Jin shiru bai ɗago ba har na tsahon daƙiƙu yasa Ɗayyib dafashi, sharaf ya zube ƙasa daga zaunen dayake kamar Gini. Ɗayyib ne ya kinkimesa da sauri ya yi gaba, Kafin su je wajen mai magani rai ya yi halinsa.
Da labarin mutuwar Bashar da abinda ake zargi, ya riski Sarki Hammam bai ce komai ba banda hutun da yake ɓukata don haka ya Yanke shawarar da zarar anyi bakwai zai bar Yankin na wasu watanni kafin nashi shima lokacin ya yi.
Mutuwar Bashar ya sanya nutsuwa a zuƙatan mutanen Yankin don gani suke yi dama Bashar da Allah Ya tonawa Asirine kaɗai matsalar Yankinsu kuma gashi ya mutu, ba su yi tunanin ina magoya bayan Bashar ɗin suke ba, domin bai isa ya yi wannan ɓarnar shi kaɗai ba.
Tuni kowa ya saki jiki suka fara ƙera Tukwane ba ji ba gani don tunkarar Kasuwar Tukwanen Zinare da ƙafar dama, har lokacin Ɗayyib ba shi da Mataimaki, shi kaɗaine Shugaba.
NAILA;
Tun tana tambayar Kakarta game da su wanene ahalin su Abduh Dhahab har ta gaji ta haƙura.
Da kowa ya fara haɗa kayan sana'ar da zai shiga Kasuwar Tukwanen Zinare da shi, kayan wasan Yaran da mahaifiyarta take yi itama dama can ta iya, tafara ƙerawa Kakarta tana tayata. Gwanin sha'awa ta ƙera su Tukwane, randar ruwa, murhu harda talabijin duk na lakar ƙasa.
Mutanen Yankin da ƙafar Dama suka shiga kasuwar Tukwanen Zinare, domin babu wanda bai siyar da kayan sana'arsa ba.
*********************************************
Kwanaki sun miƙa, Shekaru sun shuɗe abubuwa sun sauya, yawanci daga sauƙi zuwa tsanani.
SUFYAN ƊA A WAJEN ƊAYYIB;
ya zama ƙosasshen Saurayi, kyakkyawan da yake taƙama da kyansa da kuma zamowar Mahaifinsa Shugaban Kasuwar Tukwanen ZINARE. ya yi niyyar ajiye burinsa na zuwa Babban Birni ya yi ilimi mai zurfi amma ranar da faɗa ya haɗasu da Kabeer Abokinsa ɗan Gidan ƙanin marigayi Dattijo Junaid ya ce masa;
"Taƙamar mai kakeyi? Babanka Shugaban Kasuwar Tukwanen Zinare ne? Hmm! Kasuwar Zinaren da Abduh Dhahab ne yasha wahalar kafasa, bayan ransa kuke cin arziƙi shi kakeyiwa taƙama? idan ban da ajali waye ma yasan Babanka balle kai? Ko lokacin da Sulaim yake raye, shi da ma Mahaifinsa ne ya ƙirƙiri Kasuwar Tukwanen Zinaren daga filin da ya gada a wajen Mahaifansa, kuma fika kyau da nasaba bai yi mana abinda kake yimana.
Kabari duk ranar da ku ka ƙirƙiri wani cigaba na ƙashin kanku a wannan Yanki ba na cin arziƙin wa su ba sai kazo ka ɗaga mana kai. Banza mai macacciyar zuciyar da bai san komai ba sai son ace masa ya na da kyau ɗan daudu kawai!"
waɗannan kalamai na Kabeer sun sosa ranshi tare da sashi kukan da zuciyarsa ce kawai bai haɗiya ba. tsanar Kabeer kuwa babu inda bai ratsaba a jikinsa.
