sanadiyar mutuwar Ummeena kika gudu kika samu daula kika manta dani, idan kuwa baki yi haka ba to tabbas! baki cika butulu ba Mairam dake da ahalinki! Wallahi da na cigaba da ganin fuskarki Gara kisa ayimin kisa mafi ƙanƙanci akan na Mahaifiyata," Naila ta ƙarasa faɗa kamar zata daketa.
Mairam batayi gigin kawo farin sol ɗin hannunta ba gudun abinda Nailar tayiwa Barirah.
Sak Mairam tayi tana kallon Naila, kafin rufuwar Seconni saiga Mahaifanta da kuɗi yaƙara gyarasu sun bayyana.
Kamannin Mahaifiyar Naila a bayyane yake akan fuskarta da gangar jikinta don kallo ɗaya sukayimat suka shaida ta amma saboda su tabbatar sai Mahaifinta ya ce;
"yarinya daga ina kike?"
Babu shakka balle kwana-kwana Naila tace ;
"Yankin Tudu Daular Sarki Hammam, Naila ƴar gidan Mahmoud Maɗinki wacce ta rasa Mahaifiyarta dalilin baiwa Mairam Matar Abduh Dhahab kariya."
Ido Mahaifin Mairam ya rutse son zuciya na bijiromasa da kuma burin da suka san ya jima a zuciyar ƴarsu ya ce;
"Yarinya bamu sanki ba, Barirah maza kira jami'ai"
Kallon tsohon Naila takeyi bata ce komai ba.
Mahaifiyar Mairam ba tayi magana ba, sai kuka da takeyi alamun lamarin baiyi mata daɗi ba.
Za'a iya kiran musayar yawunsu da Naila na farko daya taɓa faruwa tsakaninsu da masu yi musu Hidima tun bayan kafuwar Dhahab. Don haka kafin kace kwabo ƙofar sashen su Ummi Mairam ya cika da asalin mutanen Dhahab.
Ita dai Mama da ta rako Naila kuka takeyi tana magiyar suyi haƙuri.
Mahaifiyar Sulaim ce ta fito cikin shigar dake nuna matsayinta, kafin a tafi Naila kamar yadda Barirah ta basu umarni ta buƙaci jin abinda ya faru ta bakin Mama dake kuka a durƙushe tana magiya.
"Daga ina yarinyar take" Ummi Aysha ta tambayi Mama.
Da rawar murya Mama ta ce;
"Allah Ya taimake ki daga Birnin Abyad take ƴar ƙanina ce ta gayyatota kitso kuma da izinin Sir Malik, amma yanzu naji tana cewa daga Yankin Tudu take" Mama ta ƙarasa faɗa cikin kuka.
Ummi Aysha idanuwata da suke iri ɗaya da na ɗanta Sulaim ta lumshe soyayyar Abduh Dhahab daya kasa barin ranta na bijiromata.
Kai tsaye ta ce akiramata Malik kafin a tafi da Naila domin bata yarda da garaje ba a rayuwarta, domin garaje ne yasa ta tafi tabar Abduh a ranar da nasararsu ta tabbata.
Kafin su samu layin Malik, Armored Toyota LC300 Baƙi mai shaiƙi ya karyo kwanar Ɓangaren.
Basa dariya sai sunga mugunta wannan inkiyar Malik ne da Ubangidansa.
Don haka fuskarsa da babu fara'a sam yake ɗaure tsam kamar ya ɗauresa da igiya.
Baya yiwa kowa a cikin su aiki balle yayi musu biyayya don haka kowa ya kame kansa, Barirah kamar ta fashe don takaici.
Mahaifin Mairam daya biyewa farin cikin ƴarsa, gumin daya tsatsafomasa ya sharce. Ita dama Mahaifiyarta tana ciki ko leƙowa batayi ba.
Bayan ya zuro da gangar jikinsa waje, ɓakin tabaran fuskarsa ya zame. Malik yana da salon tsayuwar da yakeyi wanda dole kowa ya shiga taitayinsa.
