x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 16 - ZINARE Book 1 Complete Hausa Novels by Nafisa Aliyu Salsal.txt

  • 45001 words
  • 48000 words
  • Out of 87720 words

Category: Home Of Novels

Views 748

07 Oct 2025
tausayin Naila da ta fita shaƙar takaici da rashin samun rayuwar Ƴanci na tsarga mata, "ashe haka Naila take ji? Wallah na cuci kaina kaicona!" Ta faɗa ƙasa-ƙasa cikin kuka.

Bayan fitar Sumaya Ɗayyib ya mayar da kansa kan Sufyan. Wayar Sufyan ɗin ya miƙamai.
Babu wasa a fuskar Ɗayyib kamar ba Mahaifinsa daya sani a baya ba.

Jiki a sanyaye Sufyan ya kunna ya ajjiye yana jiran umarnin da zai biyo baya.

"A baya ina lallashinka domin ka yi min biyayya akan abinda kai ne zaka samu cigaba ba ni ba, amma ka bijiremin, to a wannan karon ba cigabanka bane kai kaɗai cigabanmu baki ɗaya, mun gayyato malami daga wani Birni, ya kuma shaida mana Kabeer ba shine Uban gidan ka ba, rufa ido ya yi mana, ba wai don ban yarda da shi ba, sai don na ƙara tabbatarwa nakeson ka kira wanda ya miƙa katin gayyatar bikinka wajen GM ɗinku ka ji dagaske ne ko a'a"

Sufyan yaso ya musa, amma tuna irin yankar da ya sha yasa ya fara lalubo number jikinsa yana rawa.

Bugun farko aka ɗaga da Muryar jimamin da ya nuna andaɗe ana naiman mutum ba'a samesa ba. Bayan sun gaisa da hanzari Baturen yake tambayar lafiya, bai dawo aiki ba ko fushi yake yi GM bai samu halartar taron shagalin bikinsa ba, ya yi haƙuri uzuri ne ya tareshi, ga ayyuka ta ko ina a office amma ba bu shi, don Allah ya dawo.

Daga Sufyan har Ɗayyib ajiyar zuciya suka sauke mai ƙarfi kafin Ɗayyib ya tashi ya rungume Sufyan cikin kukan farin ciki ya ce;

"ɗana Sufyan ina mai neman afuwarka, sai dai banason wannan damar ya zama abin sakankacewa garemu, inaso ya zama fitilar haska mana asalin wacece ta ƙara dawo da Dhahab a tsakanin Nanaah Faɗima da Aysha" Sufyan da yake son tambayar su wanene Faɗima da Aysha shiru ya yi tuna Mahaifinsa zai iya tuhumar mai yasa bai sansu ba.

A haka Ɗayyib ya share hours ya bar Sumaya zaune a waje ba tare da damuwar komai ba. A wannan yanayin Hindu ta iso Asibitin kallon inda Sumaya take batayi ba balle ta amsa gaisuwarta.

A wannan karon ma ɗari bisa ɗari Ɗayyib ya amince da batun da Hindu ta zo dashi, tare da bawa Sufyan umarnin sakin Sumaya da zarar sun koma Birnin Abyad ya ajjiye maganar Soyayya ya fuskanci gobensa. Sai dai dole sai sunyi taro na musamman a kan yadda za'a shayar da Naila sihirin da Hindu ta zo da shi.

Shi dai Sufyan kai kawai yake ɗaga musu saboda tsoron yin magana ma yake yi.

Tun a baya kowa yasan mutanen Yankin Tudu da son kansu da tsananin butulci, sai dai talauci da tsananin rayuwa ya sa suka sauya zuwa mutanen ƙwarai, amma duk da haka ba'a rasa nono a ruga kuma baza'a taɓa taruwa a zama ɗaya.


NAILA
Sartaj ya na ɗaya daga cikin matasan da suke yawan shigowa Gidan Kaka, kuma yana daga cikin waɗanda suka dinga bata kariya, yawan shigowarsa ya haifar da shaƙuwa a tsakaninsu har yakan ci abinci Gidansu.

Da ƙwaɗayin asalin jinin Yankin Tudu da butulcinsu da bai gama barin jinin Sartaj ba su Ɗayyib su ka samu dama sukayi amfani da shi. Sai dai shure-shure baya hana mutuwa....✍🏻

Na gode da Addu'o'inku Allah Ya bar mu tare Ya kuma bar zumunci.
[7/28, 9:46 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥




NAFISA ALIYU SASAAL




Page 22

Kuɗi masu nauyi a hannu da rashin albarka wajen sauke buƙatu Jalal da kansa ya biya Sartaj, bayan ya siyar da yardar da amince dake tsakaninsa da su Naila.

