bige-bige da ayyana irin ramuwar gayyar da zai yi akan abinda Naila ta yi mai sai ya ɗauki hanyar Gidan su Sumaya.
Kukan da take yi da irin maganganun da take saki Iyayenta na ƙara tunzura ta ne su ka ƙara harzuƙa Sufyan, cikin tsananin fushi ya buge kofin tangaran ɗin da su ka zuba masa lemo a ciki, a take ya fashe. Sumaya tana yunƙurin zaginsa ya zuba mata marin da ya taɓa zuciyar Iyayenta, Babanta ma na yunƙurin kwasamai mari ya riƙemai hannu, kafin ya jefar da hannun da iya ƙarfinsa. Cikin isa da takaici ya ce;
"ki je mun rabu! kuma karki ƙara nemana tunda har yau baki fuskanci Naila itace mukullin ƙofar nasarata ba" yana gama faɗa ya bar madaidacin living room ɗin da aka ƙawata da kuɗin Naila kafin ya samu aiki.
Da sakakken baki ya bar su, saukar kalmarsa na "sun rabu" na cakar zuƙatansu sama da raɗaɗi marin da ya saukewa Sumaya da hannun Mahaifinta da ya jefar, saboda Sufyan da shi suke taƙama domin sanadiyyar haɗuwarsa da Sumaya rayuwarsu ta sauya ba kaɗan ba. Sumaya kuka take yi har da birgima, danasanin abinda ta aikata na mamaye zuciyarta. Sufyan baya ɓoyemata tasan da kuɗin kitson Naila suke ci suke sha a makarantar kuma sanadiyyar Naila ya samu aikin da ya ke yi, amma ita ta rasa dalilin da ya sa ta tsani Naila.
Daga wannan rana Sufyan ya ƙauracewa kiran Sumaya. Ga hotuna da ya ke saki masu kyan gaske a shafukansa, duk domin Sumaya tasan ko a jikinsa. Ya yi narasa kuwa domin Sumaya ƙara gigicewa tayi. Ba dare ba rana kullum sai ta turamai saƙo.
Rasa yadda zata shawo kanshi yasa ta turamai saƙon tayasa fakon Naila, har ya samu damar mayar da ita Yankin Tudu kamar yadda yake yawan faɗe tun kafin ya tafi Babban Birnin Abyad.
cikin jimami ta zauna zaman jiran amsar da zai bata.
NAILA; cikin nasara da wadatacciyar nutsuwa ta fara gudanar da karatunta.
A ɓangaren sana'arta kuɗi ta ke samu ba kaɗan ba, saboda ƴaƴan manyan mutane da suke Campus ɗin su waɗanda kansu ya ke kitsuwa a wajenta suke yin kitso.
Cikin watanni ta ƙara zama wayayyiyar mace sai sanyin kyau da ɗabi'a. Ba ta shiga sabgar da bai shafeta ba tana kuma tsayawa a iya matsayina.
Tana zuwa Gida jefi-jefi musamman ranar sati. Batun Sufyan kuwa tuni ta share shi a ranta, ta mayar da hankali kan abinda ya kaita Makaranta. Yasar kullum shi yake ba ta ƙarfin gwiwar yin karatu idan sunyi waya, domin shine matakin zamanta a Birnin Abyad na din-din har ta kawo Kaaka su ƙarasa rayuwarsu. Wannan ƙwarin gwiwar da Yasar yake bata ba ƙaramin dadinsa ta ke ji ba.
A hankali komai ya yi ta sauyawa watanni na shuɗewa, shauƙin son zuwa Yankin Tudu domin ganin Kaaka na ƙara mamaye ran Naila, a haka suka fara shirye-shiryen zana jarabawar da zamu yi hutu mai ɗan tsahon da zata iya zuwa Yankin Tudu ta taho da Kaaka. Kamar yadda Yasar ya shawarceta tunda tana samun kuɗi.
