x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 759

07 Oct 2025
cikamin alƙawarina na roƙeka, ina shan wahala ka taimakeni ba ni da kowa a Birnin Abyad ka ji ƙaina ka faɗamin ina SULAIM yake? da gaske ya ƙone ya mutu?"

kamar yadda Naila ta yi tsammani bai tsaya ba tana ji tana gani su ka haɗa ido cikin ido da mutumin da ta ke ganin sak Salman sannan yaƙarawa Motarsa gudu ya barta a wajen. Ƙasa ta zube ina kuka.

Yasar da ya ga komai kuma ya kasa jurewa nufo inda Naila ta ke ya yi, ya kamo hannunta ya kawota har harabar gidansu. Cikin taushin murya ya ce;

"Naila menene ya ke damunki, ka faɗamin gaskiya daga ina ki ke(ma'ana Yankinta) "

kasa magana ta yi saboda shesheƙa.

Naila ta ɗauki mintina a haka, kafin ta daki ƙirjinta saitin zuciyarta inda ke ji kamar zai fashe, sannan na fara magana sheshekar kuka na tare ta;

" ina shan wahala🥹, ina so na koma Yankina, ina ji kamar zan mutu..."✍🏻
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c

🔥ZINARE🔥



SASAAL


15

Tana na gama furta ciwo da raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyata, sai ta ƙasa magana saboda kukan da ya ci ƙarfina.
Kamar talabijin haka Yasar ya zubamata fararen idanuwansa.

Ta kai wa su daƙiƙu tana kuka, kafin ta cigaba da magana;

"Sufyan ya na ganamin azaba, ya na dukana, ba ya barina na mori kuɗin da na ke samu. Ruwaida ita ce take taimakamin kuma ya yi mata sharri saboda ina tara kuɗi a wajenta ta bar gidan nan. Ni marainiya ce, ba ni gata kuma ba ni da ƙarfin yin komai ka taimakamin na koma Yankina"

Kai ya sunkuyar ƙasa saboda tausayi ya jima a haka kafin ya ɗago ya ce;
"Ina ne Yankin ku Naila? Kuma maiyasa ƴan uwanki tunda sun san ba su da halin da za su iya taimaka miki a ko wani lokaci su ka ba wa Sufyan ya taho da ke har Birnin Abyad? Wannan gangancine mai girman gaske"

Ba bu ƙarya a maganarsa amma ƙaddara ta riga fata. Cikin sanyin yanayin da ya ɗan fara shigar Naila ta ba shi labarin Yankin da ta fito. Amma ba ta ba shi labarin dalilin da yasa ta ke bibiyar mutumin da ta ke zargin Salman ba ne.

Yasar ya gamsu da bayaninta, amma sai ya ƙara jefomata tambayar "maiyasa ki ke kiran Mutumin da ya wuce ɗazun har ki ke cewa ya taimaka miki? Wanene kuma Sulaim ɗin da kike tambayarsa ɗan uwanki ne? Ki faɗamin gaskiya idan da hali zan iya taimakawa."
Ƙur Naila ta yiwa Yasar da ido, tarihin abinda ya faru na kusantowa ganina kamar a lokacin su ke faruwa.

Waje ta samu ta zauna Yasar ya biyo bayanta.
A baya labarin Yankinta da mahaifanta sun mutu kawai ta faɗamai da rashin adalcin danginta na ɓangaren Uwa da na ɓangaren Uba, amma tunda ya nuna zai taimaketa ta koma Yankinta to dole ya san asalin inane Yankin Tudu da kuma surƙullen da ya ke cikinsa.

Kamar Yasar ya na ganin komai haka ta ke ba shi labari tun da ga lokacin da ta yi wayo har zuwa mutuwar Salman da abubuwan da suka faru bayan nan har aurenta da Sufyan da kuma manufar Mahaifansa a kanta.

Mamaki ne zalla a saman fuskar Yasar, banda yana da ilimin nazatar Ɗan adam da kai tsaye zai ƙaryata Naila, wani irin Yanki ne wannan? Wa su irin mutanene ma su ƙaracin basira ne a Yankin?

