x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 20 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 57001 words
  • 60000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 754

07 Oct 2025
da bai taɓa faruwa ba barin Hadimai suyi shagalin bikinsu a Dhahab, don haka ku kula da kanku Naila, ba lallai na ƙara kiranki a waya ba domin ga dukka alamu Sir Malik yasan da zuwanki, idan har ya san da zuwan naki kamar yadda na faɗa to dukka maganganunmu da zarar mun shiga Dhahab tamkar a kunnensa mu keyi, haka tsarinsu yake kuma ina kyautata zaton shine Malik ɗin da kike nema. Ko da wani zai tamabayeki game da Yankin Tudu, karki nuna kinsani ko kin taɓa rayuwa a ciki. Karki sanar da Kaka abinda na faɗa domin zata iya sakin layi har Sir Malik ya gane mun tattauna dake, duk da zuwa yanzu nasan labarin muna tare ya je mai.

Ki barta tayi maganganunta domin nasan bamu da wani mugun abu da zata faɗa wanda zai iya kawomana matsala. Ki kula Naila domin daga yanzu zakiyita ganin abubuwan da zasu baki mamaki da tsoro matsawar dagaske shi ne Malik ɗin da kike nema."

Yasar yana gama faɗa ya gyara zaman rigarsa yana barin Motar. Zuciyarta tsabar bugu kamar zai fasa ƙirjinta ya fito.

Yasar ya na fita suma Naila suka fito ƙafafuwan Naila da take ƙoƙarin saitawa suna rawa.

Kaka kuwa har ƙanƙance idanuwanta takeyi wajen kallon rukunin Gidajen haɗe da yiwa Ubangijin da ya halicci talaka da mai arziƙi tasbihi.

Naila itama ƙarewa gine-ginen kallo takeyi tana ganinsu kamar furen da aka shuka.

A kan idanuwansu Yasar da Driver su ka nuna shaidar shigarsu Dhahab suka bar su Naila a tsaye. Suma ba su fi minti uku ba mota mai kyan gasken dayasa kaka ƙara ƙanƙame luggage ɗinta ya fito ɗaukarsu.

Kafin su shiga motar sai da aka caje kayansu da su kansu, Naila da Kaka sai zare idanuwa sukeyi, ƙarfin gwiwar da sukejin suna da shi na kawowa Yankinsu cigaba ko ta halin ƙaƙa nayin sanyi.

Naila da Kaka kallon duniya daban sukeyiwa inda zasu shiga Musamman da zancen Sarkin tsafin Yankin Tudu yake yawan faɗomusu, ashe shiyasa Allah Ya haramta duba, da yanzu bazasu wani damuba hankalinsu kwance.

Da Bismillah suka shiga motar da ƙamshinta ya sa Naila lumshe idanuwanta, yanayin fargabar da take ciki na barin zuciyarta. Mota ce da bata taɓa hasasowa kanta shiga irinta ba, ko ba komai suma zasu bayar da labari idan Allah Ya ƙaddara komawarsu Birnin Abyad.

Duk da Kasantuwarsu a cikin mota hakan bai hanasu yin Bismillah da addu'a yayin shiga gate ɗin Dhahab ba.

MALIK

A ɓangaren da idanuwansa suke Lumshe yana sauraran maganganun da Yasar ya gama faɗawa Naila ta na'urar dake maƙale a kusa da Yasar ɗin bai sani ba, miƙewa ya yi yana yana gyara zaman earpod ɗin kunnensa.
Yaƙi taimakon Naila ne saboda bayason dawo da hannun agogo baya, shiyasa lokacin daya gane Bushra ta shigar da takardun bogin Sufyan na naiman aiki kai tsaye ya ɗaukesa don gina rayuwar Naila, sai dai daga baya ya fahimci Sufyan fa ba Naila yakeso ba, kuma ba zai taɓa sonta tsakani da Allah ba.. lamarin Naila lamarine da bai isa yayimasa kutse kamar na ragowar Mutanen Yankin Tudu ba, saboda wasu dalilai, shiyasa ya haƙura ya zubawa komai ido, ko ranar da ya ganta a gidansu Yasar tsaf ya ganeta har a wajen Siyayya duk ya gane, amma bashi da zaɓi akan lamarinta banda ya zuba ido.