SUFYAN; bai daina son Sumaya ba amma yanason ta gane shi ɗin Namijin da za'a lallaɓa ba wanda za'ayiwa hargagi ko rashin kunya ba. Ko da yaga saƙonta fuska ya yi, domin yasan ba ta da wani abun tsinanawa, kawai don ya kulata ne.
Magiya da nacinta ba dare ba rana ne ya dawo da soyayyarsu har ya fara yunƙurin tarar Mahaifansa da batun ta, tare da shawarar da ya yanke na sawwaƙewa Naila kafin ya aiwatar da ƙudirinsa a kanta.
Cikar Sufyan shekara ɗaya a ma'aikatar Dhahab yasa sukayi mai kyautar da ya hanasa runtsawa. Waya kuwa kwana sukayi suna yi da Ɗayyib, cikin isa Sufyan yake bada umarnin abinda za'ayi da kuɗin. Ba bu lissafin yinƙurin yin wani abu na cigaban Yankinsu a kason kuɗin da duk wani kuɗi da yake turawa sai Gidan Sarautar su da aka ƙara ƙawatawa, musamman ɓangaren Mahaifansa Ɗayyib da ɓangaren Kakansa Jalal.
Ba bu wani tsarin tallafi da suka tsiro da shi a matsayinsa na Ɗan Yankin da ya samu cigaba a Babban Birnin Abyad sai dai mutanen gari su gani a jikin Iyayensa, ƴan Masarautar su da Gidajensu, duk da mummunar talaucin da suke fama da shi. Har lafiyayyen titi aka shimfiɗa daga farkon shigowa Yankin Tudu har ƙofar Masarautar su.
A ɓangaren Ɗayyib da Sufyan ya fara samun kuɗi Gidan Game ya buɗe ƙato matasa su samu kuɗi suyi ta bugawa Yara kuma su sato kuɗin Mahaifansu. Abun takaicin sai Matasa da Iyayensu sun sha wahala sun ƙera Tukwane sun samu an siya daƙyar sai Ƴaƴan su kwashe kuɗin su gudu gidan Game ɗin Ɗayyib.
Cikin ƙanƙani lokaci shima ya fara zama hamshaƙi.
Dukka wannan facakar sai dai ƴan uwan Naila da Kaakarta su ji labari, kamar dai gama garin mutane ba surukan Sufyan ba.
Ɓullowar batun auren Sumaya da Sufyan, ya tayar da ƙura a tsakanin Hindu da Ɗayyib don sai da sukayi faɗan da ya kaita ga tafiya Gidansu. Ta kafe bata yarda da auren ba matsawar ita ta haifi Sufyan domin malaman tsibbunta sun sanar da ita sakin Naila zai rusa komai, haƙurin mutanen da suka zubawa Sufyan ɗin ido ya na zaluntarta har suka ɗaukesa aiki zai ƙare daganan suyi masa ɗaurin talalar da zai mutu a ɗaure.
Sam Ɗayyib bai yarda da batun Hindu ba, acewarsa ɗaukakar Sufyan daga Allah ne, babu wata Naila don haka dole su bar Sufyan ya rayu da abinda yake so.
Ankai ruwa a tsakanin su har sai da Jalal Mahaifin Ɗayyib ya shiga faɗan da suke yi a sirrince don bakowa ba ne yasan Hindu bata gidan ba.
Sai da Mahaifiyar Hindu ta saka baki, sannan ta yarda da auren amma da sharaɗin ko zai saki Naila sai lokacin da ta yarjemai. A kan haka suka bar zancen.
Da tsananin rawar kai Sufyan yake rabon katin aurensa ga Manyan ma'aikatarsu. A cewarsa ma bai taɓa Aure ba.
Labarin auren Sumaya da Sufyan sai da yaje har kunnen Bushra, ba tare da ɓata lokacin ba ta naimi Yasar ya toshe duk wata hanya da Naila za ta iya jin labari, saboda kar hakan ya kawomata tsaiko a jarabawar da take zanawa. Kuma da zarar ta gama ya shirya mata tafiya Yankin Tudu.
