x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 24 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 69001 words
  • 72000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 750

07 Oct 2025
Naila ta ƙara tuntuɓarsa.

Malik murmushi ya ɗanyi yana waskewa daga tambayar data yi mai na wanene Mai Dhahab, sai amsar biyanta albashi duk wata da ya yi. Tare da alƙawarin ɗaukar duk wani ɗan Yankin Tudu aiki matsawar zai dinga tura kuɗi gida.

Babu wanda ya leƙo su Naila har suka yi kwana biyu.

A kwana na ukun su a Dhahab Mota da Drivern daya sa Naima jinta wata ta musamman ya zo ɗaukarta wai Inji Sir domin kaita Makarantar da batasan yaya yake ba Malik dai ya turo mata Numbern wanda zata kira.

Shigar Naila Jami'a mafi tsada a Babban Birnin Abyad kamar yadda ta duba sunan Makarantar a wayar hannunta yasa ta ƙara tambayar kanta.

"Wanene mai Dhahab? Wani irin zuciyar taimako ne da shi?"

UMMI AYSHA
Da yammaci ta naimi Malik a waya saboda tambayoyin daya hanata ita da ƴan uwanta sukuni.

Bayan Malik ya isa Sashenta sun gaisa, ya ɗan motsa bakinsa da kayan da suka jeramai Ummi Aysha ta kallase da kyau ta ce;

"Wacece Yarinya da Sulaim ya zaɓi ajjiyewa a kusa dani? daga ina take? Menene alaƙarsu?....✍🏻
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

8

SUFYAN;
A wannan karon shi kaɗai ya yi jinyarsa da nurses da suke kula da motsinsa, sai kuma coworkers da suke shigowa dubasa.

Ya yi zuru-zuru kamar ba Sufyan ba. Tun kafin a sallamesa ya yanke shawarar zuwa Yankin Tudu ya ga halin da Mahaifiyarsa take ciki, domin ya kira wayarta sau babu adadi baya samu. Jikinsa ba ƙarfi ya kunna wayarsa.

Ko minti biyu baiyi da kunna wayar ba kiran Ɗayyib ya shigomai.

Jiki a sanyaye ya ɗaga da Sallama.

Cikin alhini kamar gaske Ɗayyib ya ce;

"Ɗa na Sufyan mai kake gudu daga gareni ka ƙauracewa waya da ni?"
Kai Sufyan ya ɗan girgiza kamar Ɗayyib yana ganinsa ya ce;
"Baaba ba ni da lafiya, amma cikin satinnan ina nan zuwa duba lafiyar ku"

Duk nacin da Ɗayyib yayi wajen sanin taƙamaimai abinda yake damunsa, Sufyan bai faɗa ba, daga ƙarshe haka sukayi sallama ran kowannen su cike da zullumi.

Kwana biyu bayannan aka sallamo Sufyan ya naimi alfarmar zuwa dubo Mahaifiyarsa.

A ranar ya kimtsa kayansa ya nufi Yankin Tudu.
Lokacin da ya isa iyakar Yankin Tudu, wani Matashin da bai taɓa ganinsa ba, ya miƙomai farar Takarda a nannaɗe wai inji Sir Malik.

Tuni gumi ya fara tsatsafowa sassan jikinsa, hannunsa yana rawa ya warware takardar don ganin maiya ƙunsa....


BARIRAH;

A ɓangaren Barirah kullum fuskar a kumbure kamar an kwaɓa fanke ya tashi. Breakfast ma bata sonyi. Dama ba wani ɗasawa sukeyi da Simbi ba a wasu lokutan, don haka Simbi da take jin haushin abinda Barirah ta aikata duk da sunan son abinda yafi ƙarfinta tattarata tayi ta watsar kamar batasan abinda ya faru ba.

Ummu Malik data kasa jurewa yanayin Barirah janyota a jiki tayi saboda Mahaifinsu bayanan.

