Simbi Babban Birnin Abyad, ta yi yunƙurin bincike don tabbatar da ainihin abinda yasa Yasar ya iya yin kasadar tararta kai tsaye saboda matsalar Naila kawai da kuma abinda ya kawo Nailan Birnin Abyad, kafin komai ya lalace. Ta hanyar kiran Bushra da take sa'arta, wacce suka zama tamkar zuri'a ɗaya a Dhahab, kuma take kyautata zaton zata iya yimata bincike akan Naila, saboda ba ta so take wajen Naila da kanta ta ganeta. babu ja Bushra ta amince dama kuma tana Birnin Abyad itama bata koma ba.
NAILA ; kamar kullum da sassafe ta yi ayyukanta bata wahalar da kanta wajen girkawa Sufyan Breakfast ba saboda ba ci zaiyi ba, idan ta yi a wajen yake barmata kayanta.
Wanka ta yi ta ɗauko Abayar da ta zamemata tamkar ta gado ta saka, saboda tana jin tsoron saka wanda Yasar ya aikomata da su gudun duka da ga Sufyan, domin wanda Sufyan ɗin ya siyomata masu sauƙin kuɗine marasa quality duk sun zaizaye wa su guraren ma duk sun yage.
Bayan ta gama saka kaya turare ta fesa saboda customers kamar yadda Rufaida ta ɗorata a kai tuntuni saboda a wasu lokutan jikin mutum ya kan ɗanyi tsami wanda hakan ya ke takurawa ma su zuwa kitso musamman idan suka ɗora kansu a tsakanin ciyoyi.
Sana'ar da ya zamemata jiki ko da yaushe ta zauna yi( tunani) wa ni lokacin ta saki kuka wa ni lokacin kuma ta yi dariya. Ta na cikin tunani ta ji ana ƙwanƙwasa ƙofa. Da hanzari ta miƙe ta nufi ƙofar, ta buɗe.
Bata taɓa ganin fuskarta ba, don haka tayi mata tarba na musamman tana washe haƙoran da suke ƙara bayyana ramata. Ƴar gayu ce kuma da alama daga Gidan arziƙi ta fito.
A lokutan baya Naila ba ta da yawan surutu ba ta da yawan dariya irinna rashin kamun kai, amma tunani da ƙunci rayuwa suka sa ta zama mai tsananin surutun da ita kanta batasan tanayi ba, ga dariya da take yawan yi na rashin dalili wanda ya zarta a kirashi fara'a.
Ba mai yawa wacce yazo kitson ta ce ta na so ba, don haka ta yi mata irin yadda take buƙata.
Da ta tashi tafiya kuɗi mai yawan da daa abayane ta bawa Naila su ihun murna zatasa saboda tana da yaƙinin zata tara ta gina Gobena da su, amma yanzu Sufyan ya na dawowa zai ƙwace.
Rashin fara'ar Naila da yadda ta yi ƙasa da kaine yasa wacce ta zo kitson ta magantu;
"Baiwar Allah ko kuɗin ne ba su yi miki ba, na ga kamar ranki a ɓace" ta ƙasara faɗa tana karantar yanayin Naila.
A hankali Naila ta ɗago idanuwanta da ƙwalla yasa ta ke ganinta dishi-dishi ta ce;
"Na gode! na gode!! Allah Ya biyaki, amma dan Allah daga ina kike na baki kuɗin ki taramin?" Naila ta ƙarasa faɗa kamar wacce batasan me take yi ba.
Idanu ta zaro ta ce; "ta yaya ba ki Sanni ba zaki bani ijjiyar kuɗi bakya tsoron na gudu da su? saboda me ke bazaki ɓoye a ɗakinki ba ko ɓarayi su na damunku na sanar da jami'ai?"
Kai Naila ta girgiza hawayen da bata iya yiwa idanuwanta shamaki da su ya tahomata.
Idanuwa wacce ta zo kitso ta ƙara zarowa wannan karan da mamakin bayyane a saman fuskarta, cikin tashin hankali ta ce;
"Menene matsalar Baiwar Allah?"
Cikin kuka Naila ta ce;
"Inaso na koma Yankina amma bana iya tara kuɗi Mijina kwashewa ya ke yi domin gina gobensa, ya na dukana kullum, ki taimakamin kinji Don Allah nasan kinfi ƙarfin su bazaki Gudu da shi ba"
kamo Naila ta yi zuwa jikinta tana shafa bayana ta ce;
" Ya ya sunanki kuma ina ne Yankin ku? Ko zan iya taimakawa"
Da sauri Naila ta ce ; " sunana Naila, yankin mu shine Yankin Tudu"
Naila tana jin lokacin da zuciyar wacce ta zo kitso wajenta ya ya buga da sauri, saboda kanta dake jingine har lokacin a saman Kafaɗarta.
