x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 736

07 Oct 2025
Aysha ta gudu, sai Sulaim da ya tarar da takarda a hannu. Abduh ya yi kuka shi da Ɗanshi kafin su haƙura su fuskanci rayuwarsu da sam babu walwala a ciki.

Ba ji ba gani Abduh ya ke ƙera Tukwane.

Ranar da ya rage saura kwana biyu ranar da ya yi alƙawarin kafa Kasuwar Tukwanen Zinare ya cika bai runtsa ba kwana ya yi kaiwa Allah kukansa....

Wane fata kuke yiwa Abduh Dhahab da masu irin zuciyarsa???

SASAAL


09

★Washe gari Abduh ya tuntuɓi Abokanansa su Ɗayyib, Mahmoud( Mahaifin Naila), Mallam da Mahaifin Malik su fito da Kayan sana'ar su idan da rabo sai su sayar batare da sunyi wahalar bin Kasuwanni da suka saba ba. Ga mamakin Abduh babu wanda ya yi yunƙurin tankamai, kamar ma ba su san abinda ya ke faɗa ba. Kunya suke ji su fitar da Kayansu azo ba'a siya ba ayi mu su dariya. Mahmoud Madinki ne, kayan yara da na manya dinkakku yake bi Kasuwanni yana siyarwa, Mallam kuma Qur'ani da littafan addinin musulunci yake fansarwa, Mahaifin Malik kuma maganin gargajiya yake siyarwa. Ɗayyib ne kawai baya sana'ar hannu taƙamaimai sai abinda ba'a rasa ba. Da Abduh ya fuskanci inda suka dosa sai ya nuna kamar bai damu ba, amma har cikin zuciyarsa baiji daɗi ba.
Da yaƙini Abduh ya share ƙaton filin Ubaidu Mahaifinsa da kaɗai ya rage filinsa basu wawashe ba, ya jere Tukwanen da ya ƙera.

A gefe ya shimfiɗa buhu shi da Sulaim suka zauna bakinshi bai gajiya ba da ambaton Sunan Allah. Har lokaci ya fara tafiya babu wanda ya zo daga waɗanda sukayi alƙawarin zuwa.

Mutanen Yankin sai suka fara leƙoshi su na dariya, bai nuna ya gansu ba, balle su gane abinda suke yi mai yana sukar zuciyarsa. Yunwa da ƙishi ne yasa Abduh Dhahab yunƙurin miƙewa tunda yasan ko yunwa zai kashe Sulaim ba zai yi magana ba. Har ya miƙe hayaniyar mutane daga nesa ya dakatar da shi. Fuskokin mutane ƙalilan ya gane a cikinsu amma ragowar duk yawon kasuwannin da ya gamayi bai taɓa ganin su ba. Waɗanda sukayi alƙawarin zuwa siyan Tukwanensa ne, bakin Abduh kamar zai yage wajen tarbar su, kafin shuɗewar hour ɗaya sun yi ciniki sun siye Tukwanensa gaba ɗaya. Mutum ɗaya a cikin su ne ya tambayi ina zai samu fansar Qur'anin akan sari?. Abduh Dhahab manta abinda su Mallam suka yimasa ya yi, ya nufi hanyar Gidajensu da sauri kamar zai tashi sama, batare da tunanin za'a iya sace masa Ɗansa ko dukka kuɗin cinikin da ya yi ya zuba a ƙarƙashin buhu ba, shi dai burinsa ya kira Abokansa ayi musu ciniki.

Jiki na rawa, Mahmoud da Mallam da Mahaifin Malik suka nufo Kasuwar Tukwanen Zinare da Kayansu. Da rububi akan siye kayan har sai da suka ƙara komawa Gida suka ɗebo wasu. Mahaifin Malik ne kawai maganin gargajiyarsa ta ɗan yi ragowa.