kwatsam satin da ya wuce Sashen Hidaman Gidan suka naimi alfarmar mai kitso zata zo tayimusu kafin su fara shagalin Biki acan gidansu, da ya bincika ya gano Naila ce zata yi musi, sai ya basu dama su yi bikin ma a Dhahab gaba ɗaya ko Allah zai sa a wannan karon ya samu damar takarar lamarin Naila..

Barkanmu da zuwa DHAHAB BABBAN BIRNIN ABYAD🤗

[8/8, 8:33 AM] nafisaaliyusasaal: SASAAL

2

A ɓangaren Sufyan
Duk kiran da Sumaya take ƙwalawa masa bai saurareta ba har ta cimmai.

"Menene dukka wannan Sufyan? I'm tired of all this, har sai tsahon wani lokaci zamuyi zaman farin ciki a tsakaninmu? kai ne kullum Baabanka da Ummeenka su kiraka tambayar kuɗi, yaya kake rayuwa? mai kakeyi yanzu? su yi ta tambayarka kamar baka da Iyali, it seems kamar ma ɓoyemusu kakeyi muna tare.

Yau ka firgita gobe ka zabura duk sai wahalar da ni kakeyi, yanzu gashi ka fito kanaji ina kiranka amma kayimin banza, gaskiya na gaji"

Sumaya ta faɗa cikin fushi.

"Ina ruwanki da kuɗin da suke tambaya, kuɗin ki ne? Okay so kikeyi kar su kira su tambayi lafiyata saboda ke ko? Kinsan ya ya akayi ma na zo nan eh!? Kin gaji da zama da ni kika ce ko? To kije na sakeki mun rabu nima na gaji" Sufyan ya ƙarasa faɗa ko a jikinsa, yana ƙoƙarin tarar Taxi .

Cikin masifa da hargagi Sumaya ta zagayo saitin fuskarsa ta ce;

"Daga ganin wannan Yankin naku dole ka zama Violet person! tunda na lura kamar da rashin zaman lafiya da wulaƙanta Ɗan adam aka gina Yanki..."

Marin da zai sauƙaƙawa Sumaya gane da gaske Sufyan Violet person ne ya sauke mata a dama da hagun fuskarta yana tura ta gefe, har sai da ta faɗi ƙasa dafe da ƙuncinta. Kafin ta yunƙura ya tari Taxi ya shige.

Ƙurawa Taxin idanuwa tayi kamar zasu iya dawo da Taxin baya.

Ganin dai da gaske Sufyan ya tsere mata bayan furta kalmar sun rabun da ta tsana, sai ta durƙushe a ƙasa tana kuka.

A haka ƴan uwanta da suka ji shiru suka sameta.

Tana kuka ta na fizgewar su ƙyaleta ta bi Sufyan suka turata cikin Mota.


A ɓangaren Naila

Daa can yawan surutu da rawar kai ba halinta ba ne, amma maganganun da Yasar ya faɗamata kafin shigowarsu Dhahab yasa ta ƙara nutsuwa tare da gumtse bakinta.

Basu yi wata tafiya mai nisa ba, suka sha kwana, anan rukunin Gidaje masu kyau suka bayyana, ba irin waɗanda suka wuto ba.

A hankali Driver ya dai-daita parking duka sauko.

Cikin rashin riƙe zance duk ƙanƙantarsa Kaka ta ce;

"Yanzu Bawan Allah menene abun hawowa Mota a nan? ji fa ga baki ga hanci, ku dai kam masu arziƙi akwai ku da son jiki wallahi" ta ƙarasa faɗa tana kallon hanyar da suka biyo.

Hannunta Naila ta kama haɗe da ɗan matsawa.

