Kamar yadda nta alƙawartawa Sufyan da maƙotansu da su ke cikin gida ɗaya ta fara, ba ta jin turancin arziƙi amma kuma hakan bazai daƙusar da ƙudirinta ba. Ko da kwatacce ne da haɗe-haɗen iya wanda ta iya zata yi mu su bayani har su fahimta.
Biyun dukka Mata ne kuma tayi sa'a dukkansu gashinsu na kitsawa ne amma ɗaya kai tsaye ta shaidamata bata da ra'ayin yin kitso saboda zafi ya ke mata. Cikin ƙanƙan da kai kamar ta saba da ita ta kwantantamata ta zo ta gwada yimata hannuna ba shi da zafi. Ga mamakinta cikin raha ta ce to ta je around 2:00pm na dawo.
Abinda Ruwaida Maƙociyarta ta ce mata na ta je ta dawo ya ƙaramata ƙarfin gwiwar tunkarar ko ina domin tallata sana'arta. Mutum na ƙarshe a gidansu Namijine ɗan asalin ƙasar Abyad fatarsa fara fat.
Ta na shiga Sashensa Da sauri ta fito duk kiran da ya ke ƙwalamata bata juyo ba, tama jiyoshi ya na dariya da alamun mamakin Gidadancita ya ke yi.
Duk Gidan da zata shiga Daƙyar ake barinta, wasu su yimata tarba mai kyau wasu kuma su wulaƙantata. Gida na ƙarshe kuma mafi kyau a layin shi ta tunkara sai dai kai tsaye dakarun da su ke gadin Gidan su ka hanata Shiga.
A gajiye na dawo Gida, saboda ba laifi ta yawatu, ba kuma komai yasa ta dage ba, sai don sauya tunanin Sufyan daga wanda Mahaifiyarsa ta ɗorashi a kai.
Kamar yadda Ruwaida ta ce ta dawo ƙarfe biyu haka ta koma akan lokaci.
Yanayin ɗiban kitson da yadda ya kwanta a saman farin tafin kan Ruwaida ya yi matuƙar ƙayatar da ita ga shi sam ba zafi, godiya tayimata da tsananin farin ciki a saman fuskarta.
Da Ruwaida ta tashi sallamarta, da iya adadin kuɗin a ke biyan makitsa a Birnin Abyad ta biyata, nutsuwarta ce kawai ta riƙe Naila.
A lissafin kuɗin da tayi zuwa na ƙasarsu, ko Iyalan Sarki Hammam da ake matuƙar ji da su, suke biyanta da kuɗi ma su ƙauri ba su taɓa bata kwatankwacinsa ba.
Ƙwalla ƙwance a ƙasan idanuwanta ta ke yiwa Ruwaida godiya.
Dariya Ruwaida ta saki cikin mamakin yadda Naila ta damu ta tambayeta daga ina take?
Saboda ta ƙara tausayamata ta naimomata customers, Naila ta fara ba ta labarin ita da Mijin tane su ka zo, ya zo Karatu ne kuma kuɗin iyayensu sun ƙare shine suke neman kuɗin cin abinci da sauran buƙatun rayuwa. Dafata Ruwaida tayi cikin tausayawa ta yimata alƙawarin zata naimo mata mutanen da zata dinga yi musu kitso ta na samun kuɗi amma na tambayi Mijina shin zai barta zuwa Gida-gida yin kitso?
Naila ba ta zaɓi yanke hukunci ba tare da ta tambayi Sufyan ba, don haka ta ce ta bari na yi shawara da shi idan ya dawo.
Daga haka dukayi sallama kuɗinta ma ƙanƙame a hannunta.
SUFYAN;
Lokacin da su ka isa Jami'ar Birnin Abyad da Ubangidan Ɗayyib ya yi cuku-cukun samo masa ya yi mamaki tare da ƙaƙabawa zuciyarsa cika alƙawarin Mahaifiyarsa babu gudu babu ja da baya.
Bayan sun gama yin komai. A ranar ƙarfe 12:00pm Sufyan ya fara ɗaukar lectures saboda tuni su ka fara ba bu shi.
Bayan sun gama lecture Harabar Makarantar ya fito ya naimi wajen zama, tunanin kuɗi da yadda zai yi kalar rayuwar da zai samu Mace wayayyiya ƴar Birnin Abyad ɗin da zai yaƙi mutanen Yankin Tudu da ita na ya zauna yi. Ya na cikin wannan yanayin wata matashiya mai kyan gaske ta raɓa gefenshi ta zauna. Sanye take cikin ƙaƙanun kayan Saint Laurent riga da wandon da suka amshi farin fatarta sai lulluɓin da ya lulluɓe iyakacin wuyarta bai sauko kafaɗunta ba.
