a tsakankanin Iyayensa, wannan ya tunamata da nata Iyayen dalilin haka sai kukanta ya ƙaru, takaicin yadda ƴan uwan Mahaifinta su ka dinga ƙasƙantar da kansu duk don samun wajen zama a wajen Ɗayyib kamar ya kasheta.
A ranar ta zagaya Masarautar Yankin Tudu ta kuma tabbatar da kyansa da mutane su ke zuzutawa, har gaban Sarki Hammam sai da ta kai gaisuwa. Bayannan aka miƙata ɓangaren da zata kwana.
Bata shafe hour biyu da kwanciya ba Matasan mata ma su kusan shekaruna su ka shigo, da alama turosu akayi don tayata kwana. Ba su san ba barci ta ke yi ba su ka fara hira.
Cikin jimami ɗaya ta ce;
"Ai ni na jiyo abinda yafi ƙarfina, ni dama na yi zargin Uwar gida Hindu bazata taɓa yarda wannan makirin ɗan nata ya auri ƴar ƙaramin Gidan da su ke talakawan fitik ba sai da wata manufa"
Cikin rashin yarda ɗayar ta ce "Ni kam sam na kasa yarda da zancenki Ƙawata, ta ya ya zata sadaukar da dukiyarsu da ake zuzutawa a kan abinda ba ta da tabbaci a kai, anya kuwa kin jiyota da dakyau?"
"Wallahi tsaf na jiyota, ke harda sharaɗi ta ce ta kafamai, karya kuskura ya kusanci Matar kar a haifo mu su ƙasƙantaccen jika, ya bari su ga kalar ɗaukakar da zai samu."
Naila tana jin su suka kwashe da dariya haɗe da tafawa, kafin ɗayar ta ƙara cewa;
"To wallahi ki adana wannan dogon bakin naki idan ba haka ba shi zai kai ki ya baro kin ji na gayamiki."
Da sauri ta damƙi bakin na ta kafin ta saki su ƙara kwashewa da dariya.
Daga kwancen da Naila take jikinta ya fara rawa, gumi da zazzaɓi su ka lulluɓeta lokaci ɗaya. Kuka mara sauti mai fitowa tun daga ƙasar zuciya na zuwar mata, ƙwarin gwiwarta na bin iska. Ta ɗauki lokaci tana kuka mara sauti kafin wahalallen barci ya fara ɗaukarta, har barci ya ƙarasa ɗauketa ba su daina tattaunawa ɓoyayyun sirrinkan da su ka shafi Masarautar ba.
★washe gari da ta farka da su tayi tozali su na barcinsu hankali kwance, daga yanayin suturun jikinsu ta gane ba Bayi bane Ƴaƴan Gida ne.
Shagali na musamman aka ƙara shiryawa kafin tafiyarsu Ƙasat Abyad.
Faɗa sosai Jalal kakan Sufyan da Mahaifinsa Ɗayyib su ka yimata. A ɓangaren Mahaifiyar Sufyan Hindu faɗar hannunka mai sanda tayimata mai surke da baƙaƙen maganganun da ke nuna ba Mata ta aurawa Sufyan ba Baiwa ta auramai. A gabanta ta ƙara jaddadawa Sufyan Umarninta, wanda bata raba ɗayan biyu akan hirar da taji ƴammatan jiya su na yi ne. Ba bu wani mai faɗa aji a Masarautar Yankin Tudu da baiyimata nasiha ba, wa su na su nasihar ta lallami suka yi mata wa su kuma gori da nuna iyaka ne kai tsaye.
Daga haka Drivern da zai kaisu iyakar Yankin Tudun da zasu hau Motar ƙasar Abyad ya ƙaraso. Sufyan da ke sanye cikin tsadadden farin yadi mai taushi, malalacin murmushin da ke nuna jin kanshi ya saki haɗe da ɗagawa Mutanen Yankin da su ka yi kirco-kirco su na washe baki hannu.
Idanuwansa a kan Mahaifiyarsa suka tsaya daga ƙarshe, alamar jinjina ya yi mata kafin ya shigo Mota ya na gyara zamansa a gefen da Naila ta ke.
Da sannu da sannu motarsu ta fara motsawa har lokacin mutanen Yankin na ɗaga musu hannu, kukan da Naila take ɓoyewa ya bayyana saboda tuna Mahaifana da Kakata da na san tana can tana kuka.