Da taushin murya ta fara yi mata nasiha;

" Ba ina yimiki iyaka da Mairam ba ne, amma ina yi miki gargaɗi akan abinda take ƙoƙarin ɗoraki akai, daga mu har ita babu mai gadon Dhahab a cikinmu, domin tuni Sulaim ya fitar mata da haƙƙinta. Ba ita ba ko Aysha da ta haifesa rayuwa suke yi a mabanbanta duniya, sannan ke saboda sokuwa ce sai ta ƙara ɗoraki akan lallai sai kin auri mutumin da ya yiwa duniyar iyayenki da Iyayensa nisa. Kiyi tunani Barirah ko Sulaim bai taka wannan Matsayin ba, ba ajin aurenki ba ne, kuma itama Mairam tasan haka, Nailar da kike ƙoƙarin mayar da kanki sakarya akanta ki tuna ita ce ta samu damar raɓarsa bayan Mahaifinsa, kuma kinji labarin da Malik ya bayar da kunnenki, lokacin da Maihaifinsa zai taushesa da mutanen da zai iya riska bayan mutuwarsa har da Naila a cikinsu. Nasan baki ɗaukeni a matsayin Uwa ba tuntuni, amma ki sani Macen da tayi butulci wa irin halaccin da Mahaifiyar Naila tayi mata to tabbas kema wata rana zata yimiki wanda ya fisa Zafi"

Ummu Malik ta ƙarasa faɗa muryarta cike da haushin abinda Mairam take ƙoƙarin ɗora Barirah akai.

Barirah ba tace komai ba, sai kuka da takeyi kamar ranta zai fita.

Da Ummu Malik ta faɗa mata sashen da aka kai su Naila su zauna a Dhahab da irin Makarantar da Naila fara zuwa birkicewa tayi, kuka harda bige-bige tana cewa; ita tafiya zatayi.

Domin zuwan Naila Babban jami'a irin wannan a Babban Birnin Abyad na bata tabbacin labarin zuwan Naila Dhahab ya riski Sulaim.

Tana cikin wannan rashin kirkin Malik ya shigo, bai yi wata-wata ba ya wanketa da marukan da sukayi connecting jijiyoyin ƙwaƙwalwarta ta dawo hayyacinta ta nutsu waje ɗaya tana sauke ajiyar zuciya.

Da zafin muryar takaicinta ya ce;

"Za ki tafi who cares? Za ki kashe kanki who cares? Kinsan wa ma kike so kuwa? Sau nawa nake ja miki kunne? Ohh wannan yawon Barar da mukayi a Birnin Abyad ne bai isheki ba ko so kikayi ki koma?
Wallahi Daga yau idan na ƙarajin motsinki akan Naila sai na maimaita miki Tarihin shekarun baya da suka wuce, fool!"
Babu wanda ya motsa a living room ɗin, saboda girman muryarsa da ya cika ko ina. Ya na fita Barirah ta bi bayansa da kallo kamar zata haɗiyi zuciyarta.


A ɓangaren Ummi Aysha;
Babu wani kwana-kwana Malik ya sanar da ita gaskiyar komai.
Bayan tafiyarsa hirar su ce take ta kai kawo a cikin zuciyarta, ba ta ƙin Naila, amma tabbacin Sulaim yanayin dukka waɗannan abubuwan ne domin faranta ran Naila yasa ta buƙaci ganinta, ta ga menene take da shi wanda sauran mata basu da shi, ko kuma kawai sa'ace Allah Ya bata....

ROYAL UNIVERSITY ABYAD; har Naila ta bar Makaranta bayan ta haɗu da wanda Malik ya ce ta kira ya cikemata komai, bata daina sawa wanda ya biyamin kuɗin Makarantar albarka ba.

Da Driver ya zo ɗaukarta a Mota mai taushin kujeru da sanyin raɓa sai ta lumshe ido daɗi kamar ya sumar da ita har wani matse hannu takeyi tana ɗan zaro harshe ko wa take yiwa gwalo oho? Ta faɗa a cikin zuciyata tana sakin dariya.

Wajen cin abincin da ya dawo da ita asalin ƴar Yankin Tudun da bata taɓa zuwa ba Driver ya kai ta, wai ta huta ta ɗan ci abinci karta ƙarasa gida da yunwa inji Sir Malik.

