ya daɗe da sumar da ita. Mamaki da tsoron ne ya dirarwa mutanen Yankin Tudu, amma dayake yawancin su ma su ƙaranci tunani da kuma hangen nesa ne, sai suka fara surutun;
"ai shi ya jawowa kanshi, tunda ya ce shi bazai kama bakinsa ba"
Ba bu wani cikakken damuwa ko alhinin abinda ya faru da Dattijo Junaid a zuƙatan mafi akasarin mutanen Yankin, wannan ya sa suka cigaba da harkokin gabansu, tare da alƙawartawa kansu jan bakunansu su yi shiru tunda ba su shiryawa mutuwa ba, don babu wanda yaji ko da ihun naiman taimakon su Dattijo Junaid da Matarsa balle su sa ran idan sunyi ihu za su iya samun taimako.
Cikin hikimar Ubangiji numfashin Dattijo Junaid ya dawo cikin tsananin azabar rayuwa ko mutuwa tunda Allah bai ƙaddara ajalinsa a hannun waɗanda suka zo kashesa ba, Itama iyalinshi ta farfaɗo banda kuka babu abinda take yi. Keɓantaccen wajen da babu mai shiga sai Sarki Hammam da mai Maganin da zai dinga duba lafiyarsa Sarki Hamman ya tanada a cikin Marasautar tare da kashe maganar bincike akan kisan su Abduh Dhahab.
Ba bu wanda ya gamsu da maganar Sarki Hammam saboda sun san dole yayi bincike ta ƙarƙashin ƙasa. Don haka waɗanda suke da alhakin kisan suka shiga tararrabi tare da fara tunanin ƙirƙiro abinda zai kawar da hankalin mutanen Yankin da shi kanshi Sarki Hammam.
NAILA;
tun tana sa ran wata rana Sulaim zai dawo har ta gaji da cire rai, sai dai Gidan su ya koma dandali taruwa Yara abokannan wasanta tana ba su tahirin rayuwarta da Sulaim, har da tatsuniyoyi ta ƙirƙira na labarinta da Sulaim. Ba ta fita wasa kullum tana Gida kamar ba Naila mai son wasa da neman tsokana ba.
A cikin watanni biyu da mutuwarsu Abduh Dhahab wani gagarumin Talauci yafara kunnowa Yankin kai. Rana ɗaya suka wayi gari babu Malaman Makaruntun su, Asibitin Mallam da Sarki Hammam yasa aka gyara dukka ma'aikatan jinyar sun gudu. A cikin yini biyu Mutane biyar suka rasa ransu saboda rashin ma'aikatan jinya. Ba bu wani Ɗan Yankin Tudu da hankalinsa bai tashi ba, ciki har da Ɗayyib da bai jima da samun sauƙi ba.
A rana ta uku Mahaifin Naila da ya tashi da tsananin ciwon ciki shima ya rasa ransa zuwa yammaci duk da maganin gargajiyan da akayita ɗirkamai don sun je Asibitin Gwamnati ba ma'aikata. Asibitin Mallam dama tuni aka rufeshi tunda dukka ma'aikatan sun gudu.
Rasuwar Mahmoud Maihaifin Naila wani babban gibi ne mai girman gasken da su Naila ba su da abin maye gurbinsa har abada.
A cikin watannin da suka biyo baya wani irin Talauci ya yi wa Yankin mamaya mai ƙarfin gaske, ga shi babu wadataccen ilimi ba bu Ma'aikatan lafiya masu sanin makamar aiki. Zuwa Lokacin Dattijo Junaid ya samu lafiya amma babu damar yin magana.
Suna cikin wannan yanayin Abdullah ya bayyana a matsayin ƙwararren Likitan da Gmannati ta turo.