Naila ta bar Yankin Tudu da tarin rauni da tabo a cikin zuciyarta, ko yaya zamanta a ƙasar Abyad zai kasance??
Duk kukan da Naila ta ke yi, Sufyan ya na jinta amma bai ce kanzil ba. Sai da ya fuskanci ba kukan ganin ido ba ne na gaske ne, sannan cikin isa da izzar fitarshi zakka a kaf faɗin ahalinsa saboda samun nasarar tafiya ƙasar Abyad yin karatu ya ce;
"Kukan na menene? Kinsan ina zakije kuwa? Dan Allah karki ɓatamin farin cikina, ke da ma baki da Iyaye, ko ni da na ke da Iyaye a raye bandamu sai ke. Kar ki bari tun kafin tafiyarmu ta yi nisa ki fara saɓawa umarni na kinji na gayamiki" da ga haka ya ɗora farin yatsun hannunsa da bai san wahalar komai ba a saman dogayen yatsun Naila.
Maganganunq sun soketa irin sukar da Marainiya ƴar uwa ta ce kawai za ta san zafin su, saboda ƙara jaddada matan da ya yi da gaske bata da Iyaye don haka bata da abin yiwa kuka.
Bata ƙara ko da tari ba sai idanuwanta da ta lumshe tana jin yadda Drivern Motar su ya ke kwarara gudu.
A tashar da zasu hau Motar da zai yi tafiyar kwanaki kafin isarsu ƙasar Abyad Drivern da ya ɗaukosu ya sauke su. Hannun Sufyan maƙale da nata, ya je ya siyamusu tikiti, suka shiga ƙaton Mota mai ɗaukar fasinja da yawa zuwa ƙasar Abyad.
Ba su jima a ciki ba bayan sunci abinci, aka fara sanarwa tashin motar da komai na cikinsa ya ke kamar na jirgin Sama.
A gefen Sufyan ta ke zauna, kamar zai sumbaceta haka ya sunkuyo da sunan ɗauramata belt. Bayan ya ɗauramata ya ƙara kamo hannunta ya sarƙewa da na shi.
Murmushi mai ciwo ta saki a cikin zuciyarta, tana ganin ba lallai Sufyan ya cika alƙawarin da ya ɗaukarwa Mahaifiyarsa ba.
Tafiyar su bana yini da kwana ba ne tafiyar kwanaki ne, saboda da su Sufyan hamshaƙan ma su arziƙine da jirgin sama za su biya masu ba mota ba. Duk inda zasu tsaya ba bu magana a tsakaninta da Sufyan sai kayan guzurin da Mahaifiyarsa ta zubamai a ƙaramin Akwati mu ke ci akai-akai.
```BIRNIN ABYAD```
Lokacin da Motarsu ta iso Birnin Abyad, yanayin sanyin ƙasar, hasken Mutanen ciki, gina-ginensu, da wasu irin motoci ma su kyan gani a ido da kwaɗayin son shigarsu ne su ka haske mudu idanuwa.
Idanuwan Naila da ta ke jinsu kamar madara saboda haske a Yankinsu sai ta ke jin su a Birnin Abyad kamar sun koma jajaye saboda kyawun mutanen Birnin da take gani da gine-ginen su. Sai ta ke hasaso Yankinsu kamar wani kusurgumin daji mai duhu da ya ke da ƙaracin kayan more rayuwa. Fatarsu da na ke ganinsa mai haske da kyau a Yankinsu a take ya dusashe a idanuwanta ya koma sak na ƴan karkara, ƴan karkarar ma su ƙarancin komai na cigaban rayuwa.
A maganganunsu ta fuskanci ba sa kai ƙarshen zance sai sun haɗa da harshen nasarar da Malaminsu yake ta kwaɗaitar da su, su koya.
Wa sun su kuma nasarar kawai su ke yi babu sirki.
Tunano yadda Mutanen Yankin Tudu su ka dinga ɗago musi hannu lokacin tahowarsu sai tausayin su ya ƙara tsargamata musamman Kakarta da Mahaifanta.
Mahaifinta ya ƙare rayuwarsa a dinki ƙarshe rashin gatan Asibiti ya yi sanadiyar ajalinsa, haka Mahaifiyarta. Kakarta ce dai ba ta cire rai tare da Yaƙini haɗe da fatan wata rana ta zo taga duniyar Birnin Abyad ba.