"Barka dai kyakkyawan Matashi, sunana Sumaya, kai fa?" Ta faɗa da harshen nasara mai ɗauke da cikin wani irin sanyi murya tana miƙamai hannu.
"Kyakkyawan Matashin" da ta faɗa ya fi bugar da kan Sufyan a kan kyan fuskarta. A ƙiyastin da ya yi a cikin daƙiƙu zata yi sa'ar shekaru da shi, babu wani abu mai kyau a saman fuskarta da gangar jikinta da Naila da take cikin talauci bata da shi currently. sai wayewar da ta fi Naila da kuma hasken fatarta mai tsananin haske sosai.
Cikin salo da yadda ta birgesa har cikin ransa da jin nan take ya samu Abokiyar rayuwa ta zahiri matsawar ba ta fi ƙarfinsa ba ya ce;
" Barka dai ya ke kyakkyawa Sunana Sufyan na ji daɗin haɗuwa da ke" ya ƙarasa faɗa yana damƙar hannunta.
Daga haka kamar wasa hira mai cike da aji da zuzutawa kyansa irin yadda ya ke buri da ga Naila batayi ya ɓarke a tsakaninsu, har da musayar lambar waya.
Kan Sufyan bai ƙara ɗaukar zafi da kwaɗayin mallakar dukiya ba sai da yaga Sumaya har ɗan ƙaramin mashin mai kyau take da shi, ba irin na shi na Yankin Tudu ba.
Da aka tashesu Da sakin fuska ta yi masa tayin hawa, ba tare da ɓata lokaci ba ya ɗane.
A hirarrakin su kafin su isa Gida Sufyan ya fuskanci Sumaya ba wata ƴar ma su kuɗi ba ce a Birnin Abyad, naiman kuɗi ne ya kawo Mahaifanta har su ka haifeta a nan ta kuma yi dacen samun scholarship a Makarantarsu.
Ran Sufyan fari fes Sumaya ta saukeshi a layin Gidan su, kamar kar su rabu haka su ka yi sallama, Sufyan ya nufi hanyar Gate ɗinsu da ƙayataccen murmushi a saman fuskarsa.
NAILA;
Wanka ta yi taƙara shirya kanta cikin abayar ta dai mai adon saƙi, sai dai ba baƙi ba ne kamar ragowar. Ta na ƙoƙarin shiga kitchen don duba abinda zata iya dafawa daga Abinci da Ubangidan Ɗayyib ya kawo mu su, ta ji ana knocking. ƙofar ta nufa da saurinta, tana buɗewa taga ashe Ruwaida ce, kanta ba bu kallabi da alama bata da mu dashi ba duk da kasantuwarta cikakkiyar Musulma. Mazubin abinci mai kyau ta gani a hannunta. Cikin gwari-gwarin Turanci da zata fahimta Ruwaida ta shaidamata Abinci ta kawomata sannan gobe idan Mijinta ya amince ta shirya zata kaita wani Gida a ƙarshen layinsu da zan ta yi kitso. Godiya mai tarin yawa Naila ta yi mata sannan su ka yi sallama.
Bayan Naila ta koma ciki
Kasa taɓa abincin ta yi, ta zauna zamam jiran dawowar Sufyan su ci tare.
Sufyan;
Da murmushi a saman fuskarsa ya ƙwankwasa Naila ta buɗe mai ya shigo, yana ganinta ya kalli Abayar jikinta sai ya sauya fuska. Har cikin ranta bata kawo komai ba, sai ɗaukar da ta yi masa a matsayin bauɗaɗɗen mutum mai saurin fushi.
Fuska ba walwala ya amsa gaisuwata haɗe da sumbatar ƙuncinta kamar yadda al'adar Yankinsu ya ke.
Ruwan wanka ta nufi hanyar ɗakinsa domin haɗa mai ya dakatar da ita, ya miƙe ya shige har da mirzo mukulli, ita dai Na'ilah ba ta damu, ta dawo ta zauna
Bayan ya fito ta gabatar masa da Abincin da Ruwaida ta kawo musu, ba bu tambayar ina ta samo? Ta ci ko ba ta ci ba? Ya zauna ya take cikinsa sai kaɗan da ya ragemata. Jiki a sanyaye ta ɗauka ta ci ranta babu daɗi.