Sarki Hammam ya yi Farin cikin bayyanar Abdallah a matsayin Likitan da gwamnati na musamman, Saboda sabon abune a garesu, domin shi da al'ummar Yankinsa rayuwa suke yi tamkar ba ƴan ƙasa ba, babu gwamnati da hukuma sam a lamuransu, sai ɗan abinda ba'a rasa ba, shiyasa kowa yake yin abinda ya ga dama
Bayan kwana biyu
Cikin iko Allah marasa lafiya suka fara samun kulawa ta musamman. Mutanen Yankin sun saki jiki da Abdullah tare da wani irin so da sukeyimai saboda sauƙin kansa da iya mu'amalarsa. Wannan dalilin yasa ya buɗe aji koyawa Matasan da suka kai shekaru 18 mata da Maza dabarun kula da mara lafiya da karɓar haihuwa cikin Hikima.
Da kayan aikin dayazo yake koyawa mu su. Kafin rufuwar wata biyu wasun su har sun ƙware.
A hankali labarin alkhairin Abdullah ya fita ko ina na Yankin sai ya zamana har a maƙotan Yankin su ana zuwa ɗaukar Matasa wala Namiji ko Mace don duba majinyaci ko karɓar haihuwa. Cikin lokaci ƙanƙani talauci Yankin ya fara raguwa walwalarsu ta fara dawowa.
A cikin watanni shida Abdullah ya yaye Ɗalibansa haɗe da ƙara ɗiban wa su. Sarki Hammam da Dattijo Junaid baƙaramin alfahari sukeyi da Abdullah ba, girmamashin da suke yi ma na daban ne.
A na cikin haka aka tsinci ƙaramar Yarinya anyi mata fyaɗe mara kyan gani a bayan Ofishin Abdullah.
Duka na rashin imani da manta halacci Mutanen Yankin sukayiwa Abdullah. kafin sanarwar ya isa ga fadar Sarki Hamman har sun sumar da shi.
"Wani irin ƙwaƙwalwa ne a cikin kan Mutanen Yankin Tudu, kuma wacce irin zuciya gare su mai tsanin butulci da manta alkhairi? Ta ya ya Abdullah zai iya yiwa Yarinya ƙarama fyaɗe na rashin imani irin wannan? shin ina hankalin su yake? Maiyasa ake amfani da toshewar basirar su wajen sa su su dakushe cigaban Yankin su da kansu batare da sun sani ba?" Dattajo Junaid ya tambayi kanshi zuciyarsa na Suya.
Daƙyar Fadawan Sarki Hammam suka fatattaki Mutanen Yankin da bulalai.
Babu wani ƙwararren Likita a ƙasa da zai iya kula da Abdullah, sai masu maganin gargajiya aka nemo.
★washe gari duk da haka Mutanen Yankin basu haƙura ba gangami sukayi har Asibitin suna faɗin abi mu su haƙƙinsu, a cikin su har da waɗanda Abdullah ya koyar kuma suke samun alheri. A cewar su "dama sun san dole akwai wanda ya turoshi don cin mutuncin Yankin su" Daƙyar fadawan Sarki Hammam suka ƙara fatattakarsu da bulalai.
★washe gari da sassafe aka tashi da labarin guduwar Abdullah daga Asibiti bayan ya farfaɗo, fadawan Sarki Hammam ne suka bada labarin wani ne yazo da sunan dubanshi shikuma Abdullah ya yi mishi rakiya a daddafe zuwa motar daya zo dashi gabannin Asubahi daganan kuma basu ƙarajin ɗuriyarsa ba.
Labarin sam bai yiwa Wa su marasa goyon bayan lamarin daɗi ba musamman Sarki Hammam da mutanensa. Dattijo Junaid kuwa har da kukansa.
Labarin abinda mutanen Yankin sukayiwa Abdullah da labarin guduwarsa har wajen Yankin wannan sai ya sa musu baƙin jini tare da kafa tsoron su da ƙyaƙyamin kulla alaƙa da su a zuƙantan maƙotan Yankunan su.