Da sanyi murya wacce ta zo kitso wajenta ta ce;
" Maiyasa ba zaki bawa Mijinki kuɗinki ya gina gobensa ba, gina gobensa ai tamkar gina na ki ne"
Kuka Naila tasa tana roƙonta ganin kamar ba ta fuskanceta ba.
Gwauron numfashi ta sauke, tana kallon Naila ta ce;
"Zan karɓa amma sai kin sanar da ni dalilin dayasa baƙyason mijinki ya mori kuɗinki alhali kuna tare bai sake ki ba"
Kamar wacce take jira haka Naila ta soma sako mata zance da wanda ta tambaya da wanda bata tambaya ba.
Da Naila ta gama labari
Ba ta ce mata komai sai bayanta da ta ɗan bubbuga tayi mata sallama ba tare da karɓi kuɗinba.
Ba kowa Ba ce tazo wajen Naila kitso ba fa ce Bushra wacce Simbi ta Turo, kuma ta naɗi dukka hirarsu da Naila.
SIMBI; Recording ɗin da Bushra tasa mata, da yake Bushra gwanar tausayi ce ta kuma sauraro tana kuka.
Daga wannan ranar kullum sai Simbi ta tura Bushra Gidan Naila da sunan tayata hira a haka suka samu dukka bayanan da suke so, amma har lokacin Simbi ba ta tuna fuskar Sufyan ba tunda sun bar Yankin Tudu ya na yaro.
Har lokacin komawar Simbi Dhahab ya yi, ba su samu damar bincikar Sufyan ba, don haka ta bar ragowar aikin a hannun Bushra ta tattauna da Yasar a sirrince domin ya taimaka musu wajen bibiyar Sufyan.
NAILA
Dalili yawan tambayoyin Bushra da yadda ta saki jiki da ita duk da kasancewarta ƴar masu hali yasa Naila ta fara zargin ko Sufyan ne ya turota, da ta fara zargin haka sai ta daina bata kuɗinta ya ɓoyemata ta nuna mata ta sauko ta fison Mijinta ya gina gobensa domin su tashi tare su tsira tare.
Babu kalar tambayar da Bushra batayiwa Naila ba akan wasu sirrika na Sufyan da ta gano amma Naila taƙi faɗa saboda tsoro.
YASAR; kamar yadda ya yi zargi bayan barin wajen Simbi za'a bibiyi bayansa haka kuwa a kayi, A sirrince ɗaya daga cikin masu tsaron tafiyar Simbi ya bi bayansa ya bincika babu makitsiya a gidan, daga haka ya ɗora mizanin maganganunsa akan shirme kamar yadda sukayi zargi tun farko.
Da sunan Ganin likita Bushra ta samu keɓewa da Yasar daya koma gaban Mahaifansa da zama saboda tsaro.
Alƙawarin naimarmasa aiki ta yi matsawar ya gayamata Ɗan gidan wanene Sufyan a Yankin Tudu.
Ko batayi alƙawarin cikamai burinsa na samun aiki a Dhahab ba ya yi alƙawarin taimakon Naila ta koma Yankin su ta kowacce fuska.
Bai ɓoyewa Bushra komai ba, ya kuma roƙeta ta riƙe amana, kuma a shirye yake domin ba da gudunmawa idan hakan ta taso.
BUSHRA
A wannan rana kwanan tunani Bushra ta yi. Matsawar Simbi tasan Sufyan jinin masarautar Yankin Tudu ne, to ba shakka ba za ta taimaki Naila ba, dama kuma can ba wai tana son taimakon Naila ta wata fuskar bane daban sai na mayar da ita Yankinsu. Amma ga Bushra ba irin wannan taimakon takeson yi wa Naila ba, wanda zatayi farin ciki na har abada takeson yi mata.
Ko da sukayi waya da Simbi kai tsaye ta sanar mata bata gama bincike ba.
A cikin kwana biyu Bushra ta binciko Sufyan ciki da wajensa har da soyayyarsa da Sumaya da abinda yakeyi da kuɗin Naila saboda ta samu tabbacin baya sana'ar komai.
Ta na son Naila taje Dhahab amma ta yaya?
