x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 742

07 Oct 2025
wani ya tanka musu ba.

SULAIM
Kisan Zubair yasa ya dakatar da Malik daga sanar da shi duk wani abu daya shafi Yankin Tudu da kowa na cikinta, duk wanda yaga ya cancanta ya taimakamai albarkacin Mahaifinsa ba sai ya sanar da shi. Wannan dalilin yasa Malik kasa taimakon Naila saboda yasan ita ba taimako take buƙata ba, burinta tasan Sulaim ya mutu ko yana raye.

Sulaim ya zama hamshaƙin Attajirin gaske a ƙasar Abyad da ya sakaye Sunansa da Muhammad Dhahab kowa da haka ya sansa,

ya kafa Unguwa guda da Rukunin Gidaje masu yawa mai suna Dhahab a Babban Birnin Abyad da kuɗi masu nauyi.

Malik da ahalinsa, Salman da Iyalinsa, sai su Kabeer, har da Mariam da Iyayenta da Malik ya binciko su ma suna aikatau a Birnin Abyad, sai wasu mutanen Yankin Tudu da cirani ya kawo kusa da Birnin Abyad sukayi katari da Malik. Su suka taru suka raya Dhahab suke rayuwa a ciki.

Matar Mallam babu inda Malik bai bincikaba amma ya kasa samunta.

Malik bai gajiya ba sai da ya binciko Mahaifiyar Sulaim da Kakarsa bayan ya kashe dukiya masu nauyi. Wannan ya ƙarawa Malik daraja a idon Sulaim.

Ranar da Malik ya kawo Aysha mahaifiyar Sulaim da Kakarsa Nanaah da kuma Farheen ƴar ƙanwar Aysha Dhahab Sulaim ya zo daga inda yake rayuwa domin ganinsu, wannan zuwa nasa sai yasa kishi ya lulluɓe zuciyar Mairam duk da Abduh baya raye, a ganinta kamata ya yi Sulaim yafi ƙaunarta akan Mahaifiyar data haifesa, tunda ta gudu ta barshi.

Da Sulaim ya tashi tafiya ƙasar da yake rayuwa da Kakarsa Naanah da yaji ya fi so a ransa ya tafi, saboda ciwon zuciya da take fama da shi, Mahaifiyarsa kuma aka ware mata Sashe na alfarma tayi rayuwa ita da ƴar ƙanwarta Farheen

A ina Sulaim yake rayuwa??

Kahala Birni mai daraja a Honolulun Hawaii, banbancin daɗin rayuwarsa da Babban Birnin Abyad, kamar babbancin Babban Birnin Abyad ne da Yankin Tudu.
Rashin son ya raɓi kowa yasa yaje can ya kafa Kasuwanci siyar da zinare da kayan sawa da kayan ƙyala-ƙyalai, cikin ikon Allah ya samu karɓuwar da ya ƙara mayar da shi Attajiri a can.

Duk wani hukunci da Malik ya yake yakewa, akanki kansa yake yi kamar yadda Sulaim ya sakarmai ragamar komai. Amma duk da haka rashin yarda da baiyi da kowa ba, yasa ya ajjiye Ma'aikata na musamman masu lura da motsin Malik a sirrince a harkokin da suka shafi Dhahab ba tare da shi kansa Malik ɗin ya sani ba.

SULAIM
Ya manta da Naila da dukka wani abu daya shafeta a zahirinsa ya kuma toshe duk wata hanya da wani zai sakomai zancen aure.

Batun wanzuwar Sufyan a ɗaya daga cikin ma'aikatansa da Kabeer, bai sani ba, shi ko Kabeer ɗin da ya fi Sufyan matsayi bai san dashi ba, Uzair da Malik kawai ya sani.

A can Dhahab
Mutanen da suke rayuwa a cikinsa suna rayuwa a matsayin sun san Sulaim yana raye bawai don suna ganinsa da idanunsu ba ko mu'amalantarsa.