Maimakon tayi shiru tunda ta fahimci abinda Nailar take nufi sai ta ƙaracewa;

"au to nayi shiru."

Kamar kurma haka Drivern daya ɗaukosu yake babu magana babu murmushi balle dariya.

Da farin cikin Amira ta tarbi su Naila zuwa ainihin cikin gine-ginen.

Kai Naila a ƙasa su ka shiga saɓanin Kaka da take kallon komai dalla-dalla domin idan ta koma Birnin Abyad ta samu abun bayarda da Labari.

Tarba na ban girma aka yimusu a living room ɗin daya amsa sunansa. Kowa ya shigo sai ace wannan itace mai kitson da Sir Malik ya amincewa shigowarta Dhahab daga Birnin Abyad. Ko sun juya da sunan tafiya sai sun ƙara waiwayo sun kalleta, ga shi babu damar yin magana kar su je ana jinsu.

A wannan rana hutawa kawai su Naila su kayi sai ɗan hira sama-sama da Kaka take yi da yayar Mahaifin Ameera da take aurar da Ƴa.

Duk Hadiman da suke shigowa Masha Allah masu kyau da su, ga kyan fatar dake nuna kwanciyar hankali da wadataccen cima mai kyan da suke samu, uwa uba albashin mai tsokar da zai sauya rayuwar mutum da ahalinsa, amma fa banda munafiki da maci amana.

Masauƙin Ɗaki daban-daban aka yiwa Naila ita da Kaka amma suka nuna ɗaya ya ishesu.

Daga Naila har Kaka kallon ko ina na ɗakin da aka kaisu sukeyi kamar ba mazauna Birnin Abyad, to idan Hadiman Gidan suna da irin wannan gatan to ina ga mutan Gidan? Kaka ta tambayi kanta tana dariya.

Duk yadda Kaka take jan Naila da hira Naila ba tacemata komai ba, cikin takaici ta ce;

"Wai ni Naila wanene wannan Sir Malik ɗin da idan aka ambaceshi sai na ga sun ƙara waiwayo sun kallemu anya babu wata a ƙasa kuwa?"

Shiru Naila tayi kamar bata jita ba, wannan dalilin yasa ta fusata tana cewa;

"Wai ni Naila mai ya canzakine kin zama kamar wata kurma, sai surutu nakeyi kin ƙi kulani, ko don kinga zaki samu kuɗi shine zaki fara wulaƙantani tun yanzu?" Kaka ta ƙarasa tambayar tana kallon Naila.

Naila batasan sanda ta saki dariya ba har da kwanciya.

"Kaka har wani irin kuɗi zan samu da zan kasa yi miki magana, ko na wulaƙanta ki? Kaka idan aka je baƙonta kame kai akeyi, kuma na ga kamar kin manta da abinda ya kawo mu" Naila ta faɗa bayan ta tsagaita da dariyar da take yi.

Ɗan jim Kaka ta yi kamar mai tunani sai kuma ta zaro wayarta batare da ta ƙaracewa komai ba.

Har barci ya ɗauke Naila Kaka suna waya da Mallam yana yi mata bayani tare da ƙaramata wasu addu'o'in.

★Barcin mai daɗin da sukayi a lallausar katifar audigar dake Ɗakin da aka basu yasa suka makara sallar Asuba Kaka har da ɗan yawun barcinta a gefen kumatu.

Da sauri Naila ta watsa ruwa ta ɗoro alolar sallar Asubahi saboda Masallin da ta ke kyautata zaton a gidan yake har sun tayar da Sallah.

Da gari ya yi haske bayan an kawo musu lafiyayyen Abincin kari, sun karya, Ameera ta zo tafiya da Naila.

Yini sukayi tana kitsa musu gashin kansu mai tsaho da shaiƙi, duk hirarrakin da sukeyi Naila batasa musu baki ba, na dariya dai takan ɗan murmusawa lokaci zuwa lokaci.

Basu gama ba sai wajen ƙarfe taran dare.