Sufyan fahimtar sauyi a fuskar Naila yasa ya fara ƙorafin ai bai san bata ci ba, kuma maiyasa ma ba tasa hannu sunci tare ba? Batace mai komai ba, amma na ɗan ji sanyi a raina yadda ya nuna kulawarsa.
Bayan ta gama ci ta kai kwanukan madafi, ta fito da kuɗin da Ruwaida ta bata, da kuma naiman izininsa akan Gidan da ta ce zata kaita, ga mamakinta Sufyan ƙanƙameta ya yi yana dariyar nishaɗi, ba tare da wani jinkiri ba ya fara kasafta kuɗin.
"Naila kuɗinnan kawai abinda ya kamata shine na ƙara riga ko kala ɗayane ragowar kuma na samu na cin abinci a Makaranta Kinga yau ma da yunwa na wuni. Allah Ya yi miki albarka Naila" ya ƙarasa faɗa yana shafa duk inda hannunsa ya kai.
Tambayar izinin fitarta gobe da ta tambayesa murya na rawa ya ce ya amince ya na ƙara samata albarka.
Cikin dabara da girman zaluncin rashin tunanin halin da zan faɗa idan tasa buƙatar ta biya ya fara ragewa kanshi zafi, har sai da yaji ya gamsu dai-dai misali sannan ya tattara ya yi daƙinsa ya bar Naila a wajen.
SUFYAN;
Bayan ya shiga ɗakinsa wanka ya ƙarayi fuskar Sumaya da ya ke maƙalemai a cikin zuciyarsa na wasa da nutsuwarsa, sai ya ke ganin anya batafi Naila kyau ba? Dariya ya saki ya na lalubo wayarsa. Ba shi da kati kamar yadda ya sanar da Sumaya don haka ya zauna zaman jiran kiranta.
Kiranta ya na shigowa ya yi maza ya ɗaga.
Sun jima su na hira kafin su yi sallama ran kowannen su fari fes.
Sumaya da Sufyan soyayyar da zai kai su ga aure sukewa junansu, duk da yinin su ɗaya da haɗuwa.
Sumaya tana ganin ta samu Talaka irinta tunda Sufyan ya gayamata Karatu ya zo yi da Yarinyar da Mahaifansa su ka dage sai sun aura mai kar ya zo Birnin Abyad ya na neman Mata, idan ya so duk ranar da ya gama Karatu ya saketa idan kuma ya ji yana sonta to su cigaba da zamansu, shi kuma baya sonta ba kuma zai iya rayuwa da ita bayan ya gama Karatu ba. Ɗari bisa Ɗari Sumaya ta yarda da zancen Sufyan.
Shima Sufyan gani ya ke yi Sumaya itace Macen nunawa. Mace ƴar Birnin Abyad mai kyan sifa da tarin ilimi kuma ba ƴar talakawar fitik irin Naila ba.
Tabbas! Mahaifinsa Ɗayyib zai yi alfahari da shi Kuma Tarihi zai maimaita kansa domin kamar yadda Marigayi Ubaidullahi Dhahab ya dawo Yankin Tudu da tarin dukiya da kuma zankaɗeɗiyar Matar Aure haka shima zai koma Yankin Tudu da tarin Dukiya da kuma Sumaya a matsayin Matarsa..✍🏻
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c
🔥ZINARE🔥
SASAAL
13
Har Dare ya yi Sufyan bai ƙara fitowa ba, dama ba wani damuwa ya yi da nemi Masallaci ba, kuma ya riga ya cika cikinsa..
NAILA;
Ba ta damu da rashin fitowar Sufyan ba tayi kwanciyarta bayan ta shiga Madafi da samawa cikinta wani abun..
★washe gari bayan Sallar Asubahi ba ta koma barci ba kamar jiya.
Bayan ta gama azkar ta tashi na ƙimtsa ko ina. Abinci mara nauyi ta dafa musu, ta jere a kan teburin cin abinci. Da ta tabbatar komai ya kammala sai ta koma ɗakinta domin yin wanka.
Sufyan ranshi fari fes ya tashi, saboda mafarkin ya zama hamshaƙin mai Dukiya sanadiyyar Sumaya. Bai koma barci ba, sai dai ba zama Karatun Alkur'ani ko azkar ya yi ba, wanka ya shiga.
Har Naila ta kammala girki gaban madubin washroom ya na kallon kansa, fatarsa kuwa tsabar dirza da soso a tunaninsa hakan zai sa ya ƙara haske, har zafi ya ke mai. Duk motsin Naila ya na jinta har ta kammala ta wuce daƙi.