Ta na kuma son Sufyan ya ɗanɗani azaba ƙiri-ƙiri irin ɗanɗanar da zai gusar da nutsuwar zuciyarsa yana ji yana gani, amma dole sai ya riski Dhahab to amma ta yaya riskarsa Dhahab zai yiwu?
Tsakiyar Dare ta naimi layin Mahaifanta, sunyi magana ya fi na hour huɗu, kafin ta suyi sallama, ba tare da jinkiri ba, ta dannawa Yasar kira. Suka tattauna yadda zasu ɓullowa Sufyan.
★washe gari Bushra da ke lulluɓe cikin shigar larabawa ita da Yasar suka kaiwa Sufyan ziyara Makaranta. Sufyan tsaf ya gane Yasar, wannan dalilin yasa ya tsamke fuskarsa ya na bawa Sumaya umarnin ta jirasa yana zuwa.
Da suka keɓe bayan sun Gaisa sama-sama
Suka ce masa takardunsa daga kan na primary har na secondary suke so da kuma shaidar takardun jami'ar da ya ke zuwa zasu samar masa aiki a Dhabah amma sai takardun Makarantarsa sun kasance na Birnin Abyad, za kuma a samar mishi sabon jami'a a can idan ya kama aiki.
Kwaɗayin da burin duniya su suka taru suka lulluɓewa Sufyan ido ya kasa tantace cuta da so da kuma tantance ina ne Dhabah maiyasa suka zaɓi naima mai aiki. Jikinsa na rawa ya tashi gefe ya kira Mahaifinsa.
Ɗayyib ihun murna yasa ba tare da tsayawa saurarar sunan Ma'aikatarba ya kira amininsa.
Ɗayyib ya na kiran Amininsa ya sanar da shi buƙatarsu
Kai tsaye amininsa ya sanar da shi bashi da hanyar da zai samarwa Sufyan takardun bogin primary da sakandaren ƙasar Abyad.
Ko da Ɗayyib ya kira ya sanar da Sufyan a take jikinsa da ke rawar murna ya yi sanyi laƙwas.
Jiki a sanyaye ya dawo wajensu Yasar ya yi musu bayani. Bushra da ke tantance son banza irin na Sufyan kai tsaye ta ce zata samar mai amma sai ya yi mata alƙawarin barin matarsa ta naimi jami'a ya kuma daina karɓe mata kuɗin sana'arta.
Son banza bai sa Sufyan ya tambayar kanshi ina Bushra ta samu labari ba, ya ce ya amince amma a iya bakinsa ya tsaya, domin har cikin ransa ya yi alƙawarin jami'a sai dai Naila ta ga anayi....
A cikin kwana biyu Bushra da ƙarfin ikon Mahaifinta a ƙasar Abyad suka samarwa Sufyan takardun bogi.
Tare da Takardun Yasar Bushra ta shigar ta hanyar yanar Gizo tare da addu'ar dacewa,.domin batason Malik yasan aikinta kai tsaye duk da akwai kyakkyawar fahimta a tsakaninsu.
Duk wannan wainar da ake toyawa Naila batasan ana yiba, sai shige da ficen Sufyan da take gani a ruɗe.
BUSHRA
★washe gari abinda ya shigar da Bushara Toilet ya fi sau uku shine Ɗaukar Sufyan aiki tare da wani irin albashin da ya tsoratata. Ba ita kaɗaiba dai-dai da Mahaifinta ya shiga zullumi da ta sanar mai, ya kuma gano akwai babban Yaƙi domin ko rantsuwa ya yi bazai yi kaffara Malik da ya ɗaukesa aiki ya gano wanene SUFYAN.....✍🏻
[7/23, 9:38 PM] +234 702 541 3080: 🔥ZINARE🔥
SASAAL
17
Har yamma ta yi liƙis nutsuwar Bushra bai dawo jikinta gaba ɗaya ba. Idan wayarta ta yi vibrating har firgita takeyi.
Dole zancen Mahaifinta ya zama gaskiya banda haka Sufyan bai cancanci ya samu aiki lokaci ɗaya haka ba, dama dai Yasar ne da takaddunsa suke nunawa gogewarsa.
Har dare Mahaifinta bai kirata ya samu kira daga saman Dhahab ba wanna dalilin yasa ta ɗan samu nutsuwa a ranta, amma duk da haka sai da ta kira Simbi.
Yanayin muryar Simbi da shawarar da take bata na ta dawo ta ƙyale Naila domin ita ta fasa taimakonta ne yasa Bushra ta ɗan jo sanyi a ranta, saboda da an samu matsala zata ji a bakin Simbi, sai a lokacin ta samu sukunin kiran Yasar tayimai bayani.