A wannan dare cikin fargabar da ya ragewa su Naila saura kwana ɗaya su koma Birnin Abyad ba tare da sunga wani canji daga abinda suke zargi ba Barci ya ɗaukesu.

A rana ɗaya Ubangiji yake ƙaddara ɗaukaka ko kawo ƙarshen zaluncin da al-umma suka jima a ciki, duk da za'ayi shafe shekaru ana gwagwarmaya ba tare da anci nasara ba.

★Washe gari da Safe kamar jiya Ameera ta shigo kiran zamu gaisa da BARIRAH tace kitson da ta gani a kawunansu ya birgeta a kira Naila ta ganta ko zan yimata irinsa.

BARIRAH itace wacce aka wakilta daga cikin Dhahab ɓangarensu Malik domin ta isar da kyautar da Mahaifiyar Malik tayiwa Amarya saboda ita bazata samu damar fitowa ba.

Ta canza irin canjin da zaiyi wahala idan mutanen Yankin Tudu suka ganta su ganeta, ta ƙara fari da kyan jiki kamar ka saceta ka gudu, taƙama da izzarta da talauci ya danne a shekarun baya ya bayyana daga yanayin zamanta.

Kamar bata taɓaganin mai irin halittarta ba haka Naila ta nuna tare da gaisheta tanayin ƙasa da kanta alamar girmawawa.

A ɗan firgice Barirah ta amsa tare da furta tambayar da ta kasa dannewa;

"Ya ya sunanki? "

A taƙaice ta ce "Naila"

Sai da ta ƙara gyara zamanta tana matse yatsun hannunta da zobunan zinare ke jere waje ɗaya ta ce;

"Daga wani Yanki kike bayan Birnin Abyad, ina nufin asalin ƴar ina ce ke?"

Cikin ladabin da ya ɓoye rawar da jikin Naila yake yi ta ce;

"Birnin Abyad shine asalin Yankin da na fito"

Ba ta gamsu ba tace akira mata Kakar Naila.

WAIWAYE;
Shekarun baya rashin jituwar Mahaifin Naila da ƴan uwansa yasa Mahaifinsa bayason Mahaifiyar Naila, wannan dalilin yasa ya hana Kaka zuwa Gidansu Naila, a waccen lokacin sai ya ce ita take zuga Mahaifiyarta basa jituwa da Matan Yayyan Mijinta tunda ba ita ta haifesu ba. Wannan dalilin yasa su SIMBI da BARIRAH ba su wani san Kaka ba, sannan kuma daga Shekarun da suka bar Yankin Tudu zuwa yanzu Kaka ta ƙara tsufa, irin tsufan da shekarunta ba su kai ba, saboda jarabawar da yayita samun mu.

DAWOWAR LABARI
Wannan dalilin yasa ko da Kaka ta fito Barirah bata ganeta ba, itama Kaka da bawani saninta tayi ba sam bata ganeta ba.

Ko da ta tambayi Kaka, bayan Kaka ta gaisheta kai tsaye Kaka tace mata su asalin ƴan Birnin Abyad ne.

Cikin rashin gamsuwa da kuma son ƴar uwarta Simbi ta bambance mata da gaske Naila ce ko ba ni bace ta ce;

"Salon kitson ki ya birgeni matuƙa, kuma an sanar dani lokacin tafiyarku ya yi, inason ku ƙara kwana biyu gobe sai kiyimin jibi ku wuce. Hadimai zasu rako ki."

Bata jira amsar Naila ba ta miƙe tana sharce gumin daya tsatsafomata a goshi duk da na'urar sanyaya wajen da yake aiki 24/7.

Bayan ta kai ƙofa sai da ta ƙara waiwayo ta kalli Naila sannan ta bar living room ɗin.

Su na shiga ɗaki Naila ta zube akan katifa tana dafe saitin zuciyarta.

Tambaya Kaka ta titsiyeta da shi;

"Naila wacece wannan? sam banyarda da ita ba, ki yimin bayani menene ya haɗaku? kinsan ta ne a wani wajen? maiyasa take son sanin ko daga wani Yanki muke?"