Driver yana fita kafin ya zagayo ya buɗemata ƙofa ta saki dariya tana jijjiga kaina tare da juya idanuwana kamar zata wurgosu ƙasa.

Gaba ɗaya ɗan daɗin da ta ɗanɗana na wannan rana sai ya sata jin kanta da ganin kanta kamar wata ta musamman.

Da ta kai Gida Kaka tasha labari har da ƙari da zuzutawa kamar a gabanta akayi komai.

Bayan Magrib saƙon kiran Ummi Aysha ya riskesu ita da Kaka.

Zuciyarsu fal tsoro suka nufi Sashen.
Sautin Hermes flat shoe da ƙamshin turaren ta ne ya ankarar da su Naila fitowarta, Naila da Kaka nutsuwarsu suka tattaro waje ɗaya.

Bayan mun gaisheta ta amsa sai da ta ɗan ƙarewa Naila kallo na ɗakiƙu sannan ta ce;
"Naila"
Da sauri Naila ta amsa tanayin ƙasa da kanta alamar ladabi.

Da maganar mai cike da nutsuwa Ummi Aysha tace;
"Sunana Aysha Matar Abduh Dhahab, Mahaifiyar Sulaim" ta ƙarasa faɗa tana kallo yanayin Naila

A zabure Naila ta miƙe ta nufeta ta rungumeta da ƙarfi kamar zata ɓallata tana cewa;

"Dama nasan dole jinin Sulaim ne ya kafa Dhahab, kema kin ji labarin ƙonewarsu ko?"

Ido Ummi Aysha ta zaro tana kallon Kaka dake saitinta, kai Kaka ta girgiza mata.

Jin tayi shiru yasa Naila ta dawo hayyacinta ta saketa da sauri tana zamewa ƙasa.
Kafin Naila ta fara bata haƙuri Ummi Aysha ta ce;

"Ban sani ba Naila! dama Sulaim ya ƙone har ya mutu shine Malik ya kasa sanar dani don yaga bazan iya zuwa Yankin Tudu ba, maiyafaru bayan tafiyata? wanene ya ƙona min Ɗana da Mijina Abduh" Ummi Aysha ta faɗa kamar gaske, dama kuma ta jima tana naiman wanda zai bata labarin bayan tafiyarta don ta kasa tambayar kowa saboda kunyar guduwar da ta yi.

Ita dai Kaka kallonsu take yi musamman Ummi Aysha.

Kamar an kunna gidan radiyo haka Naila ta zauna tana bawa Ummi Aysha labari, wasu labaran duk ba a haifeta ba aka yi su a bakin Kaka ta ji.

Wasu Labaran Ummi Aysha ta murmusa wasu kuma ƙwalla ya tararmata a ido.

Sai da ta gama taji maganar Ummi Aysha
"Idan Sulaim zai dawo a raye zaki so shi kuyi Aure?" Ummi Aysha ta tambayetahar cikin zuciyarta domin a bayaninta ta fuskanci sam Nailan batasan Sulaim yana raye ba.

NAILA; murmushi nayi kunyar maganarta ya sata ƙarayin ƙasa da kanta, sai lokacin kunyar zubar da ta dage tanaayi, ita a dole masaniyar tarihin rayuwar Sulaim ya kamata.

Ummi Aysha bata ƙara ce mata komai ba, har masu hidimar shashenta suka gabatar mu su da Abincin dare.

Bayan tafiyarsu Naila..
Ummi Aysha kasa runtsawa tayi har sai da ta shawarci ƴar ƙanwarta Farheen da Naila ta taɓa gani a Birnin Abyad a gidansu Yasar lokacin dayake jinya.

Farheen Bata yanke hukunci ba ta ce ta bari gobe da safe taje har sashensu Naila ta ganta kafin su san abin yi.