A wannan yanayin Mahaifan Maman Naila suka zo ɗaukarta tunda ta gama Takaba tuntuni. ko da aka buƙaci su tafi da Naila tunda Yarinyarce, ƙin amincewa sukayi bayan baƙaƙen maganganun da suka gasawa Mahaifiyar Mahmud kakar Naila tare da yin Allah wadai su tafi Yankinsu da jinin mutanen Yankin Tudu.
Dole Naila ta koma wajen Kakarta ta wajen Uba da zama bayan kukan da ta sha har da zazzaɓi.
Cikin watannin da suka biyo baya, Mutanen Yankin suka ƙara komawa Talaucin da yafi na baya muni da raɗaɗi. Ga ƙyama da suke fuskanta daga dukka ƙabilun dake kewaye da su, ko Aure ɗan Yankin Tudu yaje nema ba'a ba shi.
Rana ɗaya dukka matasan Yankin suka yi zuciya suka koma Gona har da Ƴaƴa mata saboda raɗaɗin Talauci da rashin abin yi. Don ko aure Mazan Yankin suka fita nema a mokatan Yankin su ba'a ba su, balle su yarda Ɗan su ya auro mu su Ƴar Yankin Tudu. Wannan dalilin yasa suka fara auren Junansu cikin tsananin Taulauci.
Bayan amfanin Gona ya yi, suka fara fita dashi kasuwanni Yanki-Yanki. Abin mamaki duk Yankin da suka kai ba'a siya sai su ce "Allah Ya raba su da cin kayan amfanin gonar mutanen Yankin Tudu" kamar waɗanda sukayi bar ruwa da guba haka Kayansu ya koma a idon Mutane. Ko wani bare daga wani ɓangaren da bai sansu ba ya yi niyyar siya sai aja kunnensa da kar ya kuskura idan ba haka ba kuwa, tamkar ya kirawa kansa mutuwa ne.
Mutanen Yankin Tudu suna ji suna gani suka ƙara komawa Talaucin dayafi na da raɗaɗi da azaba
Suna cikin wannan yanayin Salman ya shigo Yankin a matsayin mai koyar da sana'o'in da gwamnati ta turo...✍🏻
Bayyanar Salman a Fadar Sarki Hammam a matsayin mai koyar da Sana'o'i ya yi matuƙar faranta ran Mutanen Yankin kamar dai lokacin Abdallah, saboda ya zo akan gaɓar da suke tsananin buƙatar ire-irensa.
Ɗayyib ne ya kawo shawarar mai zai hana a kai Salman Gidan marigayi Abduh Dhahab da tun bayan Mutuwarsa yake a garƙame a matsayin Masauki?. Ba bu jaa kowa ya yi na'am da shawarar Ɗayyib tunda Salman ya ce shi ma Maƙeri ne.
Bayi Sarki Hammam ya bawa mukulli suka gyara gidan.
Ɗayyib da kansa yayiwa Salman rakiya har gidan Abduh.
Bayan sati ɗaya.
Da tsananin Farin ciki da wani ƙauna mara iyaka Ɗayyib ya nufi Salman bayan ya gama kallon irin Tukwanen da Salman ƙera. Rungumesa ya yi ya sumbaci gefe da gefen kunchinsa, sannan ya ce;
"A ina ka koyi ƙera irin Tukwanen da Aminina Abduh Dhahab yake ƙerawa? Tun bayan mutuwar Abduh muka shiga wani yanayin na ƙangin rayuwa, saboda mutuwar Kasuwar Tukwanen Zinaren da yasha wahala kafin kafuwarsa, ba bu wanda ya yi hikimar koya a cikin mu lokacin da ya ke raye, daga shi sai Ɗansa Sulaim ne kawai suka iya ƙerawa. Sai ga shi bayan munfidda rai da ƙarasamun rayuwa mai daɗi Allah Ya Kawo mana kai. Alhamdulillah!" Ɗayyib yaƙara faɗa ƙwalla kwance a ƙasan fararen manyan Idanuwansa.
