Sarki Hammam da kansa ya faɗi sunan wanda yakeso ya zama Shugaban Kasuwar da kuma Mataimakinsa. Salman bai musa ba, shi dama aikinsa koyar da Tukwane kuma ya yi ya gama.
Sai dare sosai ya dawo Gida.
★washe gari kowa na Yankin bakinsa a washe, saboda dawowar Kasuwar Tukwanen Zinare babban nasara ne gare su baki ɗaya.
Bayan anci ansha Salman ya fara jawabi;
Bayan ya yi godiya ga Allah ya ɗora da jawabin godiya da kuma muhimmancin sana'ar da suka koya.
Can murnar kowa ya tsaya lokacin da Salman yake ƙoƙarin sanar da Shugaban Kasuwar Tukwanen ZINARE. Kowa burinsa ace shine ko wani nasa ne.
A bisa tattaunawar da Salman ya yi da Sarki Hammam bayan sun gama cin liyafar daya gayyacesa a daren jiya, ya sanar da ƊAYYIB a matsayin shugaba DATTIJO JUNAID kuma mataimakinsa.
Hayaniya ne ya ɓarke wasu suna ganin Dittijo Junaid da baya iya magana bai cancanci ya zama Mataimakin Ɗayyib ba, wa su kuma daga Ɗayyib har Dattijo Junaid ɗin duk basa so. A haka taro ya watse wasun su rai a ƙuntace da alwashi kala-kala.
Salman tare da Dattijo Junaid da Ɗayyib, gidan Abduh Dhahab dayake a matsayin Masauƙin suka wuce don yin bankwana saboda washe gari zai koma ƙasar su.
Sun shafe awanni suna tattaunawa kafin dukkan su su miƙe suna ƙarayin musabaha. Dai-dai lokacin da suke yunƙurin fitowa sukaji ana kwaɗa sallama haɗe da ɗan bubbuga Gidan.
Tare suka fito Salman ya buɗe ƙofa, kafin ya ankara aka fara sararsa ta ko ina...
Kamar dai Shekarun baya lokacin su Abduh babu wanda ya leƙo, duk da anajin kururuwarsu✍🏻
★washe gari da dukuku Maƙotan da suka ji kururuwarsu suka kai koken sun ji ihu a gidan Marigayi Abduh Dhahab jiya da daddare.
Sarki Hammam a kiɗime ya miƙe shi da Muƙarrabansa suka nufi gidan Abduh.
Kafin gari ya ƙarasa haske labari ya karaɗe ko ina.
Kafatanin Mutanen Yankin Tudu ne suka yiwa Gidan Marigayi Abduh Dhahab zobe, kowannen su zuciyarsa cike da tsoro da wani fargaba mai girma gaske. Yunƙurin faɗar gaskiya a Yankinsu ko kawo wani cigaba ya zama babban musibar da Mutum zai iya rasa ransa a kai.
A cikin Gidan Marigayi Abduh Dhahab Gawar Salman ne a yashe, ya yi kacha-kacha cikin jini, sai Dattijo Junaid da shima idonsa ɗaya yake a tsiyaye bayan raunuka marasa kyan ganin dayake jikinsa. Haka Ɗayyib shima wuƙa ne soke a gefen cikinsa sai raunukan da ba'a rasa ba.
Sarki Hammam kansa ya ɗaga sama, sai da ya tabbatar ya shanye ƙwallar da ya yiwa ganinsa yana sannan ya ɗurkusa a gaban Gawar Salman.
Baƙin cikin da yake ji bai tsaya a iya cikin zuciyarsa ba har saman fuskarsa, yana son Salman sama da son da ya yi wa Abduh, saboda ya taimaki Mutanensa a lokacin da suke da tsananin bukata, amma wannan baisa sun rangwantamai ba har sai da suka kaishi ƙasa kamar yanda su ka kai Abduh. Fari ƙal ɗin hannunsa da ya ɗan fara yamushewar tsufa yasa ya shafi fuskar Salman, kafin ya miƙe don a samu damar fitar da su daga Gidan.