A ɓangaren Sufyan shima ji ya yi duk ya muzanta, wannan jiji da kan da sumarsa da ya tara duk domin ya zo ya Yaƙi Ƴammatan Birnin Abyad sai ya bi ruwa, ya na jin inama da yana da hula a kusa ya lulluɓe gashin saboda Kunya. Farin fatar da ya ke yiwa Mutanen Yankin Tudu yanga da shi sai ya ga ashe da sauransa, Kananun kayan da idan ya sa a Yankinsu maza da mata su ke bi su na kallo har da tuntuɓe sai ya tashi kamar na ƴan Karkara.
Lambar wayar wanda zai kai su gidan da Iyayen Sufyan su ka kama musu ya zaro a ƴar ƙaramar jakar da ya ɗauko ya na yanga da shi a Yankin Tudu saɓanin isowar su Birnin Abyad da ya ɓoyeshi a hammata.
Cikin ƙarfin hali ya tambaya aka nunamai wajen kira. Shi kanshi sakayayyen wajen kiran da aka sakaye da gilashi abin a yaba ne.
Naila Nutsuwar ya ne ya ta taimaka wajen sakaya gidadancinta, saɓanin Sufyan da dama can ba wani cikakken nutsuwa ce da shi ba, dan dole ya ƙaƙabawa kanshi nutsuwar dole kamar ba Sufyan Ɗan gidan Ɗayyib shugaban kasuwar Tukwanen Zinare ba😂.
Ba su wani jima ba, Uban gidan Ɗayyib mazaunin Birnin Abyad ya zo ɗaukarsu.
Sai da suka tashi hawa Motar inda zamu je Makka ta fahimci ABYAD sunan ƙasar ne Birnin Abyad kuma shine inda aka sauke su kuma anan Mahaifan Sufyan su ka kama Gida, BABBAN BIRNIN ABYAD kuma shine asalin Babban Birnin da kaf faɗin ƙasar ba bu kamar shi.
To idan har Babban Birnin Abyad da take ji a bakin Mutanen Yankin Tudu ya fi inda suke ciki kyau da tsari to ya ya kyansa da mutanen cikina za su kasance??? Naila ta tamabayi kanta, lokacin da suka isa inda zasu shiga Mota.
Bayan sun shiga motar da za ta kai su Gidan da aka kama musu, idanuwanta su ka faɗa kan Motocin da akace su ne masu shiga Babban Birnin Abyad, ko da batayi karatu mai zurfi ba, bata kuma saba riƙe kuɗi ma su nauyi ba tasan ba motocin shigar mutane ne irinsu ba.
Tafiyar Motocin take kallo tana jin kamar ta fito ta bi su. Sai ta ke jin kamar tana ƙewar abinda ita kanta batasan menene a inda za su je ba, tana kallon tafiyar motocin wani yanayi na tsarga zuciyarta, haka ta yi taji har Motocin suka ɓacewa ganinta.
Kasa jurewa ta yi ta tambayi wanda ya zo ɗaukarsu; " hour nawa ne tsakanin Birnin Abyad da Babban Birnin Abyad"
Amsar "hour biyar" ya ba ta tare da shaidamata mutum zai iya zuwa a ranar ya dawo a ranar. Sufyan da ya ke tunanin ta yi tambayar ne domin ta nuna Iyayensa ƙarya suke yi, da su ka ce sun kama mai Gida a Babban Birnin Abyad harara ya watsomata ya na cije baki.
Unguwar su da Gidan da aka kama musu abun a yaba ne, duk da ba ta jin komai akan Sufyan na soyayya ko makamancin haka sai da ta ji ya ɗan birgeta, saboda gida ne da bata taɓa mafarkin zata kwana a cikin irinsa ba har ƙarshen rayuwata.
SUFYAN;
Da Sufyan ya yi tozali da living room da two Bedrooms ɗin da su ka sha kayan ado dai-dai misali a matsayin hidimar da Mahaifansa su ka yi mai sai ya ji kwaɗayin son karya alƙawarin Mahaifiyarsa akan Naila na bin iska daga gangar jikinsa.