A rabon Invitation card da Sufyan yake yi ne, Baturen da yake sama da shi ya bashi shawarar ya shirya katin gayyata na musamman ga GM wataƙila ya samu alheri mai yawan gaske.
Da yake Sufyan ɗan son banza ne a daren ya biya kuɗi mai yawa aka shiryamai katin gayyata na musamman. Washe gari kafin ya shiga office ya miƙawa ogansa ya bawa GM ba tare da nutsuwa ya yi tunanin maiyasa tunda ya ke aiki a Dhahab bai taɓa ganin GM ba, ko da gilmawarsa ne.
Gaba ɗaya sai Sufyan ya matsu ranar Aurensa ya zo, irin shagalin da ya tanadi maƙudan kuɗi za'ayi a Yankin Tudu na sanyashi jin alfaharin da bai taɓa jiba.
Ɗayyib da su Sarki Hammam da ya yi kwantan ɓauna kamar yana tare su ne su suka zo Birnin Abyad Gidansu Sumaya naimawa Sufyan aure. A take Iyayen Sumaya da suka matsu da komai suka ce sun bashi sati mai zuwa a ɗaura aure su tafi da Ita Yankin Tudu su je can suyi Biki, a maimakon wata ɗaya da suka tsara da Sufyan tun kafin zuwan Iyayensa ya yi rawar kan buga katin gayyata.
Iyayen Sumaya sun ce su basu da wani shagali da zasu yi bayan ɗaurin Aure.
Abin takaici daga Ɗayyib har da muƙarabansa da suka zo Birnin Abyad tare ba bu wanda ya tambayi ina ƴarsu Naila Ƴar Yankin su take? a wani yanayi take ciki?. Kowannen su fuska ya yi yana dirzar duniyar da ya samu.
Da rawar jiki Sufyan yake ƙara bawa manyansa haƙurin matso da lokaci kusa an samu akasi. Wa su sun nuna zasu je wasu kuma tambayarsa suka yi babu wani shagali da za'ayi ranakun da zasu biyo bayan ɗaurin auren da zasu iya zuwa? Da sanyin jiki ya sanar da su na Yankin Tudu tunda yasan ba lallai su je ba.
Ga ɗumbin mamakinsa washe gari ya samu saƙo GM ya ce ya amsa gayyata amma ba zai samu zuwa ɗaurin aure ba, sai dai na Yankin Tudu da za'ayi In Shaa Allahu. Sufyan ihu yasa ya na tsalle, har ya fara hango irin ƙafafa da zafin kan da zai yi, inama da Naila tana wajen ya nunamata ko babu ita shi ya zama kafin Allah a Dhahab sai dai ta mutu da baƙin ciki.
Cikin walwala da son Daular da ya ke iya canza tunanin ɗan Adam lokaci ƙanƙani su Ɗayyin suka cika sati guda a Birnin Abyad.
Ranar Ɗaurin aure
Irin fareren Turawan da suka zo ɗaurin auren Sufyan da Sumaya a Birnin Abyad ne yasa bakin Ɗayyib yaƙi rufuwa. Bayan komai ya lafa sun keɓe Ɗayyib ya murmusa cikin alfahari ya ce;
"Sufyan ina alfahari da kai akanka na fara samun cikar burina na tsayin shekaru, kaga Ubangidana ko, sam bai halarci ɗaurin aure nan ba kuma nasan yana gari, dama ina sane da shi, tun daga kan takardun da na ce ya samar maka ya ƙauracewa waya dani, to dama haka rayuwa take, yau ina jina na daban ya ya ma kace sunan wannan Ma'aikata taku mai albarka." Ya ƙarasa faɗa yana kafa lemo mai tsada a baki.