Salman bai ce masa komai ba sai murmushinsa daya faɗaɗa yana komawa wajen Tukwanen daya ƙera. Har Ɗayyib ya gama santin Tukwanen ya bar gidan Salman bai ce komai
Da Ɗayyib ya kaiwa Sarki Hammam labarin Tukwanen da Salman ya ƙera, Umarni Sarki Hammam ya bawa Fadawansa su bi layi-layi suyi shelar Bayyanar Salman a matsayin mai koyar da Tukwanen Zinare sak irinna Marigayi Abduh Dhahab.
A yammacin ranar suka cika umarninsa,
Nan da nan farin ciki ya mamaye zuƙatan Mutanen Yankin, maimakon su godewa Allah su ƙara sanin amfanin Marigayi Abduh Dhahab a Yankinsu sai suka hau Sukarsa da ce wa;
"Allah Ya sa shima wannan ba irin Abduh Dhahab ba ne mai mugun zuciyar da zai yi sihirin da Kasuwar Tukwanen Zinaren zai ƙara rushewa idan bayanan" da ire-iren kalaman sukai ta sukar Marigayi Abduh Dhahab kenan.
Ba su tsagaitaba har sai da labari ya jewa Sarki Hammam. Da kakkausar Murya ya yi gargaɗin duk wanda yaƙara sukar Abduh Dhahab abisa son zuciyarsa to zai fuskanci hukunci mai tsanani.
Ba bu kunya mutanen Yankin suka cika gidan Abduh Dhahab, Yara da Manya, Maza da Mata Don koyan ƙera Tukwane.
ƊAYYIB
Da wani irin takaici yake kallon ɗansa Sufyan, ba don kalamansa suna yimasa daɗi ba ya cigaba da saurararsa.
"Baaba tayaya zan koyi ƙera Tukwane da wannan kyan nawa? Baabah ba ƙera Tukwane ne ya dace da Matashi kyakkyawa irina ba. Ni burina shine naje Babban Birni nayi Karatu mai zurfin da zan kawowa Yankina cigaba, amma ba koyan ƙera Tukwane ba gaskiya" Yaƙarasa faɗa yana yin ƙasa da kansa da suma baƙi mai laushi ke kwance luf a kai.
Tabbas! Ɗanshi Sufyan kyakkyawane amma idan aka haɗa kyansa da na Sulaim daya ƙare rayuwarsa wajen bautar ƙera Tukwane to tabbas Sufyan ɗin ba komai bane.
Da taushin Muryar da yake burin Sufyan ɗin ya fuskancesa har yagane abinda yake yimasa kwaɗayi ya ce;
"Sufyan Idan har Sulaim da Allah Ya yiwa baiwar kyau ninkin baninkin naka zai ƙare rayuwarsa wajen ƙera Tukwane bisa umarnin Mahaifinsa, to banga dalilin da zai hanaka bin nawa umarnin ba. Sana'a baya hana karatu sai dai ma ya taimaka wajen ragewa Iyayenka ɗawainiya kuma kai kanka sai ka fi jindaɗin kayiwa kanka abu batare da ka jira an ɓata maka lokaci ba. Kaje kayi shawara da Mahaifiyarka amma kasani idan har ka saɓawa umarnina to babu ko sisina a harkar neman Iliminka." Ɗayyib ya na gama faɗa ya miƙe ya bar wajen.
Sufyan ba a iya Cikin zuciyarsa yake jin raɗaɗi kalaman Mahaifinsa ba har a kan fuskarsa.
Yaushe labarin kyan Sulaim zai gushe a zuƙantan mutanen Yankin. Ya na son ace yana da kyau duk da yayi imanin shi ɗin kyakkyawane, don matan Yankinsu da na maƙotan Yankinsu har so suke yi yayi musu magana. Amma duk wannan yabon kyan nasa da sukeyi da zarar hirar Sulaim ya ratso sai su hau ƙodashi da faɗin da Sulaim ya girma a raye to da babu wani Matashin da zai kamosa a kyau kaf faɗin Yanki, a wasu lokutan ma sai su ce har da maƙotan Yankunansu, duk ranar da irin haka ta ratso a gabansa ko labari yazo kunnensa yini yakeyi yana kallon ƙaton madubin Gidansu.