Da farko kafin tahowar su ya yi zargin ashe dukiyar da ake zuzutawa Kakansa na wajen Uwa ya mutu ya bari duk ƙaryane, banda ƙarya ne tayaya za'ace da dukka wannan dukiyar da wanda Mahaifinsa ya samo akayi hidimar kamamai Gida ba ma Siyamai ba da biya masa Makaranta a Birnin Abyad? Sai da ya gani da idonsa sannan ya tabbatar da dagaske ba ƙananun dukiya ba ne za su zaunar da mutum a unguwar da aka kama mu su Gida ba.( a nasa ganin kenan, domin a wajen masu zuzurutun dukiya, gadon da ake taƙamar Hindu tana da shi, bai wuce kuɗin kashewar mai arziƙi a yini biyu ba).
Idan har Mahaifiyarsa za ta yi irin wannan sadaukarwa saboda ɗaukakarsa ba tare da damuwar komai ba, to ba bu abinda zai hana shima ya sadaukar mata da na sa farin cikin.
Amma duk da haka dole ya rage zafi, domin ba zai iya kwana ɗaki ɗaya da Naila ya tashi da ita ba tare da ya rage zafi ba.
Gidan ba su su ƙadai ba ne, mutum huɗu ne a Gidan amma kowa rayuwarsa yake yi, ba tare da damuwa da rayuwar Ɗan uwansa ba.
NAILA;
wanka ta yi ta ƙimtsa jikina. Sai a lokacin taga kamar ta ɗanyi kyan gani, saboda dattin Motar da ta wanke daga jikina. Ɗakin da Sufyan ya bata a matsayin nata take ƙarewa kallo, nutsuwa na saukarmata.
Cikin baƙaƙen Abayoyin da ta taho da su masu adon saƙi ta shirya ta tayar da Sallah ta inda ta ga an shimfiɗa abun Sallah alamun nan ne gabas.
Bayan awannin;
Uban gidan Ɗayyib ya hidimta musi ƙwarai da jikinsa da lokacinsa har ma da kuɗin aljihunsa. Abinci mai daɗin da basu taɓa ci ba ya siyomusu Da Suturar sawa kala biyu da ya siyo Sufyan don fara zuwa Makaranta sai wayar hannu da layi a ciki shima mai kyau dai-dai misali.
A kunyace Sufyan ya sa hannu ya karɓa ya na ƙara tabbatar da ashe ba shi kaɗai bane ya raina kayan jikinsa ba dagaske kyan ne ba su da shi.
Da yake saukar Safiya suka yi bayan sunci abinci, Uban gidan Ɗayyib ya yi mu su Sallama da sunan washe gari zai dawo.
Barci ya kwashe kowannensu a ɗakin da ya ke.
Ba su farka ba sai azahar shima babu wanda ya fito a cikin su tunda kowanne da abinci da zai ci a na dakin. Sai wajen ƙarfe 9 da ƴan mintina na dare Sufyan ya shigo ɗakin Nsila.
Gaisheshi ta yi ta ƙara gyara lulluɓin kanta.
Wayo da kuma shekarun da Sufyan ya fita yasa ya fara goge maganganun ƴan matan da ta ji a Masarsutar Yankin Tudu. Da farko kusa da ta ya matso ya zauna saboda ya lura kamar ta na da sani ko hasashe a kan abinda ya ke ranshi. Cikin taushin lafazin da lumshe idanuwansa da su ke tsaye ƙyam a kan fuskarta ya ce;
"Na san surutai da yawa za su yi ta zuwa kunnenki Naila, amma iyakacin wannan Gidan da kuɗin motar da Iyayena suka kashe mana ya kamata ace kin watsar da surutun auren manufa akayimana da ke, Mahaifiyata Mace ce mafaɗaciya kuma tana tsananin so na wannan dalilin yasa ta kuɗiri niyyar auramin matar da zata bauta min kamar Sarki da Baiwarsa, amma kisani Naila har cikin raina ban zaɓe ki domin kisha wahala a Gidana ba, sai domin muyi zaman aure ki bani goyon baya ɗari bisa ɗari akan karatu na. Mun zo nan ga shi kuma kuɗin Mahaifana ya ƙare a wannan hidimar da suka yimana, kuma a halin yanzu ina buƙatar suturun sawa kuɗin hidindimun makaranta da kuma abinda zamu ci Naila."
Naila da batasan sanda ta ɗago kanta ba, idanu ta zubamai domin sam bata fahimci ina ya dosa ba.
Fahimtar hakan ya sa ya cigaba da magana cikin ƙaramin sauti.