A ranar ya fuskanci zamowar Mahaifinsa Shugaban Kasuwar Tukwanen Zinare kaɗai bai wadatar ba bai kuma zama wani abin kambabawa ko abin ayaba a wajen Mutanen Yankin ba, sai ma ƙara dawo musu da soyayyar Abduh Dhahab da Iyalinsa da ya yi a cikin zuƙatansu, shi kuma ba wannan ne burinsa ba. Burinsa kowa ya manta da Abduh Dhahab ne ya ƙirƙiri Kasuwar Tukwanen Zinare, su riƙi Mahaifinsa tamkar shi ya ƙirƙiri Kasuwar tun usul, su kuma girmamashi a matsayinsa na Ɗa Namiji ɗaya tilo a wajen Shugaban Kasuwarsu.
Ko da ya bawa Mahaifiyarsa labari, maimakon ta tausheshi sai ta ƙara zugeshi tare da ƙara tadamai tsimin burinta na tafiya Babban Birnin ya yi ilimi boko mai zurfi.
HINDU MAHAIFIYAR SUFYAN
Tabbacin amincewar Sufyan da ta samu ne, ya sa ta shiryawa tafiya Yankinsu wajen Malaman dubanta, don su duba mata Matar data dace Sufyan aura don tafiya da ita Babban Birni ta dinga yi masa Bauta kamar yadda ta tsara a baya.
NAILA
Itama ta zama kyakkyawar Budurwa kuma makitsiyar da mutanen Yankinta suke alfahari da ita.
Ba ta daina sana'ar ƙera kayan wasannin Yara na laka ba, sai dai ta daina fita da su Kasuwar Tukwanen Zinare saboda harajin da ake tsawwalawa ma su ƙananun sana'o'i irinta. A ɓangaren kitso tana samun ciniki don ba Makitsiyar da ta iya kowani kalar kitso kamarta. Har Daular Sarki Hammam take zuwa yiwa Iyalinsa kitso su biyata da kuɗi mai tsoka.
Duk tsayin wannan shekarun fuskar Sulaim na manne a cikin zuciyarta don har kuɗi ta biya ƙwararren mai zanen Yankin ya zanata ita da Sulaim a waje ɗaya, ta kai Gidan hoto aka wanke mata ƙaraminshi, da shi take yawo duk inda zata je.
**********************************************
Tsawwalawar Haraji ya kawo koma baya ga masu ƙananun Sana'o'i a Yankin Tudu harma da ma su manyan jari. Ga ɓullowar Gidan rawar daya zamewa Yankin musiba, a cikin Kasuwar.
Gidan rawa an ƙirƙirar shine ne a cikin Kasuwar Tukwanen Zinare, har da Masauƙin da aka kewaya da katakwaye da langa-langa kamar Ɗaki ga waɗanda dare ya yiwa, kuma kowa ya kasa tunkarar Ɗayyib da yake shugaban kasuwar su ji wanene ya kawo gidan rawa, su kuma shaida ba sa so, saboda dalilin haka Matasan Yankin sai su sha wahala su ƙera Tukwane da zarar sun siyar sai su wuce Gidan rawa da Kuɗin, haka ɓaki ma su shigowa, wa su ma suna shigowa ne kawai don suyi sharholiyarsu su koma ba don su sayi komai ba.
Wannan lamari yana ciwa Mutanen Yankin tuwo a ƙwarya amma tsoron rashin sanin wanda ya kafa Gidan rawan, tunda ga shi Shugaban Kasuwar Ɗayyib bai hana ba kuma bai kai ƙara wajen Sarki Hammam ba, wannan yasa suke Kwana da ɓakin ciki suna tashi da shi. Ƙewar Marigayi Abduh Dhahab da suka mayar abin zagi a baya na damun zuƙatansu, da maganganun Marigayi Dattijo Junaid.
Ƙara ta'azzarar komai ga shi kowa yakasa magana yasa Kabeer Abokin faɗan Sufyan yanƙurawa, don bazaiyiwu saboda tsoron mutuwa su kashe kan su da Kansu ba.