Fito da Salman a luluɓe har kaa, saɓanin ragowar yasa zuciyar kowa ƙara karyewa. Banda koke-koken muryoyi daban-daban ba bu abin yake tashi a ƙofar Gidan.
To ko dai Tukwanen Zinaren ne ba'a so a Yankinsu tunda shine sana'ar da yafi kowawa Yankinsu kuɗin shiga? Wanene yake musu wannan Ta'addacin a Yanki? Daga Abduh Dhahab har Salman dukkan su maƙera ne, ma su kamaceceniya a ɗabi'u har ma da wasu maganganunsu. kenan anfiso su cigaba da rayuwa cikin azaba da ƙangin Talauci? Tambayar da Mutanen Yankin Tudu suke ta yiwa junansu kenan.
Kamar shekarun baya da suka shuɗe, Daular Sarki Hammam aka wuce da Gawar Salman anan aka Sallacesa, bayan an miƙa su Dattijo Junaid da Ɗayyib Asibitin da babu likitocin azo a gani.
Fargaba mai gusar da nutsuwa ne ya dabaibaye zuciya Sarki Hammam, dalilin haka yasa Jininsa ya hau dole aka buƙaci Likita daga Babbar Birnin Abyad don kula da shi da su Ɗayyib.
Kafatanin Mazan Yankin Yaransu da Manyansu ne suka tafi kai Salman makwancinsa cikin su har da Manya masu faɗa aji a fadar Sarki Hammam.
Daf da zasu shiga Maƙabarta aka sani harbin bindigar da yasa mutane dayawa darewa . Ma su ɗauke da Gawar Salman ma ajjiyesa su ka yi sai dai su ba su gudu ba, su na dai tsaitsaye. Ƙarar Harbin da'asaki sau biyu a jere ne yasa suma suka tarwatse aka bar Iya Gawar Salman.
Mota mai tudu baƙi mai tsananin sheƙin dake bayyana girman dukiyar da'a zuba kafin mallakarsane ya yi parking a gefen Gawar Salman.
Maza majiya ƙarfine suka fara fitowa ɗaya bayan ɗaya har su uku a jere kafin fitowar na huɗunsu.
Fitowar na huɗunsu ne yasa Bashar kawun Ɗayyib kuma mai faɗa aji a Masauratar Yankin Tudu da ke laɓe a ɓoyarsa shi kaɗai kuma ya sawa zuciyarsa dole sai ya ga duk abinda zai faru zare dukka girman fararen manyan idanuwansa na Usul ɗin Mutanen Yankin Tudu. Fitsari mai ɗumin gaske na biyo jikinsa, a take ya ji idanunsa na ƙyaƙyayin azaba. Amma duk da haka taurin zuciya, da kafawa duk abinda yasa a gaba ƙahon zuƙa sai yaga bayansa yasa ya ƙi kulle idanuwansa kamar yadda ragowar su ka yi a maɓoyarsu.
Ba bu rahama a fuskar na huɗunsu da yafi su girma da tsaho, hannu ya sa ya ɗauke Salman a makara, yanayin yanda ya ɗagashi na bayyana rauninsa. dasauri ragowar ukun suka buɗemasa bayan mota ya shimfiɗesa.
Harbi suka ƙara saki amma duk da haka fararen idanuwan Bashar da suka koma jajaye na tsaye ƙyam a kansu. Yunƙurin shigar su Mota yasa ya ɗan lumshe idanuwansa na seconni ko zai samu sassaucin zugin azabar da idon yake mai.