Rasa tambayar da zata fara amsawa a Kaka tayi. Don haka ta fara bata labarin wacece Barirah ba tare da tsoron Malik yana jin su ko baya jin su ba kamar yadda Yasar ya faɗamata, tunda Ubangijin da zai karesu Yana tare da su.

Manyan idanuwanta Kaka ta zaro kamar zasu zubo ƙasa

"Barirah ƙanwar Malik?? tayaya Naila????"


MALIK!

Duk maganganunsu Naila da abubuwan da Barirah ta aikata duk bai samu damar saurara ba saboda uzurin da ya taso mai.


Kafin ya tafi uzurin da ya taso masa sai da ya kira Bushra ya kwantar mata da hankali ta juyemasa labarin rayuwar da Naila tayi da Sufyan da kuma wanda take kanyi da Kakarta.

Kamar yadda yafi tafiya a lokutan Asubahi kafin ketowar alfijir ko Cikin dare, a yau ma haka ya yi. Baƙaƙen kayan da ya fi amfani da su ya sanya hatta gilashinsa da ya sakaya idanuwansa dashi baƙine. Da ƙaramin Luggage ya bar Dhahab zuwa nahiyar Turai.

YANKIN KAHALA BIRNIN HONOLULU JAHAR HAWAII

Lemon da aka ajjiyemai Malik ya taɓa haɗe da ɗanyi balance yana danna wayarsa.

Ƙarfin ƙamshi da takun dake ƙara kusantosa ne yasa ya ɗan zabura yana gyara zamansa haɗe da zame baƙin tabaran fuskarsa.

Balmin Shirt dark blue, da Black three quarter trousers Matashin da ya bayyana a gaban Malik yake sanye da su.

Zama ya yi a Couch ɗin da ke kallon na Malik suna fuskantar juna.

Malik zamansa ya gyara tare da haɗe yatun hannusa waje ɗaya bayan ya tattaro nutsuwarsa sannan ya ce;

"Barka da yamma"

Maimakon amsa fararen idanuwansa dake kan fuskar Malik ya lumshe, wanda a wajensa shine a madadin amsar gaisuwa.

A hankali Malik ya ɗago fuskarsa bayan ya ƙara saita nutsuwarsa, cikin daƙiƙa biyu ya ƙarewa Matashin da ƙirar jikinsu yake kusan iri ɗaya kallo, sai ɗan tsaho da Matashin yafishi, kansa ya mayar ƙasa a hankali ya motsa laɓɓansa da tambayar "ya ya mai jiki?"

Tambayar ya ya mai jikin da Malik ya yi masa ne yasashi ƙara ɗago idanuwansa yana kallon cikin idanuwan Malik.

Da ɗaurarrariyar fuskarsa mai tsananin kyan gasken dake ɗauke da idanuwa masu haske ya cigaba da kallon Malik ba tare da ya ce komai ba.

Kasa jurewa kallon fuskarsa yasa Malik yin ƙasa da nasa kan yana murza Diamond Bracelet ɗin hannunsa.

ya ɗauki daƙiƙu yana karantar Malik kafin ya furta;

"Alhamdulillah" da muryasa mai tsada a wajen mutane da daɗin sauraro ga wanda ya samu ji😄

KAFIN MU SAN WANENE WANNAN MATASHIN BARI MU SAN AINIHIN DALILIN DAYA JANYO KASHE-KASHE A MARAUTAR YANKIN TUDU DA KUMA SU WANENE SUKE AIKATA SHI, SANNAN MUSAN SHIN DAGASKE SU ABDUH DHAHAB SUN MUTU, KO KUWA SUNA RAYE KU BIYO NI;







[8/8, 8:34 AM] nafisaaliyusasaal: SASAAL

3

Kamar yadda Kaka ta taɓa bawa Naila labari a baya a zamanin mulkin Sarki Musa ya yi sauƙin kai ga mutanen Masarautarsa da na Yankinsa wannan yasa kowa yake sonsa.