Bayan Kasuwa ta tashi kowa ya adana kuɗinsa bakin kowannen su a washe, sai suka ɗaga Abduh Dhahab sama suna dariya jindaɗi da waƙeshi da waƙe kala-kalan da ke nuna jarumtarsa da dagiyarsa.

Daga wannan rana Abduh Dhahab ya kafa Kasuwar Tukwanen ZINAREN da kafatanin mutanen Yankin su ke amfana da shi.

Bayan komai ya dai-daita Abduh Dhahab ya fita wani Yankin ya auro Mairam. A dalilin Mairam Mahmoud ya ga Mahaifiyar Naila ya aura saboda yawan zuwa Gidan da takeyi, kafin daga baya Abduh Dhahab ya haramtawa Mairam shiga ko ina, don dalilin shigarta Gidan Mahmoud ne aka fara samun masu zugata, ta dinga yi masa Satar kuɗi tun da baya bata sai tayasa aiki..

Halaccin Abduh Dhahab yasa Mahaifin Malik ba shi Malik ya dinga yi masa hidima, tunda lokacin Sulaim ba shi da ƙarfin da zai taimakawa Abduh da wasu hidindimun.

A sirrince ba tare da sanin kowa ba Abduh Dhahab ya ƙirƙiri Makarantun boko da na Islama da Asibitoci a Yankin da taimakon abokanan kasuwancinsa na Babban Birnin Abyad, amma babu wanda ya sani nima Mahmoud ne ya sanar da ni ko Ɗayyib bai sani ba. Ya damƙa amanar komai a hannun Mallam ne saboda shi kaɗai ne mai ƴan uwa masu ƙarfin arziƙi a Babban Birnin Abyad da Sarki Hammam da mutanen gari zasu gamsu taimakon daga garesu yake, amma a baɗini Mallam ko ƙofar Gidajen Ƴan uwan nasa bashi da matsayin zuwa.

Abduh Dhahab ya yi hakane don kawar da idon mutanen Masarautarsu akan lamuransa duk da sun san yana samun kuɗi amma ba su isa su ƙiyasta iya adadin abinda yake samu ba.

Abin mamakin duk da wannan girman halaccin na Abduh Dhahab ga mutanen Yankinsa bai sa sun ɗagamai ƙafa ba, a wasu lokutan sai su ce

"ai Mahaukaci ne, banda Mahaukaci wanene zai zaɓi sadaukar da iya Gadon da Mahaifinsa ya barmai domin ya yi suna ya burge mutanen gari?" Babu wasu kalmomin su na ɓatanci da baya dawomai amma bai taɓa damuwa ba domin yasan a sannu zasu gane ranarsa.

Mutanen Yankin Tudu a ɓangaren halayya mutane ne ma su son kansu, butulci da rashin damuwa da damuwar Ɗan uwansu.

A ɓangaren siffa kuma Usul ɗinsu suna da kyan fuska da haske fata, manyan idanuwa buɗaɗɗu, yalwataccen kashin kaa da kaurin jiki, mafi akasarinsu ba su da tsaho daga gajeru masu faɗi da jiki sai masu matsakaicin tsaho da kaurin jiki, idan kaga mutum da siffa saɓanin wannan to Mahaifiyarsa ko Mahaifinsa ba asalin ɗan Yankin Tudu bane. Kamar dai ke Naila baki da irin siffarsu sai irin gashin kansu haka Sufyan ɗan wajen Ɗayyib shima ba laifin yana da tsaho da ginannan jiki amma duk da haka ya sirko da irin ƙibarsu da idanuwansu, dukka saɓanin Sulaim ku ke domin Sulaim ba shi da siffa ɗaya na mutane Yankin tudu kalar fatarsa idanuwansa, tsayuwar ginannen jikinsa tun yana yaro dukka ba irin nasu bane, shi yasa suke ganin a kaf faɗin Yankin babu Matashin da daya girma a raye zai shafe Tarihin duk wani Matashi ɗan ƙwalisa a Yankin Tudu. Sai shima Malik irin hasken fatarsu da idanuwansu ya ɗauko amma sam siffarsa tsayuwarsa kamar sun aroshi daga Mahaifiyar Abduh Nanaah da Sulaim yake kama da ita. Wannan dalilin yasa Abduh ya ke son Malik har ranar da waɗanda ba'asan su waye ba, sukayi nasarar kaishi ƙasa.