Da tattacen kayan marmari Sartaj ya fara amfani. Ya na zaune suna hira da Naila har ta shanye. A kwana na biyu da yankakkun kayan marmari ma su kyan gani a ido ya yi amfani. A kwana na ukun da ya kasance na ƙarshe da abincin Gidan Kaka ya yi amfani.

SUFYAN; Sufyan bai ƙarasa warkewa ba suka tattara suka koma Birnin Abyad da sunan idan sun isa ya miƙawa Sumaya takardar ta kafin ya wuce Babban Birnin Abyad bakin aikinsa.

NAILA;
Labarin tafiyar Sufyan bai zama abin damuwa a gareta ba, domin abinda kake so shi kakeyiwa kishi.

A hankali ta fara ramewa ƙasusuwan jikinta suka fara bayyana kansu kamar ba ta cin abinci, kasalar rashin son yin Sallah a kan lokaci da ƙinyi azkhar na neman zamemata jiki.
A cikin kwana biyar tayi wani irin ramar da ya tsoratar da kowa.
Kaka bata wahalar da kanta wajen kai Nsila Asibiti ba, tunda tasan su wanene Iyayen Sufyan. Malamin da ya taimaka mata a waccen lokacin da Hindu ta ciyar da ita Tufa mai ɗauke da sihiri ta nufa.

Bai buƙaci a kawo Naila ba da kansa ya zo. Ya na ganinta ya tabbatarwa da Kaka abinda take zargi, sai dai sihirin da aka yiwa Naila ba irin nata bane, samun maganinsa abune mai matuƙar wahala domin a wajen wani Malami da ke gabashin Yankin Tudu za'a iya samu maganin karya Sihirin.

Cikin kuka Kaka take faɗin; "wanene ya zaɓi Duniya akan lahira?, wanene ya zaɓi shayar da marainiyar Allah sihiri irin wannan, Allah bamu da kowa sai Kai!"

Babu wanda bai tausayawa su Naila ba.

Cikin fusata matasan Yankin suka nufi da suka samu labari suka nufi Gidan Sarkin tsafin Yankin Tudu ya duba musu wanene ya shayar da Naila Sihiri?..

A take kuwa yana dubawa ya gano Sartaj ne.
Gangamin Matasan Yankin Tudu ne sukayiwa Gidansu Sartaj zobe, Sartaj ba shi da Uba sai Uwa itama ta fara tsufa.
Cikin alhini da fargaba take sanar da su yanzunan Sartaj ya ce mata zaije Fadar Sarki Hammam gurin Mai girma Jalal wai yana naimansa.

Bayaninta ya ƙara fusatar da Matasan tare da ƙara tabbatar da maganar Sarkin Tsafi, don haka suka koma Gidajensu kowa ya ɗebo makamai sai fadar Sarki Hammam.

A fito musu da Sartaj su yankemai hukunci dai-dai da abinda da ya aikata. Suke ta nanatawa bayan isarsu Harabar gidan Sarki Hammam.

Ihun su da maganganunsu ma su khaushi ne yasa Sarki Hammam umartar fadawansa su lallashesu su kuma sanar da su Sarkin Tsafin Yankin Tudu ba gaskiya ya faɗa ba, so yakeyi ya hanasu zaman lafiya tunda ya ci amanar Masarautarsu ta koresa shiyasa su ma yake so ya tunzura su. Kuma lallai ya na bada umarnin kar wanda ya taɓa lafiyar Sartaj idan ba haka ba zai fuskanci hukunci mai tsanani.

Duk da an sanar da Matasan Yankin Tudu wannan jawabi na Sarki Hammam basu motsa ba, har sai da Sarki Hammam ya fito da kanshi ya taushesu da kalamai ma su taushi tare da tabbatar musu da ƙarya Sarkin Tsafin Yankin Tudu yake yi, Sartaj da ya ke na hannun damar Naila tayaya zai ciyar da ita sihiri?

Ba don sun gamsu ba sai don bin umarnin Sarki Hammam wajibi ne a garesu suka tattara suka dawo Gida.

Da labarin abinda ya faru ya isa wajen Kaka ba tace komai ba sai kuka da takeyi tsoron mutane da rashin yarda da su na ƙara kamata.

Bayan zuwa Matasa wajen Sarki Tsafi, da kansa yazo duba Naila har ya faɗi wasu maganganun da Kaka tayi watsi da su nan take.