Faɗan da ya tada hazo ne ya ɓarke a tsakanin Kabeer da mai gadin gidan rawar. Dayake Kabeer matashine mai garin jiki da zafin nama sak Siffar mutanen Yankin Tudu kuma baya shaye-shaye ya sa yasamu damar yiwa Matashin da ba su ma san asalin ɗan ina bane saboda duhun fatarsa dukkan tsiya.
Ba bu wanda baiji daɗin abinda Kabeer ya aikata ba, don wasun su sun cire tsoro sun fito sunata maganganun sam bai dace ace an gurɓata Kasuwar Tukwane da Gidan rawa ba...
Kabeer ko a jikinsa zuciyarsa sakayau ko ba komai, yasamu ya amayar da abinda yake sukar zuciyarsa da na Mutanen Yankinsa. saɓanin Mahaifinsa da zuciyar ke cike da tsoron abinda zai biyo baya.
Tun Mahaifin Kabeer yana jin tsoron martanin da zai biyo bayan abinda ɗansa ya aikata har ya saki ransa ya cigaba da harkokinsa..
Bayan wata ɗaya, watan cin Kasuwar Tukwanen Zinare yaƙara zagayowa. A gaggauce Kabeer da Mahaifinsa suke kimtsa Tukwanen su don fita Kasuwa. Su na zuwa suka tarar da Rumfar su.....✍🏻
Su na zuwa su ka tarar da rumfarsu a rushe, yanayin shafewar wajen ma kamar ba'ataɓa kafa Rumfa ba. Kafin Mahaifin Kabeer ya dawo daga ɗimuwar da ya shiga, tuni Kabeer ya nufi kewayayyen rumfar da ke matsayin ofishin Ɗayyib.
Abin mamaki kamar wanda ake jira tun kafin ya kaiga inda ya nufa, matasa masu irin Shekarunsa suka rufe shi da duka ta ko ina.
Ihun naiman taimakon Kabeer ne ya fito da Ɗayyib haka Mahaifinsa daya ƙaraso a guje ya na haki.
Dakatawa su kayi da dukansa saboda ihun da Mahaifinsa ya kurma, kowannensu na numfarfashi saɓanin Kabeer daya goge jinin bakinsa ya yinƙura ya miƙe yana kallon inda Ɗayyib yake tsaye. Da zafin da yake ji a cikin zuciyarsa da gangar jikinsa ya fara magana;
" da a haka Abduh Dhahab da muka mayar abin aibatawa ya gina Kasuwar Tukwanen Zinare da bai kai ko ina ba zai mutu, ban nufo ofishinka don naci zarafinka a matsayinka na Shugaba garemu ba, sai don na kawo maka ƙorafin rushewa Mahaifina Rumfa da akayi. Menene laifina? Idan faɗan da nayi waccen watan ne, ina neman yafiyarka ka dawowa da Mahaifina Rumfarsa. Ni na haƙura da zuwa Kasuwar gaba ɗaya, don matsawar ina zuwa dole wata rana zan kasa jurewa nayi yunƙurin dakushe duk wani abinda zai kawowa Yankina koma baya ko akan waye kuw.." bai ƙarasa ba saukar naushin da yasa shi zubewa ƙasa warwas ya dakatar da shi daga Matasan da suka yi masa duka.
Da gudu Mahaifinss ya nufoshi yana kuka haɗe da kiran sunansa. Ɗayyib ma tsawa ya dakawa Matasan da su ka bar wajen.
Rige-rigen ɗaukar Kabeer kowa yake yi don kaishi Asibitin Mahaifinsa ya hana yace a barshi ya kaishi Gida yana da maganin da zai bashi.
Bayan su Kabeer sun je Gida, aka Turo kiran Mahaifinsa daga Fadar Sarki Hammam, bai wani jima ba ya dawo..
Mutanen Yankin;
Abinda ya faru da Kabeer yaƙara zama zanannen layin da kowa zai ji tsoron ƙetarawa, har ya yi azarɓaɓin faɗar gaskiyar a kan duk wani abu ba dai-dai ba da ake aikatawa. Jiki a sanyaye kowa yaci Kasuwarsa ta wannan rana.