Da sauri ya fito ya cinye kusan dukka abincin, yanajin alamun fitowarta ya tattara ya fita da sauri.
NAILA;
Lokacin da ta fito ta ga son zuciyar da Sufyan ya aikata bata yi mamaki ba, saboda tana san ran zai iyayin sama da haka matsawar hudubar Mahaifiyarsa bai bar zuciyarsa ba.
Ragowar ta ƙarasa cinyewa, bayan abincin ya ɗan sauka ta nemi waje ta kwanta tana jiran zuwan Ruwaida.
Misalin ƙarfe ɗaya da rabi na rana Ruwaida ta ƙwanƙwasa ƙofar sashensu. Da hanzari Naila ta lulluɓe sumar kanta har zuwa ƙasan kafaɗuna da yalwataccen malulluɓi. Da fara'a sosai na tarbe Ruwaida. Kamar dai jiya ba bu lulluɓi a ƙanta sai ƙaramin scarf ɗin data nannaɗe gashinta da shi. Ba ta karɓi tayin shigowarta Sashen su ba ta ce ta taho su tafi.
Su na tafe su ɗan hira har su ka kusa kai wa ƙofar Gidan da ya yi matuƙar birge Naila, amma jiya da ta je zata shiga tallata kitsonta aka hanata shiga. Nunawa Ruwaida gidan tayi haɗe da yimata bayanin abinda ya faru. Da farko dariyar da ya sa ta ɗan ranƙwafawa Ruwaida ta yi kafin ta ƙara kallon Naila ta kuma sakin murmushi, da sauƙin turancin da ta san zan fahimta ta ce "Karki ƙara zuwa saboda ba wajen zuwanki ba ne"
"Saboda me?" Naila ta tambaye Ruwaida da mamaki kwance a saman fuskarta.
Babu wasa a saman fuskar Ruwaida ta ce;
"Gidan Simbi ne, Matar Uzair. Ahalin Shahararren ɗan kasuwa a Babban Birnin Abyad, ta zo gudanar da wani bincike ne a Asibitin jami'ar mu. Rayuwata ba bu sakewa sam, yawan zuwanki da sunan makitsiya zai iya janyomiki matsala don haka ki kula."
Naila jigum ta yi mutum ɗaya ta taɓa ji da irin sunan a Yankinsu, kuma itace ƴar autarsu Malik uwa ɗaya uba ɗaya. Don haka faɗar sunanta sai ya dawomata da tunanin abinda su ka faru shekarun baya. Simbi sun bar Yankin Tudu ta na yarinya ƙarama ta girmemata da Shekara ɗaya.
Naila a ranta ta ce;
"Nasan ma ba ita ba ce domin babu yadda za'ayi ko Malik da ya ke Babban yayansu ya mallaki irin wannan Gidan a Birnin Abyad balle ita."
Bata ƙara cewa Ruwaida komai ba har suka zo giftawa ta dai-dai saitin Gidan.
Naila ba ta da ciwon ido balle ta ce shi ya haddasamata ƙarancin gani, fitowar Mota mai ɓakin gilashin da akayi ƙasa da shi kaɗan saboda ɗagawa dakarun da su ke gadin gidan hannu ne yasa Naila tayi baya kafin ta saki ƙarar da ya ja hankalin har na cikin motar ya ɗago kai saitin da suke kafin ya zuge gilashinsa gaba ɗaya ya fice daga layin.
"SALMAN!" Naila ta faɗa a sarari, sai kuma ta tuna Salman to ai ya mutu, tun shekarun baya, to idan ba Salman ba ne wanda ta gani yanzu a Mota to wanene wannan? ko ƙaninshi ne? Ta tamabayi kanta.
Da hanzari Ruwaida ta tarota ta na faɗin "Naila! Menene ya sameki, kinsan shi ne? Ko bakyajin daɗi ne mu koma gida?"
Razanarta Naila ta shanye ta miƙe tsaye ba tare da bin bayan Motar da kallo ba ta ce;
"Na shiga razani ne sai na ke ganin kamar na sanshi"
Ajiyar zuciya Ruwaida ta sauke kafin ta ce "ohh Allah! Naila kin bani tsoro to ai mutane ma su kamaceceniya su na da yawa a duniyar nan ki kwantar da hankalinki kinji?" Kaina Naila ya ɗaga mata alamun na gamsu.
Gidan da suka je dukka su ƴammatane su biyar kuma abokanan karatun Ruwaida. da alama Makarantarsu a kusa da nan yake.
