi domin ko da mutum ba shi da niyyar siya zai so ya ga yaya Tukwanen Zinaren su ke, daganan wataƙila yaji sun yi mai ya siya.

Da ya yi shawara da iyalinsa ɗari bisa ɗari ta amince, amma daga baya da ta fuskanci ɗan abinda ya rage mu su suke samu su ci, su sha Abduh yakeson kwashewa ya kafa sana'ar Tukwane sai ta nuna sam bata yarda ba, dama can lallaɓawa takeyi ta gaji da talaucin da suke ciki shine yanzu zai ƙara kwashe abinda ya rage ya yi jarin Tukwane da shi. Da lallaɓawa da kuma nuna mata gagarumin nasarar da zasu samu, cike da yaƙini Aysha ta amincewa Abduh.

Da zallar basirar ƙere-ƙeren da ya koya a wajen a Abokansa na bakin Kasuwar Iyakar Yankin Tudu, Abduh ya ƙera Tukwanen da ya yiwa laƙabi da Tukwanen ZINARE zuciyarsa cike da ƙwarin gwiwa da kuma yaƙinin ko bai siyar ba a take wata rana zai siyar.

Lokacin da mutanen Yankin suka ga Tukwanen da Abduh ya ƙera dariya suka bushe da shi haɗe da faɗin " Abduh ya zo da abinda ba shi da wani amfani zai zallar yaudara, shikenan dan Kakansa da mahaifinsa sunyi kasuwancin ZINARE sunyi arziƙi, sai ya ce shima sai ya yi, to ai zasu ga waɗanda za su siyi waɗannan ruɓaɓɓun Tukwanen na sa, wai Tukwanen ZINARE tunda ya ɗauka kowa Mahaukaci ne irinsa."

Tsaf surutansu yake dawowa kunnen Abduh, ya na kuma sukarsa, sai dai ba shi zaisa ya ja da baya ba, sana'ar Tukwanen Zinare ba gudu ba ja da baya.

A ranar ta farko da Abduh Dhahab ya fita da Tukwanen Zinare Kasuwar maƙotan Yankinsu ba bu wanda ya siya, da ya tarkatosu ya dawo Gida sai mutanen Yankin suka dinga yi masa dariya. Matarshi Aysha da baƙin ciki ta kwana, dalilin haka ta tashi da naƙuda washe gari.

A hannun mai maganin gargajiya Aysha ta haifi Sulaim. Kallon fuskar jaririn kaɗai ƙarfin gwiwa yake ƙarawa Abduh Dhahab haka Aysha domin bai bar komai na Kakarshi Mahaifiyar Abduh Nanaah da basusan inda take ba, kamar ita ta haifeshi.
Da yawa idan suka shigo Barka da hassadar kyan jaririn suke barin Gidan.

Tsahon lokaci
Abduh Dhahab ya cigaba da gwagwarmayar fita da Tukwanensa Kasuwanni ba tare da gajiyawa ko ƙosawaba. A haka ya shafe shekaru biyu ya na wannan bautar babu wani cinikin arziƙi. Matarshi Aysha ta sha yunƙurin guduwa saboda talauci ya na lallaɓata ta haƙura.

A cikon shekaru na biyar ɗin da ya yi yana bautar bin Kasuwanni Allah Ya amshi roƙonsa aka siye Tukwanensa tsaf, har da neman ƙari. Addireshin Yankin Tudu yake ta basu tare da yi musu alƙawarin ƙera wasu Tukwanen ma su yawa ga waɗanda suka nuna su na son sari domin siyarwa. Lokaci da rana Abduh Dhahab ya tsayar mu su, tare da alƙawarin ba za su bar Yankin Tudu ba tare da iya adadin Tukwanen Zinaren da suke buƙata ba.

Da tsananin farin ciki ya nufo Gida, sai dai ya na zuwa ya tarar