Ɓude idanuwan da Bashar zai yi ya tsinci Mutum biyu a gabansa, dama ba bu wani tazara a tsakaninsu. Ya kasa ihu saboda duniyar fargabar daya tsinci kansa a ciki. Kamar Kayan wanki haka suka ɗebesa har Gaban mutumin da Kallonsa daga nesa kaɗai ya sa shi sakin fitsari. Ƙasa Bashar ya yi da kanshi jikin da dama can lallaɓawa yake yi saboda yawan shekaru ya fara karkarwa. Ɗago shi ya yi suna kallon tsakiyar idanuwan juna, idon Bashar kamar an tsiyaya jini tsabar jan da sukayi. Ƙasa Bashar yaƙarayi da kanshi saboda gudawan daya tahowa mai, ba ya kuma burin ya ƙara kallon ko da fuskarshi ne balle cikin idanuwansa saboda tsoro. Bashar bai gama saƙe-saƙen da yake yi ba yaji ya ƙara ɗago Kanshi. Da ƙarfi ragowar suka buɗemai baki. Gurnanin azabar gaske Bashar ya saki lokacin da na huɗunsu ya ciremai harshe kwatankwacin yadda aka yanke na Dattijo Junaid. Watsar da shi su kayi suka faɗa Mota kamar iska haka suka bar wajen da Yankin Tudu gaba ɗaya.
Gurnanin azabar da Bashar yake yi babu wanda bai jiyosa ba a maɓoyarsa ba, amma tsoro ya hana kowa fitowa duk da Matsayin da Bashar ya ke da shi a Daular Masarautarsu.
A ɓangaren Sarki Hammam duk bai san wainar da'ake toyawa ba saboda barcin daya ɗaukeshi, suma waɗanda suka rage a Masarautar laƙwas su kayi kamar basusan abinda yake faruwa ba, tunda wanda zai tilasta mu su fita kai agajin bai san ma anayi ba.
Sai da kowa ya yi hour biyu da ɗoriya a maɓoyarsa sannan duk su ka firfito, zuwa lokacin tuni Bashar ya yi suman azaba. Ko takan inda harshen da suka yanke yake basu bi ba suka saɓashi a guje sai Asibiti. Daga Asibiti kowa ya silale ya yi Gida haɗe da kulle ko ina.
A ɓangaren Naila tayi kukan mutuwar Salman, har sai da ya saukar mata da ciwon kai mai nauyin gaske, gashi babu damar fita kaita Asibiti saboda tsoro. Haka Kakarta tayi ta yimata jiƙe-jiƙe har zuwa washe garin da ta ji ɗan dama-dama.
Da wani kallo ta kalli Kakarta murya na rawa ta ce;
"Maiyasa ake kashe kowa haka, shin su Abduh da aka kashe basu da dangine? su waye danginsa maiyasa ba su ɗauki mataki ba? da sun ɗauki mataki da yanzu ba akashe Salman ba, Kaka su waye dangin Abduh Dhahab? maiyasa suka wofintar da al'amuransa a haka?"
Kaka murmushi ta yi tana shafa kan Naila ta ce;
"Ki bari ki ƙarasa warwarewa In Sha Allahu zan baki labari"
SARKI HAMMAM
★washe gari da Sarki Hammam ya farfaɗo ya samu labarin abin ya faru. A gaggauce ya yace a shirya mishi zuwa ganin Bashar.
Lokacin da ya isa Asibiti da ake yiwa su Ɗayyib, Dattijo Junaid da Bashar maganin gargajiya kafin ya shiga Ɗakin da Bashar yake saƙon Dattijo Junaid ya riskeshi na;
" idan ya shigo yane raye, a faɗamasa yazo gareshi yana da saƙo."
Sarki Hammam ya na jin saƙon Dattijo Junaid ya fasa shiga Ɗakin Bashar ya wuce na Dattijo Junaid bayan ya dakatar da kowa daga bin bayansa.
Kallon yadda Dattijo Junaid ya koma kaɗai wani abin fargaba ne. Bayan ya yi mai ya ya jiki ya naimi waje ya zauna.
Alama da salon maganar kuramen da Dattijo Junaid ya saba yakeyiwa Sarki Hammam bayani, cikin ikon Allah, Ubangiji ya bawa Dattijo Junaid ikon yin bayani kamar da bakinsa yake magana tsabar yanda Sarki Hammam ya ke fahimtarsa.