★washe gari da yamma Farheen ta nufi Sashensu Naila.
Tarbar dake nuna asalin tarbiyyar da su Naila suka samo tun daga tushe Farheen ta samu daga garesu ƙarin abinda ya birgeta shine wasa da dariyar su, tsayawa a matsayinsu duk da karramawar da Sulaim yayi musu na kawosu cikin su.

Bayan ta koma Sashen Ummi Aysha suka haɗa Plan ɗin da dole zai dawo da Sulaim Naila ta gansa, "ko yaya zata ji?"

Ummi Aysha ta tambayi Farheen.
Dariya suka saki lokaci ɗaya.

MALIK;
Bayan ya gama abubuwan da zai yi ya shirya komawa Kahala don dubo lafiyar Sulaim

kafin ya isa ya kira Managernsa ya haɗasa da likitan Sulaim da bai ma san ba shi da lafiya ba, tunda bai sanarwa kowa ba

Malik sai da ya jira likita suka nufo Gidan...
A living room suka samu Noorhan lulluɓe cikin Abaya fuskarta babu kwalliyar da Malik ya saba ganinta da shi.

Yana ganin haka yasan ba lafiya ba. Itama tana ganinsu ta miƙe tana kukan su taimaka, Habibi baya ɗaga kira kuma tafi hour biyu a zaune bai fito ba, tayi knocking bai amsa ba.

Malik ɗan harararta yayi ta ƙasan ido wai "Habibi mtsw" ya faɗa ƙasa-ƙasa yana nufa hanyar daƙin da Sulaim yafi zama a ciki.

Shima ya buga bai buɗe ba, don haka ya fara bi ɗakunan yana dubawa.

Malik yana cikin haka Sulaim ya shigo Gidan, Kyakkyawar fuskarsa ta faɗa sosai kamar ya yi shekara yana jinya.

Da gudu Noorhan ta miƙe sai dai yanayin tsayuwarsa da yanda yake kallonta yasa ta dakata tana wasa da yatsun hannunta. Maimakon rungumarsa da ta yi niyyar yi sai ta kamo hannunsa.

Da kai ya amsa gaisuwarsu yana zama a gefen Likitansa, hucin zafin zazzaɓinsa na busowa likitan.

Shima Malik waje ya samu ya zauna, zuciyarsa cike da mamakin rayuwar Sulaim, to ko dai kashe kansa yake son yi, tunda yana ganin kamar bashi da kowa. Banda haka tayaya namijin daya mallaki hankalinsa kamar Sulaim zai zauna yana wasa da lafiyarsa?...

Bayanin Sulaim ya haƙura su tafi Asibiti likita yake ta yi da sigar lallashi da tausasa harshe, har da ce mai Naanah Kakarsa kullum sai ta ce Sulaim ya rage zuwa.

Kalllon Likita Sulaim ya yi a hankali ya ce;
"Maiyasa zaka yi ƙarya daga wajen Naanah fa nake"

Dariya likita da Malik suka gimtse ganin ya harbo Likita kai tsaye. Banda Noorhan da burinta kawai Sulaim ya miƙe su tafi Asibiti ya yi ya warke su komawa Soyayyar su.

Malik yana shirin yin magana wayarsa ta fara vibrating. Bayan ya gama saurarar Farheen miƙewa yayi ya na furta "Innalillah! When accident ɗin ya faru?"
A ɓangaren Farheen dasauri tace " a safiyar ranar".

Kai Malik ya ɗan girgiza kafin ya naimi excuse ɗin zai ƙara kiranta. Suka yi sallama

Idon da Sulaim ya zubawa Malik na nufin ƙarin bayani, don haka Malik ya ce;

"Ummi Aysha ce ta yanke jiki ta faɗi jiya da daddare, garin zuwa dubata Naila ta zame I think kamar Farheen na bayanin ƙafar ya samu matsala, kuka ma takeyi."

"Ka shirya komai zuwa safiya mu isa Abyad" Sulaim yana faɗa ya miƙewa.