"Naila da Baiwarki zaki taimakamin Ni kuma na yi alƙawarin mayar da ke mace ƴar gata a cikin ƴan uwanki Mata."
Still Naila bata fahimci ina ya dosa ba don haka ta ƙara gyara zama.
Da kame-kame ya ce "ina so ki bi dukka Gidajen Unguwarnan ki sanar da su kina kitso, a kwai ma su ra'ayin kitso a cikin su, da wannan kaɗai zaki taimakamin Naila na roƙeki"
Dan jim Naila ta yi maganganun Kaka na dawo mata "ki mayar da hankali kan sana'arki saboda sana'ar kitso baiwane mai girma a ƙasar Abyad."
Cikin yarda da rauni irina ƴa mace Naila ta ɗaga kai alamar ta gamsu ko dan Kaka tayi alfahari da ita.
Da sauri Sufyan ya rungumeta kafin ya yi dabarar ragewa kanshi zafi, Bayan wani ɗan lokaci ya tattara ya bar ɗakin.
NAILA;
Da murmushin raɗaɗin da marata yakemin na mirgina na kwanta, abinda Sufyan bai sani ba zuciyata Macacciyace ba bu rai balle a yaudareta, da sha'awa yana da yare da ko ya taɓani baza ta ji komai ba sai dai bani da ikon hakan.
"Idan ƙarya yakemin domin ya zalunci ne Allah Shi ne gatana," daga wannan hirar zucin Barci mai nauyi ya ɗauketa...✍🏻
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/I1wZrvGJP2s3QIyUuJ4ig7?mode=r_c
🔥ZINARE🔥
SASAAL
12
★washe gari bayan nta yi sallar Asubahi bata koma barci ba, har sai da gari ya yi haske.
Barcinta bai yi nisa ba, Sufyan ya tasheta. Da kayan da aka siyomai jiya ya yi ado, ya yi kyau dai-dai misali domin baza ta ce sosai ba, a matsayinsa na Mazaunin Birnin Abyad. Bayan ta gaishesa ya ji bataƙara da komai ba sai ya haɗe rai ya na ƙara shafa wuyar Rigarshi.
Sam bata fahimci ina ya dosa ba, sai da ya yi tsaki haɗe da faɗin;
" Anya kuwa Naila ki na da lafiyar ido, na san babu Macen da za ta ce banyimata ba, amma ke kullum sai ki dinga nuna kamar Ni ɗin ba wani mai kyau ba ne, ko Hassada ki ke yimin?" ya tambaya da iya gaskiyarsa haɗe da murza zoben silver da ya ke matuƙar ji da shi.
Dariya ƙeta musamman a kan mugunta ba halinta ba ne, amma da ta ƙaremai kallo na tuna irin siffar Mutanen da suka gani a lokacin da suka iso Birnin Abyad sai da ta dara har jerarrun haƙwarana su ka bayyana. Tunda ta ke bata taɓa ganin Namiji mai son ace mai ya na da kyau ba irin Sufyan domin ko Mace albarka, "shi kuma kalar jarabawarsa kenan." Ta faɗa a cikin ranta amma a zahiri miƙewa ta yi kafaɗunsu na gogar na juna ta ce;
"Kai kyakkyawane ko ba ka yi kwalliya ba, balle yanzu da kayi ado da kayan da aka siya a Birnin Abyad, Godiya ta tabbata ga Ubangijin halittun da ya halicci Namiji kyakkyawa irinka Mijina."
Dariya da bata taɓa gani ya yi irinsa ba ya saki, ya na kamo fuskarta, sumba ya saukemata a goshi tsabar daɗin da yake ji har wani lumshe ido yake yi yana binata da kallo kamar zai lasheta.
Sallama ya yi mata, Har ya fita ya ƙara dawowa ya na jaddadamata alƙawarin da ta yi mai.
Bayanshi ta bi da kallo maganar Kaka na faɗomata; " ko wani Namiji da kalar halinsa, halin Mijin wata ba zai taɓa zama irin naki halin Mijin ba, dole a samu banbanci duk ƙanƙantarsa, don haka ki karanci halayyar Mijinki saboda samun sauƙin zama da shi." Ta gazgata zancen Kaka a kan Sufyan saboda duk daɗin soyayya ko kwalliyar da Mace za tayi domin ta ja ra'ayinsa ba ya ɗaɗashi da ƙasa a kan ta zauna ta na zuzuta kyansa da yaba kwalliyarsa sama