KABEER;
Cikin tsananin Azaba Kabeer ya farka gabannin sallar magriba bayan ɗure-ɗuren maganin gargajiyan da suka yini suna yimai. Daga Mahaifinsa har Mahaifiyarsa hannunshi suka kamo suna rige-rigen yimai sannu da jiki.
Cikin taushin harshe Mahaifinsa ya fara magana;
" Kabeer lamarin Yankin nan sai addu'a faɗar gaskiya duk ƙanƙatarsa ya zama abin tsoro, amma naje Fadar Sarki Hammam na samesa da Shugaba Ɗayyib ya yi alƙawarin kawo ƙarshen gidan rawar da abokin kasuwancinsa ya ƙirƙiro kuma ya bani haƙuri, Kabeer ko da wata ɓaraka za ta kuma kunno kai, ba na so na ƙara jin bakinka idan ba so kakeyi su kashemin kai a banza ba na roƙeka!." ya ƙarasa faɗa da kuka mai sosa zuciya.
Kai Kabeer ya ɗagamai alamar ya ji.
Fara kiraye-kirayen Sallar Magriba ne yasa Mahaifinsa yin alola ya bar Gidan. Itama Mahaifiyarsa miƙewa tayi don yin alola kafin ta taimakamai shima ya yi. Ta na yunƙurin zuba ruwa a buta taji ana bubbuga Gidan a hankali. Fasa zuban ruwan tayi ta ɗauki mayafi ta lulluɓe jikinta.
Ta buɗe ƙofar, wanda ya ke bugawa bai jira izininta ba ya yi gaba ya barta da buɗaɗɗen baki, zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta nufo cikin Gidan ƙafarta na harɗewa.
Mayafin fuskarsa ya yaye.
A take fuskarshi da yake abin tsoro a wajen duk wani Mutumin Yankin Tudu a tun shekarun baya da'a yankewa Bashar harshe ya bayyana.
Da sauri ta dafe bakinta hawaye na ɓulɓulowa wani kan wani. Kai MALIK ya girgiza mata sannan ya ce;
" mai kike yiwa kuka?" Bata kaiga ba shi amsa ba Mahaifin Kabeer ya shigo don yakasa zaman Masallacin daya saba bayan sun idar saboda fargaba.
Shima ruɗu da tashin hankali ya shiga sai dai shi ya yi ƙarfin halin zube gwiwoyinsa dukka biyu a gaban Malik ya na roƙonshi;
" ka tausayamin, haƙiƙa ni bani da wata masaniya a kan yanke harshen ɗan uwana Junaid, haka Iyalina. Ka yi haƙuri ka barmin ɗana ya rayu da mu saboda shi ya rage a kusa da mu, na roƙeƙa" Kai Malik ya ɗaga sama yana kallon ƙofar Ɗakin da Kabeer yake tsaye yana Kallonsa ya ce;
" na zo ku bani Kabeer na tafi dashi, wata rana nayi alƙawarin dawo muku da shi a yanayin da zakuyi alfahari da shi, ba lallai naushin Sihirin da su ka yimai ya barshi ya rayu ba, kuma ko da ya rayu wata rana dole zasu rabaku da shi" yana ƙarasa faɗa ya matsa inda Kabeer yake a tsaye.
A kafaɗa ya saɓashi duk girmanshi, batare jiran amincewar su ba. fuskarshi ya ƙara lullɓewa ya nufi hanyar barin Gidan. Da ya juya baya, Kabeer hannayenshi duka biyu ya ɗaga a hankali ya na yiwa Iyayenshi sallama, tausayinsu na mamaye ilahirin zuciyarshi. Suma kuka suka saki bayan fitarsu suna ƙanƙame juna.
Ba su yi tunanin zasu iya runtsawa ba bayan Malik ya tafi da Kabeer. Domin Malik tamkar mala'ikan ɗaukar rai haka yake a wajen Mutanen Yankin Tudu.