Kusantowar lokacin dawowar Sufyan ya sa Yasar gajarta tunaninsa. Cikin alhini ya ce;

"Tabbas! Naila akwai DHAHAB CITY a Babban Birnin Abyad, Unguwar da wani mashahurin mai arziƙi ya gina, Shekaru goma sha biyar baya. Ahalina ne ma su tsauri da tsantseni domin dai-dai ma su gadin alƙaryar Dhahab ababen tsoro ne, sai dai shi ba sunanshi Abduh ba sunansa Muhammad Dhahab kuma a zahirin da mu mutanen gari mu ka sani Ɗan asalin ƙasar Abyad ne, amma wa su na cewa ba shi da asali babu wanda yasan gaskiya. Duk wani mai hidima da ma'aikatan Company's ɗin su, su na da record ɗin komai na sa, rayuwar su ba bu sakewa sam duniyar su tamkar daban ya ke da namu, ba bu wanda yasan sirrinsu sai makusantan su, Tun shekarun baya na naimi aikin tsaron sashen Mahaifiyar Muhammad Dhahab a yanar Gizo kamar yadda na ga an wallafa saboda ma su irin ilimina ake nema, amma saboda sun kasa samun cikakken bayani asalin ni ɗan inane da kuma inda Mahaifana su ke zaune, sai su ka fasa ɗaukata duk da cancanta ta, na yi kuka a waccen lokacin saboda albashin aikin ninkin wanda na ke samu a yanzu ne sau huɗu. Gane rashin samun cikakken asalina ya sa suka hanani aikin sai na tattaro Mahaifana na tara kuɗi na siya mu su Gida a Birnin Abyad, saɓanin daa da su ke zaune a bayan gari. Sai dai duk da na yi haka samun aikin sai ya gagareni haka na gaji na haƙura.

Bayyanar Simbi ahalin Gidan Muhammad Dhahab a Asibitin mu sai ya dawomin da burina na baya, wannan dalilin yasa na fara bibiyarta ta taimakamin saboda zan ƙara samun sakewa wajen taimakawa mahaifana har na samu na yi aure, amma sai Simbi ta wulaƙantani dalilin da ya sa nayi zuciya kenan na haƙura da aikin.

Amma Naila dole yanzu zan ƙara zage damtse har Simbi ta saurareni, saboda shigata Dhahab zai bayyanarmin alaƙar tarihin Yankin Tudu da rayuwar su, fatana ki tayani da addu'a."

Baki, hanci, da ido dukka Naila ta saki tana kallon Yasar, cikin kokwanto ta ce "menene sunan wanda aka ce shine Mijin Simbi mutumin da ya ke yimin kama da Salman?"
Ɗan dariya Yasar ya yi kafin ya ce;
"A binciken da na yi Simbi sam ba ta da Miji, kuma wanda ki ke gani sunansa Uzair, ba shi cikakken lafiya sosai saboda ya taɓa ciwon da ya yi shekara shida a kwance kafin ya warke, bansan wani ciwo ba ne, amma na samu bayanin ne da ga Yayan Ruwaida amintaccen ma'aikaci a kamfanin su, shima a sirrince ya faɗamin don haka ki kiyaye" kafin ya ƙarasa tuni Naila ta ɗora hannuwanta dukka biyu a kan bakinta alamun ba bu wanda zai ji.

Dariya Yasar ya yi kafin ya ɗora da nasihar ta kwantar da hankalinta da ƙarfin mulkin Allah sai sunyi nasarar shiga Dhahab ko a masu goge-goge ne.

Naila sai ta ji dukka ƙuncinta ya yaye sai ta ke ganin kamar komai ya zo ƙarshe, da wannan farin cikin sukayi sallama ta koma ciki ta yi wanka ta ci abinci. Gidan kitson da bata je ba kenan ta kwanta barci.


Daga wannan ranar Naila bata ƙara ji daga Yasar ba gaba ɗaya ma sai ta daina ganinsa. Da farko ta ɗan damu sai da ya ba da gajeran saƙonsa na suturar sawa ma su kyau da kayan ciye-ciye ya risketa ta kwantar da hankalinta.

Babban akwatinta ta sauko da shi, na ɗura kayan a cikin gudun kar Sufyan ya gani saboda ya kusa dawowa. Ta na kici-kicin mayar da akwatin hotonta da na Sulaim da ta sa aka wanke mata ƙaraminsa ya faɗo, da sauri ta ɗauke saboda har ga Allah batasan ya na cikin aljihun bayan Akwatinta da ta taho da shi ba, kuma tasha zuba kuɗi a ciki na kwashe amma hoton bai taɓa bayyana kansa ba. Da wani irin farin ciki ta ke kallon hoton. Batasan ta ɗauki lokaci a haka ba sai da taji Muryar Sufyan a bayanta, dama kuma da ɗayan key ɗin Parlon ya dawo tafiya Makaranta.