Tsantsenin Cikin Dhahab da kula da motsin komai duk Sulaim ne ya tsarashi Malik yake kula da komai da taimakon ragowar Ma'aikata, domin da mutum ya yi cin amana a Dhahab gara ya barta gaba ɗaya.

Maiyasa Mairam bata taimaki Naila da kakarta ba duk da tasan inda samesu?

Kishi da burin son Sulaim ya dawo gareta yasa take ƙoƙarin duk ranar da Allah ya ƙaddara dawowar Dhahab tun bayan tafiyar da Kakarsa ta gabatar mishi da Barirah domin har biyayyar dole takeyiwa Aysha Mahaifiyar Sulaim, duk don su yi masa taron dangi ya auri Barirah. A ganinta idan Sulaim ya auri wata mantawa zaiyi da ita gaba ɗaya ƙarshe ta koma Yankinnsu da suka gudo, jawo Naila a jikinta gani takeyi shima matsalane kar Sulaim ya ganta ya tuna da shaƙuwa daya wanzu a tsakaninsu shekarun baya har ya nuna yana sonta, daganan ya aureta itama tasa ya koreta saboda kashe Mahaifiyarta da akayi ta dalilinta, gara Barirah da bawani sonta tasan zaiyi ba.

Wannan dalilin yasa Barirah take yiwa Ummi Mairam kamar yadda suke kiranta biyayya sama da Mahaifiyar Malik da yake ruƙonta.

Malik yasha jawa Baririh kunnen karta ɓata shekarunta wajen jira Mutumin da bai san da ita ba. Amma kallon mahassadi takemai.
..✍🏻
SASAAL

5

*Wani irin rayuwa Sulaim yake yi Kahala?*

Rayuwa sakewa da morewa arziƙinsa, kyansa da Mutanen Yankin Tudu suka kasa mantawa dashi yaƙara fitowa, ginannan jikinsa dake samun hutu, cima mai kyau, da motsa jikin da ya dace, yaƙara zama abin so ga duk wata Ƴa Mace musamman Mace mai son Naira da Namijin liƙawa a goshi. Rashin yawan son maganarsa bata sauya ba sai abinda ya yi gaba.

A cikin zuciyarsa kuwa babu ƙiyayya, babu ramuwa, sai dai ya goge kafanin Mutanen Yankin Tudu daga cikin rayuwarsa.

Babu yadda rayuwa Namiji kamar Sulaim zai gudana ace babu Mace a ciki, wannan daliline ya shigo da Noorhan ƴar asalin ƙasar Lebanon cikin rayuwarsa.

Noorhan;
Kyakkyawar gaske, ƴar Attajirai gaba da baya kuma ƴar gatar da ta yiwa addininta na Musulunci riƙon ganin dama, su ma Mazauna Kahala ne da Mahaifanta.

Bata da burin lallai SM Dhahab ya aureta kamar yadda take kiransa da wasu Abokanan Kasuwancinsa. Burinta soyayyarsu ta faɗaɗa ya wuce sumbata da sauransu, ya mayar da ita kamar Iyalinsa idan da hali harta haifa mai ƴaƴan da zai ƙulla alaƙa mai ƙarfin tsakaninsu har ya kaiga Aurenta ko baya so.
Kallonsa, salon tafiyarsa, iya riƙe matsayinsa da izzarsa, da rashin son hayaniyarsa wani irin birgeta suke yi, uwa uba Nairan daya tara babu magaji. Wasu lokutan tana kuka da magiyan ita ta sallama masa kanta amma sai ya yi biris da ita, idan ta matsa sai ya tuna mata abinda take so ya wuce ƙa'idarsa da ita.

Tasha sanya masa abu a lemo ya zubar, abinda bata sani ba, yarda da Mutum wani tsohon abune da Sulaim ya jima da daina yayinsa, idan har kaga ka cucesa akan kuɗi ko wani abun kasha to tabbas Allah ne ya ƙaddara hakan amma ba dai dabarar mutum ba. Da ya ga taƙi dainawa fuska da fuska ya gargaɗeta idan ta ƙara ba iya rabuwa da ita kaɗai zai yi ba har ƙararta zai kai.