Bayan ya gama bayani Hannunsa Sarki Hammam ya kamo. Junaid Amininsa ne tun suna Yara amma banbancin Gidan da suka fito ne ya nisanta Amintakarsu dole, Bayan ya zama Sarki Junaid ya dawo ƙarƙashinshi Bashar ya maye gurbinsa na Amini.
Sarki Hammam Ya na cikin wannan tunanin Allah Ya amshi ran Dattijo Junaid. Kuka ya zauna yi kamar ƙaramin Yaro. Ya yarda Bawa baya mutuwa har sai idan lokacin da Ubangiji ya ɗebarmasa sun cika, banda haka tayaya Dattijo Junaid zai yi ƙarfin zuciyar rayuwa bayan yana kallon ajalinsa a kusa dashi ko da yaushe kuma ya ja bakinsa ya yi shiru?.
Mutuwar Dattijo Junaid da hasken da Sarki Hammam ya samu dangane da badaƙalar dake addabar Yankinsa a ɓoye bai tsaya a iya hawan jininsa ba har jinya ya kwanta, don dole aka fitar dashi Babban Birni Abyad.
Mutuwar Dattijo Junaid da abinda ya samu Bashar ya kasa hankalin mutanen Yankin kashi-kashi. Wa su sun yarda waɗanda suka zo a Baƙin Mota sune suke yiwa Yankinsu aika-aika, wa su kuma suna ganin sam ba haka bane idan hakane aiba Bashar zasuyiwa haka ba kawai dai Ƴan uwan Salman ne suka zo ɗaukar fansa, to amma ta ya ya akayi suka san mutuwarsa? tunda babu komai na Salman da ba'a bincika ba amma an kasa gano daga inda yake.
Daga wannan lokacin baƙin jininsu sai ya ragu a zuƙatan Maƙotan Yankinsu saboda da yawa sunfi yarda masu Baƙin Mota ne suke yiwa Yankin ta'asa tuntuni, ba wai Mutanen cikin Yankinba
Bayan wani lokaci, Sarki Hammam ya dawo daga Babban Birni Abyad, Bashar shima ya samu sauƙi.
A Fadar Sarki Hammam aka gayyato ƙwararrun ma su zane don su zana wanda Bashar ya haukace yana ta kwatance har da kaisu gidan Abduh Dhahab, duk wannan kwatancen na shi ba bu wanda ya ɗauki hasken komai Sai Sarki Hammam dashi ƙadai yasan wanda Bashar yake nufi daga bayanin da Marigayi Dattijo Junaid ya yi masa. Shara da tsaho yake ta kwatantawa, banda wannan ya kasa siffanta komai. Sai da ƙyar ya fara zayyano siffar wanda sam babu ko mai kamanninsa a Yankin. Dole yana ji yana gani masu zane sukayi tafiyarsu.
Kwanaki bayannan Sarki Hammam yasa atara mishi mutanen Yankin don zaɓar sabon Shugaban Kasuwar Tukwanen ZINARE da Mataimakinsa tun da har lokacin Ɗayyib bai samu sauƙi ba..
41 3080: 🔥ZINARE🔥
SASAAL
Arewabooks@sasaal
06
Kamar ko da yaushe Layi-layi aka bi ana shelar Sarki Hammam ya na buƙatar ganin Mazan Yankin a Masarautarsa..
Kafin ka ce me, kafatanin Magidanta Yankin sun cika harabar Masarautar.
Bayan an ansanar da su saƙon Sarki Hammam, na shin akwai Mai son zama Shugaban Kasuwar Tukwanen Zinare a cikinsu? Ba bu wanda ya ɗaga hannu, ɗaya bayan ɗaya suka dinga sulalewa kafin Minti Talatin filin ya dawo fayau babu kowa, dalili; kowa tsoro yake ji, kar ya karɓi Shugabancin shima a biyosa har gida akashe shi.