Shawarar su haɗu washe gari a Gidansu Naila suka yanke.
NAILA; tunda ta ɗauke yardata a kan Bushra ta miƙawa Allah komai tare da alƙawarin ba zata ƙara naiman taimako a wajen kowa ba.
A tsakanin kwana da wuni Sufyan sam bai tambayeta kuɗi ba, kuma a kan idonsa ta kitsa kan mutum biyu.
Bata yi mamaki ba, domin ga dukkan alamu akwai gagarumin al'amarin da ya tisosa a gaba.
A daren cikon kwana na huɗun da ya yi da daina tambayarta kuɗi, kuma itama bata ba shi ba, ya kirata ɗakinsa.
Cikin muzurai yake sanar da ita samun aikinsa dalilin tonon Asirin da ta yi masa a wajen Bushra ɗaya gano daga baya, to ga kuɗinta ya barmata amma ta jira hukuncin da zai biyo baya.
Har ya gama kumfar bakinsa da maganganun izgilancinsa Naila batace masa komai ba.
Daga ƙarshe ya jamata kunnen karta kuskura Bushra da Yasar su naima mata jami'a ta yarda ta je. Idan kuma ta saɓawa umarninsa wallahi sai ya hukuntata da hukuncin da har ta mutu bazan manta da shi ba.
Babu abinda ya motsa daga jikinta balle ya gane na fahimcesa ko bata fahimcesa ba, takaicin hakan yasa ya haureta da ƙafa ya na faɗin;
"Fice min daga ɗaki, sha-sha-sha kawai ai gashi garin ki tonamin asiri kin janyomin daukaka, kuma wallah na rantse bazaki ci ko sisi daga arziƙina ba"
Sam surutansa ba su dameta ba, tunda zai barta ta dinga tara kuɗinta. Kuma ko su Bushra sun tambayeta tanason zuwa jami'a da babban murya zata amsa "eh". Kanzil ba tace ba har ya gama masifarsa ta bar Ɗakin.
SUFYAN; ranshi fari fes yake ji, sunan ma'aikatar da za'a samarmai aiki na kai kawo a cikin zuciyarsa, anya babu wani sirri a cikin wanda ya kara DHAHAB(ZINARE) a cikin sunansa, Abdulyasar Dhahab Ubaidullahi Dhahab, Abduh Dhahab, duk ba su bar duniya ba sai da suka zama ababen koyi, ga shi ya kuma samun wani mai arziƙin a Babban Birnin Abyad shima Dhahab. Tabbas! A kwai wani ɓoyayyen abu a cikin wannan sunan tunda shi kanshi asalin DHAHAB(zinare) ba abun yadawa bane abune da ake kokawa a kansa. Kakanninsa da suka ƙi kwantar da kai subi Abdulyasar Dhahab tun farko ai gashi za su mutu babu wanda ya sansu sai ƙananun muƙamin Sarautar da suke taƙama da ita. Anya bazai koma Sufyan Dhahab ba kuwa? Dariya ya bawa kanshi yana shafa sumar kanshi, tare da ayyanawa ransa irin girman kuɗin da zai dinga kashewa sumarsa, duk da dai bai san iyakacin albashin da za'a biyasa ba. Yanzu matsalarsa ita ce Naila, hanyar da zai rabu da ita ya korata Yankin Tudu kawai yake nema ba tare da su Bushra da Yasar sun ga baƙinsa ko butulcewarsa ba, tunda ko yana so ko baya so Naila ce sanadi. Da Sumaya yake son su tare a Babban Birnin Abyad idan komai ya yi masa yadda yake so.
Tuna irin abubuwan da zai yi idan ya fara aiki yasa ya tashi yana taka rawa.
NAILA; bayan ta koma ɗaki kuɗinta ta ƙara adanawa tana lissafa irin kayan da zata siyawa Kaaka duk ranar da Allah ya ƙaddara tafiyarta, godiya tayiwa Allah sannan na godewa Bushra tare da alƙawarin naiman yafiyarta duk ranar da Allah Ya haɗata da ita abisa munana mata zato da tayi.
Ranta babu damuwar komai sai godiyar sauyin da ta fara samu nayi alwalar kwanciya barci, cikin abinda bai gaza minti biyu ba, bayan tayi addu'o'i barci mai nauyi ya ɗauketa.
★washe gari iyakacin abincin cikinta ta girka.