Firgitarwar da bayyanar Sufyan a lokacin da bata yi tsammani ba ne, yasa ta saki ƙara haɗe sakin ƙaramin hoton ƙasa, kallon hoton Sufyan ya fara yi sannan ya yunƙuro dasauri zai ɗauka ransa na suya, kafin ya cimma hoton tuni ta yi hanzarin ɗaukewa tana zare ido.

Fes Sufyan ya ga waɗanda suke jikin hoton, ciwon da ya jima da shafesa a tarihin rayuwarsa ya yunƙuromai. Cikin ɗacin zuciya ya fara dukanta ya na ƙwallo da ita, ya na cewa;
"ba ni hoton nan wato amanata ki ke ci ko? Shi yasa kullum bakya ganin kyawuna, kina maƙale da wannan hoton shaiɗanin da ya addabi mutane duk da ba ya raye, wallahi idan baki bani ba sai na kusa kashe ki" maganganun sa ba su ƙarawa Naila komai ba sai ƙaimin ƙara dunƙulewa da ta yi da hoton waje ɗaya, idan ya kasheta ma ai ta huta da uƙubarsa.
Har ya gama dukanta bata warware daga ɗunƙulewar da ta yi ba, cikin azabar kishi ya sa mukulli ya kullota yana huci...
Kuma ya yi rantsuwar ba zai buɗeta ba har sai ta bubbuga da kanta ta yarda bashi hoton ya ƙona sannan ta ba shi haƙuri.

Haka Naila ta kwana ta wuni kulle, inda Allah Ya taimaketa akwai kayan ciye-ciyen da Yasar ya aikomata da su, idan ta ɗanci sai ta kora da ruwan banɗaki ta ɗoro alwala ta kaiwa Ubangiji kukanta.

A haka ta shafe kwana uku tana manejin abinda Yasar ya bata tana korawa da ruwa kuma cikin hukuncin Ubangiji sai ta ji na ƙoshi.

A ranta take faɗin;
Banda shirmen Sufyan idan har shi da ya ke a iya haka yana ganin yafi ƙarfina to ina ga SULAIM da ya fishi komai ace ya na raye mai zai yi da ita? Sulaim tamkar Aboki ya ke a gareta har ya bar duniya, ba bu soyayya balle alƙawarin aure a tsakaninsu. Dalilin da yasa soyayyarsa ta samun matsuguni a cikin zuciyarta shine barinsa duniya, ta hanyar da dole a tausayamai, a kuma kasa mantawa da shi. Amma ko a raye ko a Mace bazata taɓa sawa ranta lallai Sulaim sai ya so ta ko ya aureta ba, matsawar ba ƙasƙancin da Sufyan yake nunamata dama take so ta fuskanta ba.

SUFYAN; A kwana na biyu da kulle Naila a ɗaki kafatanin kuɗin da ya ɗan rage a Bankinsa saboda ya turawa Gida kuɗi a rabawa Danginsa har da Dangin Naila da Kakarta da sukai ta samai albarka tare da farin cikin Naila tana cikin daula, su ka ƙare, ga shi ya saba siyawa Sumaya kaza, da su ice cream da sauransu har Gida ya ke siyamata ta kaiwa Iyayenta.

Tun washe garin da ya kulle Naila yake sa ran yunwa zai ci ƙaniyarta ta buga ƙofar ta ba shi haƙuri haɗe da ba shi hoton, amma ya ji shiru.

Kwana uku da kulleta daƙyar ya kalato canjin aljihunsa ya tafi Makaranta. Ranar ba su ci abincin arziƙi ba don haka ya keɓe ya kira wayar da ya tura kuɗi aka siyawa Mahaifiyarsa .

Hindu masifa takeyi bayan gama saurarar Sufyan kamar zata cijeshi ta waya..