Sufyan da ke murmushin isa ɗan dariya ya yi kafin ya ce "DHAHAB"
Azababben tari ne ya sarƙe Ɗayyib lemon da ya kurɓa ya soma biyomai ta hanci da baki...
NAILA; A dai-dai lokacin da Tari ya sarƙe Ɗayyib Naila ta kammala haɗa kayan tafiya Yankin Tudu....✍🏻
Wanene General manager company sarrafa shinkafar Dhahab da Sufyan yake aiki a ƙarƙashin shi?😄
Maiyasa ya zaɓi zuwa wata ƙasar shagalin ta ya murnar ma'aikacin da ya ke ƙasan-ƙasansa duk da girman matsayinsa.
Yaya zaman Naila a Yankin Tudu zai kasance shin zata dawo ko bazata dawo ba? Kaaka tana raye ko bata raye?
Wani 🔥🔥 ne zai kama a Yankin Tudu?
Next page In Shaa Allah
[7/25, 8:47 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥
NAFISA ALIYU SASAAL
*CHAPTER 3*
*YANKIN TUDU🔥*
Page 20
NAILA; da ƙananun kayan Calvin Klein ta yi sauƙaƙaƙiyar adon da ya dace da siffarta ya kuma haska kyanta.
Fuskata ƙunshe da murmushi take kallon mutanen Birnin Abyad, farkon zuwansu Birnin ita da Sufyan na dawomata. Rashin banbancin da ke tsakanin fatarsu ta ɓangaren murjewa a yanzu yasa ta ɗan faɗaɗa murmushinta. Ashe komai zai sauya, ashe itama zata zama ƴar gayu kyakkyawar Macen da zatayi alfahari da kanta wata rana.
Dogon mota mai kyau ta hau, idonta tsaye ƙyam a kan hanyar Babban Birnin Abyad.
A wannan karon tana alaƙanta kallon hanyar da Yasar da Bushra da suke can tare da Sufyan, murmushi ta yi data tuna abinda su Bushra suka ɓoyemata, duk da Bushra tasa Yasar ya ɓoyemata koma sai da taga komai a shafin Sufyan kamar yadda take bibiya lokaci zuwa lokaci.
Babban sauyin da ta samu a komawarta Yankin Tudu shine jirgin da ta bi a maimakon Mota da taimakon mutumin Bushra bayan isarta Airport. Cikin ɗan tsoron da ya mamaye ranta saboda hawarta jirgi a karon farkon kenan jirgin su ya ɗaga zuwa Iyakar Yankin Tudu da Babbar tashar da filin saukarsa ya ke.
SUFYAN; Da hanzari ya nemo ruwa ya miƙawa Ɗayyib, haɗe da nanata kalmar "sannu" da yake tayi ba ƙaƙƙautawa.
Ɗayyib ya ɗauki tsahon mintuna ya na tari, fararen idanuwansa da suka ƙara haske saboda daular da ya samu na kwana biyu ya juyewa zuwa jajaye marasa kyan gani.
Da salon murya da Sufyan bai san Mahaifin nasa da shi ba ya ce;
"Kasan menene DHAHAB" cikin rashin fahimtar ina ya dosa Sufyan ya ce; "Zinare mana Baaba"
"Sufyan ina nufin kasan mafarin ƙirƙirar Dhahab, tunda kake a duniyarka ka taɓajin mai inkiyar banda Ahalin Marigayi Sarki Musa" cikin rashin fahimtar abu da wuri Sufyan ya ce;
"Waccen Dhabah ɗin ai zuri'arsu ta mutu Baaba, waɗannan turawa ne ba ma ƴan asalin ƙasar Abyad ba ne, kusan dukka manyan da suke samana Turawa ne."