Jamil Kakan Jalal shine Aminin Musa tare suke komai, sai dai daga lokacin da Sarki Musa ya tura Abdulyasar Babban Birnin Abyad wajen abokanan hulɗarsa da sunan naiman ilimi ya dawo da dukiya har ya samu laƙabin Dhahab, komai ya canza a ɓoye a ɓangaren Jamil acewarsa;

"mai zaisa Sarki Musa ya munafurceni ya kai ɗansa inda zai zama Attajiri amma bai haɗa da nawa ƴaƴan ba?"
Wannan arziƙi da Abdulyasar ya dawo da shi, shi yazama tsatsa a zuciyar Jamil da zuri'arsa ba tare da kowa ya sani ba.

Jamil mutum ne mugun gaske kuma mai riƙo da kafiya. A kwai fahimta sosai tsakaninsa da Sarki Musa, amma wannan dawowar ta Abdulyasar Dhahab da arziƙi mai tarin yawa daga Babban Birnin Abyad sai ya gurɓata son dayakewa Sarki Musa, a take ya fara shirya kaishi ƙasa duk da bayanin da Sarki Musa ya yi mai dayaga alamar kamar baiji daɗi ba;

" Ni ban tura Abdulyasar domin ya naimi kuɗi ba balle ya tara arziƙi. Na turashi ne domin ya naimi ilimi ya kuma samu kariya daga ragowar Iyalina" maganganun Sarki Musa tamkar rainin hankali suke a wajen Jamil da kuma ƙara tunzura zuciyarsa, amma bai nuna ba ya barwa zuciyarsa.

A hankali shida ragowar Iyalin Sarki Musa da suke ganin ya fifita Abdulyasar akansu suka yi masa sihirin da ya sashi kwanciya dogon jinya har Ubangiji Ya ƙaddarar ajalinsa.

Cikin ikon Allah, Allah Ya bawa Jamil tsahon rai har Ubaidullahi Dhahab Ɗan Abdulyasar ya ƙara zama mai arziƙi akan idanunsa. Wannan yasa ya yi alƙawari tare da alwashin yaƙi da wannan Laƙabi da suke amfani dashi, har ƴaƴansa ya cewa; "laƙabin Dhahab(Zinaren) da suke yiwa kansu sai ya zama Tarihi a Yankin Tudu nayi alƙawari! Kuma ko bayan raina ku sanar da jikokina su shirya Yaƙar Dhahab har sai sun ɓatar da fuskokinsu a Yankin Tudu da duniya gabaki ɗaya. Tunda Musa ya ci amanata to nima zanyi ramuwa gayya gareshi, ramuwa mafi ciwon da babu kamarsa!"

Jamil bai ɗora zuri'arsa akan komai ba sai hassada ƙyashi da tsananin mugunta tare ramuwar gayya ga duk wanda ya cucesu. Da haka ya raini Mahaifin Jalal, shima Maihaifin Jalal da haka ya raineshi, shima Jalal ya raini Ɗayyib a haka Ɗayyib kuma ya kasa rainon Sufyan daya fita Zakka.

Kamar yadda Jamil ya yi alƙawari kuma Allah Ya cikamasa Kafin ya koma gareSa ya girbi abinda ya shuka, Jamil bai bar duniya ba sai da yaga gawar Ubaidullah, kuma ya mallaki filin mafi girma a kaf faɗin Yankin Tudu ya haɗa har da na Al'umma a ciki...

Tun suna yara aka shirya Abotar Ɗayyib da Abduh Dhahab saboda da Ɗayyib zasu yaƙi Abduh. Ɗayyib tun yana yaro akwai basira da nuna kamar bai san komai ba kuma shi babu ruwansa a kan duk wata badaƙala dake faruwa a Masarautarsu wannan dalilin yasa Abduh ya yarda dashi irin yarda dake tsakanin Aminai. Irin wannan Abotar Ɗayyin yaso ƙullawa tsakanin Sufyan da Sulaim sai dai Zaren ba kalar yadin ba ne!

*Menene