Wannan shine asalin labarin Abduh Dhahab da Masarautar Yankin Tudu, sai kuma abubuwan da suke waɗanda ba ni da sani akai
```DOWAWAR LABARI```

Idanuwan Naila da suka ɗanyi jaa ta lumshe tana ƙara ƙanƙame hannun Kaka, itama Kaka ƙara ƙanƙame hannun Naila tayi cikin kuka ta cigaba da magana;
"Su na kashe junansu abisa son zuciyarsu, ba tare da wani haƙƙi ba. Ba su taɓa nuna ƙin bare ya shigo cikinsu kai tsaye ba sai a kanki Naila, saboda talaucinmu. Shiyasa nakejin tsoro da fargabar kar kema su kashemin ke a banza, domin bani da ƙarfin gwiwa da dukiyar da zan jaa da su."

Da ƙarfin gwiwa Naila ta girgiza mata kai tana rungumeta cikin taushin lafazi ta ce;

"bazan mutu ba har sai lokacina ya yi, idan kuma lokacina ya yi ko ba na cikin Masarautar Yankin Tudu Allah zai ɗauki raina Kaka, batun cewa a'a ko ki kai kanki gaban Sarki Hammam abisa ƙin amincewarki duk mu haƙura mu gayawa Allah, In Sha Allahu zai sauƙaƙa mana." Da haka sukayi barci hannunsu ƙanƙame da na juna.

★washe gari Kakar Naila ta tattauna da Ƴan uwan Mahaifin Naila kan su bawa Iyayen Sufyan haƙuri Naila ta kammala Makarantar sakandare tunda saura wata bakwai. Da yake babu Allah a lamuransu sai suka taso mata bakinsu a haɗe, acewarsu su kansu basu da tacewa duk abinda Shugaba Ɗayyib ya yanke dole shi zasu haƙura su bi.

Zuciyar Kakar Naila na tafasa ta nufi Gidan su Sufyan kai tsaye.
Bayan sun gaisa Kaka ta koro bayanin abinda ke tafe da ita..
Wani irin kallo Hindu take yimata da soyayyun idanuwanta da suke ƙananu a tsaitsaye farare ƙal. Murmushi ta yi kafin ta ce;
"Haba Ummu Habeebah(Kaka) ai da baki zo da kanki ba, Ni dai ina neman afuwarki akan abinda ya faru shekarun baya, sannan na fuskanceki amma bazan iya yanke hukunciba tunda Maigida Jalal( Mahaifin Ɗayyib) shi ya tura mutane da kanshi nemarwa Sufyan auren Naila. Ki bari Mahaifin Sufyan ya dawo In Shaa Allahu zan isar da saƙonki" godiya Kaka tayi mata tana yunƙurin miƙewa. Da sauri Hindu ta dakatar da ita ta hanyar faɗin;
"Bari na kawo miki abun motsa baki mana" kai Kaka ta girgiza haɗe da cewa; "bakomai Hindu, fuskantata da kikayi yafi komai yimin daɗi, Allah Ya ƙara arziƙi" duk da haka Hindu bata bar Kaka tabar Gidan batare da abinda tayi niyyar bata ba. Dama kuma tuntuni ta tanadeshi ne domin tasan har gaban abadan Mahaifiyar Habeebah bazata taɓa ƙaunarta ba.

Bayan Ɗayyib ya dawo
Ko zancen Hindu bata yi masa ba, sai shirye-shiryen tafiya Babban Birnin Abyad da suke yi domin duba Gidan da Sufyan zai zauna da Naila saboda a gaggauce takeson ayi komai duniya tasan tasan da zaman ɗanta.

A ɓangaren Kakar Naila bayan ta koma Gida ajjiye Tufar da Hindu ta bata tayi a gefe, ta na bawa Naila labarin abinda ya faru. Murmushi mai tsayawa a iya saman laɓɓa Naila ta saki zuciyarta a raunane.