"Menene yake faruwa" Malik ya tambaya da nannauyar muryarsa. Da harshen nasara shugaban Securities daya zo wajen dai-dai zuwan Malik yake tambayar kowa na wajen da karfi.
Dukkansu Barirah data kirasu suke kallo, domin babu bayanin komai tace su zo su tafi da Naila.
Haɓarsa Malik ya ɗan shafa yana matsowa wajen da kyau, sai a lokacin yaga Naila dake tsugunne taci kuka jijiyoyin goshinta sun fito sunyi ruɗu-ruɗu.
"Kowa ya koma bakin aikinsa" Malik ya faɗa idanuwansa akan Barirah data yi ƙasa da Kanta.
A zafafe Ummi Mairam ta ce;
"Babu inda zasu je, domin nice Uwar data raini wanda suke yiwa aiki don haka dole su tafi da ita, su hukuntata sannan su mayar da ita asalin Yankinta"
Baki Malik ya taɓe yana yiwa Mairam kallon da bai taɓa yimata ba ya ce;
"Ya ce in ji shi! ta rayu a Dhahab ita da ahalinta da duk wanda taga dama, bazaki sauyamin aiki ba, amma yanzu ki kirashi tunda ke Uwa ce idan ya canza magana sai muma canza"
Hannu na rawa Mairam data kwashe imaninta ta siyarwa Shaiɗan ta dannawa layin Sulaim na musamman kira"
Abune mai wahala ka kirasa ya ɗauka nan take amma tana kira ya ɗaga, cikin kukan take koramai jawabin ga wata tazo tanayimata rashin kunya ta ce akamata Malik ya ce bata isa ba.
Mahaifiyar Sulaim Ummi Aysha ƙwallane ya cika idanuwanta saboda yadda Mairam take yaƙin lallai sai ta rabata da ɗan da batasha wahalar haifarsa ba, bata wankemai bayan gida ba, bata wankemai fitsari ba, kawai abincin da Mahaifinsa yake siyowa take dafawa su ci, amma dai-dai da tarbiyya Sulaim Abduh ne yayi masa da Kansa domin barcine kawai yake rabasu.
Sulaim
Cikin taushin murya dake bayyana izzarsa ya ce;
"wacece ita? Maiyasa zatayi miki rashin ɗa'a? Kunsan juna ne?"
Shiru Ummu Mairam tayi, ta kai daƙiƙu biyu kafin ta fara lalubo abin faɗa sai da ta gama kame-kamenta ta gane ya jima da katse wayar tun bayan tambayar da ya yi mata, tayi shiru.
Saƙon Sulaim ne ya shigowa Chief securityn Dhahab.
Umarnin kora ya rubuto ga Securities ɗin da suka amsa umarnin Barirah saboda bai san kallon wani iri matsayi sukeyi mata ba, da har zata bayarda umarni subi batare zurfafa bincike ba. Sannan kowa yabi umarnin Malik a cikin daƙiƙu, wanda yaƙi a gaggauta fitar dashi daga Dhahab gaba ɗaya kuma babu dawowa.
Chief security na gama sanar da saƙon Sulaim a sarari, Malik ya goge gilashinsa da salo ya mannawa idanuwansa haɗe da bawa Securities mata Umarnin su taimakawa Naila ta miƙe.
Har Malik ya juya Ummi Aysha da ta kasa jurewa tace;
"Ka roƙamin alfarmarsa ya bar securityn da aikinsu" ta faɗa da tausayi a muryarta.
Malik bai jirkintawa maganar Ummi Aysha ba ya turamai saƙo.
Rashin bayar da amsarsa na nufin amincewarsa don haka Malik ya ce abar Securities da aikinsu, amma ayi suspending ɗinsu na watannin da suka dace domin kiyaye gaba.
Babu halin musayar yawu da hukuncin Sulaim, don haka Ummi Mairam da Barirah harma da Mahaifin Mairam da kunyar Malik ya hanasa sukuni suka shige ɓangarensu.