Babu wanda ya yiwa Sulaim cushen Noorhan da kanshi ya ganta ya tura aka haɗasu, domin ragewa kansa kaɗaici.

Kakarsa Nanaah da ya ɗauko rayuwarta kusan rabi a Asibiti yake gudana domin bini-bini jikinta ya tashi.

Malik ne kaɗai yake yawan kawo masa ziyara idan buƙatar aikinsa ya taso.
Tsakaninsa da Malik akwai girmamawa mai faɗin gaske, kasantuwarsa Ubangidan Malik kuma mai ɗauke kai da bashi damar yin duk abinda ya ga dama da dukiyarsa. A ɓagaren hira, hirar aiki ne kawai yake haɗa su banda na mutanen Yankin Tudu, kuma shima sunfi yi a rubuce saboda rubutu yafi yiwa Sulaim sauƙi akan doguwar magana, yakan jima ya na yin hira da Malik a rubuce amma idan da baki ne hirarsu taƙaitaccen ne.

Wannan shine Matashin da Malik ya je wajensa da abubuwan da suka faru tun shekaru baya a Yankin Tudu.

*DAWOWAR LABARI*

Murmushi Malik ya saki yana ƙara gyara zamansa don jiran abinda zai ƙara cewa.

"Na turo maka saƙo, idan aikin komai ya kammala sai ka wuce"
Sulaim ya faɗa yana ƙoƙarin miƙewa. Sai dai har ya miƙe ya fara yunƙurin tafiya Malik yana zaune bai motsa ba.
A wajensu dukka sabon abune rashin miƙewar Malik ɗin, don haka Sulaim ya fahimci Malik yana da saƙon dayake buƙatar attention ɗinsa.

Dawowa ya yi ya zauna idanunsa ƙyam a kan fuskar Malik dake sunkuye kafin ya ce "menene matsalan Malik?"

Sai da Malik ya saita kansa sannan ya ce
"ka gafarci furucina da kuma labarin da nake tafe da shi" kai Sulaim ya ɗaga alamun ya basa dama.

A ɗan rarrabe Malik cikin kame-kame tsoron abinda zai biyo baya ya ce;
"Nailar Yankin Tudu, ƴar Mahmoud maɗinki..."
Ido Sulaim ya lumshe har baya ganin fuskarka Malik dakyau, a hankali yayi baya ya jingina da Couch ɗin dayake kai. Hakan da yayi ne ya bawa Malik damar cigaba da maganarsa

Kamar mai karanta labarai a gidan radiyo ko talabijin haka Malik yake koromai labarin komai dalla-dalla tunda ya basa dama, har zaman Sufyan da abinda ya aikatawa Naila da cin zalin da yayi mata, da ciwon da tayi kamar yadda ya kwantarwa da Bushra hankali ta bashi labarin komai ta waya kafin zuwansa Kahala, da zuwansu Babban Birnin Abyad a yanzu a matsayin makitsiya, kuma Mahaifiyarsa ta hanasa taimakonta saboda abinda Mairam ta tsiro da shi.
Malik bai rage komai ba, tunda ɗorewar zaman amanarsu shine rashin ɓoye-ɓoye. Domin ko Noorhan Malik ne kaɗai yasan da ita a matsayin Budurwar Sulaim shiyasa yake jawa Barirah kunne.

Idanuwansa da ya zuƙe ya ɗan buɗe kaɗan yana gyara zamansa, kamar daga sama Malik yaji sassanyar muryarsa;

"Inji Ni ka sanar da Naila da Kaka! A Sauya mata Jami'a a Babban Birnin Abyad,a basu mazauni na musamman a Dhahab ta kuma daina kitso har abada. shi kuma Sufyan ku barshi ya ci abinci shi da Iyayensa daga dukiyar da Allah Ya bamu."
ya na gama faɗa ya ɗan sosa ƙarshen dogon hancinsa yana miƙewa.