Hindu Mahaifiyarsa mai taya ɓera ɓari kullum ƙara zugasa take yi da cewa; "ba wai su na zuzuta kyan Sulaim ba ne don dagaske ya na kyan ba, sai don Tukwanen Zinaren da Mahaifinsa ya ƙirƙirowa Yankin, idan shima yaje Babban Birni Ya yi karatu mai zurfin da kaf faɗin Yankin ba bu mai kwatankwacinsa to ba shakka shima zai zama abin kambabawa, kar ya kuskura ya yarda da batun Sana'ar da Mahaifinsa ya jima yana burin ya yi, idan ba haka ba Sulaim shi zai cigaba da zama Saurayi mafi kyau a Yankin duk da baya raye, idan ma ya lura sun mayar da labarin kyan Sulaim kamar wani Tarihin da suke kambawawa. musamman ga waɗanda ba su sanshi ba" har alƙawarin auren gata tayimai da wacce zata bauta mai kamar Sarki idan har ya cikamata burinta na zuwa Babban Birni karatu.
Waɗanan huɗubobin da su Sufyan yake kwana kuma yake tashi.
A ɓangaren Mutanen Yankin ma su koyan ƙera Tukwane a wajen Salman sosai suka nuna jajircewarsu da farko, amma da tafiya tai tafiya sai suka fara nuna gajiyawarsu har sai da Salman ya zaburar da su da kalaman asalin wanda ya ƙirƙiri Tukwanen;
"Ba a lokacin da muka shuka iri, zamu girbi amfaninsa ba dole sai munjira kuma munyi haƙuri tare da yin aiki tuƙuru" waɗannan kalamai na Salman baƙaramin tsoratar da Mutanen Yankin ya yi ba, musamman ga waɗanda sukayiwa Abduh Dhahab farin sani. Tsoron kar su wayi gari wata rana su ga babu Salman don sun fi alaƙanta shi da aljali saboda kalamansa masu kamaceceniya da Abduh Dhahab, sai suka ƙara zage damtse.
Labarin kamaceceniyar kalaman Salman da Abduh Dhahab dayake yawo a gari har kunnen Naila da Kakarta. Naila data kasa samun sukuni a sace ta tafi Gidan ba tare da sanin Kakarta ba.
Sai da ta yi zuwa har biyu amma ta kasa shiga sai dai ta laɓe tana Kallonsa.
A ranar zuwanta na uku Salman ya kamata. Har cikin gidan ya riƙo hannunta ya shigo da ita.
"Maiyasa kullum kike zuwa ki maƙale kina kallona, mai kike nema?"
Salman ya tambayeta yana kallon cikin idonta.
Murya na rawa Naila ta ce "inaso nasan labarinka, inaji a jikina kamar Kanada alaƙa da su Sulaim, shin dagaske Sulaim yaƙone bazai ƙara dawowa ba?"
Kamar wanda ya ke son haddace halittun fuskarta haka Salman yake kallonta kafin ya ce;
" Ki je nan da Sati biyu ki dawo zan baki labari" ya ƙarasa faɗa ya na turata waje haɗe da kullo ƙofar Gidan.
Daga wannan rana Naila ta fara lissafin kwanakin da Salman ya ɗebarmata ba tare da sanin Kakarta ba.
A ɓangaren Mahaifiyar Naila tun bayan komawarta Yankinsu, zumuncin da dama can akwai shi tsakaninta da Mairam Matar Abduh Dhahab ya ƙara ƙarfi kullum ita take kula da Mairam a gidan take wuni sai dare take dawowa gida. Mairam tana samun sauƙi amma kullum a cikin kuka take ba magana.