Ɗayyib cikin rashin gamsuwa ya ce;
" Wanene mamallakin ma'aikatar ba ina nufin GM ɗin da zai zo shagalin bikinka ba, tunda ance suna da reshe da yawa, asalin mamallakin Dhahab ɗin nake nufi gaba ɗayanta, kasan sunansa da inda yake da zaune"
Sufyan ido ya zaro cikin mamaki ya ce; " Babaa ba ni da issue da duka waɗannan abubuwan da ka lissafo burina kawai na samu kuɗi, Ni ma na zama Dhahab ɗin kaina, tunda na lura sunan ya na da wani ɓoyayyen sirri, shine kawai."
Kamar talabijin haka Ɗayyib ya zubawa bakin Sufyan ido, zuciyarsa kuwa Allah Ne kaɗai yasan faɗinta da sirrikan data ƙunsa.
Da kaushin murya ya ce;
"Daga ranar irin ta yau kafara saka lissafin abinda na tambayeka a cikin ƙwanyarka, domin ba ra'ayi ba ne ko ganin dama ba, tilas ne musan su wanene masu Dhahab, aikinka zai fara daga yau Sufyan!"
Ɗayyib yana gama faɗa ya miƙe jiri na ɗibansa sama-sama.
Kafaɗa Sufyan ya ɗaga alamun ko a jikinsa, shi ba shi da wannan ra'ayin da dai maganar kuɗi ne da kyau to da sai iya inda ƙarfinsa ya ƙare, amma ace duk Kuɗin da ya tara sai ya je yana binciken abubuwan da basu shafesa ba, why not ya ba shi shawarar ƙirƙirar wani hanyar da zai ƙara tara dukiya shima ya zama Dhahab ɗin da'akewa kokawa shekara da shekaru har ake salwantar da rayuka duk domin a kawar da su.
SUMAYA
Tasha gyara kyanta da farin fatarta sun ƙara fasowa. Sufyan daya ganta kamar ya siɗeta bini-bini ya kirata a waya su share mintina suna hira.
Kayan alfarmar da zai fitar da Sumaya ta zama ta musamman sama da yadda Ubaidullah ya kawo Kakar Sulaim Nanaah Yankin Tudu aka tanadarwa Sumaya da taimakon Ɗayyib da kansa aka fitar da adon kayan da ya dace da Masarautarsu.
Bayan komai ya kammala tsirran ƴan uwan Sumaya da kansu yake rawar Ƴar uwarsu tayi dacen gidan kuɗi da Sarauta suka fara shirye-shiryen tafiya Yankin Tudu.
Ranar Alhamis da ya rage saura kwana biyu shagin Yankin Tudu suka ɗugunzuma dukkansu, abin birgiyar daga Company su Sufyan aka turo da motoci na alfarmar da zai kaisu Airport.
Sarki Hammam da ya jima da yin kwantan ɓauna domin tsiratar da rayuwarsa da samun bayanai murmushi yake saki cikin ransa ya na mamakin ɗabi'unsu.
WAIWAYE
Shekarun baya...
Labarin da Dattijo Junaid ya bawa Sarki Hammam, labari ne akan ɓarnar da su Ɗayyib suka kwashe shekaru su na yi a ɓoye.
Bayan rasuwar Dattijo Junaid Sarki Hammam ya shiga ɗimuwa da zullumi. Saboda yasan shi ma wata rana matsawar zai yi tsayuwar tsayin daka akan gaskiya to tabbas zai bi sawun su Dattijo Junaid ba da jimawa ba..
Rasuwar Bashar ya ƙara jefa zuciyarsa cikin ɗimuwa, musamman da ya ji ƙishin-ƙishin ɗin ba fa mutuwar Allah da Annabi Bashar ya yi ba, ana zargin Ɗayyib ne ya shaƙamai guba.
A hutun da Sarki Hammam ya tafi Babban Birnin Abyad bayan rasuwar Bashar ya haɗu da Malik, ya kuma gano Dhahab ɗin da su Ɗayyib suke kokawar sai sun ɓaddashi ya na nan daram a Babban Birnin Abyad, amma kamar yadda Malik bai sanar masa wanene yaƙara kafa Dhahab daga cikin zuri'ar Marigayi Sarki Musa ba, shima bai zurfafa dole sai ya sani ba.