Itama Ummi Aysha ɓangarenta ta nufa fuskarta ɗauke da murmushin alfarmar da Sulaim yayimata a matsayin biyayya akaron farko.
UMMI AYSHA
tambayar da take yiwa kanta shine; "Wacece Naila, menene matsayinta a wajen Sulaim har da zai shiga lamarin Dhahab akanta" tattaunawar da suka wuni sunayi kenan ita da ƴan uwanta.
A ɓangaren Barirah da dare ya yi tazo kwanciya maganganun Naila ta tuna;
"Ƙarya kike Barirah! Bakiyi wannan arziƙin ba, wacece ke? Ko da bansan ƙaddarar arziƙi ba babu yadda za'ayi mai sana'ar maganin gargajiya ya mallaki Dhahab, dole arziƙin wani kuke ci"
Waɗannan Kalamai su suka addabi zuciyar Barirah, a wannan dare bata runtsa kuka kuwa tayisa kamar zata makantar da idanuwanta.
Wanda yaji daɗin cizon da aka yiwa Barirah ya dannamin like😂
In Shaa Allah gobe zai zama ranar hutu. Na gode
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL
7
SULAIM
Bayan ya gama waya da Ummi Mariam mamaki ne ya kamasa.
A kaf zamansa da ita bai san wani hali taƙamaimai na ta da zai kwatanta ta da shi ba, domin rayuwarsa a gidansu na Yankin Tudu daban yake da na ta, a wasu lokutan ma sai dare suke haɗuwa ko Safiya idan zai je Makaranta, kawai dai abinda ya sani suna kwana a gida ɗaya.
Abu ɗaya zai iya faɗa akanta shine tayi wahalar kai shi Asibitoci domin yayi walwala ya dawo kamar kowani Yaro, kenan banda wannan halin kirkin nata, tana da wani hali daban da bai sani ba?
Kulle idanuwansa ya yi saboda jin alamun shigowar mutum, yasan ba zai wuce Noorhan ba, domin ita kaɗai ce take da wannan alfarmar.
Babu alamar tana da haɗi da musulunci a yanayin shigarta, kyakkyawar fuskarta a ɗaure ta ƙaraso inda yake bakinta ɗauke da sallamar daya kafamata sharaɗinsa.
Ɗan ɓata fuska taƙarayi tana gaishe shi, kafin ta ajjiye siririn dogon farin takardar dake ɗauke da sunayen abubuwan buƙatarta.
Lumsassun idanuwansa da suka ɗan sauya kala ya ɓude akan takardar. Card ɗin daya tanada don zuba kuɗin buƙatar Noorhan ɗin ya miƙa dogon hannunsa ya ɗauko ya miƙa mata.
Tuni fuskarta ya washe tunda dama ta ɗauresa ne saboda tasan tambayar kuɗinta ga Sulaim ya zarce ƙa'ida ko Iyayen da suka haifeta, bata isa su kashe mata kuɗin da take chajar Sulaim ba.
Murmushi tayi tana juya idanuwanta ta ce;
"Inajin daɗin yadda kake kashemin kuɗi Habibi, na gode"
Kai Sulaim ya jinjina mata, tana yunƙurin sako hirar data saba yimai taga ya miƙe, kafin ta yi ƙorafi ya dakatar da ita ta hanyar sumbatar saman goshinta ya bar wajen.
Baki ta saki tana bin bayansa da kallo. Card ɗin hannunta ta zauna jujuyawa, tunanin abin yake neman sauya mata shi lokaci ɗaya takeyi mata. Ta ɗan jima kafin ta miƙe tabar Gidan.
★washe gari da yammaci da sabon kwalliyarta Noorhan ta kawowa Sulaim ziyara.
Maimakon samunsa a zaune a irin wannan lokacin yana aiki, sai ta samesa a kishingiɗe da System a gefensa idanuwansa a kulle kamar dai yadda ta samesa jiya.
Cikin ɗan takaicin abin yake shirin taɓamata shi ta ce;
"Tun zuwan Malik kwana biyu da suka wuce ka sauyamin why the Sudden change?"