Da nishaɗi Kaka ta ce "kinji daɗi ko ba ki ji ba Naila?"

Naila sai da haɗiye abinda take ji sannan ta ce "na ji daɗi Kaka Allah Ya biyaki da Alkhairin Sa" Kaka ɗauke kanta tayi tana amsawa da "Amin".

Da yammaci aka turo ana sallama da Naila, ba ta tsaya ɓatawa kanta lokaci ta zura doguwar rigar da aka yiwa ado da saki baƙi da malulluɓinsa. A tsaye ta hango Sufyan, ya yi ado cikin ƙananun kayan da suka dace da siffarsa, fuskarsa ta maza masu raina mutane na tsaye ƙyam akan ƙofar Gidan su. Mutanen Yankin kowa ya wuce sai ya waiwayo ya ƙara kallonsa shi kuma yana ƙara hura siririn hancinsa.

Tsaf yake ƙarewa Naila kallo haɗe da wassafa yadda zamansu zai kasance, tana da komai da yakeso dangane da Ƴa mace abu ɗayane kawai ya yi mata cikas a wajenshi shine rashin zamantowarta ƴar hamshaƙai ko wayayyiyar Babban Birni. Ya na son ƴar masu kuɗin ba irin Naila ƴar Madinka jikar Madinka ba.

Ƙarasowarta ne ya dawo dashi hayyacinsa, da girmamawa ta gaishe shi, ya amsa yana tattare girarsa, har ya fara hura hanci sai ya tuna da hudubar Mahaifiyarsa; na ya sakarwa Naila fuska har ya samu ayi auren. A take ya saki ranshi yana janta da hira cikin aji da kamewa. Daga "eh, a'a, uhm" sune amsoshin Naila. Sufyan kamar ya shaƙeta yana ji a ransa maiyasa bazata ɗago ta kalleshi ba kamar zata lashe shi, ko dai itama har yanzu fuskar Matacce Sulaim bai bar zuciyarta ba? Tuna wannan kaɗai sai da zuciyarsa tayi bugawar daya ɗan dafe ƙirjinsa, jin kansa da ƙarin tsanar Sulaim na dirarmasa lokaci ɗaya.

Tarin sumar kanshi ya shafo cikin isa da ɗacin dayake ji a cikin zuciyarsa ya ce " ki shiga Gida, ba ni da wani shagali da zanyi kamar yadda bani da lokacin ƙara dawowa gareki, ina fatan zakiyimin kyakkyawar fahimta" ya yi tunanin zata ji babu daɗi tayi magiya da nuna zumuɗin son dawowar kyakkyawan Matashi irinsa wajenta amma sai ya ga ta ɗaga kai alamar da gamsu. Kafin ta kai ga barin wajen tuni ya tashi lafiyayyen mashin ɗinsa ya baɗeta da ƙura. Kai Naila ta girgiza mamakin abinda ya tunzurashi na kama zuciyarta.

Kaka bayan fitar Naila ta janyo Tufar da Hindu ta bata kamar ana fizgarta ta ɗauko ta wanke ta soma ci, har Naila ta shigo tana gutsirar Tufar suna hira a hankali. Tana gama ci barci ya ɗauketa. Da mamaki Naila take kallon yadda ta kwanta a jirkice kafin ta gyara mata kwanciya ranta cike da mamaki.

★washe gari Ɗayyib da Hindu suka ɗauki hanyar Babban Birnin Abyad, sai da sukayi kwanaki a hanya.


Maimakon Babban Birnin Abyad ɗin su yi niyyar kama gida sai a Birnin Abyad suka kama, saboda zaman Babban Birnin Abyad da kuɗin Makarantarsu yafi ƙarfinsu amma sun yanke shawarar ba zasu gayawa Sufyan ba idan ya zo ga ne wa idanunsa.