Haka kawai suke jin nutsuwa a ransu tare da gasgata alƙawarin da Malik ya yi musu na zai dawo mu su da Kabeer wata rana a yanayin da zasuyi alfahari da shi.
★washe gari Mahaifin Kabeer ya fitar da labarin ɓacewar Ɗanshi, don ko mai zai faru bai isa ya ce Malik ne ya zo ya tafi da Kabeer ba, indai ba so yakeyi shima yabi Ɗan uwanshi Junaid ba.
Babu wanda bai ƙara shiga taitayinsa ba.
Ta ɓangaren Mutanen Yankin da basu da masaniya a kan komai, tsoron faɗar gaskiya da alwashin ɗauke ido akan komai suka ƙara sawa ransu.
Ta ɓangaren waɗanda suke da hannu tsumu-tsumu da waɗanda suka san abinda yake faruwa amma basu da damar faɗa suma sun shiga ruɗun wanene ya ɗauke Kabeer?....
Bayan kwanaki..
Kamar komai bai faru ba haka kowa ya cije ya cigaba da harkokin gabanshi, saboda ma su ƙarfin haline ma suke iya shiga yiwa Mahaifan Kabeer jaje, ragowar kuwa tsoron shiga Gidan ma sukeyi saboda gani sukeyi da zarar sun shiga jaje za'a biyo su Gida suma a sace su, ko a yanke musu harshe.
*****************************
A ɓangaren Hindu Mahaifiyar Sufyan taje Yankinsu, ta gana da Malaman tsibbunta har mutum Uku kuma amsar duk ɗaya ne;
"Naila Makitsiya a Yankin Tudu itace tsanin hawar matakin nasarar Sufyan. Duk tsananin duk abinda zai faru karta kuskura ta bari Aurenta ya suɓucewa Sufyan, saboda sana'ar kitsonta shine mafarin nasararsa, daganan kuma zai haifar da gagarumin abinda zai sa Sunanta da na Mijinta Ɗayyib har da na shi kanshi Sufyan ɗin ya zama abin faɗe ga kowa ba a iya Yankin Tudu kaɗai ba har ma da duniya baki ɗaya. Canji mai girma gaske zai zowa Yankinku a wannan lokacin, amma fa dukka hakan bazai tabbata ba har sai Sufyan ya auri Naila ya samu matsuguni Babban Birnin Abyad."
Kamar haɗin baki dukka amsa ɗaya ta samu daga bakin kowannen su sai dai sigar maganar da ya ke bambanta amma dukka ma'ana ɗaya yake bayarwa.
Mallakar matsuguni a Babban Birnin Abyad ko da na haya ne abune mai matuƙar tsadar da duk kuɗin da Ɗayyib yake taƙamar yana samu a Kasuwar Tukwanen Zinare bazai wadatar ba balle ta lallaɓashi ya amince.
Da farko bata taɓa kawowa Sufyan yin Karatu a Babban Birnin Abyad ba, sai hasashen garuruwan da suke kusa da shi, don ko a Yankinsu Sarki Hammam ne kawai yake iya zuwa can ya yi kwanaki amma ba ire-iren su masu iya arziƙin Yankin Tudu ba. Ta ina zata samu kuɗi masu yawan da zasu isa Sufyan ya tafi Makaranta har ya kama mu su matsuguni a Babban Birnin Abyad?...
Mahaifiyarta da kusan dukka ɗabi'unta ta gada ta tunkara da batun. Cikin ƙwarin gwiwa ta bata shawarar mai zai hana su tara dukka kadarorinsu waje ɗaya su kasa shi kashi uku su siyar da kashi biyu....
Da farko Hindu ƙin amincewa tayi da shawarar Mahaifiyarta ta har na tsahon Kwana uku. Tuno da Sufyan zai samu gagarumin ɗaukakar da sunansu zai zama abin faɗe ba a iya Yankin Tudu kaɗai ba har da duniya baki ɗaya ya sa ta amince.