Idanuwansa da suka tara ruwa aƙasa ya buɗe amma ba dukka ba, yanayin lumshewarsu kamar wanda yake fama da zazzaɓi mai zafi, cikin taushin muryar dake ƙara matar da zuciyar Noorhan akansa ya ce;
"Beg your pardon?"
Gashin kanta ta ɗan hargitsa tana matsowa kusa da shi da kyau, sai dai takasa kallon cikin idanuwansa da har lokacin suke a kan fuskarta, domin wasu lokutan idanuwansa tsoro suke bata.
Kuka ne ya fara zuwarmata kafin ta fara koro bayanin ya sauya tun zuwan Malik kuma shima yasan haka dan Allah karya bari a rabasu, ta roƙesa. Ita bazata takuramai ba duk lokacin daya shirya aurenta zata jirashi.
Har ta gama magana Sulaim bai motsa ba bai kuma daina kallonta ba, wannan dalilin yasa takai hannunta gefen wuyarsa. Zafin jikinsa yasa tayi ƙasa da Kanta, sai a lokacin ta raina wayonta da kuma dasa Ayar tambaya wa soyayyar da take yi mai anya ba na kyansa da kuɗinsa ba ne? Idan da gaske tana sonsa yakamata ta fahimci bashi da lafiya tun daga sauyin idanuwansa da zaman da yayi yakasa aiki, domin Sulaim baya wasa da naiman kuɗi.
Kanta ta juyar gefe kunyar kanta na mamayeta, cikin ƙarfin hali ta ce; "I'm sorry"
Idanuwansa ya ɗan lumshe alamun ya karɓa kafin ya ɗauki wayarsa ya tura mata saƙo. Yana tura mata ya miƙe, kunyar bin bayansa yasa tabi shi da kallo.
Tasani Allah ne yake sonta ya turomata Sulaim cikin rayuwarta amma ta lura ba lallai ya zama mallakinta ba saboda sam yanayin halayyarsu ba ɗaya bane, tsabar son da takeyimai gaba ɗaya sai ya zamana kamar tana shiga haƙƙinsa ta hanyar takuramai, gani take yi dole fa sai ta zaƙe kar a ƙwace mata shi.
Sulaim bayan ya shiga ɗaki kwanciya ya yi.
Ya kai wasu daƙiƙu a kwance kafin ya lalubo wayarsa ya danna Kiran layin Malik.
Bayan Malik ya amsa sallamarsa, da muryasa da ta yi sanyi, irin sanyi da Malik bai taɓa ji ba ya ce;
"Yaya Naila ta daina kuka? Kana ganin zamanta a Dhahab kaɗai zai sata farin ciki ko nazo ta ganni? ko kar nazo saboda kar ta ji tsoro?"
A ɓangaren Malik katse kiran ya yi, domin bai yarda Sulaim bane, ko da ya duba ya tabbatar layin Sulaim ne, kai tsaye masu kula da lafiyarsa ya kira, su shiga Gidan su bincika wani ya shiga har ya samu nasarar ɗauke wayar Sulaim.
Sulaim dake kwance da Noorhan dake zaune har lokacin a living room mamakin ƙarar da suka ji na alamun akwai matsala ne ya tashi kowannensu tsaye.
A ɓangaren Sulaim kansa ya dafe yana jinjina Soyayyar Malik garesa don ko shakka bayayi aikin Malik ne. Tunanin zasu iya riƙe Noorhan da tuhumarta a matsayin mai laifi yasa ya fito daga ɗaki.
Ya kuwa samu sun zagayeta wasu na ƙoƙarin bincika Bedrooms ɗin da suke cikin Sashen.
Fitowarsa yasa sukayi ƙasa da Kansu tare da shaidamai Umarnin Sir Malik ne, bayan tabbatar da lafiyarsa suka bar Noorhan da sakakken baki.
Suna fita kiran Malik ya shigomai bai ɗaga ba ya katse kiran nauyin kalaman da ya furta har yasa Malik yake tunanin ba shi bane ya sashi sakin ƙaramin murmushi.