Su da suka tafi da sunan kama hayar shekaru uku daƙyar suka samu mai sauƙi shima ba da asalin tsakiyar Birnin Abyad yake ba suka kama na shekara biyu. Sai guntun kuɗin da suka adana don biyan kuɗin Makaranta Sufyan idan sun samu sun haɗa da wani. Saboda Hindu shawarar siyar da ragowar kadararsu ta yanke idan ta koma.

Har suka iso Gida labarin kyan ƙasar Abyad bai bar bakinsu ba, shima Sufyan tuni ya fara tada kafaɗa zuciyarsa da kanshi tsabar yanda yakejin girmansu gani yakeyi kamar gangar jikinsa ba zai iya ɗaukar su ba. Domin shi a yanzu yafi ƙarfin duk wani Matashi a Masarsutar su bama Yankinsu kaɗai ba tunda ko Ƴaƴan Sarki Hammam mace ɗayace ta taɓa Aure a can shima bawai cikin Babban Birnin Abyad ɗin ba ne daf da shine.


A ƁANGARENSU NAILA;
Har gari ya yi haske Kaka bata motsa ba wannan dalilin yasa Naila ta birkitota da ƙarfi, idanuwanta ta gani a kakkafe. Cikin yanayinta na nutsuwa ta fara ambaton Allah kafin ta nufi Gidan Yayyan Mahaifinta.

Kwanan su biyu ana yiwa Kaka maganin gargajiya taji sauƙi amma magana kam sai a hankali, sai ta wuni batace komai ba ko baifi tayi sau ɗaya ba, tanason bawa Naila labari da yunƙurin daƙile Hindu. Saboda kai tsaye ta fuskanci Hindu ce ta bata Tufa mai ɗauke da sirihin da zai duƙufar da ita ayi komai batare da ta iya yin yunƙurin komai ba, amma ba bu hali.

Sai dai tayi ta hira da zuciyarta. Naila tayi kuka musamman da zancen zaman Aurenta a Babban Birnin Abyad ya cika lungu da saƙon Yankin. Har shishigi Ƴammatan Yankin suka fara yimata da fadanci kullum suna Gidan.

Daga wannan lokacin Naila ta fuskanci dole ta auri Sufyan, musamman idan tanaso ta tsira da lafiyar Kakarta domin itama ta gane Tufar da Hindu Mahaifiyar Sufyan ta bawa Kaka ya mayar da ita haka.

Kakarta tana cikin wannan yanayin Masarautar Yankin Tudu suka fara gudanar da shagalin gagarumin bikin da ya tashi kan mutanen Yankin, har ma da maƙotan Yankunansu.

Da ido da hannu Naila take magana da Kaka kuma ta fahimceta, duk shagulgulan da suka yi, ɗaya aka gayyaci Naila da ƙawayenta ƴan shishigi sai ƴar Yayan Mahaifinta Laila.

Sufyan ya yi kyau kamar ka sace ce shi ka gudu murnar tafiya Babban Birnin Abyad na ƙara haukata kanshi yanajin inama da Kabeer yana nan ya nuna masa shi ba'asan yinsa bane, kuma ba da iyakacin Shugabancin Kasuwar Tukwanen Zinare suka dogara ba.

Wani irin kyau Babban Birni Abyad yake da shi har Sufyan da bai taɓa zuwa ba yakewa zumuɗi???...✍🏻
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥



NAFISA ALIYU SASAAL



*CHAPTER 2*

*TAFIYAR NAILA DA SUFYAN BABBAN BIRNIN ABYAD*



Pg 10

NAILA;
A dai-dai lokacin da mutanen Yankin su ke ji inama da su ne zasu tafi Babban Birnin Abyad Naila na maƙale da Kakarta ranta ba daɗi.