★washe gari Matasan Yankin suka yanke shawarar fita naimo Malamin da zai yiwa Naila magani a Yankin gabashin da ake ce yake ko kuma ya basu maganin su kawomata.

Kaka da tana dama da ta hanasu domin ko sun karɓo bazata iya yiwa Naila amfani da shi ba, saboda bata yarda da kowa ba.

Matasan Yankin mu su Goma sha uku, sun kwashe kwanaki huɗu a gabashin Yankin Tudu amma ba su samu Malamin ba, sai maganin da suka ƙarbo daga takwarorinsa.

Da hannu bibbiyu Kaka ta karɓi maganin su, tare da tarin godiya mai yawa. Sai dai tana karɓa ta zubashi a shara.

Sartaj ya fito yana rayuwarsa kamar kowa amma bayayin nisa da Gida a wayonsa kar wani ya yi mai wani mugun abu. Hanyar Gidan Kaka tuni ya zama haramiya a garesa.

Cikin watanni biyu Naila ta ƙanƙance ta tsotse ta dawo kamar ba ita ba idan Kaka ta kalleta sai ta fashe da Kuka tana cewa;
"Ba sai mun nemo mai warware mana sihiri ba, mai warware mana yana tare da mu, kuma In Shaa Allahu da ƙarfin mulkinsa sai kinga har jikokinki Naila"

idan Kaka ta faɗi haka Naila fuskarta da ta dawo ƴar ƙarama ta yamushe take kawarwa gefe tayi kukan da batasam iyakarsa ba.

Kaka bata gajiyawa wajen kaiwa Allah kukansu, dare da rana, Safiya da yammaci. Jinkirin samun sauƙin Naila bai sa Kaka ta karaya ba.

Taimako da ake basu ne ya farayin ƙasa, abincin ci ya fara gagararsu, yunwar da ya yi sauƙi a Yankin Tudu ya dawo sabo fil, amma duk da haka da zarar sun ci kasuwar Tukwanen Zinare Matasan Yankin zasu haɗowa Kaka kuɗi, haka ƴan uwan Mahaifin Naila, a wasu lokutan har da Kakanninta na wajen uwa.

Shawarar dawo da sana'ar Mahaifiyar Naila na ƙera kayan wasan Yara na lakar ƙasa Kaka ta yanke. Drivern da yake fita iyakar Yankin Tudu ta roƙi alfarma ya dinga kaita bakin tasha tana siyarwa idan tayi ciniki ta biyashi, tunda kullum sai yaje.

Kai tsaye ya nuna mata kyauta zai dinga kaita ya dawo da ita amma tana ganin barin Naila a gida ba zai zama matsala ba, mai zai hana ta dinga lulluɓeta suna tafiya tare? Da sauri Kaka ta amince domin itama fargabarta kenan yadda zata bar Naila ita kaɗai a Gida.

Ba ta naimi shawarar kowa ba, kwana biyu bayannan suka fara bin Driver zuwa Iyakar Yankin Tudu.

A gefe Naila take rakuɓewa, Kaka kuma matafiya take bi tana tallata musu su zo su siya kayan lakar da ta ƙera Fisabilillah. Cikin hukuncin Ubangiji, sai tausayin Kaka da tausayin yadda Naila ta koma ya sa mutane suka yi ta siya har da masu ba su kyautar kuɗi.

kullum ba sa dawowa Gida da rogawa sai ya ƙare. kuma Driver bai taɓa karɓar ko sisinsu ba.
Duk wannan wahalar da Kaka take sha haka take ƙara raba dare a zaune tana kaiwa Allah kuka, domin bata iya tsayuwa saboda shekaru da wahalar da take sha.

Ƴan uwan Mahaifin Naila sun kawo ƙorafin ta dinga barin Naila a Gida, amma ta nuna sam bata yarda ba, tunda suma ba zama sukeyi ba kowa nema yake fita, matansu kuma ba lallai su kula da ita ba.

A lokacin da suka cika sati shida da fara fita Iyakar Yankin Tudu, jirginsu Sufyan ya sauka. Ya dawo Yankin Tudu, Motocin Mahaifinsa ne suka je tarbarsa amma da yake gulmar halin da su Naila suke ciki ya je mai tun kafin ya iso, sai ya gwada zuwa inda suke zama, don kawai yayimusu izgilanci kafin ya wuce.