Malik Noorhan ya kira, jiki na rawa ta ɗaga, kai tsaye tun kafin Malik ya tambayeta ta fara zubomai labarin sauyin Sulaim da zazzaɓin da ta samesa da shi. Dan Allah ya sanar da ita menene matsalar?
Kwantar mata da hankali Malik ya yi tare da bata shawarar ta koma Gida ciwone kawai ya sauyasa amma babu matsalar komai.
MALIK;
Ajiyar zuciya ya sauke bayan gama waya da Noorhan, ya ɗauka wanda ya san da zaman Naila ne ya tafi har can Kahala yake kiransa ta wayar Sulaim,
"to amma ta yaya hakan zai faru?" Ya tambayi kansa. murmushi ya saki ya ɗan marin fuskarsa.
Anya hasashensa bazai zama gaskiya ba kuwa? Na Sulaim zai dawo da soyayyarsu da Naila.
Wajensu Naila da yayi niyyar zuwa ya nufa.
NAILA;
Har aka kaita bakin Sashen su Mama a motar Malik bata daina Kuka ba, fuskar Mariam da ta wulaƙantata na sukar zuciyarta. Ta yi tunanin da ta ganta zataci albarkacin Mahaifiyarta a wajenta ko da bazata nuna ta santa ba, ta hana Barirah wulaƙantata, ashe ita zata bawa Barirah lasisin mayar da ita abar kwatance.
Kaka hankalinta a tashe ta tarbi Naila domin tun tafiyarta ta kasa zaune ta kasa tsaye, saboda tsoron tozarcin da Barirah za iya yimata.
Ko ɗakin da suke daa ba'a barsu sun koma ba Malik ya cewa Mama ta canza masu ɗaki. Ɗakinta dayasha ƙawa ta kai su jikinta yana rawa. Tashin hankali bai sa Kaka ta gane Malik ba.
Da Naila ta zo bawa Kaka labari kasawa ntayi saboda kukan dake sarƙemata murya. Rungumeta Kaka tayi tana bubbuga bayanta.
Kafin Sallar magrib zazzaɓi mai zafi ya rufeta.
Malik daya bada umarnin gyara sashen da zamu koma Mama ta kira. Gudun matsala Malik ya turawa Ubangidansa saƙo.
Umarnin akaita tsadadden Asibiti Sulaim ya bayar.
Sai bayan sun kai Asibiti anbawa Naila gado Kaka ta gane Malik.
Ɗimuwarta da Kaka ta shiga ne yasa Malik kiranta guri na musamman a cikin Asibitin.
Sai da Kaka ta tofe Naila dake barci da ƙarin ruwa a hannu da addu'o'i sannan tabi bayan Malik, zuciyarta cike taf da tsoro.
Bayanin komai da wanzuwar Sulaim a doron ƙasa yayimata, tare da shaidamata mutuwar Abduh bayan barinsa Yankin Tudu.
Kaka tayi sabon kukan mutuwar Abduh Dhahab, ta kuma yi farin cikin Sulaim dayake raye da zaman da zasuyi a Dhahab.
Sai dai a take Shaiɗan ya fara bijiromata da maganar Sarkin Tsafin Yankin Tudu dayaƙi barin zuciyarta ta huta, nan take jikinta ya yi taji murnarta na komawa ciki.
Duk da wannan Kaka bata musawa Malik zamansu a Dhahab ba, sai dai tace bazata iya shaidawa Naila Sulaim yana raye ba, duk ranar da Allah ya ƙaddara haɗuwarsu zata gani da idonta. A kan haka sukayi sallama da Malik ya wuce Gida.
Sai tsakiyar dare Naila ta farka, itama Kaka da idarwarta daga Sallar nafila kenan miƙewa tayi ta zauna a gefenta.
"Sannu" take ta maimaitawa Naila.