Gabannin sallar magrib Malamin da ya ke yiwa Kaka rubutu ya aiko da shi.

Kaka da ke cikin matsanancin damuwa saboda abubuwa ma su muhimmancin da takeson sanarwa Naila amma babu hali laƙwas tayi idonta ƙyam a kan dogayen yatsun Naila da ke juyemata rubutu a kofi.
Kanta Naila ta kamo bata saketa ba har sai da ta gama sha. Yunƙurawa tayi ta miƙe, sai dai ko taku ɗaya ba ta yi ba ta ji Muryar Kaka na ambaton sunanta
"Naila"
Da sauri ta juyo cikin mamaki kafin ta rungumeta da ƙarfi haɗe da kai mata sumba a gefe da gefe ƙuncinta. Da tsananin farin ciki ta ce;
" na ji daɗi sosai Kaka fargaba da komai ya gushe da ga gareni tunda ga shi kin faɗi sunana sosai Allah Ya cigaba da karemin ke Kaka" Kaka da tsananin farin ciki ta amsa da "Amin" sai dai bayan amsawarta ƙwallane ya cika idanuwanta da su ƙyam a kan Naila.
Ta yunƙura zatayi magana Naila ta dakatar da ita, ta hanyar girgiza mata kai. Amma duk da haka bayan wasu daƙiƙu sai da ta numfasa cikin karyewar zuciya ta fara magana;
"Kafiyata da nuna ikona ba za su yi tasiri a garemu ba, tunda tun kafin muje ko ina Hindu ta fito mana da manufarta ƙarara. Amma Allah Ba ya barci Naila, da ƙarfin mulkinSa zuwanki ƙasar Abyad babban nasara ne a gareki, makircinsu shine matakin nasararki In Shaa Allahu."
maganganun Kaka sun ƙarawa Naila ƙwarin gwiwa a kan wanda take da shi, har tanajin zata jurewa duk wasu ƙalubale da zasu biyo bayan zaman auren su da Sufyan.

A haka suka raba wannan dare su na hira saboda washe gari Naila za ta bar Gidan, mafi rinjayen hirar ta su a kan Tufar da Hindu ta ciyar da Kaka ne da kuma shawarwari da dabarun zaman Gidan Miji.

★washe gari da sassafe Dangin Mahaifin Naila su ka zo ɗaukarta, saboda sunfi son a zo ɗaukarta a inda su ka tsara. Kaka bata tanka ba sai rungume Naila da ta yi bayan ta sumbaci goshinta. Cikin ƙarfin halin danne kukan da ta ke yi ta ce; "Ki kula Naila, inanan ina jiran dawowarki wata rana da dumbin nasarar da zaki zamemin abin alfahari da Mutanen Yankinki gaba ɗaya, ki mayar da hankali kan sana'arki saboda sana'ar kitso baiwane mai girma a ƙasar Abyad. Daga ƙarshe ki tuna da shawarwarina, haƙuri, juriya da biyayya sune matakan nasararki" daga haka Kaka ta saki hannun Naila da ke kuka kamar zata shiɗe.



Barin Gidan Kaka zuwa Gidan ƙannen Mahaifinta ya tabbatarmata da ta bar Gidan Kaka kenan sai kuma wata rana idan da rai da lafiya. Bayan sun kai can zagaye ta su ka yi kowannen su na faɗar albarkacin bakinsa da sunan nasiha.

Ba bu nisihar Kawunnanta ɗaya da ya shigeta saboda kallon maƙiya ta ke yi mu su, kamar yadda su ka nunamata ƙiyayya a zahiri.

Ba ya tabbatar da ita cikakkiyar Marainiya ba ce, sai da dangin Mahaifinta su ka miƙata Masarautar Yankin Tudu. Sufyan ya na zaune