Jarumtar Naila da son ta tara kuɗi domin cikawa Kaka burinta yasa ta yi juriya kitsa mu su gashin kansu dukka irin na Ruwaida ta yi mu su. Waje ɗaya suka haɗamata kuɗin da ya sanyaya rainta ta ji zazzaɓin da ya ke shirin rufeta ya sauka. Ba su wani jimaba bayan ta gama yi mu su suka bar Gidan. Yanayin shiru-shirun da ta koma lokaci ɗaya ya sanya Ruwaida itama cikin damuwa.
Dalilin haka ya sa bayan sun kai ta ja Naila ɓangaren kafin Sufyan ya dawo.
A kan kurajerun living room ɗinta ma su taushi Naila ta lafe tana kallon shige da ficen Ruwaida daga parlo zuwa Madafi.
Cikin yanayinta na barkwanci Ruwaida ta ce Naila ta taso taa tayata girki.
Naila ta na shiga idanuwanta suka sauka a kan Tukunyar girkin Ruwaida, sunan jiki ne yasa ta ƙarasa kusa da Tukunyar da sauri, "DHAHAB" ne rubuce a jikin Tukunyar kuma tare da sunan a ka ƙera Tukunyar ba sticker aka manna ba. A take zuciyarta ta yi bugawar da ya sa na jingina da bango ƙwaƙwalwarta na tariyo mata shekarun baya.
Ruwaida da raha ta ce " kema Tukunyar ya birgeki ko?, ai Kamfanin ahalin su Simbi ne, Yayana a can ya ke aiki shi ya yi min kyautarsa ranar murnar zagayowar haihuwa ta, kinsan kuwa nawa ake siyar da Tukunyar nan, Tukunya ne mai matuƙar tsada, Ni kaɗai ce mai shi a cikin ƙawaye na, Tukunya ne da Sarakuna da ma su dukiya su ke girki da shi, shi kanshi Yayana da yake aiki a can da albashi shi muke rayuwa da ahalina a wadace, kinga kuwa ai ba ƙananun kuɗi ba n.." zubewar Naila ƙasa kamar gini ne ya dawo da hankalin Ruwaida da ke surutun Tukunyar Dhahab kanta. Hankali a tashe ta ja Naila da ƙyar zuwa living room.
Sashen Dr. Yasar moƙocinsu da Naila ta gudarwa Ruwaida ta nufa.
Da taimakon Yasar Naila ta dawo hayyacinta ko da su ka tambayeta abinda ya sameta ta faɗi bata ɓoye mu su abinda ya rikita ta ba.
Bayan ta gama ba su taƙaitaccen labarin Yakinsu Ajiyar zuciya dukkan su, su ka sauke.
Har cikin ranta Ruwaida ta yarda da gaske kamanceceniyar Mutumin da Naila ta gani sak Salman da Tukunya mai irin sunan Abduh Dhahab ne kawai su ka rikitata a matsayinsu na mutanen Yankinta ba tare da wani alaƙa ba a tsakaninsu ba, saɓanin Yasar da ya kasa yarda Naila ba ta da haɗin komai da abinda ya rikitarta sai alaƙar Yanki kawai.
Sai gabannin la'asar Ruwaida ta taimakamin na koma sashena.
SUFYAN; Bayan sun fito daga lecture, Sumaya ya sa rakasa ya zaɓo kalar rigar da take so. Sauƙin kayan sawar Ƙasar Abyad da abincin cin su ne yasa itama ya siya mata irin rigarsa su ka yi anko, ragowar kuɗin kuma abinci ya siya mu su mai lafiya suka ci suka ƙoshi, ɗan canjin da ya rage ya loda kati saboda kiran Mahaifinsa Ɗayyib.
A ɓangaren su Ɗayyib da Hindu lokacin da Sufyan ya kirasu ya basu labari sun sa masa albarka tare da nu na tsananin jin daɗin yadda Naila ta fara samun kuɗin da zai yi karatunsa hankali kwance, saboda Ɗayyib ya shaidamai bayan tafiyarsu da kwana ɗaya akaci Kasuwa bai san dalili ba sam babu cikini.
Bayanin Mahaifinsa sam bai ɗaga mai hankalin ba, tunda ya samu Naila ta fara sana'ar da su ke samun kuɗin shiga. Bai ba su labarin haɗuwar sa da Sumaya ba saboda ya san bazasu ba shi goyan baya ba, za su ce yayi wuri ya ɗakata shi kuma abinda ba ya son ji kenan.