"yanzu kai saboda ba ka san ciwon kanka ba shine zaka kulleta ka janyowa kanka asarar kuɗi ma su yawa, a kwana ukun nan banda kulletan da kayi da nawa zata samo maka? Amma wallahi Sufyan sam ba bu basira a cikin ƙwaƙwalwarka, har yanzu ba zaka daina kishi da Sulaim da yake matacce ka gina rayuwarka ba, Yankin Tudu kowa ya na samaka albarka, kai kana can kana shirme? To idan bata so Sulaim ba a matsayinsa na mutumin da su ke tafiya Makaranta tare su dawo tare su yi raha tare kuma ya ƙone lokaci ɗaya ba wa kake so ta so eh? dabba mara tunani!"

Saukar kalamanta sai da ya sauya kalar fararen idanuwansa, ya na jin kamar ana barbaɗa masa yaji, zagin da Ɗayyib Mahaifinsa ya ɗoramai da shi bayan ya karɓi watan ne yaƙarasa birkitasa, cikin rawar murya ya ke ba su haƙuri amma still Ɗayyib faɗi ya ke

" to yanzu haka Kasuwar Tukwanen Zinare ya mutu miɗis, sabuwar yunwa ta kunnowa Yankin mu kai, saboda an samu hamshaƙin mai arziƙin da ya saci fasaharmu ya mayar da su Tukwane na alfarma a kaf faɗin duniya ba bu inda ba'a siya, mu kuma an watsar da namu saboda ya zama tsohon yayi. Shine kai mun samu ka tsira zaka dawo damu baya, Allah Ya wadaran wannan son kyau na ka Sufyan! kai kullum ba ka da zance sai zancen Mutumin da tuni ya ruɓe a ƙarƙashin ƙasa, idan ka dama ka gyara to, idan kuma baka dama ba kai sani. Kasan da abinda zaka biya kuɗin hayar ku idan ya ƙare"

Sufyan kanshi ne ya ɗauki zafi a take ya fasa kuka yana ba su haƙuri. Shi gaba ɗaya ya manta da kusantowar biyan kuɗin hayar su.

Tahowar Sumaya inda ya ke ne yasa ya yi mu su sallama haɗe da yi mu su alƙawarin komai ya wuce, In Shaa Allahu zai gyara.


NAILA
Kayan ciye-ciyen da Yasar ya aikomata da shi ba laifin ya na da yawa, amma ba irin sosai ɗinnan ba, rashin sanin ranar da Sufyan zai buɗeta yasa take cancanensa kar ya ƙare ta rasa abin ci, saboda ko zai mutu bazata ba shi Hotonta da Sulaim ya ƙona ba.

Da yammaci ta na zaune a inda ta yi sallar la'asar ta ji ya buɗe kofar, fuskarsa ba yabo ba fallasa. Bai ce mata komai ba, ya bar ƙofar a buɗe ya juya ya fice.

★washe gari saboda rashin kuɗi ko Makaranta bai je ba. Ya na ɗaki ma su zuwa tambayar kitso su ka zo har mutum uku, ɗam jim Naila ta yi kamar ta ce mu su ba ta da lafiya, amma yadda su ka nuna su na son kitson ya sa ta amince. Sufyan dake laɓe yana kallonsu ajiyar zuciya ya sauke bayan ta amince ya koma ya kwanta yana murmushi.

Bayan ta gama su na fita ya yi zumbur ya fito ya ƙwace kuɗin fuskarsa ƙunshe da dariya.

YASAR; duk wata hanya da zai bi ya samu ganin Simbi abin ya ci tura, abinda ma ya lura da shi kamar ba iya son haɗuwa da shi ne ba ta yi ba, gaba ɗaya gudun mutane ta ke yi. Ranar da ya ji labarin saura kwana ɗaya ta gama abinda ya kawota ta koma Dhahab a bakin ofishinta ya wuni.

Ta na fitowa ma su gadin lafiyarta su ka rufa mata baya, kai tsaye tasa a hana Yasar bin bayanta. Sai dai kafin su kaiga riƙeshi ya taka da gudu zuwa inda motarta ya ke dai-dai inda ta ke tsaye yadda za ta jiyosa cikin yanayin maganar da matsawar tasan Naila zata fahimcesa a hankali da kuma sauri ya ce;

"Yankin Tudu, Daular Sarki Hammam Naila ƴar Gidan Mahmoud madinki, Aminin Abduh Dhahab....✍🏻
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c
🔥ZINARE🔥



SASAAL


16

"Yankin Tudu Daular Sarki Hammam, Naila ƴar gidan Mahmoud madinki, Aminin Abduh Dhahab." Yasar ya ƙarasa faɗa zuciyarsa na bugawa da sauri.