SARKI HAMMAM;
Da labarin guduwar Mutanen Yankin ya riskesa ajiyar zuciya ya sauke. Shikenan! Maƙiya Yankin sunyi nasara akan Mutanensa, dama tsoro da gudun mutuwa akeson dasa musu, su dawwama yin rayuwa cikin Talauci, da ƙin faɗar gaskiya ko da za'a kashe na su a gabansu saboda su tsira da rayukansu, duk da mutuwar dai da aka dasa musu tsoronta suke gudunta zai riskesu idan kwanansu ya ƙare.
Kansa ya dafe, ya na jin raɗaɗi a cikin zuciyarsa kenan Mutanen Yankinsa sun gwammace ko shekara nawa Ɗayyib zai yi a kwance zasu jirashi ya jagorance su, idan ya ga zai iya idan kuma ba zai iya ba su haƙura da kasuwar gaba ɗaya. "Kaico" Sarki Hammam ya faɗa a sarari.
★Kasa jurewa ya yi, washe gari ya ƙarasawa ayi shelan;
"shin da wanda ya ke so ya zama Mataimakin Ɗayyib idan ya warke?" Nan ma babu wanda ya amsa tsit sukayi a cikin Gidajensu kamar ruwa ya cinyesu.
Da aka ƙara sanar masa babu wanda ya daki ƙirji ya fito, Gaba ɗaya sai ya rasa abinda yakemasa daɗi, ba shi da wanda ya yarda da shi a kusa da shi balle ya tattauna damuwarsa da shi, saboda masu aikata ɓarnar a kusa da shi suke ta yanda ba shi da yadda zaiyi ya yakicesu, kuma ko da ya faɗi ma su aikata ɓarnar kai tsaye babu wanda zai yarda da shi.
Ya zama dole ya canza salon dabarar mulkinsa shima, don tsirar da Mutanen Yankinsa.
Bayan wani lokaci...
A ɓangaren Ɗayyib ba laifi yanata samun sauƙi saboda ƙwararrun likitocin da suke shigowa dubashi akai-akai, don da farko a Yankin Tudu ya yi ta jinya, sai dai rashin likitoci ya sa aka fitar da shi wani gari da yake kusa da Babban Birnin Abyad.
A cikin watanni ya warke tsaf kamar bai taɓa jinyaba. Da tsananin farin ciki shi da Iyalinsa suka ɗauki hanyar Yankin Tudu.
A ranar da ya dawo Gida bayan ya huta Sashen Bashar da yake a matsayin ƙanin Mahaifinsa Jalal uwa ɗaya uba ɗaya ya nufa.
BASHAR
Lokacin ya yi ido biyu da Ɗayyib da sauri ya rungumesa ya na yi mai kwataccen ya ya jiki?
Amsawa Ɗayyib ya yi haɗe da jajantamai abinda ya sameshi.
Bayan sun ƙara gaisawa, Ɗayyib ya tambayi Bashar garin ya ya haka tafaru? Da kwatancen Gidan Abduh Dhahab ya fara.
Ɗayyib mutum ne mai kaifin Basira da saurin Fahimta, wannan dalilin ya sa kai tsaye ya fahimci dole wanda ya gutsewar Bashar harshe yana da alaƙa da Gidan Abduh Dhahab.
"Sulaim ka gani, ko Abduh ko Mairam?" Ɗayyib ya tambayeshi a nutse. Shiru Bashar ya yi takaicin Ɗayyib na kamasa tayaya zai iya faɗamai bayan ya ambaci sunayen su dukka a lokaci ɗaya? Ganin ya yi shiru kamar mai tunanin yasa Ɗayyib umartar a nemo mai zane....
Bayan mai Zane ya iso..
Fuskar Abduh ya fara zanawa da kwatancen da Ɗayyib ya ke yi mai, Bashar ya ce ba shi bane an zana Sulaim da Mairam suma ya ce dukka ba su bane.