Lokacin da ya iso ɗan rumfar da suke zama Kaka tana can tallatawa matafiya kayansu Naila kuma tana rakuɓe da ruwan shan da Kaka ta bata a gefenta. Dariyarsa kawai Naila ta ji a kanta.
Kafin ya fara magana Cikin izgilanci;

"Naila korarriyar Ɗalibar da talauci ya hana iyayenta naima mata magani ta warke ta koma Makaranta, ba kina ganin zaluntarki mukayi ba, lokacin da muka yi miki gata muka kaiki Birnin Abyad muka baki makwanci. Amma saboda butulci don kawai ina karɓar kuɗin kitson da kike yi kika zaɓi tozartani, yanzu gashi Ni da ke waye yake ji a jikinsa, kalleki dan Allah."
Naila bata ɗago ba sai yawun da take ta tofawa ruwan hannuna kamar zautacciya.

Farar fuskarsa da ya ke matuƙar ji dashi ya shafa dai-dai satin Yankar da Ɗayyib ya yi masa da bai gama bajewa ba ya ƙara ce wa;
"Banso haukarki tasa bakya gane maganganuna ba, amma wannan yawun da kike tofarwa da adanawa kikayi wataƙila kya rage wannan yamutsewar da kikay..." Saukar ruwan har cikin bakinsa yasa ya kurma ihu haɗe da tsalle kamar ƙaramin Yaro kafin ka ce kwabo tuni Matafiya sun cika wajen, suna kallon Sufyan da yake ihun "Saliva! Saliva!!" Haɗe da waftar ruwan hannun mutane yana wanke fuskarsa da bakinsa.

Gudun abun kunya ba tare da bin ba'asi ba Fadawan Sarki Hammam suka jashi Mota. Abinda Sufyan bai sani ba maganar Naila ta koma kamar ta ƴan yara ba kowane yake Fuskantar ta ba, ko azabar ciwon ya tashi sai dai ta yi ta kuka bata iya bayani yadda za'a fuskanceta. Shiyasa Kaka bata wahalar da kanta wajen tambayar abinda ya faru ba ta koma wajen tallata kayanta, suma mutanen da suka taru kowa ya kama gabansa.

A hanyar su ta dawowa Naila tke yiwa Kaka kwatancen abinda ya faru. Dariyar da rabonta da yin irinsa har ta manta Kaka ta ƙyalƙyale da shi, har suka isa gida lokaci zuwa lokaci sai ta saki dariya.

A wannan dare Naila tasha azaba irin azabar da batasan yadda zata misaltashi ba, da taimakon addu'o'in da Kaka take tofamata barcin ya ɗauketa. Kafin wayewar gari ta ƙara fita hayyacinta, babu wanda hankalinsa bai tashi ba.

SUFYAN; har ya suka isa gida bai sanar da Fadawa abinda ya faru ba suma kuma ba su tambayesa ba sai sannu da suke ta jeromai.

Ya yi wanka ya fi sau biyar haka bakinsa ya wanke yafi a ƙirga. Da daddare bayan Sallar isha suka ɗauki hanyar Yankinsu Hindu Mahaifiyarsa shi da da ita.

A daren Malaman Hindu Suka turo jinnun da zasu matsawa Naila da zarar Sufyan ya zo da buƙatar komawarta tare da albishir ɗin samo Malamin gabashin da suke nema Su Kaka za su amince a mayar da aurensu.

Sufyan aka bawa maganin da Naila zata sha sihirin ya karye ya zura a aljihun bayan wandonsa.

Gaba ɗaya sai ya matsu gari ya yi haske domin a daren suka ƙara dawowa Yankin Tudu.

Da Safe ko wanka bai yi ba balle ya karyawa ya nufo Gidan Kaka da sunan duba jikin Naila kamar yadda suka tsara a daren bayan dawowarsu kafin zuwan su Ɗayyib. Babu wanda ya rakosa, fuskarsa a tsamke alamun dai ba'a son ransa zai zo ba.
Sallama ya yi Kaka da batasan shi ba ne ta basa izinin shigowa.

A tsakar gida ya samu Kaka ƙannen Mahaifin Naila su na ɗaki tare da ita kowa ya na tofamata duk addu'ar da ta zo bakinsa.

Kaka tana ganinsa ta dakata daga hura wutar da takeyi. Cikin ladabi kamar gaske ya tsugunna yana gaisheta. Kafin ya ɗago Kaka ta rarumo ƙaton iccen da ya ke ci da wuta ta nufesa. Sufyan ya na hangota ya yunƙura ya miƙe a guje, garin wannan yunƙurawa Maganin bayan aljihunsa da aka basa tun daren jiya baiyi wanka ba kuma bai cire kayan ba, dama kuma aljihun bawani zurfi ne da shi ba ya faɗo ƙasa ba tare da ya ankara ba.