"Habibi ni fa" Noorhan ta tambaya kamar zata yi kuka...☹️

Ma su son a tafi ƙasar Abyad da Noorhan ya danna❤️ mara so kuma su danna👍🏻

Mu yi voting 😂
[9/5, 8:36 PM] Maman Amatullahi: SASAAL

9

A ɓangaren Sufyan;

Yana buɗe takardar yaga an rubuta;

"Barka da zuwa Iyakar Yankinka Sufyan! Rubutu na bazai tsawaita ba saboda wa su dalilai, amma duk tsananin da komai zaiyi babu zuwan Jalal da Ɗayyib Babban Birnin Abyad. Dawowarka zai tabbata ne idan ka ƙauracewa abincin cin su da shan su. Daga ƙarshe ina tayaka alhinin rashin da kayi. Ba lallai ka fahimceni ba amma ka haddace saƙona ka kuma sanya kunne da ido akan komai, ga na'urar naɗar komai ta sirrin da zaka saurara kai tsaye ta wayar hannunka. Zaka fahimci abinda na rubuta dalla-dalla."

Sufyan gumin fuskarsa ya zarce hannunsa yana rawa ya yaga dakartar gudun kar wani ya gani sannan ya ciro ƙaramar na'urar dake ciki envelope.

A karo farkon da ya fara wasa ƙwaƙwalwarsa ya nutsar da kansa kafin ya kutsa cikin Yankunansu.

Maimakon ya wuce Yankin Tudu sai ya wuce Yankinsu Mahaifiyarsa Hindu.

Ya samu Kakarsa cikin daular rayuwar da baiyi tsammani ba, tayi masa tarba ta musamman duk da bata san da zuwansa ba. Yana kallonta komai saƙon Malik ya na dawo masa, wannan dalilin yasa bai taɓa komai da Kakarsa ta gabatarmai ba, sai Mahaifiyarsa da ya tambaya tana ina? Murmushi tayi tare da shaidamai Hindu ta tafi Nahiyar Turai jinya, ai shi yasa ma baya samunta a waya.

waje ta bashi wai huta ya ci abinci, Sufyan amfani ya yi da basirarsa wajen jagwalgwala abincin kamar ya ci, abinda bai sani ba Kakarsa tana laɓe tana kallonsa. Bayan yayi mata sallama kafin ya isa Yankin Tudu ta kira Ɗayyib ta sanar dashi isowar Sufyan amma fa baici komai ba tana zargin jimamin rashin samun Mahaifiyarsa ne ya hanasa ci.

Lokacin da Sufyan ya isa Yankin Tudu abubuwa sun sauya, Talakawan Yankin sun samu cigaba ƙwarai kamar ba Yankin Tudu ba, ko da ya tambaya bayan ya huta sai ake sanar dashi ai Naila ce da Kakarta suke turo kuɗi, yanzu haka da safe kafin isowarsa dogon mota ta kwashi matasa sun samu aiki a ƙasar Abyad duk ta sanadin Naila, shiyasa jinin Jalal ya hau yanzu haka yana kwance babu lafiya.

Sufyan yana jin haka ya nufi ɓangaren Sarki Hammam da sunan isar da gaisuwa, domin ko da suka haɗu da Mahaifinsa ya dai jashi a jiki da bashi umarnin ya kwanta ya huta amma bai sanar da shi Jalal bashi da lafiya ba.

Sufyan yasan Ɗayyib da Jalal basa dogon hira gudun kar wani ya ji su don haka daya isa living room ɗin Sarki Hammam dayake zama wasu lokuta da Iyalansa ko baƙi masu muhimmanci sai ya ajjiye na'urar da Malik ya basa a gefen da bazasu ankara da wuri ba.

Da ya je Sashen Jalal ba a barsa yaga Jalal ba don haka ya koma nasu sashen, a living room ɗin Mahaifiyar ya zauna yayi shiru.