Ranar da ta buɗi baki ta tambayi Ruwa, gidan ruɗewa sukayi da farin ciki ba iya su kaɗai ba har mutanen Yankin da labari ya je wa. Murnar fara maganar Mairam kaɗan-kaɗan yasa Mahaifiyar Naila yanke shawarar kwana a gidan, acewarta " yau kwana zamu yi muna hira" ta ƙarasa faɗa tana dariya.
Babu zato babu tsammani
A daren ranar aka kawo mummunar harin da ya faɗa kan Mahaifiyar Naila.
★washe gari da Sassafe Jama'ar Yankin suka kewaye gidan.
kuka mai raɗaɗi da ciwon gaske Kakannin Naila suka ƙanƙanme juna su na yi, lokacin da sukayi ido biyu da gawar ƴarsu. Ga shi Mairam da Mahaifanta sun gudu, tun Asuba..
Bayan an kimtsa gawar Mahaifiyar Naila kafin a kaita, Mahaifinta shi da Mutanen Yankinsa sukai gangami har Fadar Sarki Hammam, don suna kyautata zaton fara maganar Mairam ne yasa suka zo kasheta don karta faɗi abinda ta sani tsautsayi ya faɗa kan ta su ƴar.
Bayan sun samu shiga Daular Sarki Hammam maganganun ma su nauyi a harshe da raɗaɗi a zuciya Kakan Naila da mutanen Yankinsa suka fara zazzagewa Sarki Hammam da Muƙarrabansa. Zafin kalamansu dayake nuna cin fuska ƙarara ga Sarki Hammam yasa Fadawansa nufarsu da manyan bulalai.
Sarki Hammam dakatar da su ya yi, sannan ya yi wa Kakan Naila alƙawarin yin adalci matsawar ya bincika ya gano dagaske da hannun Mutanen Yankinsa akan kisan gillar da akayiwa Ƴarsu to zai hukuntasu dai-dai da abinda suka aikata.
Da wannan yarjejeniyar Kakan Naila da mutanensa suka bar Yankin, ko kallon Naila dake kuka kamar ranta zai fita basu yi ba.
Su na tafiya Naila da Kakarta suka shirya suka nufi Yankin.
Abun takaici bayan isarsu ko wajen zama ba'a basu ba, a cikin bainar jama'a, Kakanninta suka ce sun yafe ta, babu su babu ita, kuma karsu ƙara ganin ƙafarta a Yankinsu.
Naila tana kuka suka dawo Yankin Tudu.
A yammacin ranar sai da Sarkin Yankinsu Kakannin Naila na wajen Uwa, yaje har Yankin Tudu duk dai akan kisan gillar Mahaifiyar Naila, alƙawarin da Sarki Hammam ya yiwa Kakan Naila shi yaƙara yiwa Sarkin su.
Bayan Sarkin su ya dawo ya tattauna da Kakan Naila. A take Kakan Naila ya yafewa Iyayen Mairam tunda tafiyar tasu shine nutsuwar su da na Mutanen Yankin gaba ɗaya.
Naila bayan sun koma Gida kafin dare ya yi zazzaɓi mai zafin gaske ya rufe ta har bata gani da kyau.
A haka tasha jinyar da tayi sati Uku a kwance. Bayan ta wartsake ta tuna alƙawarinta da Salman sai dai babu damar zuwa saboda shirye-shirye bikin sake buɗe Kasuwar Tukwanen ZINARE, da za'ayi washe gari.
A ɓangaren Salman tuni ya manta da batunsa da Naila ya cigaba da abinda ya kawosa.
A daren washe garin da za'a buɗe Kasuwar Tukwanen Zinare, Sarki Hammam ya gayyacesa cin abinci..
Salman ya samu Tarba mai kyau daga Sarki Hammam, bayan sun kammala cin abinci, Sarki Hammam ya buƙaci tattaunawar sirri da