Har lokacin idanunsa da suke bayyana jin daɗinsa ga abu ko akasinsa a lumshe suke ba a ganinsu da kyau, balle Malik ya tantace yadda ya ɗauki zance.

"Ka sauka lafiya Malik ina gaida kowa" ya ƙara faɗa yana barin living room ɗin daya lashe manyan kuɗaɗe.

LV Maimi Mule ɗin daya haska kyakkyawar ƙafarsa Malik ya bi da kallo kafin shima ya miƙe a hanzarce yana ɓoye ainihin yanayin dayake ciki.

Malik ya na fitowa harabar Gidan ya samu waje ya zauna yasha murmushin da ya kasayi a ciki, yana godewa Allah domin matsalar Naila ce Matsala ta Farko tun bayan barowarsa Yankin Tudu da ƙiri-ƙiri yasan arziƙine maganinsa amma ya kasa maganceshi, saboda wanzuwar Naila a Dhahab kamar dawo da Tarihin Yanki Tudu ne a rayuwar Sulaim, shiyasa bai isa ya yisa kai tsaye ba shi kaɗai.

Yasan da wahala Namijin da ya taka Matsayin Sulaim ya so Mace irin Naila, da wannan saƙe-saƙen ya duba saƙon Sulaim kafin ya wuce addireshin wajen taron daya turamai.

Sai yamma liƙis su Malik suka gama taro ya nufi masauƙi, ko Rigarsa bai gama cirewa ba saƙo ya shigo ta E-mail ɗinsa. Bai kawo saƙo mai muhimmanci ba ne, don haka ya shiga wanka ya gabatar da Sallah.

Bayan ya ci abinci yakira Ummeensa yana bata labarin abinda ya faru, hamdala tayi kafin suyi sallama, Bushra ya yi niyyar kira amma yafasa ya janyo ɗaya wayarsa don turawa Sulaim saƙon yadda komai ya wakana ga mamakinsa ashe saƙon Sulaim ne ya shigomai tuntuni. Sunan Jami'a ya turomai da taswirar Dhahab sannan ya yi pointing ɗin wani guri, ko Malik bai tambaya ba yasan yana nufin anan yake so a ajiye su Naila, sai guntun rubutun nemarwa dukka ahalinta da suka nuna suna ra'ayin aiki a Dhahab, a bashi aiki da matsuguni na musamman a estate ɗin Companynsu( inda Sufyan yake).

Sai da Malik ya gama ƙyaƙyata dariyar muguntarsa daya haɗe da zallar nishaɗi sannan ya binciko sunan jami'ar da Sulaim ya turomai. Iya adadin kuɗin Makarantarne yasa Malik ƙara sakin dariya, kafin ya ƙara zuƙo Taswirar Dhahab daya turamai dakyau, inda Sulaim ya yi pointing gine ne dake tsakanin inda Mahaifiyarsa da Danginta da suka ƙara biyota daga baya suke rayuwa, ginin babu kowa a ciki domin an tanadeshi da can saboda Sulaim ɗin kansa amma ya nuna baya so, kuma ɓangaren shine ɓangare mafi samun tsaro dakyau a Dhahab. "kenan anan Naila da Kakarta zasu zauna?" Malik ya tambayi kansa wani dariya ya ƙara kwashewa da shi har da kwanciya.

Rasa wanda zai kira da yasan Naila suyi sharing ɗin daɗin dayake ji yasa ya kira Bushra.

Bayan sun Gaisa ya gama bata labari ihun
Bushra ihu murna tasa tana tsalle tare da alƙawarin baro ƙasar da take domin taya Naila murna.

"amma kana ganin Mahaifiyarsa(Aysha) zata amince baza'a samu matsala da ita ba, tunda ba wai auren Nailan ya ce zai yi ba" Bushra ta faɗa murnarta na komawa ciki.