Har zuwa wasu ɗaƙiƙu yana zaune zaman jiran tsammani da abu maƙale a kunnensa, yana ƙoƙarin miƙewa sai ga Ɗayyib da sallamarsa.

lallashinsa ya hau yi akan rashin Mahaifiyarsa da ta tafi nahiyar Turai jinya kafin ya sako masa zancen yana so ya bishi Babban Birnin Abyad idan zai koma domin ya ga yaya ma'aikatarsu take. Sufyan kai tsaye ya ce; "haba Baabah ba Lallai su amince ba kuma ai babu abinda zaka je yi, amma bari mu gani zuwa safe idan na tuntuɓesu"

Shafa kanshi Ɗayyib ya yi da wani irin salo ya ce;

"Babu Matsala Sufyan ka tuntuɓesu, yanzu bari a kawo maka abinci da abin sha ko?"

Kai Sufyan ya ɗaga alamar ya ji.

Ɗayyib yana fita ƙwaƙwalwar Sufyan ya harba maganganun Malik suka ƙara dawomai kenan cin abinci daga garesu na nufin dole ya kaisu Babban Birnin Abyad ko da a ɓoyene su rayu da shi domin kutsawa cikin Dhahab, shin maiyasa Mahaifansa basason kwanciyar hankalin Talakawansu wacce iriyar zuciya garesu da babu tausayi da imani?

Yana cikin wannan tunanin Abinci ya iso, maimakon zama a inda yake, abincin ya ɗauka ya shiga chan ƙuryar ɗakin Mahaifiyarsa mai duhun da babu wanda zai iya ganinsa sai Mahalaccinsa.

Yana shiga ya ajjiye abincin a gefe ya mayar da hankalin kan hirar da Sarki Hammam yake yi da iyalinsa. Minti uku bayannan Muryar Ɗayyib Mahaifinsa ya bayyana.

ƊAYYIB
Bayan sun gaisa da Sarki Hammam, Sarki Hammam yake tambayarsa

"ya ya jikin Jalal?" Ɗayyib baiyi magana ba ya yi shiru har na wasu daƙiƙu sannan ya ce;

"Abincin da Jalal ya tanada ya isa ga Sufyan, ranar tafiyarsa zamu tafi tare da shi, mu bincika ina mutanen Yankin Tudu suke zuwa a cikin ƙasar Abyad, sannan mu san wanene mamallakin ma'aikatar su Sufyan"
Gwauron numfashi Sarki Hammam ya sauke ya ɗan kalli abinda Sufyan ya ajjiye danna ya ce
"Amma kana ganin babu wanda zai faɗawa Sufyan azabtar da ka ganawa Hindu bayan yin wayarsu ta ƙarshe, har binnenta da kayi shekaran jiya da ranta" Sarki Hammam da zuciyarsa sam babu sukuni ya tambayi Ɗayyib yana fatan Sufyan ya jishi.

A kasashe Ɗayyib ya ce;
"Babu wannan Mutumin a duniya, domin babu wanda ya sani kuma duk wanda ya ci amana a tsakaninmu to zai bi Hindu inda taje, na binne Hindu da ranta a tsakiyar ɗakinta ne domin ta girbi abinda ta shuka, saboda itace ta ɓata komai ta zuga Sufyan ya tafi Birnin Abyad, har da Naila. Yanzu gashi Talakawa duk suna walwala a Yankin Tudu su na jinsu kamar kanmu ɗaya da su, ba ni da haufi akan hukuncin da na yankewa Hindu ko da Sufyan zai ji wata rana. Domin abinda ya shuka shi ta girba"

A ɓangaren Sufyan kuka ya kece da shi jikinsa ya na rawa, katse komai ya yi, ya kuna fitilar wayarsa, cikin zafin nama ya ɗaga gadon Mahaifiyarsa, guri ya gani manne da tiles ɓaki sabo. Kuka ya saki yana kwanciya a wajen, saƙon Malik ya tuna "ina tayaka alhinin rashin da kayi" tayaya Malik ya sani, tabbas yana buƙatar ganin Malik ko ta halin ƙaƙa amma ta yaya zai tserewa su Ɗayyib????


SULAIM
kallon mamaki ya yiwa Noorhan na daƙiƙu, amma ko don tasan matsayinta ya kamata taje ƙasar Abyad. Idanuwansa ya mayar kan Malik da yake jiran umarninsa ya rausayar da kansa alamar ya