Hindu bata dawo Yankin Tudu ba sai da kuɗi masu yawan gasken da ta zubo a Akwatin ƙarfe garƙame da mukulli.
A daren ranar ta tari Sufyan da zancen. Manyan idanuwansa farare ƙal ya zaro, tsabar ruɗewa hannuwansa har rawa sukeyi wajen kamo nata hannun.
"Ummi ki ka ce me? rayuwa a Babban Birnin Abyad? Kina nufin na kai matsayin da zan tafi can nayi Karatu Ummi ki ƙara faɗa dan Allah ko nine banji da kyau ba" Sufyan ya faɗa a ruɗe.
Dariya ruɗewarsa ya bata, don haka da ta ɗan dara, kafin ta zayyanomishi duk abinda ya faru da shawarar da Kakarshi ta bata har ta samu ta dawo da kuɗi ma su yawan gasken da zasu isheshi ya naimi Makaranta, su kama Gida har na tsahon shekaru biyu.
Lokacin da ta sa ɗan mukulli ta buɗe Akwatin kuɗin zabura Sufyan ya yi har sai da ya miƙe tsaye yana nuna kuɗin, duk girman kanshi da jinkanshi kasa jurewa ya yi yasa kuka yana ƙanƙameta, haɗe da faɗin;
"Ummi ba Naila ba kowa kike so na aura na amince, na gode Ummi Allah Ya sa na cikamiki burinki kamar yanda kika cikamin Burina" Bayanshi take shafawa ranta fari ƙal.
Bayan Ɗayyib ya dawo ya huta ta sanar dashi duk abinda ya faru bata ɓoyemai ba. Da farko ya ɗanyi jim da bata laifin da ba taje wajen Malaman tsibbu ba, da bata tono abinda yafi ƙarfinsu da zai kaita ga siyar da kadarorinsu na manyan kuɗaɗe irin wannan ba.
Ƙara marairaice murya tayi har sai da tasan yanda tayi ta yaudareshi ya yi alƙawarin nemo kuɗi ma su yawan gaske domin Sufyan ya ƙara a kai, su biya kuɗin hayar shekaru uku maimakon biyu, kafinnan sun san komai zai bayyana kanshi. Hindu zata iya cewa bata taɓa kwanan farin ciki irin na wannan ranar ba.
Shima Sufyan a ɓangarenshi yakice batun Naila ta taɓa abota da Sulaim ya yi ya amincewa rungumar Aurenta hannu bibbiyu kafin ɗaukakarshi ta bayyana.
Kwana biyu bayannan Hindu ta bayyana a Gidansu Naila da sunan ta zo kitso. Ba iya Naila da Kakartane kaɗai ne sukayi mamaki ba, har da maƙotansu da waɗanda suka ga gilmawarta.
A iya sanin da sukayiwa Iyalan Gidan MUSAA DHAHAB Magadan Sarautar Yankin Tudu kuma masu faɗa aji a Yankin Mutanene ma su girman kai, da kai Kansu inda Allah Bai kai su ba, kama daga kan asalin ƴan Gidan har zuwa kan baren da'aka auro, idan ka cire Marigayi Abduh Dhahab da ɗansa su kaɗai ne suka banbanta.
Zuwan Hindu Iyali ga Ɗayyib Uwa ga Sufyan da yake ƙafafa da jin yafi kowa, saboda Shugabancin Kasuwar Tukwanen Zinaren dayake hannun Mahaifinsa waɗanda ganta ta shiga gidansu Naila suka san dole da manufa ba wai don zuwa wajen Naila kitso kaɗai ba.
CIKIN GIDANSU NAILA;
Rasa wajen da zata bata ta zauna Kakar Naila ta yi, duk da akwai ƴar tsama a tsakaninsu tun shekarun baya, amma saboda Sashensu na Masarautar Yankin Tudu ya fi nasu gidan kyau nesa ba kusa ba da ababen more