Sun yi taƙaitacciyar tattaunawa da Malik.
A cikin tattaunawarsu Malik ya bashi shawarar ya shiga jikinsu Ɗayyib domin sanin motsinsu, ya zubawa zaluncinsu ido har zuwa lokacin da Ubangiji zai ƙaddara ƙarshensu. Idan kuma suka yi zaluncin da ya ratso da haƙƙin wani to ya sanar masa, shi kuma zai yiwa kowaye a cikinsu hukunci dai-dai da abinda ya aikata..
Bayan dawowar Sarki Hammam daga Babban Birnin Abyad sai ya zama ɗaya daga cikin Informer Malik a cikin Masarautar Yankin Tudu, da ma Yankin baki ɗaya ba tare da kowa ya ankara ba...
*YANKIN TUDU*
NAILA; lokacin da jirgin su ya sauka a iyakar mafarin shiga Yankunan su, murmushi ta saki, zuciyarta na azalzalata tanajin ƙarfin gwiwar da bata taɓa jiba.
Cikin kasuwar chanjin wajen da yake kusa da Airport ta shiga aka canza mata kuɗin ƙasar Abyad zuwa na ƙasarsu, bat rage ko sisi ba. Kuɗine masu yawan gaske don haka ta zuba su a cikin jakar da ta tanada domin su. Masauƙin baƙi ta nufa na canza Suturar jikint zuwa Abayar da suka fi amfani da shi a Yankin Tudu duk da wanda bata da ɗan bambanci.
Drivern da ya ɗaukosu ita da Sufyan shekarun baya shi ya ƙara ɗaukarta. Da shi da Motar tasa duk sun tsufa sun jeme.
Gudu yake yi amma sai take ganin kamar baya sauri saboda yadda ta matsu ta riski Kaka ta ga ko ita yaya ta koma?
Hirar yadda Yankinsu ya koma Driver yake yimata muryarsa a raunane da yadda Sufyan ya ke kashe Kuɗi a iya Masarautarsu da mutanen cikinta.
Naila bata tsawaita magana da shi ba, saboda yadda zuciyarta take suya.
Lokacin da suka shigo Yankin Tudu batasan sanda dariyar da ya bayyana jerarrun haƙwaranta ya kufcemata ba.
Suna isa ƙofar gidan Kaka da zumuɗi ta buɗe murfin motar, kuma tayi sa'ar babu mutane. Duk suna cikin Gidajen su sai tsirran da ba'a rasa ba. Da taimakon shi ta sauko da kayan tsarabar da ta jibgo. Kuɗi ma su nauyi ta ɗauko ta bashi da sunan kuɗin da ya ɗaukota. Ƙasa ya zube yana kuka cikin shesheƙa ya ce;
"Allah Ya aramin ranar da zan saka miki da abinda kikayimin Allah Ya haska gabanki Ya haska bayanki, Na gode! Na gode!!!" Kai ta girgiza mai haɗe da kutsawa Gidan Kaaka.
Murnarta ce ta koma ciki sanda tayi ido biyu da yadda Kaaka ta rame ta lalace fatarta ta yamushe kamar babu ruwa a jikinta.
Da farko Kaka bata gane Naila ba, sai daga baya, da gudu ta taso garin ta iso inda Naila ta ƙame a tsaye ta zube ƙasa saboda tuntuɓen da ta yi. Da sauri Naila ta ƙarasa suka ƙanƙame juna, tana kuka itama Kaka tana kuka.
A haka Drivern ya gama shigo mata da kayanta. Kaka kallon Naila tayi ta shafa fatarta sai ta fashe da kuka, ta yi haka ya kai sau uku, kafin ta miƙe tayi hanyar waje.
Naila bayanta tabi da kallo tana share hawayebta.
Jakar kuɗin