Ƙur Kaka take kallon magananin, kafin ta yi Bismillah ta na yunƙurin kai hannunta.

Muryar mutum taji a bayanta.....✍🏻
[7/29, 10:01 PM] nafisaaliyusasaal: 🔥ZINARE🔥


NAFISA ALIYU SASAAL




Page 23


Da hanzari Kaka ta ɗauke ƙullin maganin ta wurgashi kwanon gefenta.

Yayyan Mahaifin Naila ne suke yunƙurin fitowa. Sallama su kayi mata, tare da alƙawarin kawo wani malamin ya ƙara duba jikin Naila. Su na fita Kaka ta sauke ajiyar zuciya, ba ta koma ɗakin ba tasa mayafi ta lalluɓe jikinta sai gidan Mallam.

Mallam
Juya maganin yake yi a hannunsa fuskarsa da yalwataccen murmushi ya ce "Tabbas! Allah ba Ya barci, sun biyota har gida sun shayar da ita sihiri, Allah kuma Ya ƙaddara su zasu ƙara biyota gida da makarin sihirin." Kaka da ke ta zare ido alamun bata fahimta ba domin ta ɗauka wani bala'in Sufyan ya ƙara kawo musu. Dalla-dalla Mallam ya yi mata bayani.
Ko
Cikin kuka Kaka takai goshinta ƙasa tana yiwa Allah godiya.

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, shayar da Naila maganin a Yankin Tudu zai dawo da hannun agogo baya, domin da zarar sun ga ta warke zasu ɓullo ta wata hanyar, mai zai hana tunda Naila tana da matsugunin haya a Birnin Abyad da kuɗinsa bai ƙareba tunda Bushra kuɗin shekaru uku ta biya kamar yadda Naila ta faɗa, Kaka ta bi can suyi jinyar tare.

Kaka wani irin kallo take yiwa Mallam fuskarta ɗauke da murmushi, kafin ta fashe da kuka domin ta rasa abun faɗa, bata taɓa kawo irin wannan shawarar a cikin zuciyarta ba balle ta samu mafitarsa a zahiri sai gashi Mallam ya haska mata hanya. Ta na godiya tana kuka.

Bayan tasha kuka sai ta ƙara naiman shawararsa akan yadda zasu tara kuɗin motar zuwa Birnin Abyad.

Kaka da murnar da ta danne a cikin zuciyarta ta dawo Gida, cikin jakar da take adana muhimman abubuwa ta anada maganin makarin sihirin jikin Naila.

Kaka har Yankinsu Mahaifiyar Naila ta yi tattaki ta kai mu su koken ance akwai malami a Birnin Abyad da zaiyiwa Naila magani ta warke kuma ita bata da halin da zasu iya tafiya tare, su taimaka mata da abinda suke da shi.

Kakan Naila mutum ne mai jama'a, don haka kafin tafiyar Kaka ya shiga layi-layi yana roƙon a taimaka mai za'a kai jikarsa ƴar gidan marigayiya Birnin Abyad neman magani kuma basu da hali a taimaka. Kafin rufuwar hour uku sai ga kuɗi masu yawa sun taru. Kakannin Naila ba su cire ko sisi ba suka bawa Kaka kuɗin tare da alƙawarin kowawa Naila ziyara kafin su wuce.

Kaka ɓoye kuɗin ta yi ta tunkarin yayyan Mahaifin Naila bayan ta dawo, suma ɗari bisa ɗari suka bayarda da goyon bayansu, saboda samun lafiyar Naila ta koma bakin karatunta shine burinsu domin daga gareta suke sa ran samun canji. Suma layi-layi suka bi suna shela.

A ranar dai ba'a samu waɗanda suka bayar da kuɗi ba, amma washe gari bayan sun ci Kasuwar Tukwanen Zinare suka dinga kawo kuɗi, kafin kace me kuɗin zuwa Birnin Abyad har da na cin abinci da extra sun haɗu.

Su ma Yayyen Mahaifin Naila tasu gudummawar suka kawo, tare da tattaunawa sirri da Kaka, akan idan Naila ta warke kar su dawo, su yi zamansu a can ta dinga kula da Naila, tunda ta iya riƙe Sufyan har da taimakon Mahaifansa da sana'ar kitsonta to suma zasu samu ingantacciyar rayuwa a chan, za su ƙara taro wasu kuɗin da zasu dinga cin abinci kafin jikin Naila ya ƙarasa warwarewa.

Kaka tana kuka tana godiya suma kukan suke yi suna nuna mata cigaban Naila shine burinsu.

Bayan komai ya lafa Kaka ta koma gidan Mallam domin yimasa