Bashar miƙewa ya yi yana kwatanta tsaho da shara, har ya gama kwatanta iyakacin abinda zai kwatanta babu wanda ya fahimcesa.
Dole Ɗayyib ba shi da zaɓi tunda sam yakasa fahimtar wanda Bashar yake nufi don haka ya sallami mai zane.
Mai zane yana tafiya shima ya bar Sashen zuwa na Jalal Mahaifinsa ransa babu daɗi.
Da Daddare
Bayan Ɗayyib ya koma Gida, har dare ya nutsa, ya kasa runtsawa har wajen ƙarfe ukun dare. Babu irin tunanin da baiyi ba game da wanda Bashar yake nufi amma yakasa gano wanene wannan. Ba don yana jin barci ba ya kwanta haɗe da rintse idanuwansa.
★washe gari da Asuba da tsananin ciwon kan rashin samun isasshen barci ya ɗora alolar Sallar Asubahi, har lokacin da tunanin wanda Bashar yake nufi maƙale a cikin zuciyarsa. Dama baya zuwa Masallaci, a tsakiyar ɗakinsa ya shimfaɗa abun Sallah ya tayar.
Ɗayyib yana cikin sallah raka'ar ƙarshe ƙwaƙwalwarsa ta harba. Shaidan ya samu damar wasa da hankalinsa haɗe da tuna masa abinda ya kasa tunawa
"shara? tsaho? Anya ba MALIK Bashar yake nufi ba?
WANENE MALIK;
MALIK hadimin Gidan Abduh Dhahab ne, kullum shi yake sharar harabar Gidan duk Safiya kuma Ɗa ne ga Amininsu Ɗayyib da Abduh Dhahab. Tun yana Yaro Mahaifinsa ya bawa Abduh Dhahab shi yake masa Hidimar share-share.
Bayan kai gawar su Abduh Dhahab makwanci aka naimi Malik da Iyayensa aka rasa sun gudu, babu wanda yakawo tunanin komai a ransa, sai tunanin sun gudune don tsiratar da rayuwarsu, tun da Malik yasan wasu sirrikan na Abduh Dhahab sama da su Ɗayyib da suke Abokanansa.
Malik ya na da tsaho na gaban kwatacce don dalilin tsahonsa yasa Abduh Dhahab yake tsananin sonsa saboda irin siffar Sulaim Ɗansa dana Mahaifiyarsa Nanaah yake da shi, ba irin Siffar Mutanen Yankin Tudu ba, Taƙaitaccen labarin Malik kenan...
Ɗayyib cikin rashin nutsuwar zuci da na gangar jiki ya sallame. Daƙyar ya taushi kansa har ya bari gari ya yi haske. Wani ƙulli ya ɗauka ya zura a aljihunsa, sannan ya bar gidan.
Wajen masu zane ya fara biyawa ya taho da har mutum uku, suka nufi Gidan Bashar..
Bayan sun haɗu a Sashen Bashar da kansa ya kwatanta mu su Malik suka zanashi kamar zai yi magana.
Bashar yana ganinsa ya miƙe jikinsa yana rawa haɗe da gyaɗa kai alamar shine.
Ɗayyib bai ce komai ba har sai da ya tabbatar ya sallami ma su Zane sun tafi, saura isu-isu ƴan Gida sannan ya matso kusa da Bashar yana kallon tsakiyar idanuwansa ya ce;
" Idan Malik da kowa yasan matsayinsa a Gidan Abduh Dhahab zai kamaka kai kaɗai akaf faɗin Yankinan ya yankemaka harshe to ba shakka kanada masaniya akan Kisan Abduh. Menene gaskiya?" Ɗayyib ya tambayi Bashar idanuwansu sarƙafe a cikin na juna.
Wani irin yaushi idanuwan Bashar sukayi haka tattaurar zuciyarsa. Bai ce komai ba sai ƙasa da ya yi da kansa domin tambayar