Sufyan fita ya yi ya jubgowa kanshi siyayyar lafiyayyen Breakfast daga kuɗinta da yake tarawa a Banki.
Daga dawo
Ko kallonsa batayi ba ta tattara na bar living room ɗin. Hakan da tayi ba ƙaramin haushi ya bashi ba, don haka ya hau zage-zage da gorin ai ta kusa daina ganinsa sai ta dafa gidan ta cinye ni kaɗai idan ta samu kuɗin biyan haya, domin wallahi shi bazai biya ko sisi ba, ko ta tattara ta koma Yankin Tudu tunda bata da kunya ta fara rainashi bazatw roƙeshi ya sammata abinda ya siyoba ta sawa kanta girman kai alhali ita ba ƴar kowa ba ce face ƴar Madinkin da ya ke talakan fitik ta sanadiyyar rashin kuɗin zuwa Babban Asibiti ciwon ciki ya kasheshi.
Kamar babu mutum a gidan haka Naila tayimai shiru, amma a ɗaki kuka takeyi zuciyarta na suya.
Bai daɗe da gama Breakfast ba su Yasar suka iso Gidan.
Jiki na rawa ya shigo da su Living room yana baza kunnuwar jin dalilin zuwansu har Gida. Ba su fara bayani ba sai dai suka bashi umarnin kiran Naila.
Da ya shigo kiran Na'ilah sai da ya
Na mata kunnen karta kuskura ta saɓawa abinda zai ce ya yi mata, sannan ya kamo hannunta muka fito tare.
Naila tana hangosu ta ƙwace hannunta ta nufi Bushra.
ƙam ta rungume Bushra tana nanata kalmar ta yafemata ta zargeta da cin amanarta ashe tanadin da ban taɓa tunani ba tayimata.
Sufyan harara yake watsowa Naila ta ƙasan ido saboda ya matsu ya ji dalilin da ya kawo su. Sai da Naila ta nutsu tukunna sannan Bushra ta fara yi mai bayanin samun aikinsa da kuma irin albashin da za'a dinga biyansa duk wata.
Duk yadda Sufyan ya so yaja aji ko ya kame kansa kasawa ya yi ya miƙe zurbur yana zaro idanunsa, kafin ya fashe da kuka yana yi musu godiya. Kai suka girgiza a tare suna haɗa bakin faɗin;
"Naila zaka yiwa godiya dalilin gwagwarmayarta kakai matsayin da kake kai a yau, don haka karka manta alkhairinta domin shine tsanin nasararka" da gigin farin ciki ya fara nanata "Naila na gode! na gode!! na gode!!!" A tunanin Naila Sufyan ya sauya kenan don haka ta taso ta ƙanƙamesa tana yiwa su Bushra godiya, suma murmushine kwance a saman fuskokinsu.
Bushra bata nanata naimarwa Naila jami'a ba tunda sun riga sun yi maganar da Sufyan tun farko kuma ya nuna ya amincewarsa. Bayan wani lokaci Yasar yayimusu sallama Bushra kuma ta zauna Naila ta kitsa mata kanta. Shima Sufyan barin Gidan ya yi da sunan zuwa Makaranta, zuciyar Bushra na suya tabi bayansa da kallo saboda ko shakka batayi wajen Sumaya zaije. Kenan Sufyan ba zai taɓa sauyawa ba.
Naila da bata fahimci komai ba bakinta a washe take yiwa Bushra kitso tana janta da hira.
A hankali a hankali hirarsuu ta faɗo kan Sulaim da yadda suka haɗu da sanadiyyar mutuwar Mahaifiyarta da ko Yasar Naila ba ta faɗawa ba, ta dai ce masa Mahaifiyarta ta mutu.
Bushra tari ne ya sarƙeta ta hau yi babu kakkautawa, sannu Naila ta fara yimata kafin ta wuce kitchen ta ɗauko mata ruwa.
Bayan tarin ya tsagaita sai ta yiwa Naila murmushi ta ce;
"idan har kin aminta dani inaso ki ɗaukomin hoton Sulaim na gani."
Da hanzari Naila ta miƙe tana dariya na nufi Ɗakina.
Bayan ta ɗauko ta miƙawa Bushra,
Bushra ta ɗebi mintina tana kallon hoton, sannan ta miƙamin tana janyo gilashinta mai ɗan duhun da Naila take iya ganin idanuwanta amma ba sosai ba ta manna.
Naila ba ta kawo komai ba a ranta ta hau yaba gilashin da ƙoda irin kyan da ya yi mata.