Dariya da kai tsaye za'a kirasa na isa Malik ya saki ya ce

"Bushra! baki ji na ce miki ya ce "Inji shi" ai ya gama magana kenan, Mahaifiyarsa Macece mai sanyi, kuma barinsa da tayi tsayin shekaru yasa take lallaɓashi babu shaƙuwa a tsakaninsu. Baya magana mutum ya sauyamai sai dai Allahn da Ya haliccesa! Don haka ina jiran zuwanki" Dariya Bushra ta saki tana jero Sulaim kiraraki, da shaƙiyancinsu suka ƙare wayar.

Ajiyar zuciya Malik ya sauke Noorhan da yake ganinta a matsayin katanga mai tsaho a tsakanin Sulaim da Naila na faɗomai domin bayasa Barirah a lissafinsa....

Washe gari da Asuba ya ɗauko hanyar Ƙasar Abyad, bayan ya ajjiyewa Sulaim saƙo don bai koma gidan ba...
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

6


SUFYAN;
Bai yi nadamar furucinsa ga Sumaya ba, saboda yana ganin abinda ya dace da ita kenan, burinsa kawai ya gansa a Babban Birnin Abyad a ofishin aikinsa ba su sallamesa ba.

Masauƙin da suka sauka shida Sumaya ya je, ya kwashe kayan amfaninsa ya nufi Airport.

Gabansa ya na faɗuwa ya nufi estate ɗin Companynsu.

Ajiyar zuciya ya sauke lokacin daya da zura ɗan mukullin ɓangarensa yaji ya buɗu.
A gaggawace ya shirya cikin baƙin kayan da suka yi mai kyau, sannan ya lalubo wayarsa hannunsa da zuciyarsa suna rawar amsar da Driver zai ba shi ya danna masa kira ya ce ya zo ya kaishi Office.
Da girmamawa ba tare da ɓata lokaci ba Driver ya ce gashinan zuwa.

Sufyan bai san sanda ya zamo ƙasa ya yiwa Allah sujjud ba, domin ya yi imanin a yanzu shine Kaɗai gatansa.

Babu abinda ya sauya a ofishinsa sai ƙamshi ma da yake yi a gyare tsaf. Rintse ido Sufyan yayi yana yiwa kansa alƙawarin riƙo da gaskiya tare da aiki da amana.

Bayan ya dawo gida
Da dare ya raba kasa barci ya yi ƙewar Naila da yadda yake bautar da ita ya juyata yadda yaga dama na addabar zuciyarsa, babu ƙewar Sumaya ko wani abu daya dangaceta a cikin ransa, saboda don ita da Mahaifinsa ya kashe wayarsa Karma su kira su samesa.

Sallar daren da Sufyan bai taɓayi ba a rayuwarsa ya ɗauko prayer mat bayan yayi alola ya tayar, zuciyarsa cike da yaƙinin samun mafita a wajen Ubangijinsa.

★washe gari da ya fita ofishi yaƙara ganin abubuwan da suka ƙara kwantar dashi, saboda zazzaɓi mai zafin da ya rufe sa. Ya ga Kabeer ido da ido a matsayin Uban gidansa, sannan ya ga Dr. Abdallah da ya taɓa zuwa Yankin Tudu shekarun baya.

Menene yake faruwa? Daga ina suke ɓullowa, ko dai kasheshi suke son yi? Tambayoyin da yake ta yiwa kansa kenan

Har gari yayi haske Sufyan bai runtsa ba. A daddafe ya nufi office kansa kamar zai faɗo, Misalin ƙarfe tara na safiya ya shiga ɗakin taron da zasuyi, fuskokin wasu daga cikin mutanen Yankin Tudu ya fara gani ciki har da Sartaj da'aka nema aka rasa. Bibbiyu ya fara gani kafin ya ƙwala ƙarar da ya janyo hankalin mutane kansa.

Rai a hannun Allah aka wuce da shi Asibiti a karo na uku.

NAILA;
Ita da Kaka kwanan fargaba sukayi, har ɗaki Ameera ta biyo Naila tana bata haƙurin irin tambayoyin da Barirah ta titsiyemsu da shi.

Ɓarawon barci ne yayi nasarar ɗaukesu bayan sallar Asubahi.