Dukan mai laifi kai tsaye ba tare da gudanar da ƙwaƙwaran bincike ba laifi ne mai girman gaske a ƙasar Abyad. Wannan dalilin yasa ko da jami'ai masu tsaron lafiyar Simbi suka cimma Yasar ba su taɓasa ba sun dai yi mai katanga tsakaninsa da ita.
SIMBI; Designer jakar hannunta mai tsananin nauyin kuɗin da ya dace da arziƙinsu ta ƙanƙame da fararen hannunta ma su sanyi kyau ga mai Kallonsu, kafin ta juyo da kyakkyawar fuskarta. Idanuwanta da suke farare ƙal ta zubawa fuskar Yasar, batason dogon magana da shi, saboda doguwar magana a tsakanin su tamkar karya alƙwarin Alhalinta ne, don haka ta ce;
"A ina kasan dukka wannan?."

Jira take yi ya saki layi ta sa akamashi saboda gudun shigarta matsala amma da yake Yasar wayayyene akan aikinsa da kuma fahimtar inda ta dosa kai tsaye ya ce;

"Layinmu gidan na uku hannun hangu makitsiya mai ƙaracin shekaru."

Jami'an tsaronta shirme suka ɗauki kalaman Yasar saboda ba su fuskanci ina kalamansa su ka dosa ba tunda ba su ji abinda ya faɗa lokacin da ya risketa ba. Umarnin barin wajen suka ba shi, bayan Simba ta shiga Mota.
Yasar bai musa ba ya juya ya bar wajen, maimakon ya koma Gidansa sai ya wuce na Iyayensa saboda yasan dole abi bayansa, domin ko shakka ba ya yi labarin tare Simbi da ya yi da tsayawarta ya isa Babban Birnin Abyad.

SIMBI; bata manta fuskar Yasar ba, saboda tun ranar da ta gansa ta ji ya birgeta a ƙofar Gidan da ya faɗa, kuma a wannan ƙofar Gidan ya naimi taimakon aiki da gareta gaba da gaba na ƙarshe lokacin ta fito workout, gudun matsala da sanin abun da take saƙawa zuciyarta akansa ba zai taɓa tabbataba yasa tasa a wulaƙantashi saboda ya yi zuciya kar ya ƙara bibiyarta.

Bata manta Naila ba, ba kuma zata mantata ba har abada, saboda ƙawarta ce kuma maƙiyiyar Ƴar uwarta Barirah.

WAIWAYEN SHEKARUN BAYA
Lokacin wasannin ƙarshe mako a Daular Sarki Hammam akwai wata matashiya mai kusan Shekarun Sulaim da ta kwashewa Naila ƙafafu saboda ta matso kusa da inda su ke wasa, har Naila ta kawo ƙararta wajen Sulaim. Ƙanwar Malik ce Uba ɗaya Sunanta Barirah.

Mahaifinsu Malik, ya auri Mata biyu matarsa ta farko ita ce Mahaifiyarsu Malik, tun da suka haifi Malik ba su ƙara samun wani ba har Malik ya kai shekaru biyar, son ƴaƴa ya sa shi ƙara aure, ya auri Mahaifiyar Barirah. Bayan wani lokaci ta haifin Barirah sa'ar Sulaim daganan itama ba ta ƙara ba, sai Mahifiyar Malik da ta ƙara haihuwar Simbi, baƙin kishi da rashin son zaman lafiyar Mahaifiyar Barirah ya sa Mahaifin Malik sauwwaƙemata ya kuma karɓi ƴarsa Barirah.

Barirah muguwar gaske ce musamman idan taga ta fika ƙarfi, ba ta baro komai na halin Mahaifiyarta ba. Da farko bata tsani Naila ba tana dai cin zalinta matsawar suka haɗu, amma daga lokacin da Sulaim da take son ya kulata ya riƙe Naila a matsayin ƙawa ta tsaneta ko aikota akayi Gidansu sai ta ranƙwasheta.

Wannan tsanar bai sauya zani ba duk tsayin shekarun da su Barirah suka kwashe a cikin daula.

DAWOWAR LABARI

A cikin Mota Simbi take hira da zuciyarta
Tabbas! bata manta fuskar Naila ba, amma mai ya kawo Naila Birnin Abyad? Allah Ya sa ba wani Yaƙinne yake shirin tunkaro su ba.


Bayan kwana ɗaya kafin Komawar