Sai da Naila ta ɗan huta Kaka ta haɗa mata Shayi tasha sannan ta fara bata labari abinda ya faru, sai bayan ta gama Kaka ta sakomata hirar zamanmu a Dhahab. Ɗan jim Naila tayi itama maganganun Sarkin tsafin Yankin Tudu da Kaka ta sanar da ita na neman yiwa nutsuwata Illa, ambaton Allah tafarayi a cikin zuciyarta tana neman tsari daga sharrin shaiɗan.
Haka suka ƙare wannan a kan tattaunawar zamansu a Dhahab.
★washe gari maimakon a sallami Naila sai akace saita ƙara hutawa.
A yammacin rana Malik ya zo duba su, da zai tafi ya buƙaci mukullin sashensu na Birnin Abyad domin kwaso takardun Makarantar Naila da kuma bawa masu gida mukullinsu. Jakar da ke tare da Kaka ta duba ta ɗauko mukullin ta basa..
Bai jima ba ya bar Asibitin.
Washe gari sai ga Bushra ta kawo musu ziyara.
Naila tayi farin cikin ganin Bushra bayan tsahon lokacin da suka kwashe Basu ga juna ba. Ta wayarta suka gaisa da Yasar, ya tayamu murnar zaman da zasuyi a Dhahab da kuma nasihar Naila ta mayar da hankali kan karatuntaa daga haka suka yi sallama, duk da akwai abubuwan dayawa da Naila take so su tattauna.
Da aka sallami su Naila washe gari Bushra da Driver ne suka zo ɗaukarsu, maimakon su nufi Gida wajen siyayyar kayan sawa suka wuce.
Ba su yi mamakin irin siyayyar da Malik ya bawa kuɗi Bushra tayi mu su ba kamar yadda ta faɗa, sun jima Bushra tana kwasar suturar sawa da duk wani kayan buƙatarsu sannan su ka nufo gida.
Kyan Muhallin da aka basu a Dhahab ba ƙaramin birgesu ya yi ba, saboda ba su san ma yadda zasu kwatanta kyan matsugunin na su ba, a taƙaice dai zasu iya kiransa da aljannar duniya.
Kaka manta ƙalubalen dake gabansu ta fara takawa bayan tayi sujudar godiya ga Ubangiji.
Bayan sun gama murna sun huta, Naila ta kalli kan Bushra dake tsafe tace ta taho tayi mata kitso.
Kai Bushra ta girgiza ta ce;
"mai Dhahab ya ce babu ke babu kitso har abada, ko kina so afara hukuncin ta kaina ne? ke da ma baki da lafiya"
Ƙyam Naila tayi da idona akan fuska Bushra ta ce.
"wanene mai Dhahab? Shin shi zai dinga biyana kuɗin da zan kai cigaba Yankina ne da har zai hanani yin sana'ar kitso?" Naila ta ƙarasa faɗa tana haɗe fuskarta
Da mamaki Bushra ta amsamata daa;
"Malik bai faɗamiki wanene shi ba, sannan ai yace ku faɗi duk wanda kuke so a ɗauka aiki a danginku"
Naila ko a jikinta ta ce;
"Ban san shi ba, kuma bashi da hurumin dakatar dani, idan ya ɗauki Matasa masu ƙarfin a jiki aiki, waɗanda suka tsufa fa kuma ba su da ƴaƴa ko Mijin da zasu turo ya ya zasuyi?"
Dariya Bushra ta saki haɗe da kama bakinta mamakin irin son da Naila take yiwa Mutanen Yankinta na kamata.
Bushra zata ƙara magana Kaka ta katseta da ce wa;
"Bushra ɗan zo mana kinji"
Ba musu Bushra ta miƙe tabi bayan Kaka.
Jan kunnen Bushra Kaka tayi, kar ta sanar da Naila komai ta yi shiru har sai ranar da idonta ya gane mata.
Duk nacin da Naila tayi Bushra bata bari n
tayi mata kitso ba har ta bar Dhahab.
Bayan tafiyar Bushra
Da lallashi da ban baki Kaka ta taushi Naila ta haƙura da zancen kitso, amma duk da haka da Malik ya dawo sai da