Da gari ya yi haske bayan sun karya Ameera aka turo ta kirasu, wai Barirah tace su taho har da Kaka, ɗan yamutsa fuska Naila ta yi ta ce;

"ba ta da hurumin da zata ce don zan yimata kitso sai na tafi da Kakata, idan bata son zuwana ni kaɗai ku biyani haƙƙina mu koma inda muka fito"
Dan jim Ameera tayi kafin ta ce;

"okay ba damuwa muje"

Naila ta na kallon Kaka ta na yunƙurin kamo hannunta tayi kamar banganta ba, ta bi bayan Ameera.

Da suka fito Parlon
Mama Yayar Mahaifin Ameera da zata raka Naila da mamaki take tambayar ya ya basu fito tare da Kaka ba? Abinda Naila ta gayawa Ameera na maimaita mata.
Itama ɗan jim tayi kafin tayi gaba Naila binta a baya.

Ɓangaren Mahaifan Malik suka fara zuwa jami'an wajen suka sanar da su saƙon Barirah, wai ta ce su biyota ɓangaren Ummi Mairam.

Cikin biyayya Maman da ta raka Naila ta sunkuyar da kanta haɗe da ƙarayin gaba.

Zuciyar Naila kamar ana hura wuta saboda takaici.

Babu hassada living room ɗin su Ummi Mairam abin a yabane ta kuma jinjinawa ƙwararren da ya tsarashi.

Mairam Matar da Mahaifiyar Naila ta fuskanci mutuwar azaba ta sanadin kula da ita, idanuwan Naila suka ganemata, Tayi kyau irin kyan dake bayyana hutu da sukunin rayuwar da take ciki.
Kamar bata taɓa ganin Naila ba haka ta ɗauke kai tana shan ruwan tataccen kayan marmarin da yake hannunta. Barirah tana zaune a gefenta tana latsa waya.

Naila tsayawa a matsayinta abune da ta jima da sanyawa zuciyarta shi, don haka ta naimi ƙasa na zauna, kamar bata sansu ba dukkan su.

"Ina Kakarki, maiyasa baku zo tare ba?" Barirah ta tambaya cikin isa.

A take Naila ta bata amsa!
"Banzo da ita ba, saboda ba ta iya tafiya mai nisa, kuma ai bata iya kitso ba, Ni kaɗaice na iya."

wayar hannunta Barirah ta ajiye a gefe tana ƙanƙace idanunta, sannan ta ƙara cewa;

"Ke har kina da Audacityn bani irin wannan amsar, lafiyar ƙwaƙwarki kuwa?"
Cikin kameme Mama tace;
"Ayi haƙuri kinsan halin Yara, Kakarta ta ce batajin daɗi"

"Ko bata jin daɗi a ɗaukominta ita haka, tambaya nakeson zanyi musu tare"
Barirah ta ƙara faɗa a gadarance tana juya wayar hannunta.

Zuciyar kamar ana hura wuta a maƙera, baƙin ciki tuni ya lulluɓe ganinta, kamar zata amayar da wuta ta ce;

"Ƙarya kike Barirah! Bakiyi wannan arziƙin ba, wacece ke? Ko da bansan ƙaddarar arziƙi ba babu yadda za'ayi mai sana'ar maganin gargajiya ya mallaki Dhahab, dole arziƙin wani kuke ci." Naila tƙarasa faɗa tana huci.

Mari Barirah ta taso zata tsinkawa Naila.
Naila ta kama hannunta na gantsara mata cizon da iya kaifin haƙwarana daya da Barirah kwarara ihu.

Cikin zare ido Mairam ta saki kofin hannunta ta ce;

"Ke fita ki kiramin Securities su fitarmin da wannan abun" Mairam ta ƙarasa faɗa tana pointing Naila.

Ƙasa Mama ta durƙushe tana bata haƙuri

Cikin zafin murya da zafafan kalaman da suke fitowa tun daga ƙasar zuciyar ta ce;

"Ba iya kamani zakisa ayi ba kisa akasheni kamar yadda kikayi